Category:Adjectives

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Adjectives kalmomi ne masu ƙara bayani. Su na daɗa kwatanta Nouns da Pronouns. Shi rassansa uke ne manya:

 1. Qualitative adjectives
 2. Quantitative adjectives
 3. Distinctive adjectives

Sifa (Adjective) kalma ce da ake amfani da ita don a kara bayyana suna, watau sifa d'in a kullum k'ara bayani take. Wannan k'arin bayani na iya kasancewa don kyau ko muni ko inganci ko nak'asa da dai dalilai masu kama da wad'annan. Misali, idan muka d'auki 'Musa' wanda yake suna ne na yanka, muna iya k'ara bayani a kansa kamar haka:

 1. Musa bak'i ne. <> Musa is black.
 2. Musa siriri ne. <> Musa is skinny.
 3. Musa dogo ne. <> Musa is tall.
 4. Musa k'ak'k'arfa ne.
 5. Musa kyakkyawa ne. <> Musa is handsome.
 6. Musa mahaukaci ne. <> Musa is crazy.

Kenan, kalmomi irin su bak'i da siriri da dogo dak'ak'k'arfa da kyakkyawa da mahaukaci duk kalmomi ne na sifa. Domin sun kara bayyana sunan Musa.

Haka kuma, za mu iya cewa:

 1. Farar kaza <> A white chicken.
 2. Bak'ar akuya <> A black goat.
 3. Jar mota <> A red car.

Kalmomi irin su 'fara' da 'baka' da 'ja' duk kalmomi ne na sifa. Domin sun kara bayyana mana sunan kaza da akuya da mota. [1]

 1. Order of adjectives [2]

Pages in category "Adjectives"

The following 200 pages are in this category, out of 580 total.

(previous page) (next page)
(previous page) (next page)