Bible/1/JHN.1

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from Category:Bible/1/JHN.1)
Jump to: navigation, search

Contents

#: In the beginning was the Word, and the Word was with God, and the Word was God. <> Tun fara farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. = Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. = A cikin farko akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah, kuma Allah akwai Kalma.

#: The same was in the beginning with God. <> Yana nan tare da Allah tun fara farawa. = Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. = Ya kasance tare da Allah a cikin farkon.

#: All things were made by him; and without him was not any thing made that was made. <> Ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa; in ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. = Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. = Dukan abubuwa da aka sanya ta Shi, kuma wani abin da aka yi da aka yi ba tare da shi.

#: In him was life; and the life was the light of men. <> A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. = Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. = Life a gare Shi, kuma Life kuwa shi ne hasken mutane.

#: And the light shineth in darkness; and the darkness comprehended it not. <> Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba. = Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba. = Kuma Haske na haskakawa cikin duhu, da kuma duhu bai fahimta shi.

#: There was a man sent from God, whose name was John. <> Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. = Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. = Akwai wani mutum da Allah ya aiko, sunansa Yahaya.

#: The same came for a witness, to bear witness of the Light, that all men through him might believe. <> Ya zo a matsayin mai shaida domin yǎ ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. = Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. = Ya isa zama shaida a bayar da shaida game da Light, sabõda haka, duk yin ĩmãni da shi,.

#: He was not that Light, but was sent to bear witness of that Light. <> Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken. = Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken. = Ba shi ne hasken, amma ya kasance ya bayar da shaida game da Light.

#: That was the true Light, which lighteth every man that cometh into the world. <> Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya. = Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. = The gaskiya Light, wanda haskaka kowane mutum, yana zuwa a cikin wannan duniya.

#: He was in the world, and the world was made by him, and the world knew him not. <> Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba ta gane shi ba. = Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. = Ya kasance a duniya, da kuma duniya da aka yi, ta hanyar da shi, da kuma duniya ba ta san shi.

#: He came unto his own, and his own received him not. <> Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. = Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. = Ya tafi nasa, kuma nasa bai yarda da shi.

#: But as many as received him, to them gave he power to become the sons of God, even to them that believe on his name: <> Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ʼyaʼyan Allah—  = Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, = Amma duk da haka, wanda ya yi yarda da shi, waɗanda suka gaskata da sunansa,, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah.

#: Which were born, not of blood, nor of the will of the flesh, nor of the will of man, but of God. <> ʼyaʼyan da aka haifa ba bisa hanyar ʼyan adam, = wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah. = Wadannan suna haife, ba daga jini ba, ba daga nufin jiki, ko nufin mutum, amma daga wurin Allah.

#: And the Word was made flesh, and dwelt among us, (and we beheld his glory, the glory as of the only begotten of the Father,) full of grace and truth. <> Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya. = Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa. = Kuma kalmar ya zama jiki, kuma ya zauna a cikinmu, kuma mun ga daukakarsa, daukaka kamar na wani kawai Ɗansa, haifaffe daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

#: John bare witness of him, and cried, saying, This was he of whom I spake, He that cometh after me is preferred before me: for he was before me. <> Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ” = Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” = John yayi shaida game da shi, kuma ya ɗaga murya, yana cewa: "Wannan shi ne wanda na ce game da wanda: 'Shi da yake zuwa a bãyãna, An sanya gaba da ni, domin ya wanzu kafin ni. ' "

#: And of his fulness have all we received, and grace for grace. <> Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka. = Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. = Kuma daga falala tasa, mu duka sun samu, har alheri kan alheri.

#: For the law was given by Moses, but grace and truth came by Jesus Christ. <> Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi. = Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. = Domin Shari'a, da aka bai ko Musa, amma, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu.

#: No man hath seen God at any time; the only begotten Son, which is in the bosom of the Father, he hath declared him. <> Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi. = Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi. = Ba wanda kullum ga Allah; kawai Ɗansa, haifaffe shi, wanda ke a cikin Uba, shi da kansa ya bayyana shi.

#: And this is the record of John, when the Jews sent priests and Levites from Jerusalem to ask him, Who art thou? <> To, ga shaidar Yohanna saʼad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne. = Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. = Kuma wannan ita ce shaidar Yahaya, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su da shi, dõmin su tambaye shi, "Kai wanene?"

#: And he confessed, and denied not; but confessed, I am not the Christ. <> Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.” = Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” = Sai ya faɗi gaskiya shi kuma bai yi musu ba shi; da kuma abin da ya shaida ya: "Ba ni ne Almasihu ba."

#: And they asked him, What then? Art thou Elias? And he saith, I am not. Art thou that prophet? And he answered, No. <> Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Eliya?”Ya ce, “Aʼa, ni ba shi ba ne.”“Kai ne Annabin nan?”Ya amsa ya ce, “Aʼa.” = Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” = Kuma suka tambaye shi: "Sa'an nan abin da ku ke? Iliya ne kai?"Sai ya ce, "Ni ba." "Shin kun Annabi?"Sai ya amsa ya ce, "A'a."

#: Then said they unto him, Who art thou? that we may give an answer to them that sent us. What sayest thou of thyself? <> A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?” = Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?” = Saboda haka, Suka ce masa: "Kai wanene, domin mu sami amsar da wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?"

#: He said, I am the voice of one crying in the wilderness, Make straight the way of the Lord, as said the prophet Esaias. <> Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ” = Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.” = Ya ce, "Ni murya ce ta ihu a cikin hamada, 'Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,'Kamar yadda Annabi Ishaya ya faɗa. "

#: And they which were sent were of the Pharisees. <> To, waɗansu Farisiyawan da aka aika = Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su. = Kuma wasu daga waɗanda aka aiko su daga Farisiyawa.

#: And they asked him, and said unto him, Why baptizest thou then, if thou be not that Christ, nor Elias, neither that prophet? <> suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Eliya ba, ba kuma annabin nan ba?” = Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” = Kuma suka tambaye shi, ya ce masa, "To, don me kuke yi baftisma, idan ba ka da Almasihu, kuma ba Iliya, kuma ba Annabi?"

#: John answered them, saying, I baptize with water: but there standeth one among you, whom ye know not; <> Yohanna ya amsa, ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba. = Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, = Yahaya ya amsa musu da cewa: "Na yi baftisma da ruwa. Amma a cikinku tsaye daya, wanda ba ku sani ba.

#: He it is, who coming after me is preferred before me, whose shoe's latchet I am not worthy to unloose. <> Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.” = shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.” = A wannan ne wanda ya ke zuwa a bãyãna, wanda aka sanya gaba da ni, da madaurin na wanda ko takalmansa ma ban isa ga sassauta. "

#: These things were done in Bethabara beyond Jordan, where John was baptizing. <> Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma. = An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma. = Wadannan abubuwa ya faru a jikin Betanya, hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

#: The next day John seeth Jesus coming unto him, and saith, Behold the Lamb of God, which taketh away the sin of the world. <> Washegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya! = Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! = Kashegari, Yahaya ya tsinkayo ​​Yesu na nufo shi,, kuma sai ya ce: "Ga shi, Ɗan Rago na Allah. Sai ga, wanda ya ɗauke zunubin duniya.

#: This is he of whom I said, After me cometh a man which is preferred before me: for he was before me. <> Wannan shi ne wanda nake nufi saʼad da na ce, ‘Wani mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’ = Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ = Wannan shi ne wanda na ce game da wanda, 'Bayan da ni isa wani mutum, wanda aka sanya gaba da ni, domin ya wanzu kafin ni. '

#: And I knew him not: but that he should be made manifest to Israel, therefore am I come baptizing with water. <> Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Israʼila.” = Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” = Kuma ban san shi. Amma duk da haka shi ne domin wannan dalili da cewa na zo, nake baftisma da ruwa: don haka abin da ya iya bayyana a Isra'ila. "

#: And John bare record, saying, I saw the Spirit descending from heaven like a dove, and it abode upon him. <> Sai Yohanna ya ba da wannan shaida: “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa. = Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. = Kuma John miƙa shaida, yana cewa: "Gama na ga Ruhu na saukowa daga sama kamar kurciya; sai ya zauna a gare shi.

#: And I knew him not: but he that sent me to baptize with water, the same said unto me, Upon whom thou shalt see the Spirit descending, and remaining on him, the same is he which baptizeth with the Holy Ghost. <> Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ = Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ = Kuma ban san shi. Amma wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya ce mini: 'Ya kan wanda za ku ga Ruhu na saukowa da sauran a gare shi, wannan shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki. '

#: And I saw, and bare record that this is the Son of God. <> Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.” = Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.” = Sai na ga, Na kuma ba da shaida: cewa wannan daya ne Ɗan Allah. "

#: Again the next day after John stood, and two of his disciples; <> Washegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa. = Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. = Kashegari kuma, Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.

#: And looking upon Jesus as he walked, he saith, Behold the Lamb of God! <> Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!” = Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” = Kuma kamawa gaban Yesu na tafiya, ya ce, "Ga shi, Ɗan Rago na Allah. "

#: And the two disciples heard him speak, and they followed Jesus. <> Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. = Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. = Kuma almajirai biyu da aka sauraron shi magana. Kuma suka bi Yesu.

#: Then Jesus turned, and saw them following, and saith unto them, What seek ye? They said unto him, Rabbi, (which is to say, being interpreted, Master,) where dwellest thou? <> Da juyewa, sai Yesu ya ga suna binsa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?”Suka ce, “Rabbi,” (wato, Malam), “ina kake da zama?” = Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?” = Sai Yesu, juya a kusa da kuma ganin suna biye da shi, ya ce musu, "Me kake nema?"Kuma suka ce masa, "Ya Shugaba (wanda ke nufin a translation, Malam), ina kake zama?"

#: He saith unto them, Come and see. They came and saw where he dwelt, and abode with him that day: for it was about the tenth hour. <> Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.”Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen saʼa ta goma ce kuwa. = Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. = Ya ce musu, "Ku zo ku gani." Sai suka je suka ga inda yake da zama, kuma suka zauna tare da shi da cewa rana. Yanzu shi ne game da goma hour.

#: One of the two which heard John speak, and followed him, was Andrew, Simon Peter's brother. <> Andarawus ɗanʼuwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun da suka ji abin da Yohanna ya faɗa wanda kuma ya bi Yesu. = Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. = kuma Andrew, da ɗan'uwan Bitrus, yana daya daga cikin biyun nan da suka ji game da shi, daga Yahaya suka kuma bi shi.

#: He first findeth his own brother Simon, and saith unto him, We have found the Messias, which is, being interpreted, the Christ. <> Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗanʼuwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi). = Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe. = Da farko, ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus,, sai ya ce masa, "Mun sami Almasihu,," (wanda aka fassara a matsayin Almasihu).

#: And he brought him to Jesus. And when Jesus beheld him, he said, Thou art Simon the son of Jona: thou shalt be called Cephas, which is by interpretation, A stone. <> Ya kuma kawo shi wurin Yesu.Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan = Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus. = Sai ya kai shi wurin Yesu. Kuma Yesu, kallo a gare shi, ya ce: "Wato kai ne Saminu, dan Jonah. Za a kira Kefas," (wanda aka fassara a matsayin Peter).

#: The day following Jesus would go forth into Galilee, and findeth Philip, and saith unto him, Follow me. <> Washegari Yesu ya yanke shawara yǎ tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.” = Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” = Kashegari, da ya so ya tafi zuwa ƙasar Galili, kuma ya sami Filibus. Sai Yesu ya ce masa, "Bi ni."

#: Now Philip was of Bethsaida, the city of Andrew and Peter. <> Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne. = Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. = Yanzu Filibus kuwa mutumin Betsaida, garin su Andarawas da Bitrus.

#: Philip findeth Nathanael, and saith unto him, We have found him, of whom Moses in the law, and the prophets, did write, Jesus of Nazareth, the son of Joseph. <> Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa-Yesu Banazare, ɗan Yusuf.” = Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” = Filibus ya sami Nata'ala, sai ya ce masa, "Mun sami wanda Musa ya rubuta game da wanda a cikin Attaura da Annabawa: Yesu, ɗan Yusufu, daga Nazarat. "

#: And Nathanael said unto him, Can there any good thing come out of Nazareth? Philip saith unto him, Come and see. <> Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?”Filibus ya ce, “Zo ka gani.” = Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” = Nata'ala ya ce masa, "A iya samun wani m zama daga Nazarat?"Sai Filibus ya ce masa, "Ku zo ku gani."

#: Jesus saw Nathanael coming to him, and saith of him, Behold an Israelite indeed, in whom is no guile! <> Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Israʼila na gaske wanda ba shi da haʼinci.” = Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” = Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi,, sai ya ce game da shi, "Ga shi, Ba'isra'ile a wanda da gaske ba shi da ha'inci. "

#: Nathanael saith unto him, Whence knowest thou me? Jesus answered and said unto him, Before that Philip called thee, when thou wast under the fig tree, I saw thee. <> Natanayel ya yi tambaya, ya ce, “A ina ka san ni?”Yesu ya amsa, ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yǎ kira ka.” = Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” = Nata'ala ya ce masa, "Daga ina ka san ni?"Yesu ya amsa, ya ce masa, "Kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin itacen ɓaure, Na gan ka."

#: Nathanael answered and saith unto him, Rabbi, thou art the Son of God; thou art the King of Israel. <> Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Israʼila.” = Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” = Nata'ala ya amsa masa ya ce: "Ya Shugaba, kai Ɗan Allah. Kai Sarkin Isra'ila. "

#: Jesus answered and said unto him, Because I said unto thee, I saw thee under the fig tree, believest thou? thou shalt see greater things than these. <> Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.” = Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.” = Yesu ya amsa, ya ce masa: "Domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure, ku yi ĩmãni. Al'amuran da suka fi wadannan, ku gani. "

#: And he saith unto him, Verily, verily, I say unto you, Hereafter ye shall see heaven open, and the angels of God ascending and descending upon the Son of man. <> Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, malaʼikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.” = Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.” = Sai ya ce masa, "Amin, Amin, Ina gaya maka, za ku ga sama ta dāre, da malã'iku Allah suna hawa da sauka a kan Ɗan Mutum. "