Category:Nouns

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Suna ko Isimi: Kalma ce da ake amfani da ita wajen ambaton mutane da dabbobi da wurare da abubuwa. Misali, Ibrahim, rago, Kaduna, moda(cup) da sauran wasu.

Ire-iren Suna (Types of nouns):

 1. Suna na yanka (proper noun).
  Misali, Adamu, Hadiza
 2. Suna na gama-gari(common noun).
  Misali, malami, dalibi, yaro, yarinya
 3. Suna tattarau (collective noun).
  Misali, garke, ayari, rinji
 4. Suna na zahiri (concrete noun).
  Misali, kujera, teburi
 5. Suna na Badini (Category:Abstract_Nouns).
  Misali, rad'ad'i, talauci, ilimi
 6. Sunan abubuwan da za a iya kirgawa (countable noun).
  Misali, takalmi, dutse, fensiri
 7. Sunan abubuwan da ba a iya kirgawa (uncountable noun).
  Misali, ruwa, toka, kasa, gishiri.

Source: https://www.facebook.com/permalink.php?story_fbid=1688103588073382&id=1685995344950873

Duk wata kalma da a ka yi anfani da ita don ambaton wani mutuum, wata dabba, wani wuri, ko wani abu, ita a ke nufi da ‘noun.’

Misali:

 1. Sunanayen mutane: Muhammad, Adam, Maryam, Isa, John, da dai sauransu.
 2. Sunanayen dabbobi: Lion (zaki), elephant(giwa), goat (akuya), snake (maciji), da dai sauransu
 3. Sunayen wurare: Kano, Niger, market (kasuwa), hospital (asibiti), da dai sauransu
 4. Sunayen ababuwa: tree (bishiya), spoon (cokali), charcoal (gawayi), pen (alkalami/biro), da dai sauransu.

Irin wadannan misalai kusan ba su da iyaka.

Source: https://www.bakandamiya.com/page/turanci-a-saukake/tab/blog/content_id/15

External Links

 1. http://aflang.linguistics.ucla.edu/Hausa/Hausa_online_grammar/Noun%20modifiers/genitives.html

Pages in category "Nouns"

The following 200 pages are in this category, out of 6,118 total.

(previous page) (next page)

1

4

A

(previous page) (next page)