Larabci

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Arabic

https://ha.wikipedia.org/wiki/Larabci

Flag of the Arab League.svg

Mutanen dake da asali da harshen larabci, a cikin harshen Hausa ana kiransu larabawa mutum daya kuma ana kiran sa balarabe hakanan kuma mace ana kiran ta balarabiya

Arabic ko kuma muce larabci a harshen Hausa , Yare ne wanda ya fito daga iyalin yaruruka na AfroAsiya Kuma yare ne wanda ake amfani dashi a yanki gabas ta tsakiya da kuma wasu sassa na kudancin da gabashin nahiyar Afrika dama wasu bangarori na nahiyar Turai .

Yawan mutanen da suke amfani da harshen larabci ya kai Miliyan Dari Biyu Da Chasa'in [290m]

MUHIMMANCIN LARABCI A WAJEN MUSULMAI

Akasarin musulmai masu wani harshe daban suna amfani da harshen larabci sabo da shine harshen da ya zama na addinin musulunci . Da harshen larabci ne aka saukar da Alkur'ani, kuma da harshen larabci ne aka rubuta manya manyan litattafai na addinin musulunci .

Bayan litattafan addinin musulunci kuma, akwai dimbin litattafai da aka rubuta su a cikin harshen na larabci.

KASASHEN DA AKE AMFANI DA LARABCI A MATSAYIN HARSHEN KASA