Category:99 names of Allah

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Sunayen Allah

The 99 Names of God (أسماء الله الحسنى), ʾasmāʾu llāhi lḥusnā) also known as The 99 attributes of Allah, according to Islamic tradition, are the names of God revealed by the Creator(God) in the Qur'an.

The 99 Names of God (Allah) according to the tradition of Islam are:[1][2][3][4]

 1. Allah
 2. Ar Rahman (الرحمن) The All Merciful; The Compassionate (mai tausayi, jin ƙai, mai juyayialhini), The Beneficent (Mai rahama) The Infinitely (rashin iyaka, mai yawa) Good; Allah mai yalwar Rahama ne wacce ta game bayi gaba ɗayansu, Musulmi ko Kafiri, Me biyayya ko me saɓo.
 3. Ar Rahim(الرحيم) The Most Merciful; Mai jin ƙai, Allah ne mai madauwamiyar Rahama, wanda in ba a roƙe shi ba, sai yayi azaba. Wanda idan bala'i ya sami abin halitta sai ya bashi mafita.
 4. Al Malik (الملك) The King, The Sovereign Lord (mamallakin sarki ubangiji); Allah ne ma'abocin mulki isasshe wanda ba shi da buƙata a cikin halittarsa, kuma mulkin nasa ba ya karewa, kuma shi ne wanda makarfafar komai take ikonSa.
 5. Al Quddus (القدوس) The Most Holy (mai tsarki); Allah shi ne mai tsananin tsarkaka daga dukkan tawaya ko duk abin da mabarnata suke danganta masa.
 6. As Salam (السلام) The Source (mafari, majiya, asali, tushe, salsala, masomi) of Peace (zaman lafiya, sulhu, kwanciyar hankali, amana, aminci, salama) and Blessing; The Flawless (babu/rashin aibi, marasa aibu); Allah shi ne wanda Zatinsa da aikinSa suke kuɓuta daga dukkan tawaya, shi ne kuma me kuɓatar da bayi daga dukkan wata halaka, shi ne me tabbatar da aminci tsakanin bayinSa.
 7. Al Mu'min (المؤمن) The Guarantor; The Guardian (waliyi, mai kula da, majiɓinci, mutumin dake tsaran lafiyan wani mutum) of Faith (addini, amana/amanna, bangaskiya, tauhidi) The Faithful (amintacce, na Imani); Wanda ya amintar da bayinSa daga dukkanin abin tsoro, babu kwanciyar hankali sai daga Ubangiji, me gasgata kansa da kansa. Duk mai neman goyon baya a wajen Ubangiji to ya rinƙa yawaita karanta Ya Mu'minu!
 8. Al Muhaymin (المهيمن) The Guardian, the Preserver; Allah shi ne mahalicci mai gani ga duk aikin bayinSa.
 9. Al Aziz (العزيز) The Almighty, the Self Sufficient; Allah shi ne Buwayayye shi ne mai ƙarfin da babu wanda zai iya tankwara shi, shi ne wanda ya kadaita da ɗaukakarsa.
 10. Al Jabbaar (الجبار) The Powerful, the Irresistible; Allah shi ne wanda komai dole ne ya ƙasƙanta a gabansa. Maɗaukaki akan dukkan halittarSa. Shi ne mai karya ƙashin bayan masu taurin kai. Shi ne wanda iradarSa ta ratsa komai. Amma Shi kuma ba wata Irada da take iya ratsa Shi. Komai mutum zai yi sai in ya dace da abin da yake so, in bai dace ba shi ke nan yayi asara.
 11. Al Mutakabbir (المتكبر) The Tremendous; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya kadaita da girma da ɗaukaka, ba wani girma ban da nasa.
 12. Al Khaaliq (الخالق) The Creator; Allah shi ne mai samar da komai daga babu. Abin da babu shi sai ya samar da shi ba tare da yaga samfu ba a gurin wani.
 13. Al Baari (البارئ) The Maker; Allah Albari'u mai kagen halitta, wanda bai gani a gurin kowa ba. Shi ne wanda yake ba kowane abin halitta siffarsa. Tsawo ko gajarta, kauri ko sirintaka, a tsaye ko a kife, dunƙulalle ko miƙaƙƙe, mai motsi ko sandararre.
 14. Al Musawwir (المصور) The Fashioner of Forms; Allah Maɗaukaki shi ne mai kayatar da siffar ababen halitta. Shi ne wanda zai suranta abu kuma ya kayatar da shi.
 15. Al Ghaffaar (الغفار) The Ever Forgiving; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake sutura zunubai na bayinSa. Kuma yake shafesu da tuba.
 16. Al Qahhaar (القهار) The All Compelling Subduer; Allah Maɗaukaki shi ne mai rinjaye, wanda ba wanda zai iya jurewa ukubarsa. Duk wanda ya ɗorawa, bai isa yace yayi taurin kai ko yai jarunta ko dauriya akan abinda ya ɗora masa ba.
 17. Al Wahhaab(الوهاب) The Bestower; Allah Maɗaukaki shi ne mai maɗauwamiyar baiwa, Shi kullum bayarwa yake, baya hanawa. Sannan yana bawa wanda yake da buƙata abinda yake buƙata. Amma ba dan wani buri da Allah yake da shi ba, ba kuma dan musaya da za ayi masa ba, kawai shi bayarwa yake.
 18. Ar Razzaaq (الرزاق) The Ever Providing; Allah Maɗaukaki shi ne mai arzurtawa, kuma shi ne me halittar arzikin gaba ɗaya, Shi ne mai arzurta jiki da abinci, Shi ne kuma yake arzurta rayuka ko ruhi da sani na Allah Subhanahu Wata'ala.
 19. Al Fattaah(الفتاح) The Opener, the Victory Giver; Allah Maɗaukaki shi ne mai buɗe taskokin rahama ga halittarsa, kuma Shi ne wanda ya buɗe zukatan bayi muminai, da sani kuma ya buɗewa masu saɓo ƙofa ta gafara in sun nemi gafara zai gafarta musu.
 20. Al Alim (العليم) The All Knowing, the Omniscient; Masani wanda babu abin da yake ɓoye a gare shi, na nesa ko kusa. Shi ne wanda Ya san abin da ya kasance da abin da yake kasancewa da abin da ba zai kasance ba.
 21. Al Qaabid (القابض) The Restrainer, the Straightener; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake miƙa mulki hannun wanda yaso. Shi ne wanda yake karɓar rawuka yayin mutuwa, kuma shi yake tashinta gobe Alƙiyama.
 22. Al Baasit (الباسط) The Expander, the Munificent; Allah Maɗaukaki shi ne mai shimfiɗawa, wato wanda yake yalwata arziki ga wanda yaso daga cikin bayinSa.
 23. Al Khaafid (الخافض) The Abaser; Allah Maɗaukaki shi ne yake ƙasƙantar da wanda ya so. Musamman ma wanda yake da jin ƙai, mai alfahari, to sai ya yadda shi ba wani ba ne.
 24. Ar Raafi' (الرافع) The Exalter; Allah Maɗaukaki shi ne yake ɗaga darajar muminai ya basu rinjaye akan maƙiyansu, kuma shi ne yake ɗaga darajar wanda yaso ya kuma ɗaukaka shi duk duniya aso shi.
 25. Al Mu'izz (المعز) The Giver of Honor; Allah Maɗaukaki shi ne me buwayar da wanda ya bi shi, shi ne kuma yake bada mulki ga wanda ya so.
 26. Al Muzil (المذل) The Giver of Dishonor; Allah Maɗaukaki shi ne mai ƙasƙantarwa. Shi yake ƙasƙantar da maƙiyansa ta hanyar hanasu gane Ubangiji, kuma yake jifan waɗanda suka saɓe shi da ƙasƙanci da wulaƙanci.
 27. Al Sami' (السميع) The All Hearing; Allah Maɗaukaki shi ne mai riskar dukkan abin ji, sannan babu wani abu na ji da yake tsere masa. Jin roƙon wani ko tasbihin wani ko zikirin wani ba ya shagalar da shi ga barin jin kira ko zikiri ko tasbihin sauran bayinsa.
 28. Al Basir (البصير) The All Seeing; Allah Maɗaukaki shi ne yake Mahalicci, kuma yana ganin komai. Duka abin da suke cikin Sammai Maɗaukaka da abinda yake cikin Ƙasa da abinda yake tsakanin Sama da Kasa da abinda yake ƙarƙashin Ƙasa duk ba wanda yake ɓuya a gare shi.
 29. Al Hakam (الحكم) The Judge, the Arbitrator; Allah Maɗaukaki shi ne wanda hukuncinsa yake zarcewa kan komai, babu mai juyar da shi.
 30. Al 'Adl (العدل) The Utterly Just; Allah Maɗaukaki shi ne tsarkakakke ga barin zalunci ko danniya. Allah babu zalunci ko danniya a cikin lamarinSa.
 31. Al Latif (اللطيف) The Subtly Kind; Allah Maɗaukaki shi ne Masani da abin da dukkan abubuwan da suke ɓoye, kuma shi ne wanda yake tausasawa bayinSa ta inda ba su sani ba. Shi yake tsare musu abubuwan da zai taimakesu da mas'alarsu ta rayuwa ta inda basa zato, kuma basa tsammani, kuma Shi ne wanda yake ɓoye ƙarshen al'amura a cikin afkuwar kishiyoyinsu lokacin da suke afkuwa.
 32. Al Khabir (الخبير) The All Aware; Allah Maɗaukaki shi ne wanda babu wani abu da yake iya ɓoye masa.
 33. Al Halim (الحليم) The Forbearing, the Indulgent; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake yin gafara, bayan kuma ya suturta. Kuma ba ya gaggawar kamu ga wanda ta saɓe shi, haka kuma baya gaggawar ukuba, sannan kuma yana kau da kai ga dukkanin kuskure da ɗan Adam zai yi, kuma yana yiwa mai yin saɓo jinkiri har sai lokacin da zai tuba.
 34. Al 'Azim (العظيم) The Magnificent, the Infinite; Allah Maɗaukaki shi ne mai girman da babu wanda ya kai shi, bare ya fi shi girma, sannan hankali bai isa ya siffanta shi ba. Haka ma gani ko basira ta ƙwaƙwalwa bata isa ta faɗi hakikaninsa ba.
 35. Al Ghafur (الغفور) The All Forgiving; Allah Maɗaukaki mai yawan gafara ne, kuma mai karɓar hanzari ne.
 36. Ash Shakur (الشكور) The Grateful; Allah Maɗaukaki shi ne mai yiwa bayinsa muwafuka su godewa irin ni'imar da yayi musu, sannan kuma shi ne wanda yake sakamako akan 'yar ƙanƙanuwar ɗa'a, ya bada gwaggwaɓar daraja. Sannan kuma shi ne zaka yi ƙanƙanin aiki sai ya baka ni'imar da bata da iyaka.
 37. Al Ali (العلي) The Sublimely Exalted; Allah Maɗaukaki shi ne mai ɗaukaka daraja ta bayinsa. Shi ne Maɗaukaki a irin darajar da yake da ita, babu wani mai darajar da zai kai tasa.
 38. Al Kabir (الكبير) The Great; Allah Maɗaukaki shi ne mai girma a cikin girman nasa. Yafi gaban wata gaba wacce take ji ko gani ko shaka ko dadado ko shafa ko hankali su riske shi.
 39. Al Hafiz (الحفيظ) The Preserver; Allah Maɗaukaki shi ne mai kiyayewa, kuma mai sanin dukkan ayyukan bayi. Shi ne mai tantance dukkan ayyukan bayi, baya barin sa ya ɓata.
 40. Al Muqit (المقيت) The Nourisher; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake bawa halitta gaba ɗayanta abinci.
 41. Al Hasib (الحسيب) The Reckoner; Allah Maɗaukaki shi ne mai yiwa bayinsa hisabi akan dukkanin ayyukan da suke yi, babba da ƙarami.
 42. Al Jalil (الجليل) The Majestic; Allah Subhanahu wata'ala shi ne Maɗaukaki wanda yake da girma, ya ɗaukaka a bisa abin da bai dace da shi ba. Shi ne wanda yake cikakke a zatinsa da siffarsa da ayyukansa, babu tawaya a gare shi.
 43. Al Karim (الكريم) The Bountiful, the Generous; Allah Maɗaukaki shi ne mai yawan baiwa, me madauwamiyar kyautatawa.
 44. Ar Raqib (الرقيب) The Watchful; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake kiyaye ayyukan bayinsa gaba ɗaya, me rubuta aikin da ɗan Adam yayi kafin ya mutu da bayan ya mutu.
 45. Al Mujib (المجيب) The Responsive, the Answerer; Allah Maɗaukaki shi ne me amsawa wanda ya roƙe shi.
 46. Al Wasi' (الواسع) The Vast, the All Encompassing; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ma'anoni da sunansa da siffofinsa suke ƙunshe basu da iyaka.
 47. Al Hakim (الحكيم) The Wise; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake da adalci wajen ƙaddara abu da kuma gwada shi.
 48. Al Wadud (الودود) The Loving, the Kind One; Allah Maɗaukaki shi ne me tsananin ƙauna ga bayaninsa.
 49. Al Majid (المجيد) The All Glorious; Allah Maɗaukaki shi ne mai girma, wanda ya kaɗaita da maɗaukakiyar daraja, wadda take cikakkiya.
 50. Al Ba'ith (الباعث) The Raiser of the Dead; Allah Maɗaukaki shi ne me aiko Manzanni da hukunce-hukunce, shi ne me tashin tayuka bayan an yi bacci, shi ne mai tashin halitta bayan an mutu kuma ya yiwa kowa hisabi.
 51. Ash Shahid (الشهيد) The Witness; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake mahalicci wanda baya ɓuya ga barin wani abu, babu kuma wani abu da yake ɓoye masa a cikin mulkinsa.
 52. Al Haqq (الحق) The Truth, the Real; Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya cancanci a bauta masa, kuma tabbataccen da ba ya gushewa.
 53. Al Wakil (الوكيل) The Trustee, the Dependable; Allah Maɗaukaki shi ne me jiɓintar lamarin bayinsa gaba ɗaya. Shi ne wanda ake jiɓinta masa kowanne irin al'amari. Shi ya fi kowa ƙarfi, ya fi kowa sani, kuma ya fi kowa jin ƙai.
 54. Al Qawiyy (القوي) The Strong; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake da cikakkiyar ƙudura iko da kuma cikakkiyar daraja, shi ne mai rinjaye ba'a rinjayarsa, shi yake bada mafaka, shi kuma babu wanda ya isa ya ba Shi.
 55. Al Matin (المتين) The Firm, the Steadfast; Allah Maɗaukakin Sarki shi ne wanda ba abinda ya gagare shi a cikin mulkinsa gaba ɗaya. Sannan halittu gabaki ɗaya ba wanda yake da tasiri akan su in ban da Shi.
 56. Al Wali (الولي) The Protecting Friend, Patron, and Helper; Allah Maɗaukaki shi ne wanda yake jiɓintar lamarin bayinsa, ta hanyar kiyaye su da tattalinsu da kuma riritasu. Shi ne yake jiɓintar lamarin masoyansa ya dinga taimakonsu, kuma ya karya musu abokan gaba.
 57. Al Hamid (الحميد) The All Praiseworthy
 58. Al Muhsi (المحصي) The Accounter, the Numberer of All
 59. Al Mubdi (المبدئ) The Producer, Originator, and Initiator of all
 60. Al Mu'id (المعيد) The Reinstater Who Brings Back All
 61. Al Muhyi (المحيي) The Giver of Life
 62. Al Mumit (المميت) The Bringer of Death, the Destroyer
 63. Al Hayy (الحي) The Ever Living
 64. Al Qayyum (القيوم) The Self Subsisting Sustainer of All
 65. Al Waajid (الواجد) The Perceiver, the Finder, the Unfailing
 66. Al Maajid (الماجد) The Illustrious, the Magnificent
 67. Al Waahid (الواحد) The One, the All Inclusive, the Indivisible
 68. Al Ahad (الاحد) The Unity, The indivisible
 69. As Samad (الصمد) The Long, the Impregnable, the Everlasting
 70. Al Qaadir (القادر) The All Able
 71. Al Muqtadir (المقتدر) The All Determiner, the Dominant
 72. Al Muqaddim (المقدم) The Expediter, He who brings forward
 73. Al Mu'akhkhir (المؤخر) The Delayer, He who puts far away
 74. Al Awwal (الأول) The First
 75. Al Aakhir (الآخر) The Last
 76. Az Zaahir (الظاهر) The Manifest; the All Victorious
 77. Al Baatin (الباطن) The Hidden; the All Encompassing
 78. Al Waali (الوالي) The Patron
 79. Al Muta'al (المتعالي) The Self Exalted
 80. Al Barr (البر) The Most Kind and Righteous
 81. At Tawwaab (التواب) The Ever Returning, Ever Relenting
 82. Al Muntaqim (المنتقم) The Avenger
 83. Al 'Afuww (العفو) The Pardoner, the Effacer of Sins
 84. Ar Ra'uf (الرؤوف) The Compassionate, the All Pitying
 85. Malik al Mulk (مالك الملك) The Owner of All Sovereignty
 86. Dhu al Jalal wa al Ikram (ذو الجلال و الإكرام) The Lord of Majesty and Generosity
 87. Al Muqsit (المقسط) The Equitable, the Requiter
 88. Al Jaami' (الجامع) The Gatherer, the Unifier
 89. Al Ghani (الغني) The All Rich, the Independent
 90. Al Mughni (المغني) The Enricher, the Emancipator
 91. Al Mani' (المانع) The Withholder, the Shielder, the Defender
 92. Ad Dharr (الضآر) The Distresser
 93. An Nafi' (النافع) The Propitious, the Benefactor
 94. An Nur (النور) The Light
 95. Al Hadi (الهادي) The Guide
 96. Al Badi (البديع) Incomparable, the Originator
 97. Al Baaqi (الباقي) The Ever Enduring and Immutable
 98. Al Waarith (الوارث) The Heir, the Inheritor of All
 99. Ar Rashid (الرشيد) The Guide, Infallible Teacher, and Knower
 100. As Sabur (الصبور) The Patient, the Timeless

Allah is the personal name of God and Muslims worship God mostly by this name. The names refer to "characteristics" and "attributes" of God (Allah).

The English translation of names may have a slightly different meaning than the original Arabic word due to the words available in each language.


References/Links

 1. Saulat. "The Names and Attributes of Allah." whyislam.org. URL accessed on 19 February 2016.
 2. "The Ninety Nine Attributes of Allah." al-islam.org. URL accessed on 19 February 2016.
 3. Huda. "Names of Allah." About Religion. URL accessed on 19 February 2016.
 4. "The 99 names of Allah; the ‘Most Beautiful Names’." BBC GSCE Bitesize. URL accessed on 19 February 2016.

Subcategories

This category has only the following subcategory.

Pages in category "99 names of Allah"

The following 9 pages are in this category, out of 9 total.