Category:Proper nouns

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

This category is for proper nouns. A proper noun is the name of a particular person, place or thing. It starts with capital letters. This is a subcategory of Category:Nouns.

Proper Noun (Suna na hakika)

Hakikanin sunan mutum, wani dabba, wani wuri ko wani abu, shi a ke kira ‘proper noun.’ Misali:

  1. Sunan Mutum: Musa, Hajara, Barau, Mary, da dai sauransu
  2. Sunan dabba: Idan a ka sanya ma wata dabba suna na musamman a na kiranta dashi, wannan sunan ya zama ‘proper noun. Misali ka sanya wa dokinka/ki ko kyanwarka/ki suna ‘Maidaji’ ko ‘Binta’ da makamantansu.
  3. Sunan wuri: Niger, Bauchi, Kankia, Jalingo, ABU Zaria, da makamantansu
  4. Sunan ababuwa: Moringa (zogale), Joy (sabulun wanka na Joy), Mahogany (iccen kuka) da makamantansu

Karin bayani: Ya na da kyau mu sani a ka’idan Turanci, dole ne a fara rubuta proper noun da ‘capital letter’ wato babba harafi, misali: Muhammad, Kazaure, Gombe da dai sauransu. Ya nuna Kenan, ko a cikin karatu mutuum ya iske kalma ta fara da babban harafi, in dai ba a san ma’anarta ba, ta na iya yiwuwa sunnan hakika ne na wani abu ne ko wani gari ko wani Mutum.

Source: https://www.bakandamiya.com/page/turanci-a-saukake/tab/blog/content_id/16