Quran/10/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Suratu Yunus, Aya Ta 1-4 (Kashi Na 318)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kuma kumshe a cikin ayar da muka saurara. Kamar kuma yadda sunan wannan shiri yake nunawa na Hannunka mai sanda muna kokari ne kawai na nunawa junanmu hanya madaidaiciya da yi wa junanmu nasihar da matukar muka yi aiki da ita ko shakka babbu za mu samu tsira da dacewa a rayuwarmu ta yau da kullum ta dukan bangarori kama da bangaren addini da akida ,zamantakewa,al'adu,siyasa da diplaumasiya da sauransu.Kuma babu wani jagora da abin da ya dace mu yi koyi da aiki da umarninsa ko haninsa kamar kur'ani da hadisan ma'asumai kamar yadda ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya yi mana wasiya da yin riko da Alkur'ani littafin Allah da kuma iyalan gidan manzo da ba su rabuwa har abada da fatar Allah ya ba mu karfin riko da wadannan abubuwa guda biyu amin.

Yanzu kuma za mu fara shirin a wannan sura ta Yunus da sauraren aya ta farko da ta biyu na wannan surar kamar:

الر تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْحَكِيمِ{1} أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَباً أَنْ أَوْحَيْنَا إِلَى رَجُلٍ مِّنْهُمْ أَنْ أَنذِرِ النَّاسَ وَبَشِّرِ الَّذِينَ آمَنُواْ أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِندَ رَبِّهِمْ قَالَ الْكَافِرُونَ إِنَّ هَـذَا لَسَاحِرٌ مُّبِينٌ{2}

-ALIF LAM RA ( Allah shi ne mafi sani abin da yake nufi da wadannan harafai ) .Wadannan ayoyi Littafi ne ( watau Alkur'ani mai hikima . - Shin ya zama abin mamaki ga mutane cewar Mun yi wahayi zuwa ga wani mutum daga cikinsu , cewa : " Ka gargadi mutane , kuma ka yi wa wadanda suka ba da gaskiya albishir cewa suna da babban matsayi wurin Ubangijinsu " ? Sai kafirai suka ce : Hakika wannan ba shakka gwanin mai sihiri ne . "

Ita wannan sura ta Yunus da ke dauke da sunan daya daga cikin bayun Allah salihu Annabin Allah (AS) da kuma ta farad a haruffan da babu wani day a san ma'anar haka sai masani gwani .Sai kuma aya ta biyu da ta ke bayyana yadda wasu daga cikin mutane ke mamakin yadda aka yi wa wani mutum daga cikinsu wahayi cewa ya gargadi mutane da yai masu nasiha kan aikata aikin Alheri da aiki na gari har ila yau ya yi wa wadanda suka bad a gaskiya albishir cewa suna da babban matsayi wurin Ubangijinsu Allah madaukakin sarki ,Amma duk da haka sai kafirai makiya suka bayyana ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarakaka a matsayin mai sihiri.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko; akwai wasu surori da ke farawa da haruffan da babu wanda ya san ma'anarsu sai Allah.

Na biyu : Hassada ke hana mutum amincewa da gaskiya da wani matsayi da wani bawon Allah ya samu matukar ya san ya fi shi.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta uku da hudu a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka:

إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُدَبِّرُ الأَمْرَ مَا مِن شَفِيعٍ إِلاَّ مِن بَعْدِ إِذْنِهِ ذَلِكُمُ اللّهُ رَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ أَفَلاَ تَذَكَّرُونَ{3} إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعاً وَعْدَ اللّهِ حَقّاً إِنَّهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ لِيَجْزِيَ الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ بِالْقِسْطِ وَالَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمْ شَرَابٌ مِّنْ حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُواْ يَكْفُرُونَ{4}

- Hakika Ubangijinku shi ne Allah wanda ya halicci sammai da kassai cikin ( gwargwadon ) kwana shida , sannan ya yi istiwa'i a kan Al'arshi , yana tsara al'amura ( kamar yadda ya so ) .Babu wani mai ceto sai da izininsa . Wannan shi ne Allah Ubangijinku . To sai ku bauta masa .Me ya sa ba kwa wa'azantuwa ? - Zuwa gare shi ne makomarku take gaba daya . alkawarin Allah gaskiya ne , hakika shi ne yake farar da halitta sannan ya mai da ita ( ranar lahira ) don ya sake wa wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na gari da adalci , wadanda suka kafirce kuma suna da abin sha mai kuna da kuma azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna kafircewa ( da shi ).

Babu wani mahalicci sai Shi Allah Ubangijin talikai wanda ya halicci samma da kasasi cikin kwanaki shidda ,sannan ya yi istiwa'i a kan al'arshinsa kuma kamar yadda ya so ne yake tsara al'amura,babu wani mai ceto said a izininsa.Wannan shi ne Allah Ubangijinku saboda haka bauta masa ya zama wajibi mu yi da kuma ya zama wajibi mu wa'azantu. Har ila yau a gare shi ne makomarmu take gaba daya .Alkawarin Allah gaskiya ne ,Hakika shi ne yake farar da hallta sannan ya maid a ita zuwa ranar tashin kiyama ,Mai adalci da kuma yi wa wadanda suka bada gaskiya adalci da basu sakamakon aikin da suka yi da kuma azabtar da kafirai kan kafircinsu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko : babu wani mahalicci sai Allah wanda ya halicci komi da kowa.

Na biyu: adalcin Allah ne sakawa koma daidai da aikin da ya aikata.

Dukan wadanda suka yi rabkanuwa da sha'afa da rungumar rayuwar wannan duniya da samun nutsu a cikin hakika su ne mutane dab a sa tsoron Allah da gamuwa da Shi a ranar tashin kiyama,to wannan makomarsu ta munana da kuma makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa.

Suratu Yunus, Aya Ta 5-10 (Kashi Na 319)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kuma kumshe a cikin ayar da muka saurara.

Za mu fara da sauraren ayoyi na 5 da 6 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

هُوَ الَّذِي جَعَلَ الشَّمْسَ ضِيَاء وَالْقَمَرَ نُوراً وَقَدَّرَهُ مَنَازِلَ لِتَعْلَمُواْ عَدَدَ السِّنِينَ وَالْحِسَابَ مَا خَلَقَ اللّهُ ذَلِكَ إِلاَّ بِالْحَقِّ يُفَصِّلُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{5} إِنَّ فِي اخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ اللّهُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ لآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَّقُونَ{6}

- Shi ne wanda ya sanya muku rana ta zamo mai kyalli da kuma wata ya zamo mai haske , ya kuma sanya shi mai masaukaidon ku san yawan shekaru da kuma lissafi ( na lokatai ) . Allah bai halicci wannan ba sai a kan gaskiya . yana ayoyi ne ga mutanen da za su gane . - Gome da sassabawar dare da rana da kuma abubuwan da Allah ya halitta cikin sammai da kassai hakika akwai ayoyi ga mutanen da suke tsoron Allah .

Allah mai hikima Shi ne ya halicci rana da wata da sanya su masu haske da kyalli da hakan zai bam u damar lissafin raneku da shekara da watannio da sauran lokuta kuma ya halicce su kan gaskiya da zama ayoyi ga mutane domin su bada gaskiya da imani kan haka. Har ila yau bug da kari sassabawar dare da rana da kuma abubuwan da Allah ya halitta cikin sammai da kassai hakika akwai ayoyi ga mutanen da suke tsoron Alla. Amma wadanda suka kasance suna kafircewa ni'imarsa bas u san da haka ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko; rana da wata wata babbar ni'ima ce daga Allah madaukakin sarki.

Na biyu : da babu rana da wata lissafi zai yi mana wuya.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 7 da 8 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka;

إَنَّ الَّذِينَ لاَ يَرْجُونَ لِقَاءنَا وَرَضُواْ بِالْحَياةِ الدُّنْيَا وَاطْمَأَنُّواْ بِهَا وَالَّذِينَ هُمْ عَنْ آيَاتِنَا غَافِلُونَ{7} أُوْلَـئِكَ مَأْوَاهُمُ النُّارُ بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ{8}

- Hakika wadanda ba sa tsoron gamuwa da Mu , suka kuma yarda da rayuwar duniya , kuma suka nutsu da ita, da kuma wadanda suka rafkana daga ayoyinmu . - Wadannan makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa Dukan wadanda suka yi rabkanuwa da sha'afa da rungumar rayuwar wannan duniya da samun nutsu a cikin hakika su ne mutane da ba sa tsoron Allah da gamuwa da Shi a ranar tashin kiyama,to wannan makomarsu ta munana da kuma makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:babban kuskure ne yin dogaro da wannan duniya.

Na biyu: makomar masu yin dogaro da wannan duniya da nutsuwa da ita wutar jahannama ce.

Sai a saurari aya ta 9 da 10 a cikin suratul Yunus (AS) kamar haka:

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ يَهْدِيهِمْ رَبُّهُمْ بِإِيمَانِهِمْ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الأَنْهَارُ فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ{9} دَعْوَاهُمْ فِيهَا سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلاَمٌ وَآخِرُ دَعْوَاهُمْ أَنِ الْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ{10}

9- Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na gari , Ubangijinsu zai shirye su saboda imaninsu: koramu suna gudana ta karkashinsu cikin aljannoni na mani'ima . 10- Addu'arsu a cikinta " Muna tsarkake ka ya Allah" , gaisuwarsu kuma a cikinta " Salamun " , ( watau aminci ) karshen addu'asu kuma ita ce : " Godiya ga Allah Ubangijin talikai .

Mutanen da suka bada gaskiya da kuma su ka yi aiki na gari hakika Ubangijinsu zai shirye su saboda imaninsu, a cikin aljannar da za su shiga cikinta akawai koramu na gudana a karkashinta da kuma ni'imomi masu yawan gaske da aka yi masu tanadi. Wadanda suka shiga cikin wannan aljanna babu wata addu'a a suke yi sai cewa; Muna tsarkake ka ya Allah, gaisuwarsu kuma a cikinta salamun watau aminci karshen adduasu kuma it ace godiya ga Allah Ubangijin talikai.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko; Sakamakon Aljanna shi ne yafi dacewa ga wadanda suka aikata alheri.

Na biyu; babbar dacewa ita ce ta shiga gidan aljanna.

Suratu Yunus, Aya Ta 11-14 (Kashi Na 320)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kuma kumshe a cikin ayar da muka saurara.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 11 da 12 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka:

وَلَوْ يُعَجِّلُ اللّهُ لِلنَّاسِ الشَّرَّ اسْتِعْجَالَهُم بِالْخَيْرِ لَقُضِيَ إِلَيْهِمْ أَجَلُهُمْ فَنَذَرُ الَّذِينَ لاَ يَرْجُونَ لِقَاءنَا فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ{11} وَإِذَا مَسَّ الإِنسَانَ الضُّرُّ دَعَانَا لِجَنبِهِ أَوْ قَاعِداً أَوْ قَآئِماً فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُ ضُرَّهُ مَرَّ كَأَن لَّمْ يَدْعُنَا إِلَى ضُرٍّ مَّسَّهُ كَذَلِكَ زُيِّنَ لِلْمُسْرِفِينَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{12}

-Da dai Allah zai gaggauta (karbar addu'ar ) mutane ta sharri kamar ta alhairi to da karshen rayuwarsu ya zo . Sai dai Mukan bar wadanda ba sa tsoron haduwa da Mu cikin tsaurin kansu su yi ta faganniya.

- Idan kuma wani matsi ya sami mutum, sai ya roke Mu, ya kishingide ne ko a zaune ko kuma a tsaye . To lokacin da Muka yaye masa cutarsa sai ya ci gaba (da halinsa) kamar bai taba rokon Mu game da wata cutar da ta shafe shi ba . Kamarhaka ne aka kawata wa mabarnata abin da suka kasance suna aikatawa.

Rahamar Allah ce ta jinkirta karbar Addu'ar kafirai da mushrikai sabanin yadda yak e gaggauta karbar Addu'ar alheri ta mutanan kirki da suka aikata ayyukan alheri to da karshen rayuwarsu ta zo.Sai dai Allah yana barin wadanda ba sa tsoron haduwa da Allah dam u cikin tsaurin kansu su yi ta faganniya.Irin wadannan mutane idan kuma wani matsi da hadari ya same su sai su koma roken Allah ta kowa ne hali da yanayi day a samu kansa amma a duk lokacin da aka yaye masu wannan matsala da yake fama da ita sai ya sha'afa da koma aikinsa day a saba tamkar bai taba shiga cikin matsala ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:idan mutum ya shiga matsala yafi tunawa da Mahalicci.

Na biyu : mutum mai yawan mantuwa da sha'afa ne.

Dukan wadanda suka yi rabkanuwa da sha'afa da rungumar rayuwar wannan duniya da samun nutsu a cikin hakika su ne mutane dab a sa tsoron Allah da gamuwa da Shi a ranar tashin kiyama,to wannan makomarsu ta munana da kuma makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 13 da ta 14 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَاءتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ وَمَا كَانُواْ لِيُؤْمِنُواْ كَذَلِكَ نَجْزِي الْقَوْمَ الْمُجْرِمِينَ{13} ثُمَّ جَعَلْنَاكُمْ خَلاَئِفَ فِي الأَرْضِ مِن بَعْدِهِم لِنَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ{14}

-Hakika kuma Mun hallakar da al'ummun wadansu zamuna da suka gabace ku ,lokacin da suka yi zalunci,kuma manzanninsu suka zo masu da ayoyi mabayyana, sai ba su zamana sun bada gaskiya ba.Kamar haka ne muke saka wa mutane masu laifi.

-Sannan bayansu Muka mayar da ku madadinsu a bayan kasa don Mu ga me za mu aikata.

Duk da cewa Allah madaukakin sarki na bawa dan adam da ya aikata leifi wata damar da jinkirta hallakar da shi a wannan duniya sai dai fushin Allah kan al'umma da jama'ar da yawancinta suka aikata zalunci da sabo a doran kasa yana banbanta tsakanin al'ummomi wani lokaci zai hallaka wannan al'umma. Kuma wani hamzari ba gudu ba tushen wannan zalunci da sabo shi ne kafirci da rashin imani da addini da hakan ke zama tushe da musabbabin al'umma ta bijirewa bin hanya madaidaiciya da annabawa ke kiransu da ringuma da binta sai dai kawai su ci gaba da yin riko da aikata leifi da sabo.

To sauran al'ummomin da za su zo gabaninsu da rayuwa bayansu dole su yi tarihin abin da ya wakana da labarin al'ummomin da suka gabace su ya zame masu darasi a rayuwarsu kuma su kwan da sanin cewa matukar suka rungumi munanan ayyukan mutanan da suka gabace su to ko shakka babu za su yi karo da fushi da azabar Allah kamar yadda ta samu mutanan da suka gabace su. Allah ya kiyashe mu amin

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa akalla guda uku kamar haka:

Na farko: aikata sabo da zalunci na shinfidawa da gina ramin hallaka amma ga wadanda ba su da wata dama da fata ko bil-bidin imani da neman gyara abin day a wakana da tuba kan ayyukan da suka aikata.

Na biyu: makomar kowa ce al'umma yana hannunta kuma niya da aikata ayyukan alheri ko lala shi ne zai kasance sakamako da makomarsu ta alheri ko lala.

Na uku: idan muka yi sa'ar hukuma da wani mulki ko mukami ya shiga hannunmu mu kwan da sanin cewa; wata jarabawa ce daga Allah domin mu dukanmu a gurin Allah daya muke babu sarki babu talaka babu mai kudi babu matsiyaci ko mace ko namiji face kowa aikinsa ke fushe shi da niyarsa ta gari.

Suratu Yunus, Aya Ta 15-18 (Kashi Na 321)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kuma kumshe a cikin ayar da muka saurara.

Da fatar Allah ya sa mu dace yanzu kuma za mu saurari aya ta 15 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

وَإِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ قَالَ الَّذِينَ لاَ يَرْجُونَ لِقَاءنَا ائْتِ بِقُرْآنٍ غَيْرِ هَـذَا أَوْ بَدِّلْهُ قُلْ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أُبَدِّلَهُ مِن تِلْقَاء نَفْسِي إِنْ أَتَّبِعُ إِلاَّ مَا يُوحَى إِلَيَّ إِنِّي أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ{15}

Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai wadanda ba sa tsoron haduwa da Mu su ce: ka zo da wani alkur'anin ba wannan ba,ko kuma ka sake shi. Ka ce da su Bai dace da ni ba in sake shi ni da kaina .Ni ba abin da nake bi sai abin da kawai aka yo mini wahayinsa. Hakika ni dai ina tsoron azabar rana mai girma idan na sabi Ubangijina.

Wannan aya tana bayyana mana irin makirci da yaudarar Mushrikai da masu bautawa guma da a kullum ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa yake kiransu zuwa ga addininin Musulunci kuma a maimakon su tuba da rungumar gaskiya da daina yin yaudara da kaucewa hanya sai suka bukaci ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da gabatar masa da munanan bukatunsu cewa ya canja ayoyin da ke hana su bautawa guma dama shafe su daga cikin Kur'ani ko kuma ya zo masu da wani Kur'ani ba wannan ba Kur'anin da a cikinsa babu ayoyi makamantan wannan to ta haka ne za su yi imani da ma'aikin Allah da abun day a zo masu da shi .Alhali burin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa shiryar da al'umma ba wai tara jama'a tare da shi da neman amincewarsu ba kuma shi ma'aikin Allah ba ya amincewa da bukatun mutane na karya da son rai da ya kaucewa shirya domin kawai ya tara yawansu .Da yawansu da karamcinsu duk daya ne a wajensa.

A cikin wannan aya za mu iya ilmatuwa da abubu biyu.

Na farko babu wani hatta shi kansa ma'aikin Allah da ke da hakkin canja wata aya daga cikin ayoyin kur'ani ko wani littafi da aka sabko daga sama kuma dukan Annabawa da Manzonni sun a biyayya da mika wuya ne ga wahayin da Allah ya yi masu.

Na biyu: Tushe shi ne abin da Allah yake fada yawan mabiya da magoya baya ba shi da tasiri wajen canjawa ko soke wani abu na tushen addini.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 16 da 17 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

قُل لَّوْ شَاء اللّهُ مَا تَلَوْتُهُ عَلَيْكُمْ وَلاَ أَدْرَاكُم بِهِ فَقَدْ لَبِثْتُ فِيكُمْ عُمُراً مِّن قَبْلِهِ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{16} فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الْمُجْرِمُونَ{17}

-Ka ce da su: Da Allah Ya so da ban karanta muku shi ba,kuma da ban fi ku sanin sa ba . hakika na zauna cikinku shekaru masu yawa tun gabaninsa. Me ya sa ne kwa hankalta?

-Ai ba wanda ya fi zalunci irin wanda ya kirkira wa Allah karya ko kuma ya Karyata ayoyinsa.Hakika su dai masu laifi ba sa su rabauta ba.

Wadannan ayoyi ci gaban bawa mushrika da kafirai da suka bukaci ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da suka bukaci ya canja ayoyin kur'ani da cewa; wannan ma'aiki ya yi shekaru arba'in yana rayuwa tare da ku,idan wannan kur'ani shi ne ya rubuta shi karkashin irin tunaninsa to da kuwa an gani a cikin wadannan shekaru ya furta wani abu da bakinsa da ke bayani kan tunaninsa kuma kar ku manta cewa babu wani da ma'aikin Allah ya yi karatu a gurinsa da daukan darasi balantana a ce Kur'ani ya samo tushe ne daga irin abubuwan da ya koya ko aka ilmantar da shi saboda haka duk wani da yake son ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya canja wannan Kur'ani ko ya soke wasu ayoyi da ke cikinsa, a hakikanin gaskiya yana karyata ayoyin Allah ne kawai da kulla yaki da Allah kuma wannan babban zalunci ne ga Allah ,Ga Alkur'ani da kuma ga Ma'aikinsa.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu yawa amma za mu iya takaituwa da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Litttafan da Allah Ya Sabko da ya hada da Kur'ani Wahayi ne daga Allah ba wai tunani kagowa ta Annabawa ko wata koyarwa ta wasu.

Na biyu; babban zalunci shi ne zalunci na al'adu da canja hakikanin abubuwa da suka shafi addini da akida.

To madallah a yanzu kuma za mu saurari aya ta 18 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

Suna kuma bauta wa wani ba Allah ba ,abin da zai cutar da su ba kuma zai amfana musu ba ,suna kuma cewa; Wadannan su ne macetanmu a wurin Allah. Ka ce da su: Shin yanzu za ku ba Allah labarin abin da bai sani ba ne a cikin sammai ko kuma a cikin kasai ? Tsaraki ya tabbata a gare Shi Ya kuma daukaka daga abin da suke tara Shi da shi.

Mushrikai da ke bautawa gumaka suna yin haka ne ba don tsoran su azabtar da su ko aiko masu da bala'I jin tsoran haka sai su bota masu ko kuma za su samu wani alheri gwadayin haka sai su botama gomaka a'a babu daya daga cikin dalilai makamantan haka amma suna fakewa da dalilin cewa suna bautawa gumaka ne a matsayin wani shimge ko jagora a tsakaninsu da Allah to wannan dalili nasu ba karbabbe ba ne. Domin wannan matsayi ne da su suka bawa Gumaka Ba Allah ya ba su wannan matsayi ba kuma bai amince da aiki makamancin wannan ba. Kuma yana da kyau su fahimci cewa akwai bambanci tsakanin neman falala da alhurmar manzonni da waliyan Allah da neman Shafa'arsu da kuma mummunan aikinsu na bautawa Gumaka kuma su bar yin kiyasi. Saboda na farko su manzonni da waliyan Allah ba duwatsu da sassaken itatuwa ba ne da su da rai. A'a sunada rai da rayuwa tare da Allah a duniyar Barzahu.

Na biyu : Allah da kansa ya fifita su a kan mutane kuma ya bukaci mutane da su rungume su da sanin madaidaiciyar hanya ta Allah ta hanyarsu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: masu bautawa gomaka da yin Shirka suna ganin gumaka a matsayin mai sadarwa tsakaninsu da Allah alhali Allah bai bawa gumaka wannan matsayi ba.

Na biyu: Babu wani ko wani abu da zai zama kishiyar Allah kuma babu wani da za a ba shi wannan matsayi na Shafa'a matukar ba Allah da kansa ya ba shi wannan matsayi .

To masu saurare a nan ne zan dasa aya da fatar Allah ya raba mu da duk wani abu mai kama da shurka ya kuma tabbatar da mu kan imani na hakika da hanya madaidaiciya ta Annabawa da waliyan Allah amin. Kafin mako mai zuwa ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 19-23 (Kashi Na 322)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kumshe a cikin ayar da muka saurare.

To masu saurare za fara cunduma a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda gadangadan ta hanyar sauraren aya 19 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَمَا كَانَ النَّاسُ إِلاَّ أُمَّةً وَاحِدَةً فَاخْتَلَفُواْ وَلَوْلاَ كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ فِيمَا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ{19}

A da can mutane al'umma daya ne a kan addini daya,to sai suka sassaba. Da ba don wata kalma da ta gabata daga Ubangijinka ba, to da an yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassabawa a kai.

Allah madaukakin sarki ya halin bil adama baki daya tare da fitira ta tauhidi wato kadaita Allah saboda haka farko al'umma da rayuwa tad an adam a doran kasa al'umma daya ce amma bayan wani lokaci da makircin shaidan wani wani bangare na al'umma ya fara yin shirka da hakan ya taimaka wajen rabuwar al'umma zuwa gida biyu.Bangare na farko mai kadaita Allah da bauta yayinda na biyun bangaren yake yin shirka ma'ana hada wanin Allah da Allah wajen bauta. Amma Allah cikinm hikimarsa shi ne ya bawa bil Adama wannan dama ta zabar hanyar da ya ga ta dace da shi. Kuma kan haka ya kebe wani lokaci da dama ga wadanada suka kaucewa hanya da aikata sabo da banna a doran kasa su aikata abin da suka ga dama da isasshen lokaci na yin tuba ko ci gaba da sabo. Kuma idan ba don wannan sunnar ta Allah ba , da a cikin wannan duniya ya maidawa da kafirai mummunan aikinsu da kawo karshen wannan bambanci tsakanin mumunai da kafirai.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farkonsu; matsayi da daukakar mutun tana tattare da wannan matsayi na zabi da Allah ya ba shi kuma shi kansa ya yi imani ko a'a babu matsi da tilasta masa da aka yi ko ya yi imani ko ya kafirce ya rage a gare shi zabar abin da yaga dama ko ya aikata alheri da zai amfane shi duniya da lahira ko kuma ya aikata mummuna da ganin sakamakon mumunan aikinsa duniya da lahira ya rage a gare shi.

Na biyu kuma : Shi sabani,bambance-banbance a cikin akida ko a cikin aikiwani abu ne da yake tattare da rayuwar dan adam da ya yi daidai da yanayinsa a wannan duniya.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 20 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَيَقُولُونَ لَوْلاَ أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ فَقُلْ إِنَّمَا الْغَيْبُ لِلّهِ فَانْتَظِرُواْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ{20}

20- Suna kuma cewa: Don me ba a saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ba ? To ka ce da su Sanin gaibu na Allah ne kawai,sai ku saurara,hakika ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.

Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa kamar sauran takwarorinsa Annabawa da Manzonnin Allah (AS) yanada mu'ujiza kuma babbar mu'ujizarsa shi ne kur'ani mai girma da Mushrikai baki dayansu suka gagara kawo ko da aya guda da ta yi kama da ta Kur'ani. Amma da ke su mushrikai a kullum suna neman wani abu da za su fake da shi a kowa ce rana suna gabatar da shawarar kawo wata sabuwar mu'ujiza da bukatar ma'aikin Allah day a kawo wani abu da suke so day a yi dai da bukatarsu.

Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya amsa masu da cewa; ita mu'ujiza tana hannun Allah madaukakin sarki kuma a duk lokacin da Allah ya ga dama yana nuna mu'ujizarsa da kudurarsa kuma ku abin da kuke bukata ba komi ba ne face neman fakewa. Kuma dole mu fahimci cewa sau tari bukatun mushrikai ya sabawa hankali day a kamata kamar yadda muka fahimci haka a ayoyin da suka gabata sun bukaci ma'aikin Allah annabin rahama (SWA) da ya zo masu da wani sabon Kur'ani ba wannan ba a wani bangaren kuwa suka bukaci ma'aikin day a tashi zuwa sama tamkar wani tsuntsu ko ya gina wata fada ta zinariya.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farkonsu:Tushe da manufar Kafirci da shirka ba shi ne rusa mu'ujiza da duk wani dalili ba sai dai kawai jayayya da bijirewa gaskiya.

Na biyu; Mu sani cewa mu'ujiza tana hannun Allah ne kuma Allah na aiko da mu'ujizarsa ne lokacin da yaga dama bawai bin bukata da son ran mutane ba.

Sai aya ta 21 a cikin suratul Yunus:

وَإِذَا أَذَقْنَا النَّاسَ رَحْمَةً مِّن بَعْدِ ضَرَّاء مَسَّتْهُمْ إِذَا لَهُم مَّكْرٌ فِي آيَاتِنَا قُلِ اللّهُ أَسْرَعُ مَكْراً إِنَّ رُسُلَنَا يَكْتُبُونَ مَا تَمْكُرُونَ{21}

21 Idan kuma muka dandana wa mutane dadi bayan wahala ta same su,sai gas u suna kulla makirci ga ayoyinmu. Ka ce da su: Allah shi ya fi gaggawar sakayya ga makirci.Hakika manzanninmu suna rubuta abin da kuke kullawa.

Ya zo a cikin tarihi cewa; birnin Makka ya fuskanci matsalar fari da karamcin ruwan sama amma saboda albarkacin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan fgidansa ya sabkar da ruwan sama da ni'imarsa da kubutar da su daga wannan bala'I na rashin ruwan sama da fari. Amma da yake duk yadda ka yi da Jaki sai ya ci kara sai mushrikai suka fara cewa; ai an gumakan da suke bautawa ne suka yi ruwan saman ko saboda sun e aka yi wannan ruwan. Ganin haka sai Allah madaukakin sarki mai komi da kowa ya sabkar da wannan aya da ke yi masu kashedi da cewa idan ku ma'abuta fahimtar gaskiya ne to ku sani wannan ruwan sama mu'ijiza ce daga Allah.Amma don jayayya da neman boye gaskiya da bakar kiyayya, wannan lutufi na Allah kuma danganta shi da gomakan da kuke bautawa da nuna sun fi ma'aikin Allah matsayi da daukaka a gurin Allah. To dole ku sani cewa; mala'ikun Allah da sauran mala'ikunsa day a ke aiko su zuwa ga mutane suna rubuta dukan ayyukan kuma Mushrikai sai su shiryawa bada amsa kan abubuwan da suke rayawa a ranar tashin kiyama. Sai dai wani hamzari ba gudu ba a wannan duniya ma Allah madaukakin sarki yana bas u amsa da maida masu makirci da yaudarsu kuma bas u da wani iko da karfin kaucewa kaddarar Allah.

A Cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko : Mutane na amfanuwa da ni'imomin Allah amma da dama daga cikinmu a maimakon gode masa suna kokarin kafircewa da neman yin wata dubara da wayo na banza.

Na biyu; duk wata azaba da azabar da dan adam ke fuskanta suna samo asali ne da kafircewa Allah da kokarin nuna wa ni'imar Allah wata dubara ta yaudara.

Da fatar Allah ya kiyashe mu da wannan mummunan aiki to yanzu kuma za mu saurari aya ta 22 zuwa 23 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

هُوَ الَّذِي يُسَيِّرُكُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ حَتَّى إِذَا كُنتُمْ فِي الْفُلْكِ وَجَرَيْنَ بِهِم بِرِيحٍ طَيِّبَةٍ وَفَرِحُواْ بِهَا جَاءتْهَا رِيحٌ عَاصِفٌ وَجَاءهُمُ الْمَوْجُ مِن كُلِّ مَكَانٍ وَظَنُّواْ أَنَّهُمْ أُحِيطَ بِهِمْ دَعَوُاْ اللّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ لَئِنْ أَنجَيْتَنَا مِنْ هَـذِهِ لَنَكُونَنِّ مِنَ الشَّاكِرِينَ{22} فَلَمَّا أَنجَاهُمْ إِذَا هُمْ يَبْغُونَ فِي الأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّمَا بَغْيُكُمْ عَلَى أَنفُسِكُم مَّتَاعَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ثُمَّ إِلَينَا مَرْجِعُكُمْ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{23}

- Shi ne wanda yake tafi da ku a tudu da cikin kogi ,har dai lokacin da kuka shiga cikin jiragen ruwa,jiragen kuwa suka yi gudu da su tare da iska mai dadi,suka kuma yi farin ciki da su jiragen sai kuma iska mai karfi ta zo musu ta kowane wuri, suka kuma tabbatar cewa dais u rika rokon Allah suna masu tsarkake addini gare shi suna cewa;wallahi idan ka tserar dam u daga wannan, lallai za mu zamo cikin masu godiya.

- To lokacin da ya tserar da su sai ga su suna barna a bayan kasa ba a kan wata madogara ba .Ya ku mutane,hakika sakamako barnarku a kanku kawai yake,wannan jin dadin rayuwar duniya ne ,sannan daga karshe zuwa gare Mu,ne makomarku take,sannan Mu ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.

A farkon wannan shiri mun bayyana cewa; Allah ya halicci kowa a cikin tafarki na tauhidi ita ma wannan aya tana cewa ne ;suma masu yaudara suna sanya irin wannan riga ta fitira da shagaltar dad an adam amma a kowane irin yanayi da rikici dad an adam ya fada ba ya yanke kauna da kuma bay a yin dogaro da kowa da sarkafa da shi idan ya kai wannan matsayi ya tabbatar da fidirarsa ta yin dogaro da Allah cikin ikhlasi zai rika ambaton Allah ya kubutar da shi daga wannan bala'I day a fada .Misali duk mutuman day a samu kansa a cikin hadari ko da kafiri ne kamar ya fuskanci nucewa a cikin teku sai rika neman Allah ya kubutar da shi kuma a daidai wannan lokaci ba ya yin dogaro da kowa sai Allah. Sai dai kashe dan adam nada saurin mantuwa da gafala duk da cewa a rayuwar wannan duniya a takaice take bay a la'akari da rungumar fiyayyar hanya ta kadaita Allah da aikata ayyukan alheri da za su kubutar da mu a kotun ranar kiyama da ba a boye komi a wannan kotun.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko: abubuwa na dabi'a na kara ruruta jiji da kai da girman kan dan adam a dabra guda fitira ta Allah na tada shi daga barci da fadakar da shi daga gafalarsa.

Na biyu;mu sani yin imani na wani gajeran lokaci mai wucewa ba shi da wani amfani, shi imani dole ya zama dauwamamme da kasancewa tare dam u a kullum ko a cikin ni'ima da wadata ko da kuma a cikin kunci da wahala.

Na uku; yawancin mutane ba mu yin godiya da lutifi da ni'imar Allah a mai makon mu yi godiya sai mu kafirce masa.

Da fatar Allah ya sanya mu daga cikin bayunsa masu yawan gode masa amin. A madain wadda ta hada mana sauti malama Julayi ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa:wassalam…

Suratu Yunus, Aya Ta 24-27 (Kashi Na 323)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kumshe a cikin ayar da muka saurare.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 24 a cikin wannan sura ta yunus kama haka

إِنَّمَا مَثَلُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاء أَنزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الأَرْضِ مِمَّا يَأْكُلُ النَّاسُ وَالأَنْعَامُ حَتَّىَ إِذَا أَخَذَتِ الأَرْضُ زُخْرُفَهَا وَازَّيَّنَتْ وَظَنَّ أَهْلُهَا أَنَّهُمْ قَادِرُونَ عَلَيْهَا أَتَاهَا أَمْرُنَا لَيْلاً أَوْ نَهَاراً فَجَعَلْنَاهَا حَصِيداً كَأَن لَّمْ تَغْنَ بِالأَمْسِ كَذَلِكَ نُفَصِّلُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ{24}

Hakika dai misalin rayuwar duniya kamar ruwa ne da muka saukar da shi daga sama,to sai shukokin da suke kan kasa suka cudanya da shi daga abin da mutane da dabbobi suke ci,har lokacin da kasa ta kawata da shi ta kuma yi ado ,masu ita kuma suka sakankance cewa su masu ikon cin amfaninta ne , sai kaddararmu ta zo mata cikin dare ko rana,sai muka mayar da ita a girbe kamar dadai bat a rayu ba a jiya. Kamar haka Muka bayyana ayoyi ga mutanen da suke tunani.

A cikin alkur'ani mai girma Allah madaukakin sarki domin ya bayyana mana wasu abubuwa na hakika yana bada misalai da siffofin da zai taimaka mana wajen gane wadannan abubuwa na hakika . To ita ma wannan aya ta siffata rashin dauwama da saurin rushewar duniya da filin da yake yin canwa shard a zarar ruwan sama ya sabka amam da zarar sanyi ko zafi da ambaliyar ruwa da iska mai karfi sai su lalata wadannan tsirre tamkar wata ciyawa bat a taba fitowa a wannan guri ba ko a yankin baki daya.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farkonsu ; Abubuwan masu kyau da kayatarwa na dabi'a kar su zama wani dalili da zai sa dan adam ya yi riko da rungumar wannan duniya domin duk wani abu a cikin wannan duniya mia karewa ne.

Na biyu;Rayuwar dan adam a wannan duniya tamkar rayuwar tsirre ne da ciya mai saurin lalacewa don haka kar ya yi tunanin zai dauwama a wannan duniya.

To yanzu kuma za mu saurari aya ta 25 a cikin wannan sura ta yunus kamar haka;

وَاللّهُ يَدْعُو إِلَى دَارِ السَّلاَمِ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{25}

25-Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (watau Aljanna) Yana kuma shiryar da wanda ya so zuwa tafarki madaidaici.

Wannan aya tana ilmantar da mu cewa; a dabra da rayuwa a wannan duniya mai karewa akwai rayuwar lahira da ke dauwama da Allah ya yi mana tanadi kuma yake kiran dan adam ta hanyar aiko masa da manzonni da ma'aikansa (AS) domin kiran dan adam zuwa ga riko da hanya madaidaiciya da rayuwar da ke dauwamammiya. A fili lamarin yake duk wanda ya yi riko da hanyar shiriya to Allah ya yi masa tanadi da sakamakon day a yi daidai da aikinsa kuma babu wata baraza da za su fuskanta ta yin nisa da hanya madaidaiciya wato mutanan da Allah ya shiryar da su.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko jin dadi da fara'a a wannan duniya nada dadi amma jin dadi da fara'a a lahira it ace mai dauwama.

Na biyu hanay daya tilo ta isa ga hanyar hutu da kwaciyar hankali na hakika ita ce riko da madaidaiciyar hanay ta Allah tabaraka wata'ala da a wannan duniya ke cusa nucuwa da farin ciki a zucciyar dan adam yayinda a lahira ya shiga gidan aljanna cikin sa'ada da ni'ima. Da fatar Allah ya sa muna daga cikin bayunsa da za su shiga cikin aljannar firdausi amin.

To madallah yanzu kuma lokaci ya yi da za mu saurari aya ta 26 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

لِّلَّذِينَ أَحْسَنُواْ الْحُسْنَى وَزِيَادَةٌ وَلاَ يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلاَ ذِلَّةٌ أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{26}

Wadanda suka kyautata aiki suna da sakamakon Aljanna da kuma Kari.Wani kunci da bakin ciki kuma ba za su same su ba. Wadannan su ne yan Aljanna,su masu dawwama ne a cikinta.

A cikin ayar da ta gabata ta nuni da gidan aljanna yayin da wannan aya take cewa; Allah madaukakin sarki mai rahama yayi wa wadanda suka aikata aikin alheri da sakamako na gidan aljanna da za su dauwama a cikinta kuma sakamakon da ya yi masu tanadi ya zarta ayyukan da suka aikata ta fuskar yawa da kyau kamar yadda a cikin wata ayar ke cewa; duk wanda ya aikata aikin Alheri zai samu sakamakon da aka rubinya har sau goma kuma dangane da ciyarwa da bada sadaka aka rubinya ladan har so saba'in.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko; Allah madaukakin sarki yana gayyatar mu da kiranmu ya kuma nuna mana hanya madaidaiciya har ila yau ya karfafa mana da kwadaitar da mu ya kuma sakama da wadanda su ka yi riko da hanya madaidaiciya da alheri har ma da kari to don mene ne ba mu amsa kiransa sai mu karkace da bin wata hanyar ta daban.

Na biyu kuwa shi ne cewa; mu sani aikata aikin alheri da ya dace yana tabbatar da rayuwa ta gari cikin sauki da isa ga Aljanna da aka yi tanadin ni'imomin Allah masu yawa a cikinta.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 27 a cikin wannan sura ta Yunus da ke cewa;

وَالَّذِينَ كَسَبُواْ السَّيِّئَاتِ جَزَاء سَيِّئَةٍ بِمِثْلِهَا وَتَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ مَّا لَهُم مِّنَ اللّهِ مِنْ عَاصِمٍ كَأَنَّمَا أُغْشِيَتْ وُجُوهُهُمْ قِطَعاً مِّنَ اللَّيْلِ مُظْلِماً أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{27}

Wadanda kuma suka yi mummunan aiki,to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma wulakanci zai lullube su,ba su da wani mai kare su daga azabar Allah,kamar dai an lullube huskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu baki kirin. Wadannan su ne yan wuta,masu dawwama ne a cikinta.

Ita kuwa wannan aya kamar wadda ta gaba ce ta da ke magana kan wadanda suka aikata alheri da irin lada da sakamakon da aka yi masu tanadi,tana magana kan wadanda suka aikata mummunan aiki da sabo da kuma irin fushin da ke jiransu da Azabar Allah da aka yi masu tanadi kuma ba su da wata hanya ta kaucewa wannan lamari matukar suka bari har aka isa wannan rana ta sakamako.fushi da azabar Allah da ke jiransu ta yi muni da tsanani inda take kona jikinsu su yi baki lut. Sai dai adalcin Allah yana nan inda azabar da za a yi masu ta yi daidai da ayyukan da suka aikata ba a wucewa sabanin yadda lutifin Allah da rahamarsa ga wadanda suka aikata Alheri ake saka masu da lada da aljanna fiye da aikin da suka aikata.

Da fatar Allah ya sanya mu daga cikin wadanda lutifinsa da rahamarsa za ta lullube da dacewa da gidan alajanna ya kuma kiyashe mu da shiga Jahanna amin.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko; A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka; mu sani cewa Allah cikin lutifinsa ya halicci mutum cikin yanci da zabi idan ya ga dama ya aikata alheri ko kuma ya zabi hanyar da yaga dama ba tilastawa.

Na biyu kuwa shi ne cewa;A cikin tsarin tarbiya irin ta Musulunci ana fifita salon karfafa guiwa da jinjinawa kafin tsoratarwa da azabattarwa.

Kuma a nan ne ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa ;wassalam.

Suratu Yunus, Aya Ta 28-33 (Kashi Na 324)

Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren aya ko ayoyin kur'ani kana daga bisani mu kawo fassararta har ila yau mu yi dubi tare da ku a cikin irin nasihohin da ke tattare da kumshe a cikin ayar da muka saurare.

To madallah yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 28 zuwa 29 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعاً ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُواْ مَكَانَكُمْ أَنتُمْ وَشُرَكَآؤُكُمْ فَزَيَّلْنَا بَيْنَهُمْ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمْ إِيَّانَا تَعْبُدُونَ{28} فَكَفَى بِاللّهِ شَهِيداً بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ إِن كُنَّا عَنْ عِبَادَتِكُمْ لَغَافِلِينَ{29}

-Ka tuna ranar da za Mu tara su ga baki daya ,sannan Mu ce da wadanda suka yi shirka: Ku tsaya cak a wurarenku ku da abokan tarayyarku. Sai kuma Mu raba tsakaninsu,sai abokan tarayyarsu kuma su ce:Ba mu ne kuka kasance kuna Bauta wa ba.

-To kuma Allah Ya isa shaida tsakaninmu da ku:mu kam hakika bautarku da kuka yi mana ba mu san da ita ba.

Wadannan ayoyi na suranta mana yadda ranar tashin kiya mana za ta kasance da yadda Allah ke tambayar bayunsa kan ayyukan da suka aikata a wannan duniya.Mushrikai da abubuwan da suke bautawa wato gumaka inda kowa ne daya daga cikinsu daya bayan daya ake tambayarsa mene ne dalilinka na bautawa gumki da sauran abubuwan yin shirka da kuka kirkiro yayin da shi kuma gumkin a tambaye shi mene ne ya sa ka amince da wannan bauta da ake yi maka.duk da cewa wadannan gumaka itatuwa ne da aka sassako ba su magana a wannan duniya amma sai Allah ya ba su ikon magana inda za su baranta da ayyukan da mushrikai suka yi masu na bauta da cewa; mu ba mu dauki kanmu ba a matsayin kishiyoyin Allah ku ne mushrikai kuka sanya wannan tunani a cikin kwalluwarku kuma a gaskiya ba mu kuke bautawa ba kawai kun fake ne da mu domin isa da wani abu da kuka boye. Ita ma aya ta 41 a cikin suratul Saba ta yi nuni da wannan lamari da cewa; mala'iku na nuna kayama da fushinsu kan wannan aiki na mushrikai na bautawa wanin Allah ba Allah ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko; A ranar tashin kiyama bayan mutane za a tayar da wasu bayun Allah da su ma za su ganewa idonsu yadda kotun ranar kiyama za ta kasance domin su shaida.

Na biyu kuwa shi ne cewa;A wannan duniya akwai wasu abubuwa da suke tare dam u da rayuwa tare amma a gobe kiya bayan ba su tare da mu za su kuma kasance makiyanmu da kuma bada shaida a kanmu kamar yadda gabobin jikinmu za su yi.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 30 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

هُنَالِكَ تَبْلُو كُلُّ نَفْسٍ مَّا أَسْلَفَتْ وَرُدُّواْ إِلَى اللّهِ مَوْلاَهُمُ الْحَقِّ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{30}

- A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar a duniya,an kuma mayar da su zuwa ga Allah Ubangijinsu tabbatacce,abin da kuma suke kirkira ya bace musu.

Wannan aya tana magana ne kan yadda mushirkai da abubuwa da suke bautawa da fakewa kamar gumaka kowa ke zargin kowa da raba gari ,su mushrikai ba za su iya samun wani taimako daga gumaka ba da suka bautawa sai suka koma ga maula na hakika da babu abin bauta sai shi kuma daga karshe dai ba za su ga sakamakon aikinsu da suka aikata a wannan duniya kuma sun tashi a tutar babu da bata lokacinsu da rayuwarsu a wannan duniya na bautawa gumaka da ba za su amfanar da su da komi ba duniya da lahira da fatar Allah ya kiyashe mu da aikin banza duniya da lahira amin summa amin.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko; Ranar tashin kiyama rana ce ta ganin sakamakon ayyukan da muka aikata a wannan duniya kuma a gaskiya lamari aljanna da Jahannawa sakamako ne na ayyukan da muka aikata na alheri ko lala.

Na biyu kuwa shi ne cewa;A ranar kiyama duk wani lamari da ya shafi karya da makamantanta da ke da tushe a wannan duniya za su wargaje kawai gaskiya da hakika za su dawwama.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 31 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ أَمَّن يَمْلِكُ السَّمْعَ والأَبْصَارَ وَمَن يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيَّتَ مِنَ الْحَيِّ وَمَن يُدَبِّرُ الأَمْرَ فَسَيَقُولُونَ اللّهُ فَقُلْ أَفَلاَ تَتَّقُونَ{31}

Ka ce da su Wane ne yake arzuta ku ta sama da kasa? Ko kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wane kuma yake tsara al'amura? To ai za su ce: Allah ne . To ka ce da su Yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?.

Ayoyin da suka gabata suna magana ne kan kumci da halin ni iyasu da mushrikai ke samun kansu a ciki a ranar kiyama. Allah madaukakin sarki na cewa manzonsa day a tambaye su ku da kuka yi imani da Allah da arzikinku ke hannnunsa da kuma ya kewaye ku to mu ya sa a maimakonsa kuke botawa gumaka da wasu abubuwa a matsayin wasila tsakaninku da mahalicci me yasa ba za ku bautawa Allah ba. Kamar yadda sauran ayoyi da kuma wannan aya ke bayani cewa; mushrikai a lokacin jahiliya sun amince da Allah a matsayin mahaliccinsu na hakika amma lamuran da suka shafi tsarin rayuwa suna danganta su da mala'iku da wasu lamurra na dabi'a hart a kai suna ganin tafiyar da lamarin duniya ya mika su a gare su da zama a gefe daya amma kur'ani ya yi watsi da wannan tunani na bata da daukan irin wannan tunani a matsayin wani nauyi na shirka.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: samar da tambaya da ke bukatar amsar da za ta taimaka wajen shiryar da jama'a da fadakar da su zuwa ga fitira ta gaskiya ta tsarkake Allah yana daga cikin hanyoyin da manzonni ke bi wajen fadakar da jama'a da fahimtar da su.

Na biyu kuwa shi ne: Duniya na bukatar tadbir na hakika kuma tadbir na bai daya a wannan duniya alama ce ta cewa Allah mahalicci shi kadai ne abin bota.

To Madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 32 zuwa 33 a cikin wannan sura ta Yunus (AS).

فَذَلِكُمُ اللّهُ رَبُّكُمُ الْحَقُّ فَمَاذَا بَعْدَ الْحَقِّ إِلاَّ الضَّلاَلُ فَأَنَّى تُصْرَفُونَ{32} كَذَلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى الَّذِينَ فَسَقُواْ أَنَّهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ{33}

- To wannan Shi ne Allah Ubangijinku Tabbataccen sarki.Bayan gaskiya kuwa babu wani abu sai bata. To ta ina ne aka juyar da hankalinku?

-Kamar haka ne kalmar Ubangijinka ta tabbata a kan wadanda suka yi fasikanci cewa su ba za su ba da gaskiya ba.

Yadda wannan duniya ake tafiyar da ita cikin tsari da kwarewa da yadda Allah yayi tsari a sammai da kassai ya sanya mushrikai amincewa da gaskiya cewa Allah shi ne mahalicci. Don haka wannan aya take tabbatar da cewa; irin wannan Allah shi ne ubangijinku ku ma kuma ba wai kawai mahalicci ne ba ne shi ne abin bauta kuma abubuwan da ku ke yin shirka da su su kansu mabukata ne a gare shi.

Ci gaban ayar na yin galgadi da kashedi da cewa; a tsakanin gaskiya da karya wato bata babu wani abu a matsa yin a uku duk wani abu a wannan duniya ko gaskiya ne ko kuma karya kuma idan ba gaskiya ban e to tabbas karya ne. Day a ke Allah gaskiya ne to gumaka da abubuwa da ku ke yi wa shirka da kuka kirkiro karya ne ba za su iya zama gaskiya ba saboda haka duk wanda ta hanyar jayayya da bujirewa yaki bin gaskiya da aiki da ita to ba zai yi katari da shiriya da imani ba.

To a cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: Babu wata hanya tsakatsakiya a tsakanin gaskiya da karya duk wani abu da ba gaskiya ba ne ko karya da bata ne saboda haka ko gaskiya ko kuma karya dayan biyu babu matsayi na uku.

Na biyu kuwa shi ne: duk mutuman da ya rungumi hanyar sabo da fasikanci yana toshe hanyar isa ga imani .

Da fatar Allah madaukakin sarki ya sa mu kasance daga cikin masu aiki da gaskiya da kuma watsi da karya da bata duniya da lahira amin summa amin. Da kuma wannan fata ta alheri ce a madadin wadda ta hada mana sauti malama Julayi, Ni Tidjani malam lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 34-38 (Kashi Na 325)

Jama'a masu sauraremu a shirin wannan shiri na hannunka mai sanda barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku da fatar kuna cikin koshin lafiya amin summa amin kuma kamar yadda shirin ya nuna shiri ne na yi wa junanmu nasiha da galgadi irin na Musulunci kamar yadda sau tari Allah madaukakin sarki a cikin alkur'ani da kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa ke galgadinmu dam u yi wa kawunanmu wa'azi da tsarake zukatanmu kuma babu wanda yafi dacewa kamar mai yiwa kansa wa'azi da fahimtar leifinsa domin ya gyara gaba yayinda kuma babu tababbe kamar wanda yake sha'afa da take leifinsa ya hango na wani domin ya fallasa shi da fatar Allah ya kiyashe mu daga aikata irin wannan leifi amin.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 34 zuwa 35 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka:

قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ قُلِ اللّهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ فَأَنَّى تُؤْفَكُونَ{34} قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ قُلِ اللّهُ يَهْدِي لِلْحَقِّ أَفَمَن يَهْدِي إِلَى الْحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لاَّ يَهِدِّيَ إِلاَّ أَن يُهْدَى فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ{35}

- Ka ce da su Shin daga cikin gumakanku ko akwai wanda yake Kaga halitta,sannan ya maida ita? To idan ba su da wata amsa ka ce da su : Allah Shi ne wanda Yake kaga halitta sannan Ya maida ita gare shi lokacin tashi .To ta ina ne aka juyar da hankalinku?.

- Ka ce da su Shin daga gumakanku ko akwai wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya ? Ka ce da su Allah Shi ne wanda Yake shiryarwa ga gaskiya .To yanzu wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya shi ya fi cancanta a bi, ko kuwa wanda bay a shiryuwa sai dai a shiryar da shi? To me ya same ku ne ? Yaya kuke irin wannan hukuncin?

A cikin ayoyin da suka gabata suna magana ne kan bukatun masu shirka a ranar tashin kiyama da kuma yadda abubuwan da suka yi wa shirka bas u iya tabuka masu da komi ba, to wannan aya tana cewa; idan muka yi nazari kan halittu za mu fahimci cewa babu wani da ke iya yin halitta face Allah daya abin bauta mai hikima day a halicci komi da kowa da samar da rayuwa kuma gumaka da sauran abubuwan da ke wannan duniya shi ne mahalittunsu kuma suna bukatuwa da mahalicci to saboda haka ta yaya ne za su zamanto da lokaci guda masu yin halitta?

Kuma idan muna bukatar hidaya da shiriya to ku sani a kashin kansu bas u da hidaya da kuma za su iya nuna maku hanya kuma idan suna da karfin isa ga sa'ada to dole su fara shirya da kansu kafin ku da hakan zai bas u damar shiryar da ku. A daidai wannan lokaci ku sani ne Allah ne mai shiryarwa da dora ku a kan hanya madaidaiciya hanyar gaskiya kuma haka lamarin yake tafiya a dabi'ance Allah ya na amfani da hanyar Annabawa da manzonni da littafai na wahayi wajen shiryar da mu.

To madallah a cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: hanyar tambaya da amsa suna daga cikin hanyoyi mafi kyau na bincike da jayayya tare da wadanda suke da sabani na tunani da akida kuma Allah yana ilmantar da manzonsa wannan salo.

Na biyu kuwa shi ne: Allah madaukakin sarki shi ne mahaliccin wannan duniya amma bayan ya halicci abubuwan da ke cikinta sai ya bar kowa ya zabi abin da yake so.Shi ne mahalicci da ke nunawa dukan halittunsa hanyar kamala da sanya su a cikin wannan hanya.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 36 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka:

وَمَا يَتَّبِعُ أَكْثَرُهُمْ إِلاَّ ظَنّاً إَنَّ الظَّنَّ لاَ يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئاً إِنَّ اللّهَ عَلَيمٌ بِمَا يَفْعَلُونَ{36}

- Yawancinsu kuwa baa bin da suke bi sai mummunan zato.Hakika irin wannan zato kuwa ba ya wadatar da komai game da gaskiya. Ba shakka Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne.

Bayan da ayoyin da suka gabata ke magana kan yanayin da mushrikai suka samu kansu a ciki to wannan aya tana magana da bayani kan tushen kaucewa hanya da tunaninsu da yadda ya samo asali da cewa; rungumar zato kirkirowa maras tushe da asali da sassakawa sune suka haddasa kaucewa hanya ta hakika da yin riko da tunanin bata da zato na karya ,alhali kuwa duk wani zato da kirkirowa a cikin lamari na tunani da akida bas u da matsayi kuma tamtamcewa da yakini sun e ked a matsayi da suke isar dad an adam ga gaskiya bugu da kari wani abu day a yi fice a tsakanin jahilai da akidarsu shi ne yin riko da uwaye da kakannu da tsananin kabilanci kan karya da ba shi da wani matsayi na ilimi da hankali.

To madallah a cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: A lamari day a shafi akida da kyawawan dabi'u ba a aiki da yawan jama'a a matsayin dalili na sanin gaskiya. Kuma sau tari yawanci jama'a suna kaucewa hanya a bangaren tunani da aiki kuma wannan ba zai zamanto dalilin tunaninsu na kan gaskiya ko abin da suke aikatawa daidai ne.

Na biyu kuwa shi ne: Kafirci da shirka bas u samo asali daga fahimta ta ilimi ba ko hankali kwai wani abu ne na zato da kirkiro ta karya.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 37 da 38 a cikin suratul Yunus kamar:

وَمَا كَانَ هَـذَا الْقُرْآنُ أَن يُفْتَرَى مِن دُونِ اللّهِ وَلَـكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ الْكِتَابِ لاَ رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ الْعَالَمِينَ{37} أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ قُلْ فَأْتُواْ بِسُورَةٍ مِّثْلِهِ وَادْعُواْ مَنِ اسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ اللّهِ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{38}

37-Wannan Alkur'anin bai yiwuwa a kage shi daga tunanin wani wanda ba Allah ba sai dai shi gaskatawa ne ga abin day a gabace shi na littattafan da aka saukar kuma bayani ne na hukunce-hukuncen da Allah ya saukar babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake.

38- A'a ,kuwa cewa suke yi : kagar say a yin e? Ka ce da su To ku kawo sura daya tal irinsa a fasaha da sauransu kuma ku kirawo wanda duk za ku iya ya taimaka muku wanda ba Allah ba idan kun kasance masu gaskiya.

Suratu Yunus, Aya Ta 39-44 (Kashi Na 326)

Jama'a masu sauraremu a shirin wannan shiri na hannunka mai sanda barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku da fatar kuna cikin koshin lafiya amin summa amin kuma kamar yadda shirin ya nuna shiri ne na yi wa junanmu nasiha da galgadi irin na Musulunci kamar yadda sau tari Allah madaukakin sarki a cikin alkur'ani da kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa ke galgadinmu da mu yi wa kawunanmu wa'azi da tsarake zukatanmu kuma babu wanda yafi dacewa kamar mai yiwa kansa wa'azi da fahimtar leifinsa domin ya gyara gaba yayinda kuma babu tababbe kamar wanda yake sha'afa da take leifinsa ya hango na wani domin ya fallasa shi da fatar Allah ya kiyashe mu daga aikata irin wannan leifi amin.

Zamu fara shirin na yau da sauraren ayoyi na 39 da 40 a cikin suratul yunus kamar haka:

بَلْ كَذَّبُواْ بِمَا لَمْ يُحِيطُواْ بِعِلْمِهِ وَلَمَّا يَأْتِهِمْ تَأْوِيلُهُ كَذَلِكَ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الظَّالِمِينَ{39} وَمِنهُم مَّن يُؤْمِنُ بِهِ وَمِنْهُم مَّن لاَّ يُؤْمِنُ بِهِ وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِالْمُفْسِدِينَ{40}

-Ã'a, sun karyata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar wadancan ne wadanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãkibar azzãlumai ta kasance?

-Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga mabarnata.

Sai a saurari aya ta 40 da ta 41 a cikin suratul Yunus kamar haka;

وَمِنهُم مَّن يُؤْمِنُ بِهِ وَمِنْهُم مَّن لاَّ يُؤْمِنُ بِهِ وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِالْمُفْسِدِينَ{40} وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّي عَمَلِي وَلَكُمْ عَمَلُكُمْ أَنتُمْ بَرِيئُونَ مِمَّا أَعْمَلُ وَأَنَاْ بَرِيءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ{41}

- Daga cikinsu kuma akwai wanda yake ba da gaskiya da shi Alkur'anin ,akwai kuma wanda bay a bad a gaskiya da shi,Ubangijinka kuma Shi ne mafi sanin wadanda suke mabarnata.

-Idan kuwa suka karyata ka ,to ka ce da su Sakamakon aikina,yana gare ni,sakamakon aikinku kuma yana gare ku, Ku babu ruwanku da sakamakon abin da nake aikatawa,ni kuma babu ruwana da sakamakon abin da kuke aikatawa.

Da farko Allah yana bamu labarin yadda musulmi suka bada gaskiya da kur'ani da kuma wadanda tun da farko suka bada gaskiya da wannan littafi mai tsarki na alkur'ani.Kuma Allah madaukakin sarki masani ya san wadanda suka yi barna a doran kasa,kum idan suka karyata ma'aikin Allah amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa ka ce masu sakamakon aikina yana gare ni yayinda sakamakon aikinku kuma yana gare ku ko ya yi aikin da zai fishe shi a wannan duniya da kuma ranar sakamako.

A cikin wannan aya za mu ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da fadakarwa .

Na farko: yin imani da alkur'ani da ma'aikin Allah lamari ne mai muhimmanci matuka.

Na biyu kuwa shi ne: duk wani aiki tanada sakamako.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 42 zuwa 44 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ أَفَأَنتَ تُسْمِعُ الصُّمَّ وَلَوْ كَانُواْ لاَ يَعْقِلُونَ{42} وَمِنهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيْكَ أَفَأَنتَ تَهْدِي الْعُمْيَ وَلَوْ كَانُواْ لاَ يُبْصِرُونَ{43} إِنَّ اللّهَ لاَ يَظْلِمُ النَّاسَ شَيْئاً وَلَـكِنَّ النَّاسَ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ{44}

-Daga cikinsu kuma akwai wadanda suke sauraron ka .Yanzu kai za ka iya jiyar da kurame ko da ba su da hankali.

-Hakika Allah ba Ya zaluntar mutane da komai ,sai dai mutane da komai ,sai dai mutane kawunansu kawai suke zalunta.

-Hakika Allah ba ya zaluntar mutane da komai,sai dai mutane kawunansu kawai suke zalunta.

Wadannan ayoyi na yi mana bayani ne dalla-dalla kan yadda mutuma day a ki yin imani da gangan da juyawa gaskiya baya ba za a iya shiryar da shi ba tamkar kurma ne da duk wani kokari da mutum ya yi ya ji wata magana ba zai iya ba musamman ma kurman da gangam ko kuma makaho da ya ki gani da gangam ba za a iya sa shi ya gani ba domin an toshe masa idon gani na basira da kuma yadda tuhun jahilci da kafirci ya mamaye masa zucciya.Kuma Allah ba ya zalumtar kowa da komi face su mutane ne ke zaluntar kansu da kansu.

A cikin wannan aya za mu ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da fadakarwa .

Na farko:Kafirai da gangan ne suka juyawa gaskiya baya.

Na biyu kuwa shi ne:kafirai daidai suke da kuramai da makahi.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau da fatar Allah ya kara mana karfin guiwar aiki da abubuwan da muka saurara a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar kafin wani lokacin a madadin malama Julayi na ke cewa wassalam alaikum wa rahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 45-49 (Kashi Na 327)

Jama'a masu sauraremu a shirin wannan shiri na hannunka mai sanda barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku da fatar kuna cikin koshin lafiya amin summa amin kuma kamar yadda shirin ya nuna shiri ne na yi wa junanmu nasiha da galgadi irin na Musulunci kamar yadda sau tari Allah madaukakin sarki a cikin alkur'ani da kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa ke galgadinmu dam u yi wa kawunanmu wa'azi da tsarake zukatanmu kuma babu wanda yafi dacewa kamar mai yiwa kansa wa'azi da fahimtar leifinsa domin ya gyara gaba yayinda kuma babu tababbe kamar wanda yake sha'afa da take leifinsa ya hango na wani domin ya fallasa shi da fatar Allah ya kiyashe mu daga aikata irin wannan leifi amin.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 45 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ كَأَن لَّمْ يَلْبَثُواْ إِلاَّ سَاعَةً مِّنَ النَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيْنَهُمْ قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَاء اللّهِ وَمَا كَانُواْ مُهْتَدِينَ{45}

45-Ranar da zai tashe su kuwa za su ga kamar bas u zauna ba sai wani dan lokaci na rana,za su kuwa rika gane junansu.Hakika wadanda suka karyata gamuwa da Allah sun tabe ,ba su kuma zamnato shiryayyu ba.

Duk da cewa kafirai sun karyata saduwa ranar tashin kiyama da musanta wannan rana amma sun ki sun so a wannan rana za a tadar da duk al'umma da kasancewa a wannan rana ta hisabi. A wannan rana saboda tsananin girmanta da tashin hankali da kadawar hanta mutum zai ga rayuwar da ya yi a wannan duniya da wadda ya yi bayan mutuwa wato a barzahu zai dauka tamkar ya rayu ne sa'a guda a rana. Duk da cewa mutum yayi shekaru da dama barkatai bayan mutuwarsa,a ranar kiyama zai ga tamkar ya yi barci ne na wani kankanan lokaci ya tashi bad a jimawa ba,saboda za mu san juna da kuma ba za mu manta komi ba. A cikin wannan yanayi,daidai ne masu karyatawa da musanta saduwar wannan rana su shiga cikin kunci da damuwa da fahimtar hakika cewa sun kasance a wannan rana ba tare da wani tanadi ba kuma babu wata dama da hanyar komawa baya wato gidan da suka bari na duniya.

A cikin wannan aya za mu ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da fadakarwa .

Na farko: Kwanakin rayuwar duniya dan kankane net a inda ta kai yana saurin wuce da a ranar kiyama mutum ba zai iya tuna wani abu face ganin ya rayu ne kawai na wani kankanan lokaci da jin ya yi asarar damar da aka ba shi.

Na biyu kuwa shi ne: duk mutum mai hankali zai fifita rayuwa ta hakika da dauwama kan jin dadin wannan duniya mai karewa.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 46 a cikin wannan sura ta yanus:

وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ الَّذِي نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ اللّهُ شَهِيدٌ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ{46}

46- Ko dai Mu nuna maka shashin abin da muke tanadar musu tun a duniya ko kuma Mu karbi ranka,to makomarsu dai gare Mu take,sannan Allah fa Yana sane da abin da suke aikatawa.

Wannan aya tana sanar da ma'aikin Allah da mumunai cewa; a wannan duniya idan Allah bai azabtar da kafirai da kafircinsu ba to wannan yana nufin kafircinsu da sakamakon mummunan aikinsu za su gansa a ranar kiyama kuma kowa da komin zai koma ga Allah har ila yau Allah masani ne da ganin duk wani aiki da wani zai aikata ko alheri ko mummuna,dukan kafircin mutum komin kankantarsa yana ganinsa amma wannan ba yana nufin dukan azaba an yi tanadinta sai ranar kiyama a'a wasu azabobin a wannan duniya ne a daidai lokacin da muke rayuwa a doran kasa wasu muna ganinsu yayinda wasu kuma bayan mutuwar Kafirai za su fara gamuwa da azabobin da aka yi masu tanadi kafin ranar tashin kiyama.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da cewa; Mumunai bai kamata bas u dam u da kafircin kafirai da rashin azabtar da su,azaba da ganin sakamakon mummunan aikin da suka aikata wani alkawari ne na Allah kuma Allah yana aiki da alkawarinsa.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 47 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

وَلِكُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولٌ فَإِذَا جَاء رَسُولُهُمْ قُضِيَ بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ{47}

47- Kowacce Al'umma kuma tana da manzo,To idan manzonsu ya zo suka karyata shi to sai a yi hukunci a tsakaninsu da adalci,su kuma ba za a zalunce su ba.

Annabawan Allah sun kasu zuwa kashi biyu. Wani kaso ko bangare na Annabawa an aiko su da littafi da shari'a yayin da wasu an umarce sun e da yin tabligi da yada shari'a. To daga cikin ayoyin kur'ani mai girma za mu iya fahimtar cewa a cikin al'ummomi daban-daban da mutane akwai wadanda ke yin riko da koyarwar Annabawa da littafai masu tsarki da yada shari'a da kiran mutane zuwa ga rungumar hanya madaidaiciya. Babban sako mai muhimmanci da annabawa (AS) ke isarwa ga mutane shi ne tsayar da gaskiya da adalci da kuma gwagwarmaya da zalunci da danniya. Allah madaukakin sarki zai tayar da kowace al'umma da manzonnin da aka aiko mata. Kuma a gabansu sun e za a hukumta kowa da yi masa hisabi a wannan kotu ta ranar kiyama karakshin adalci na karshe.

A cikin wannan aya za mu ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da fadakarwa .

Na farko: mu sani Allah ba bu wata al'umma da kabila da ya barta haka kara zube ba bu wani mai shiryarwa ko jagora kuma jawabai da sakon annabawa da manzonni na isa ga kunnuwansu.

Na biyu kuwa shi ne: fadada adalci da gaskiya a tsakanin jama'a wata shinfida ce da gajiyar koyarwar Annabawa da littafai masu tsarki.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 48 da 49 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

وَيَقُولُونَ مَتَى هَـذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{48} قُل لاَّ أَمْلِكُ لِنَفْسِي ضَرّاً وَلاَ نَفْعاً إِلاَّ مَا شَاء اللّهُ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ إِذَا جَاء أَجَلُهُمْ فَلاَ يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً وَلاَ يَسْتَقْدِمُونَ{49}

48- Suna kuma cewa: To yaushe ne wannan alkawari zai zo idan kun kasance masu gaskiya?.

49- Ka ce da su Ban a mallakar wata cuta,ko wani amfani ga kaina sai dai abin da Allah Ya nufa.Kowace al'umma tana da lokacin da aka iyakance mata .Idan lokacin nasu ya yi ,to ba za su saurara ba daidai da sa'a guda,kuma ba za su riga ba.

Wadannan ayoyi na siffanta mana yadda kafirai ke karyata hakikanin ranar Kiyama sai su rika neman wani abu da za su fake da shi da yada tambayoyi na shaku da kawo rudani saboda haka suke dora ayyar tamba da cewa: idan Alkiyama gaskiya ce kuma ku gaskiya kuke fadi to yaushe ni lokacin abkuwarta. Wannan tambaya tasu ta nuna mana yadda suka jahilci lamura ko musantawa da gangan domin kuwa babu lazimci tsakanin wanzuwa da tabbacin wani abu na hakika da lokacinsa ,kuma ko kowa daga cikinmu ya sani da tabbacin zai bar wannan duniya ko bajima ko badade amma babu wanda ya san lokacin mutuwarsa da labarin haka.To suma Annabawa da manzonni karkashin wahayi daga Allah na sanar dam u cewa karshen rayuwa a wannan duniya zai tabbata da tayar dam u a ranar kiyama, amma kuma Allah bai ba su labarin lokacin wakanar hakan ba wato yaushe ne alkiyama za ta wakana da isar da hakan ga mutane.

A cikin wannan aya za mu ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da fadakarwa .

Na farko: Su Annabawa suna magana da bayani da mutane ne karkashin tafarkin gaskiya saboda haka a kullum suke bayyana masu gaskiya kai tsaye cikin hikima cewa mu a karan kanmu bam u da wani karfi da kudura ko mallakar wani abu na amfani ko cutarwa duk lamura na Allah ne shi ne mai zartarwa.

Na biyu kuwa shi ne: ita kuma al'umma da kuwa kowane daya daga cikinmu yana da karshe wani karshensa zuwa ga Hallaka wa iyazu billahi wani kuwa alheri da sakamako na karshe wani lokaci farin ciki da sa'ada wani lokaci kuwa akasin haka.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau da fatar Allah ya kara mana karfin guiwar aiki da abubuwan da muka saurara a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar kafin wani lokacin a madadin malama Julayi na ke cewa wassalam alaikum wa rahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 50-56 (Kashi Na 328)

Jama'a masu sauraremu a shirin wannan shiri na hannunka mai sanda barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku da fatar kuna cikin koshin lafiya amin summa amin kuma kamar yadda shirin ya nuna shiri ne na yi wa junanmu nasiha da galgadi irin na Musulunci kamar yadda sau tari Allah madaukakin sarki a cikin alkur'ani da kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa ke galgadinmu dam u yi wa kawunanmu wa'azi da tsarake zukatanmu kuma babu wanda yafi dacewa kamar mai yiwa kansa wa'azi da fahimtar leifinsa domin ya gyara gaba yayinda kuma babu tababbe kamar wanda yake sha'afa da take leifinsa ya hango na wani domin ya fallasa shi da fatar Allah ya kiyashe mu daga aikata irin wannan leifi amin.

To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 50 da 51 a cikin suratul Yunus (AS) kamar haka:

قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُهُ بَيَاتاً أَوْ نَهَاراً مَّاذَا يَسْتَعْجِلُ مِنْهُ الْمُجْرِمُونَ{50} أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ آمَنْتُم بِهِ آلآنَ وَقَدْ كُنتُم بِهِ تَسْتَعْجِلُونَ{51}

-Ka ce da su Yanzu ku ba ni labari yadda za su yi idan azabar Allah ta zo muku da daddare ko da rana,mene ne masu laifi suke yi wa gaggawar zuwanta?.

-Shin sai idan azabar ta afka muku ne za ku ba da gaskiya da shi Allah? Sai yanzu za ku bad a gaskiya alhali kuwa da can kun kasance kuna neman gaggautowarta?

Wadannan ayoyi na maida martani da bada amsa ga masu karyata ranar tashin kiyama da ma yin izgili ta hanyar tambayar cewa: Yaushe ne azabar Allah za ta sabka ? sai ma'aikin Allah ya amsa masu da cewa; kar ku yi gaggauwa dangane da sabkar azabar Allah ,idan ya ga dama ko da dara ko da dare kwacam ba ku shirya ba ba zato ba tsammahani zai sabkar kuma idan azaba ta sabko muku mai za ku yi ne ? shin ko kunada hanyar kubuta ne ko karfin hana azabar ta shafe ku ne ? kuma idan kuka yi imani lokacin da kuka ga alamar sabkar azaba to wannan imani na ku ba zai amfane ku da komi ba saboda kuwa a daidai lokacin da ake sabkar da azaba ana toshe kofofin tuba ne kuma duk wani imani da tuba bas u da wani amfani a wannan lokaci.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya fahimta da ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: ba bu tabbacin cewa azaba ta shafi kawai wadanda suka aikata sabo da dagawa a doran kasa a'a akwai yuyuwar ta shafi wadanda bas u tare da su masu yin takatsantsan.

Na biyu: yin imani lokacin abkuwar wani hadari ba shi da kima domin kuwa ya samo asali ne daga tsoro ba daga akida da zabi ba.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 52 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) .

ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ الْخُلْدِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلاَّ بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ{52}

Sannan aka ce da wadanda suka kafirce: Ku dandani azaba madawwamiya. Ai ba za a saka muku ba sai a kana bin da kuka kasance kuna aikatawa?

A cikin ayoyin da suka gabata suna magana ne kan kafirci da azabar Allah da ke sabka kan kafirai a wannan duniya da kuma take sabka a daidai lokacin da suka kasance sun sakankance ba zato babu tsammahani , To ita kuwa wannan aya tana magana ne kan azaba da sakamakon da ke riskar mutum a ranar kiyama saboda yadda ya zalunci kansa da kuma dan uwansa da kuma yadda ya kasance ya ci gaba da aikata sabo ba tare day a tuba ba to zai ga mummunan sakamako na azabar dab a tad a karshe wato ta har abada. Abin sani anan ita azabar Allah ta samo asali ne daga ayyukan dan adam a wannan duniya ,inda wannan sabo yake kasancewa tamkar butunbutumi da kuma a kullum ke tare da mutum yana azabtar da su.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: A al'adu irin na Musulunci ,zalunci ba wai kawai ya shafi saura ban e .a'a sabo shi kansa zalunci ne saboda zalunci ne ga mahalicci da kuma zalunci ne ga manzonni da aka aiko su domin shiryar da jama'a da suke iyakacin kokarinsu .

Na biyu: azabar Allah karkashin adalci da kuma sakayyar ayyukan mutum ba wai wani abu na daban ba.

To madallah za mu saurari aya ta 53 zuwa da 54 a cikin suratul Yunus (AS):

وَيَسْتَنبِئُونَكَ أَحَقٌّ هُوَ قُلْ إِي وَرَبِّي إِنَّهُ لَحَقٌّ وَمَا أَنتُمْ بِمُعْجِزِينَ{53} وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍ ظَلَمَتْ مَا فِي الأَرْضِ لاَفْتَدَتْ بِهِ وَأَسَرُّواْ النَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ الْعَذَابَ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ{54}

Suna kuma tambayarka cewa; Yanzu abin da kake fada gaskiya ne kuwa ? Ka ce I-mana,na ko rantse da Allah ba shakka za ku guje masa ba.

Da a ce kowane rai da ya kafirce ya mallaki duk abin da yake bayan kasa, to wallahi da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa su boye nadama a lokacin da suka ga azaba, a kuma yi hukunci a tsakaninsu na kuma yi hukunci a tsakaninsu na adalci, ba ko za a zalunce su komai ba.

Ayoyin da suka gabata a shirinmu na makon day a gabata suna magana ne kan sabkar azaba a wannan duniya da kuma ta gobe kiya kan kafirai da mushrikai to su kuma wadannan ayoyi na cewa; Kar ku yi shako alkawalin Allah gaskiya ne kuma tabbataccce ne azaba da sakamakon munanan aikin mutum zai gani . Kuma dukan maganganun ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi gaskiya ne.Kuma Allah ya yi rantsuwa irin wannan rana ta kiyama za ta tabbata kuma babu wata hanya da kaucewa wannan rana ko jurewa azabar wannan rana.Azaba a wannan rana ta munana ta kai inda kafiri zai yi fatar bada dukiyarsa baki daya domin a kubutar da shi daga wannan azaba. Amma sun yi jinkiri domin a wannan rana nadama bat a da wani amfani kuma kotun ranar kiyama karkashin adalci da hukunci na Allah ne.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu.

Na farkonsu:wani lokaci domin kawar da shakku ma'aikin Allah na yin rantsuwa domin isar da wannan sako ga kowa da kowa.

Na biyu: A kotun adalci kotun Allah.karfi da dukiya bas u da wani amfani kawai abin da ke aiki a irin wannan kotu gaskiya da akida da aikin mutum.

Yanzu za mu saurari ayoyi na 55 zuwa 56 a cikin wannan sura ta Yunus (AS):

أَلا إِنَّ لِلّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ أَلاَ إِنَّ وَعْدَ اللّهِ حَقٌّ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ{55} هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ{56}

Na'am, hakika duk abin da yake sammai da kassai na Allah ne.Na'am ,ba shakka alkawarin Allah gaskiya ne,sai dai kuma yawancin mutane ba su sani ba.

Shi ne Yake rayawa yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku.

Babban dalili da ke sawa yin shaku kan ranar tashin kiyama.shi ne shakku kan kudurar Allah da iradarsa saboda haka wannan aya ke cewa: mene ne dalilin day a sa muke ganin Allah ba shi da karfi da kudurar sake rayar da matattu da kuma yi masau sakamakon abubuwan da suka aikata na alheri ko lala. Shin ba ku sani ba duk wani abu da bukata ta dora da shi ne kuma shi ne mahalicci mammallakin duniya da lahira ,mutuwa da rayuwarmu tana hannunsa to mi yasa ku ke shakku da abkuwar ranar tashin kiyama.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko:mu sani iko da mallakar du wani abu hakki ne na Allah kuma duk wani abu da mutum zai mallaka zahirin lamari ne hakikanin lamari na komawa ne ga Allah saboda haka a ranar tashin kiyama.Kafirai ba su da wani abu da suka mallaka da zai zamo masu kariya da yantar da su daga azaba.

Na biyu: Ikon Allah kan komi dalili ne na karfi da kudurarsa na tabbatar da adalci da cika alkawalinsa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen irin abubuwan da za mu iya kawo muku a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali damagaram na shirya kuma na gabatar kafin wani mako na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratu Yunus, Aya Ta 57-61 (Kashi Na 329)

Jama'a masu sauraremu a shirin wannan shiri na hannunka mai sanda barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku da fatar kuna cikin koshin lafiya amin summa amin kuma kamar yadda shirin ya nuna shiri ne na yi wa junanmu nasiha da galgadi irin na Musulunci kamar yadda sau tari Allah madaukakin sarki a cikin alkur'ani da kuma ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayan gidansa ke galgadinmu dam u yi wa kawunanmu wa'azi da tsarake zukatanmu kuma babu wanda yafi dacewa kamar mai yiwa kansa wa'azi da fahimtar leifinsa domin ya gyara gaba yayinda kuma babu tababbe kamar wanda yake sha'afa da take leifinsa ya hango na wani domin ya fallasa shi da fatar Allah ya kiyashe mu daga aikata irin wannan leifi amin.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 57 da 58 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءتْكُم مَّوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَشِفَاء لِّمَا فِي الصُّدُورِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ{57} قُلْ بِفَضْلِ اللّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُواْ هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ{58}

- Ya ku mutane,hakika gargadi ya zo muku daga Ubangijinku da kuma waraka ga abin da yake cikin zukatanku,kuma shiriya ne da rahama ga muminai.

- Ka ce da su : Da falalar Allah da rahamarsa kawai za su yi farin ciki,wannan shi ya fi alheria daga abin da suke Tarawa na duniya.

A duk zamani da yanayi ba yashudewa ba tare da Annabawa da manzonni ba ko kuma masu galgadi da nuna mana hanyar Allah kuma Ubangijinmu Allah madaukakin sarki yana turo mana da rahama amma ga muminai don haka Allah ya umarci ma'aikinsa day a ce dam u; falala da rahamar Allah ne kawai za su cusa mana farin ciki a zukatanmu, kuma wannan shi ne yafi alheri ga mutane masu takawa da tsoran Allah a wannan duniya.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya fahimta da ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: a kowane zamani akwai mai shiryarwa daga Allah.

Na biyu ; burin annabawa shi ne shiryar da al'umma kan tafarkin Allah.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 59 da ta 60 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

قُلْ أَرَأَيْتُم مَّا أَنزَلَ اللّهُ لَكُم مِّن رِّزْقٍ فَجَعَلْتُم مِّنْهُ حَرَاماً وَحَلاَلاً قُلْ آللّهُ أَذِنَ لَكُمْ أَمْ عَلَى اللّهِ تَفْتَرُونَ{59} وَمَا ظَنُّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّ اللّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَشْكُرُونَ{60}

- Ka ce da su: Ku ba ni labarin abin da Allah Ya halitta muku na arziki,sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal? Ka ce da su:Yanzu Allah ne Ya yi muku izinin yin haka,ko kuwa Allah kuke yi wa kage ne?

-Mene ne kuma tsammanin wadanda suke yi wa Allah kagen karya a ranar alkiyama? Hakika Allah ma'abucin falala ne ga mutane,sai dai kuma yawancinsu bas a godewa.

Allah madaukakin sarki ta hanyar Manzonsa Muhammadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya kalubalanci kafirai da sub a shi labarin abin da Allah Ya halitta muku na arziki, da kuma yadda ya mayar da wani hala wanin kuma ya mayar da shi haram,ka ce da su : Yanzu Allah ne Ya yi maku izinin yin haka ko kuwa Allah kuke yi wa kage ne domin fadakar da su da wannan tambaya. Sai kuma wata Tambayar kan wadanda suke yi wa Allah kagen karya a ranar Tashin kiyama domin a wannan rana karaya bata da rana sai gaskiya da aiki kuma yawancin mutane ba su gane gaskiya.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu :

Na farkonsa;Godewa ni'ima ita ma wata babbar nasara ce.

Na biyu kuma : karya bat a da wani amfani a ranar kiyama.

To madallah za mu fara shirin na yau da sauraren aya ta 61 a cikin suratul Yunus kamar haka;

وَمَا تَكُونُ فِي شَأْنٍ وَمَا تَتْلُو مِنْهُ مِن قُرْآنٍ وَلاَ تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلاَّ كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُوداً إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ وَمَا يَعْزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثْقَالِ ذَرَّةٍ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاء وَلاَ أَصْغَرَ مِن ذَلِكَ وَلا أَكْبَرَ إِلاَّ فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ{61}

61-Kuma babu wani al'amari da kai Annabi kake zamantowa cikinsa,babu kuma wani abu na Alkur'ani da kake karantawa.Kuma babu wani abu da kuke aikatawa kai da al'ummarka, sai Mun zamanto Muna kallokacin da kuke kutsawa cikinsa. Kuma babu wani daidai da kwayar zarra a kasa ko a sama da zai kubuce wa Ubangijinka, babu kuma mafi kankanta ko mafi girma daga wancan watau kwayar zarra sai fa yana cikin Littafi bayyananne Lauhul Mahafuzu.

Wannan aya tana yin nuni da fadin ilimin Allah Madaukakin Sarki Masani mabuwayi da bayyana mana kara cewa; duk hali da yanayi da ayyukan da mutum zai aikata da kuma yake da tunani da niyar aikatawa yana hannun Mahalicci wanda ya halicci mutum da ilimin da ke tattare da shi kuma wannan lamari komin kankantarsa yana a rubuce a cikin Lauhin Mahfuzi da aka rubuta komi da komi tun lokacin da aka halicci wannan duniya da kafin lokacin kuma ba wai Kawai Allah ba hatta su kansu mala'iku Allah ya sanar da shaida masau haka da kuma bas u karfi da ikon ganin abubuwan da muke aikatawa da rubutawa su ajiye a matsayin shaida a kanmu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda hudu masu muhimmanci da ilmantarwa kamar;

Na farko: Tunaninmu,maganganunmu da ayyukanmu dukansu Allah da mala'ikunsa sun sani nuna gani baa bin da yake boye masu.

Na biyu: a gurin Allah sammai da kasai kanana da manya bas u da banbanci kuma iliminsa ya riski komi da ko'ina.

Na uku ba wai kawai mutane ba hatta annabawa suna karkashin kulawar Allah kuma Allah yana kollo da shaida ayyukanmu baki daya.

Na hudu duniya da abin da ke cikinsa sun hannun Allah idan ya kara mana wata dama da jinkirta mana azaba ba dalili neb a wa iyazu billahi na ya sha'afa da jahiltar abubuwan da muke aikatawa ba a'a wani lutifi ne daga gare da ba nu damar yin tuba da aikata alheri.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 62-67 (Kashi Na 330)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani bayan da muka surari aya ko ayoyi daga cikin ayoyin surorin Alkur'ani mai girma ,domin yin dubi a cikin irin nasihohin da ke tattare da irin wannan ayoyi,kuma shi Kur'ani daga aya ta farko harzuwa aya ta karshe da ke cikinsa nasiha ce illa iyaka mu yi aiki da irin wadannan nasihohi da hakan zai cece mu duniya da lahira ma'ana a wannan duniya mu samu yin rayuwa ta gari cikin sauki da wadata yayin da idan kuma muka mutu da tayar dam u a ranar Kiyama mu samu sakamako na alheri na gidan Aljanna da aka yi wa wadanda suka aika ta alheri tanadi. Da fatar Allah ya sa mu dace duniya da lahira amin.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 62 zuwa 64 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

أَلا إِنَّ أَوْلِيَاء اللّهِ لاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{62} الَّذِينَ آمَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ{63} لَهُمُ الْبُشْرَى فِي الْحَياةِ الدُّنْيَا وَفِي الآخِرَةِ لاَ تَبْدِيلَ لِكَلِمَاتِ اللّهِ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{64}

- Na'am,ba shakka waliyyan Allah babu wani tsoro a gare su, kuma ba za su yi wani bakin ciki ba.

-Waliyyan kuwa sun e wadanda suka ba da gaskiya kuma suka kasance suna tsoron Allah.

-Suna da albishir a rayuwar duniya da kuma ta lahira.babu wani sauyi ga maganar Allah.Wannan shi ne babban rabo.

A cikin sauran shirye-shiryen da suka gabata mun yi ta bayani kan halayyar Mushrikai da kafirai dab a su yi imani ba to a cikin wadannan ayoyi da muka saurara a yau suna bayani da magana kan halayye na hakika na Mumunai da Bayun Allah na hakika da haka zai bamu damar bambanta bangarorin biyu da banbanta hanya madaidaiciya ta Sa'ada da mummunar hanya,Da kuma kwanciyar hankali na ruhi da ya nisanta da bakin ciki da kunci to wannan shi ne babban rabo da ni'ima da jari da Allah ya yi wa bayunsa salihai tanadi kuma sun samu wannan matsayi da daukaka ce bayan da suka ladabtar da kansu kauracewa aikata sabo inda suka tsarkake kansu da zama makusanta da waliyan Allah kuma irin wadannan mutane suna da mushara da albishir daga Allah a fuskoki da zukatansu kuma ba za ka samu kwankwanto a cikin zukatansu.

Ma'aikin Allah madaukakin sarki tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa na cewa; Waliyan Allah hatta shirunsu ibada ne, kollonsu ibra ne, maganganunsu hikima ne kuma zirga-zirgarsu a tsakanin jama'a albarka ce .

Imam Ali (AS) na cewa: kar ka kaskantar da wani daga cikin bayun Allah da muzanta wani daga cikinsu domin Allah yana boye waliyansa a cikin mutane ba tare da sani ko wannan yana cikin su ko a'a.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: duk wanda tsoran Allah ya lullube zucciyarsa ba zai ji tsoran wanin Allah ba.

Na biyu: Imani ba tare da takawa ba ba shi da amfani mutum mumuni dole ya kauracewa aikata sabo.

Na uku:duk wanda ya yi dace da Sa'ada sai ya kasance karkashin imani da takwa da hakan zai tabbatar da sa'adarsa duniya da lahira.

yanzu kuma za mu saurari aya ta 65 da 66 a cikin suratul Yunus (AS) kamar haka;

وَلاَ يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ إِنَّ الْعِزَّةَ لِلّهِ جَمِيعاً هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{65} أَلا إِنَّ لِلّهِ مَن فِي السَّمَاوَات وَمَن فِي الأَرْضِ وَمَا يَتَّبِعُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ شُرَكَاء إِن يَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلاَّ يَخْرُصُونَ{66}

-Kada kuma wata maganarsu ta bakanta maka rai.Hakika girma gaba dayansa na Allah ne, Shi Mai ji ne Masani.

-Na'am,hakika abin da duk yake cikin sammai da abin da yake cikin kassai na Allah ne. wadanda suke bauta wa wani ba Allah ne.Wadanda suke bauta wa wani ba Allah ba gumaka ne suke bi. Ba abin da kuwa suke bi sai mummunan zato,kuma baa bin da suke yi sai karya.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka:

Na farko: Daya daga cikin shirye-shiryen makiya da makircinsu aikata kisan gilla kan shugabannin addinikuma Allah ya yi lakawalin ba za su ci nasara ba .

Na biyu: kar mu yi zaton wadanda suka riki wani ba Allah ba suna da hujja da dalilin yin hakan duk wani tafarki ba na Allah ba bata ne.

To madallah yanzu za mu saurari aya ta 67 kamar haka:

هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ لِتَسْكُنُواْ فِيهِ وَالنَّهَارَ مُبْصِراً إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ{67}

Shi ne wanda Ya sanya muku dare don ku samu nutsuwa, rana kuma don hsakakawa. Hakika a wannan ba shakka akwai ayoyi ga mutane masu ji.

Allah na yi mana muni da yin tunani kan yadda aka tsara dare da rana na tafiya ba tare da karo da junansu ba da hakan ke tabbatar da kudura da irada da tsarin wanda ya halicce su a wasu ayoyin na kur'ani daban daban a bayyana dare a matsayin kwanciya da hutu ga mutum da hakan ke nufin kwanciya da hutun gangar jiki ta hanayr yin barci da kuma ta wannan hanya ake iya samin hutun ruhi ko ta hanyar yin addu'o'I da salloli da sauran ibadodi a cikin daren.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: Ba wani lamari ne haka kwacam ya abku aka halicci wannan duniya a'a wani abu ne tsararre da ke karkashin buri da hikima daga Allah.

Na biyu:ta hanyar sauraren ayoyin Allah da jawaban jagororin addini mutum na fahimtar ilimi da kudura da hikimae Allah madaukakin sarki.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 68-73 (Kashi Na 331)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani bayan da muka surari aya ko ayoyi daga cikin ayoyin surorin Alkur'ani mai girma ,domin yin dubi a cikin irin nasihohin da ke tattare da irin wannan ayoyi,kuma shi Kur'ani daga aya ta farko harzuwa aya ta karshe da ke cikinsa nasiha ce illa iyaka mu yi aiki da irin wadannan nasihohi da hakan zai cece mu duniya da lahira ma'ana a wannan duniya mu samu yin rayuwa ta gari cikin sauki da wadata yayin da idan kuma muka mutu da tayar dam u a ranar Kiyama mu samu sakamako na alheri na gidan Aljanna da aka yi wa wadanda suka aika ta alheri tanadi. Da fatar Allah ya sa mu dace duniya da lahira amin.

Za mu fara da sauraren karatun aya ta 68 zuwa 70 a cikin suratul Yunus kamar haka:

قَالُواْ اتَّخَذَ اللّهُ وَلَداً سُبْحَانَهُ هُوَ الْغَنِيُّ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَات وَمَا فِي الأَرْضِ إِنْ عِندَكُم مِّن سُلْطَانٍ بِهَـذَا أَتقُولُونَ عَلَى اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{68} قُلْ إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ لاَ يُفْلِحُونَ{69} مَتَاعٌ فِي الدُّنْيَا ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ الْعَذَابَ الشَّدِيدَ بِمَا كَانُواْ يَكْفُرُونَ{70}

68-Suka ce Allah yana dad a tsarki ya tabbata gare Shi.Shi Mawadac ne daga da.abin da yake cikin sammai da abin da ke cikin kassai nasa ne. Ko kuna da wata hujja ne game da wannan? Yanzu kwa rika fadar abin dab a ku sani ba game da Allah.

69- Ka ce da su : Hakika wadanda suke kaga wa Allah karya ba za su rabauta ba.

70-Jin dadin ne kawai a cikin duniya sannan kuma gare Mu ne makomarsu take,sannan mu dandana musu azaba mai tsanani saboda abin da suka zamanto suna kafircewa da shi.

Daya daga cikin akidun na kafirci da shirka da al'ummomi da mutanan da suka gabata har zuwa yau wasu ke aikatawa da yin riko da wannan mummunar akida it ace ta danganta Da ga Allah kamar yadda mushrikai ke cewa mala'iku yaya mata ne ga Allah a wani lokaci baya a cikin tarihi yahudawa na danganta annabi Uzair da dan allah yayin da Kiristoci su ma ke cewa Annabi Isa (AS) dan Allah ne alhali Allah ba ya da mata balantana a danganta shi da da na biyu baya da da kuma na uku duk wani da aka halitta ba zai iya zama dan Allah ba domin da dole ya zama daga jinsin uba da uwa ;Allah kuwa ba shi da makamanci.Alkur'ani ya karyata irin wadannan maganganu maras asasi balantana tushe da cewa: masu irin wannan magana za su bayar da amsar abin da suke rayawa a ranar tashin kiyama da yin karya ga Allah.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: Allah ba ya bukatuwa da wani abu balantana ya bukatu dad a kuma ba ya bukatuwa da aboki ko mata ko da .

Na biyu:Duk wani abu a wannan duniya ragegge ne idan an kwatamta shi da na lahira.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 71 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ نُوحٍ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكُم مَّقَامِي وَتَذْكِيرِي بِآيَاتِ اللّهِ فَعَلَى اللّهِ تَوَكَّلْتُ فَأَجْمِعُواْ أَمْرَكُمْ وَشُرَكَاءكُمْ ثُمَّ لاَ يَكُنْ أَمْرُكُمْ عَلَيْكُمْ غُمَّةً ثُمَّ اقْضُواْ إِلَيَّ وَلاَ تُنظِرُونِ{71}

71: Ka kuma karanta musu labarin Annabi Nuhu ,lokacin da ya ce da mutanensa: Ya ku mutanena,idan zamana a cikin ku da kuma gargadina da nake muku da ayoyin Allah sun dame ku,to ni fa ga Allah ne kawai na dogara,sai ku tattara al'amarinku ku da abokan tarayyarku,sannan kada al'amarinku naku ya zama a boye,sannan ku zartar da shi a gare ni, kada kuma ku saurara mini.

Annabi Nuhu (AS) yana daga cikin manyan Annabawa makusanta wanda ya yi shekaru masu yawa yana kiran mutanansa zuwa ga kadaita Allah da bauta amma sai yan kadan suka yi imani da shi yayin da yawancin mutanan al'ummarsa suka kafirce da ci gaba da yin riko da hanyarsu ta shirka. Wannan ayar an sabkar da ita a Makka a daidai lokacin da zukatan mumunai ke cikin kumci da ganin wahalhalun rayuwa da karfafa masu karfin guiwa da ci gaba da yin imani da Allah kuma Allah yana tare da su da taimaka masu kamar yadda Annabi Nuhu (AS) ya yi tsayin daka da jurewa barazana da makircin mushrikai shi daya kuma bai ga karfi da yawansu ba da ce masu: dukanku ku taru guri daya ku da daukan niya da kudurta abin da kuka yi niya kaina ba ruwana domin ni na yi dogaro da tawakkali da Allah kuma da karfi da kudurarsa na dogara.

A cikin wannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka:

Na farko : tarihin abubuwan da suka wakana a baya ya fayyace mana gaskiya da karya da haskaka mana rayuwa.

Na biyu:Imani da cimma burin e babban madogarar Annabawa a tafarkinsu na gwagwarmaya da Mushrikai da kuma masu kiyayya da su har zuwa lokacin da za su yi shahada kan tafarkin Allah.

Yanzu kuma sai sura ta 72 da 73 a cikin suratul Yunus kamar haka:

فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَمَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى اللّهِ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ{72} فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيْنَاهُ وَمَن مَّعَهُ فِي الْفُلْكِ وَجَعَلْنَاهُمْ خَلاَئِفَ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ{73}

72-To idan kuka ba da baya ga gargadina to ban tambaye ku wani lada ba ,ladana yana ga allah ,an kuwa umarce ni da in kasance cikin musulmi.

73- Sai suka karyata shi sai Muka tserar da shi da wadanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa ,Muka kuma mayar da su shuwagabanni,kuma muka nutsar da wadanda suka karyata ayoyinmu. To duba ka ga yadda karshen wadanda aka yi wa gargadi ya kasance.

Annabawa da manzonnin Allah sun sadaukar da rai da rayuwarsu bas u fargaba a hanyarsu ta isar da sakon Allah kuma bas u da gwadayin kudi da dukiyar wannan duniya ko wani sakamako daga mutane saboda haka suke tsage gaskiya kan kowa da cewa: kar ku yi zaton idan ba ku yi imani dam u ba kun cutar dam u a'a ba haka ban e mu bam u neman wani lada a gare ku kawai mu muna aiki ne da nauyin da aka daura mana na isar da sako.A karshen wannan aya tana nuni da karshen aikin makiya da cewa:alokacin sabkar azaba daga Allah da ruwan dufana ya mamaye ko ina kowa ya hallaka sai wadanda suka yi imani da Annabi Nuhu (AS) wadanda suka shiga cikin jirgin ruwan day a kera kuma sun e suka ci gaba da rayuwa yayin da wadanda suka kafircewa Annabi Nuhu (AS) suka hallaka.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: duk wanda ba ya neman sakayya daga mutane a hanyar yada addini da kiran mutane da su yi riko da tafarkin Allah zai ci nasara ko shakka babu.

Na biyu: Imani da Allah da tsayin daka kan hanyar Allah zai ci nasara kan kafirai da kafa hukumar gaskiya.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 74-78 (Kashi Na 332)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani bayan da muka surari aya ko ayoyi daga cikin ayoyin surorin Alkur'ani mai girma, domin yin dubi a cikin irin nasihohin da ke tattare da irin wannan ayoyi,kuma shi Kur'ani daga aya ta farko harzuwa aya ta karshe da ke cikinsa nasiha ce illa iyaka mu yi aiki da irin wadannan nasihohi da hakan zai cece mu duniya da lahira ma'ana a wannan duniya mu samu yin rayuwa ta gari cikin sauki da wadata yayin da idan kuma muka mutu da tayar dam u a ranar Kiyama mu samu sakamako na alheri na gidan Aljanna da aka yi wa wadanda suka aika ta alheri tanadi. Da fatar Allah ya sa mu dace duniya da lahira amin.

Sai a saurari karatun ayoyi na 74 da 75 a cikin suratul Yunus:

ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِ رُسُلاً إِلَى قَوْمِهِمْ فَجَآؤُوهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤْمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ بِهِ مِن قَبْلُ كَذَلِكَ نَطْبَعُ عَلَى قُلوبِ الْمُعْتَدِينَ{74} ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَى وَهَارُونَ إِلَى فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ بِآيَاتِنَا فَاسْتَكْبَرُواْ وَكَانُواْ قَوْماً مُّجْرِمِينَ{75}

74-Sannan a bayansa annabi Nuhu Muka aiko manzanni zuwa ga mutanensu suka zo musu da ayoyi mabayyana, ba su zamanto suna gaskata abin da a da can suke karyata shi ba. Kamar haka ne Muke yumke zukatan masu shisshigi.

75- sannan daga bayansu Muka aiko Annabi Musa da annabi Haruna zuwa ga Fir'auna shi da jama'arsa da ayoyinmu,sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu ta'adda.

Wadannan ayoyi na yin nuni ne da sunnar Allah ta aiko da Annabawa da manzonni domin shiryar da mutane da cewa: dukan annabawa da manzonni ,Allah ya aiko sun e domin isar da sakonsa kuma suna dauke da mu'ujiza ne kuma mutane sun fahimci gaskiyar da ke tare da su amma saboda kafirci da kiyayya wasu sai su ki yin imani da su saboda suna son ci gaba da yada fasadi da banna a doran kasa kuma wannan shi n eke kais u ga hallaka kuma shi mutum mai mantuwa ne.misali azabar ruwan dufana kan wadanda suka kafircewa kiran Annabi Nuhu(AS) ya mamaye duniya da hallakar da kafirai sai wadanda suka yi imani da shi amma bayan haka sai wasu suka kafirce masa da aiko da wasu annabawan kamar Annabi Ibrahim ,Isma'il ,Hudu,Salihu ,Yakubu Da yusuf amma kafirai sun ci gaba da yin jayayya da su da aikata sabo da kin yin imani da su kamar yadda Annabi Musa (AS) daga cikin manyan manzonnin Allah tare dad an uwansa Annabi Haruna (AS) aka tura shi gurin Fir'auna domin kiransa zuwa ga kadaita Allah amma shi da makusantansa suka kafircewa kiran gaskiya da nuna girman kai har azaba ta abka masu da hallakar da su.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko : Allah yana turo da annabawa da manzonni domin shiryar da al'umma da mutane yayin da a dabra da haka ke bawa mutum yancin zabar abin day a ga dama babu tilastawa.

Na biyu: Gwagwarmaya da Dagutu yana daya daga cikin shirin Annabawa.Annabi Musa (AS) a farko annabcinsa ya fara gwagwarmaya da Fir'auna ne da kiransa zuwa ga yin riko da addinin Allah.

To madallah yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 76 zuwa 77 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka;

فَلَمَّا جَاءهُمُ الْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُواْ إِنَّ هَـذَا لَسِحْرٌ مُّبِينٌ{76} قَالَ مُوسَى أَتقُولُونَ لِلْحَقِّ لَمَّا جَاءكُمْ أَسِحْرٌ هَـذَا وَلاَ يُفْلِحُ السَّاحِرُونَ{77}

-Lokacin da gaskiya ta zo musu daga wurinmu sai suka ce: Hakika wannan ba shakka tsafi wato dabo ne bayyananne. -Annabi Musa ya ce: Yanzu kwa rika cewa gaskiya tsafi lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara ?.

Musa da ya ke ba su jawabi ya ce: "Shin saboda gaskiya ta zo mu ku ne ku ke kiranta sihiri? Shin wannan abin sihiri ne? Ga shi kuwa masu sihiri ba su yin nasara."

Daya daga cikin rudanin da masu adawa da annabawa su ke yi, musamman ma dai shugbanni da jagororin kafirci da shirka, su ke yi shi ne yin tuhuma ga annabawa da kuma waliyyan Allah. Kamar yadda ya zo a cikin ayoyin kur'ani kusan dukkan annabawa an tuhume su da cewa su masu sihiri wato bokanci ne, saboda su nunawa mutane cewa mu'ujizar da su ka zo da ita yaudara ce da kuma karya sannan kuma su bayyana annabawan a matsayin masu yaudara kuma masu son kare manufofin kashin kansu.

A lokacin da Fir'auna ya ga gaskiya kururu da Musa ya zo da ita sai ya bada umarnin a tara masu sihiri saboda ya nuna cewa shi( annabi Musa) da masu sihiri suna cikin sahu guda. A lokacin da annabi Musa (as) ya zamana mai fada musu cewa kawo ya zuwa yanzu ba ku ga wani sihiri da na yi ba kuma na zo da mu'ujiza ne saboda in karfafa maganar gaskiya da na ke yi, amma kuna daukata a matsayin mai sihiri ne kuma zancena a matsayin sihiri. Saboda haka kuna neman hanyar da za ku gujewa gaskiya ne kawai.

Abin da mu ke koya daga cikin wannan ayar shi ne:

1- Dole ne jagororin addini na al'umma su san cewa a tsakanin mutane da akwai wasu kungiyoyi wadanda su ke adawa da su kuma suna bayyana maganar gaskiyar da su ke yi a matsayin bata.

2- Tushen kin gaskiya da kuma tuhumar mutane ma'abota tsarki, shi ne ruhin kaucewa gaskiya da kin jininta da wasu kungiyoyin mutane su ke da su, ba wai raunin dalilin da annabawa su ke gabatarwa ba ne.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 78 a cikin wannan sura ta Yunus (AS):

قَالُواْ أَجِئْتَنَا لِتَلْفِتَنَا عَمَّا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءنَا وَتَكُونَ لَكُمَا الْكِبْرِيَاء فِي الأَرْضِ وَمَا نَحْنُ لَكُمَا بِمُؤْمِنِينَ{78}

-Suka ce : Yanzu ka zo mana ne don ka juyar da mu daga abin da muka sami iyayenmu a kansa,ku kuma kai da Haruna girman duniya ya zama naku? Mu kam ba za mu ba da gaskiya da ku ba?

Mutane da dama ba a shirye su ke ba su yi watsi da riko da akidu da al'adun iyaye da kakanni, saboda yadda su ke girmama magabatansu, suna kuma zaton cewa abinda magabatansu su ka fada shi ne daidai kuma babu wanda ya ke da hakkin ya fadi wani abu da ya saba musu. Alhali girmama magabata baya nufin mika kai ido rufe ga dukkan akidunsu da kuma nuna bakin kishi da bai dace ba akansu ba tare da dogaro da dalili na hankali ba, kuma yi wa maganganun magabata rikon danko ba abu ne da ya dace ba. Masu adawa da annabawa ba ashirye su ke su saurari da kuma karbar gaskiya ba saboda rikon da su ka yi da bautar gumaka da iyaye da kakannunsu su ke yi.

Abin da mu ke koya daga wannan aya shi ne:

1- Kwaikwayon ayyukan magabata ido rufe da nuna bakin kishi akan akidunsu suna daga cikin manyan dalilan da su ke sa mutane nuna adawa da sakonnin annabawa.

2- Kiyaye al'adun magabata, yana da banbanci da yin biyayya ga akidunsu marasa inganci. A wannan lokacin ana kiyaye da kare tsaunukan gine-gine na Fir'aunonin Masar, amma kuma mutane ba su amince da zaluncin Fir'auna ba da kuma gurbataccen tunaninsa na daukar kansa a matsayin Ubangiji.

To masu saurare da wannan ne kuma muka kawo karshen lokacin da aka diba mana a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda kafin mako mai zuwa ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 79-86 (Kashi Na 333)

Jama'a masu saurare mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu nasiha da galgadi a harkokinmu na yau da kullum da suka shafi dukan bangarori kama daga akida ,tattalin arziki,siyasa da zamantakewa.Kuma matukar muka yi aiki da irin galgadi da nasihohin da ke cikin ayoyin kur'ani ko shakka babu za mu samu dacewa a rayuwarmu ta duniya da lahira da fatar Allah ya sa mu dace amin.

To madallah yanzu kuma za mu fara shirin na yau ne da sauraren ayoyi na 79 zuwa 80 a cikin surar Yunus (AS) kamar haka:

وَقَالَ فِرْعَوْنُ ائْتُونِي بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ{79} فَلَمَّا جَاء السَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَى أَلْقُواْ مَا أَنتُم مُّلْقُونَ{80}

-Fir'auna kuma ya ce: Ku zo mini da duk wani gwanin tsafi. - To lokacin da suka jefa kayan tsafinsu,sai Annabi Musa ya ce :Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne ,lallai Allah ko zai bata shi .Hakika Allah ba ya gyara aikin mabarnata.

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa : annabi Musa (as) Allah ya aika shi a farkon manzoncinsa zuwa Fir'auna da mutanansa domin ya yi kiransa zuwa ga kadaita Allah wajen bauta a dabra da haka ya intar da bani Isra'ila daga azabtarwar Fir'auna. To wadannan ayoyi na cewa ne; Fir'auna na iya kin karbar hujja da dalilai na hankali da Annabi Musa (AS) zai gabatar masa ya yi wa mu'ijizar da ya zo da ita kollon raini da kaskantawa da kwatamta ta da bokanci da tsafi hakan kuma ya yi da tattaro bokaye da masu tsafi fitattu domin kalubalantar mu'ijizar da Annabi (AS) ya zo da ita. Amma da ya ke Annabi Musa (AS) ba shi da wani shaku kan gaskiyar da ta sa ya tunkari wannan babban kafiri azzalumi sai ya bawa matsafa da bokaye da su fara jefa abin da suka yi na tsafi da nunawa mutane da hakan zai ba su damar yin hukunci kan mai gaskiya.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka na farko: Dagutu da azzalumai domin isa ga mummunan burinsu na amfani da mutane masu ilimi da kwarewa kan wani abu domin amfani da ilimi da kwarewarsu wajen cimma burinsu.

Na Biyu :Annabawa da manzonni sun yi imani da hanya madaidaiciya da goyan bayan Allah dari bisa dari saboda haka suke yin bayani da magana cikin nucuwa ba fargaba da yin gwagwarmaya kan makiya Allah.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 81 da 82 a cikin wannan sura ta Yunus (AS)

فَلَمَّا أَلْقَواْ قَالَ مُوسَى مَا جِئْتُم بِهِ السِّحْرُ إِنَّ اللّهَ سَيُبْطِلُهُ إِنَّ اللّهَ لاَ يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ{81} وَيُحِقُّ اللّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ{82}

-To lokacin da suka jefa kayan tsafinsu ,sai Annabi Musa ya ce: Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne'Lallai Allah ko zai bata shi. Hakika Allah ba ya gyara aikin mabarnata. -Allah yana tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa mabarnata sun ki.

Wadannan ayoyi na nunin ne da cewa Annabi Musa (AS) ya kira yi mutanasa da cewa ya ku mutane, idan kun yi imani da Allan da ya halicce ku to ku mika wuya zuwa gare Shi. Da Yin tawakkali a gare shi shi kadai.Sai suka amsa masa da cewa: mun yi tawakali da Allah,amma sai Allah ya jarrabe mu da azzalumai da masu banna a doran kasa da zalunci kuma amma mu muna fatar rahamar Allah ta kubutar da mu daga sharrin gungun mutane kafirai. Domin fuskantar azabtawa da zalucin Fir'auna ,Annabi Musa (AS) ya bukaci mutanasa da su yi tawakali da Allah da yin imani da Shi kuma shi ne majibincin lamarinsu . Wadanda suka yi imani da Annabi Musa (AS) jin bayaninsa ke da wuya sai suka amsa masa da cewa; Mu bam u da wani face Allah da muka yi imani da yin tawakalli da shi kuma mun mika wuya da neman taimakonsa ya kubutar dam u daga sharri dagutu da azzalumai kuma kafirai su nisanta da mu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko:Mumunai daya dayar hanyar da suke amfani da ita wajen fuskantar matsaloli da wahala it ace dogaro da Alla domin ta hanyar dogaro da Shi ne da mika wuya a gare Shi matsalolin da suke fuskanta su samu waraka da nucuwa .

Na biyu: daya daga cikin hanyar kubuta daga matsaloli ita ce yin addu'a da kyaukyawar fata da Allah dalili kuwa idan addu'a ba ta warware matsala da Allah ba zai umarce mud a nuna mana hanyar yin addu'a ba.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 81 zuwa 82 a cikin wannan sura ta Yunus (AS)

فَلَمَّا أَلْقَواْ قَالَ مُوسَى مَا جِئْتُم بِهِ السِّحْرُ إِنَّ اللّهَ سَيُبْطِلُهُ إِنَّ اللّهَ لاَ يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ{81} وَيُحِقُّ اللّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ{82}

To lokacin da suka jefa kayan tsafinsu ,sai Annabi Musa ya ce: Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne'Lallai Allah ko zai bata shi. Hakika Allah ba ya gyara aikin mabarnata.

Allah yana tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa mabarnata sun ki.

Wadannan ayoyi na nunin ne da cewa Annabi Musa (AS) ya kira yi mutanasa da cewa ya ku mutane, idan kun yi imani da Allan da ya halicce ku to ku mika wuya zuwa gare Shi. Da Yin tawakkali a gare shi shi kadai.Sai suka amsa masa da cewa: mun yi tawakali da Allah,amma sai Allah ya jarrabe mu da azzalumai da masu banna a doran kasa da zalunci kuma amma mu muna fatar rahamar Allah ta kubutar da mu daga sharrin gungun mutane kafirai. Domin fuskantar azabtawa da zalucin Fir'auna ,Annabi Musa (AS) ya bukaci mutanasa da su yi tawakali da Allah da yin imani da Shi kuma shi ne majibincin lamarinsu . Wadanda suka yi imani da Annabi Musa (AS) jin bayaninsa ke da wuya sai suka amsa masa da cewa; Mu bam u da wani face Allah da muka yi imani da yin tawakalli da shi kuma mun mika wuya da neman taimakonsa ya kubutar dam u daga sharri dagutu da azzalumai kuma kafirai su nisanta da mu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko:Mumunai daya dayar hanyar da suke amfani da ita wajen fuskantar matsaloli da wahala it ace dogaro da Alla domin ta hanyar dogaro da Shi ne da mika wuya a gare Shi matsalolin da suke fuskanta su samu waraka da nucuwa .

Na biyu: daya daga cikin hanayr kubuta daga matsaloli ita ce yin addu'a da kyaukyawar fata da Allah dalili kuwa idan addu'a ba ta warware matsala da Allah ba zai umarce mud a nuna mana hanyar yin addu'a ba.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 83 a cikin suratul Yunus kamar:

فَمَا آمَنَ لِمُوسَى إِلاَّ ذُرِّيَّةٌ مِّن قَوْمِهِ عَلَى خَوْفٍ مِّن فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِمْ أَن يَفْتِنَهُمْ وَإِنَّ فِرْعَوْنَ لَعَالٍ فِي الأَرْضِ وَإِنَّهُ لَمِنَ الْمُسْرِفِينَ{83}

83-To ba wanda ya bada gaskiya da Annabi Musa sai wasu yan tsiraru daga zuriyay bani Isra'ila don tsoron kada Fir'auna da mutanansa su azabtar da su.Kuma hakika Fir'auna kam ya tabbata mai girman kai ne a bayan kasa.Hakika kuma shi yana cikin masu barna.

Annabi Musa (AS) da farrkon farawa an aika shi ne zuwa ga Fir'auna da mukarrabansa don shiryar da su zuwa ga kadaita Allah da bauta kafin daga bisani ya shiga gwagwarmaya da masu siri da yaudarar jama'a da kuma ya ci nasara kansu a matsayi na uku zuwa da bani Isra'ila inda da farko matasa daga cikin al'ummarsa suka yi imani da shi kuma suna daga cikin wadanda Fir'auna ya azabtar da kuntatawa da hakan ya taimaka masu wajan karbar gaskiya da bin wanda zai shiryar da su da kubutar da su daga azabar Fir'auna.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: farkon wadanda suka yi imani da Annabi Musa sune matasa masu tsarkin zucciya.

Na biyu: hatta wadanda suke karkashin iko da mulkin Fir';auna sun yi imani da Musa da koyarwarsa.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 84,85 da kuma 86 a cikin suratul yunus:

وَقَالَ مُوسَى يَا قَوْمِ إِن كُنتُمْ آمَنتُم بِاللّهِ فَعَلَيْهِ تَوَكَّلُواْ إِن كُنتُم مُّسْلِمِينَ{84} فَقَالُواْ عَلَى اللّهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا لاَ تَجْعَلْنَا فِتْنَةً لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ{85} وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ{86}

84- (Annabi) Musa kuma yace: "Yak u mutanena, idan har kun bada gaskiya ga Allah, a gareshi kawai zaku dogara in kun kasance musulmai"

85- Sai suka ce: "Ga Allah muka dogara. Ya ubangijinmu, kada ka sanya mu wurin da fitinar azzaluman mutane za ta sauka.

86- "Kuma ka tserar da mu da rahamarka daga mutane kafirai".

Musa y ace wa mutanansa yak u mutane idan kun yi imani da Allah da mika wuya a gare shi sai ku yi tawakkali da shi sai suka ce" mun yi tawakkali da shi kuma Ubangijinmu zai azabtar da kafirai da masu girman kai yayin dam u kuma za mu gamu da rahama da lutifinsa da kubuta daga sharrin kafirai na azabtar da mu da kuntata mana da hana mu yin imani da bautawa Allah shi kadai.haka mutanan Annabi Musa (AS) suka yi imani da shi da kuma yin tawakkali da Allah

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka; Na farko: Mumuni a kullum yana tawakkali da Allah idan yana cikin kunci da abkuwa wani lamari kuma yana dogaro da Allah ne wajan yayaye masa matsalolinsa.

Na biyu: Daya daga cikin hanyoyin fita daga kumci yin addu'o'i domin addu'a it ace takobin mumuni.

To masu saurare da wannan ne kuma muka kawo karshen lokacin da aka diba mana a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda kafin mako mai zuwa ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 87-92 (Kashi Na 334)

Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani da bin diddigin nasihohin da galgadin da ke tattare a cikin irin wadannan ayoyin kur'ani mai girma . Har ila yau duk wani wanda zai yi riko da ayoyin kur'ani ko shakka babu ba zai tabe ba duniya da lahira kuma babu wani abu da yafi dacewa mutum musamman musulmi ya yi riko da shi a wannan duniya da samun tsira a gobe kiyama kamar Alkur'ani mai girma da dokaka.Allah ya sa mu kasance daga cikin wasu riko da aiki da kur'ani a kullum kuma a ko da yaushe amin.

Za mu fara shirin na yau da sauraren aya ta 87 a cikin suratul Yunus:

وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوْمِكُمَا بِمِصْرَ بُيُوتاً وَاجْعَلُواْ بُيُوتَكُمْ قِبْلَةً وَأَقِيمُواْ الصَّلاَةَ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ{87}

87- Kuma muka yi wa (Annabi) Musa wahayi shi da dan'uwansa cewa: "Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla, ku tsaida sallah," Ka kuma yi ma Muminai albishir (da samun nasara).

Annabi Musa(AS) bayan da ya kubutar da bani Isra'ila daga azabtarwar Fir'auna an umarce shi day a ginawa mutanansa wani gari da zama a wani guri domin rayuwa amma gidajan da za su gina su rika kollon juna ba wai kowa ya gina nashi babu tsari wannan ya kalli gabas wancan ya kalli yamma wani ya kalli arewa ko surkurwa ko kudu ba tsari: Gidanjan da suka gina karkashin umarnin Allah zai kawo masu saukin rayuwa da gudanar taro na bai daya cikin sauki da kuma fahimtar duk wani hadari da zai sami daya da daukan mataki na bai daya a rayuwar zamantake kuma idan Fir'auna ya so kai masu harin yi masu kisan kiyashi za su iya fuskantasa.Sai dai wasu masu tafsiri na cewa ne wannan umarni sabo da kibla don yin salla da ibadodi.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:Annabawa suna damuwa da halin da mutanansu ke ciki suna daukan matakan taimaka masu.

Na biyu:bawa abubuwa na dukiya muhimmanci matuka gayya na sawa a manta da Allah.

Sai kuma karatun aya ta 88 da 89 a cikin suratul Yunus:

وَقَالَ مُوسَى رَبَّنَا إِنَّكَ آتَيْتَ فِرْعَوْنَ وَمَلأهُ زِينَةً وَأَمْوَالاً فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِكَ رَبَّنَا اطْمِسْ عَلَى أَمْوَالِهِمْ وَاشْدُدْ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَلاَ يُؤْمِنُواْ حَتَّى يَرَوُاْ الْعَذَابَ الأَلِيمَ{88} قَالَ قَدْ أُجِيبَت دَّعْوَتُكُمَا فَاسْتَقِيمَا وَلاَ تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ الَّذِينَ لاَ يَعْلَمُونَ{89}

88- (Annabi) Musa kuma y ace: "Ya Ubangijinmu, hakika ka baiwa Fir'auna da mutanensa kayan ado da kuma dukiyoyi a rayuwar duniya; Ya Ubangijinmu, don su batar (da jama'a) daga hanyarka; ya Ubangijinmu, ka kuma kekasar da zukatansu ba za su bada gaskiya ba har sai sun ga azaba mai radadi".

89- (Allah) Ya ce: "Hakika an amsa addu'arku, sai ku tabbata (a kan shiriyarku, kada ku bi hanyar wadanda ba sa sanin gaskiya).

Annabi Musa(AS) ya roki Allah da ya lalata dukiyar Fir'auna da Allah ya ba shi mai tarin yawa domin haka zai iya sawa ya yi sanyi a hanyarsa ta yin riko da kafirci da jayayya da Allah da kuma matakan day a ke dauka na nuna girman kai da tagwawa da wuce gonad a iri saboda yanada dukiya da wadata amma yana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba :Duk tsawon shekarun da Annabi Musa (AS) ya share yana kiran fir'auna da mukarrabansa domin yin imani da kadaita Allah da bauta ya ki ,Annabi Musa(AS) ya tsine masa kuma karkashin ruwaye sai bayan shekaru arba'in wannan tsinuwa ta fada masa da hallakar da fir'auna a ruwan maliya.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: kudi da mulki shi kadai baa lama b ace ta lutifi da inaya daga Allah domin Allah ya bawa kafirai dukiya da wadata.

Na biyu:A kullum mu rika addu'ar ruguza azzalumai kuma mu hada da kokarinmu.

Sai a saurari karatun ayoyi na 90 zuwa 92:

وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ وَجُنُودُهُ بَغْياً وَعَدْواً حَتَّى إِذَا أَدْرَكَهُ الْغَرَقُ قَالَ آمَنتُ أَنَّهُ لا إِلِـهَ إِلاَّ الَّذِي آمَنَتْ بِهِ بَنُو إِسْرَائِيلَ وَأَنَاْ مِنَ الْمُسْلِمِينَ{90} آلآنَ وَقَدْ عَصَيْتَ قَبْلُ وَكُنتَ مِنَ الْمُفْسِدِينَ{91} فَالْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ آيَةً وَإِنَّ كَثِيراً مِّنَ النَّاسِ عَنْ آيَاتِنَا لَغَافِلُونَ{92}

90- Muka ketarar da bani-israila kogi, sai Fir'auna ya bi su shi da rundunarshidon zalunci da ta'addanci, har sai lokacin da nutsewa ta riske shi sannan ya ce: "Na ba da gaskiya cewa babu wani sarki sai wanda bani'israila suka ba da gaskiya da shi, ni kuma ina cikin wadanda suka musulunta."

91- Sai yanzu kuma , bayan da can ka ki , ka kuma kasance cikin masu barna?

92- To a yau kan za mu tserar da jikinka kawai don ka zamanto aya ga wadanda za su biyo bayanka. Lallai kuwa yawancin mutane masu gafala ne ga lura da ayoyinu.

Wadannan ayoyi na bayani ne kan yadda aka amsawa Annabi Musa (AS) addu'o'insa da cewa: a daidai lokacin da rundunar fir'auna da shi kansa suka biyo ku domin murkushe ku sai muka sanya hanyoyi a kan ruwan maliya kuka bi kuka wuce lamin lafiya amma Fir'auna da rundunarsa kuma hallakar da su da nutsar da su a cikin wannan ruwa na maliya kawai sai gangar jikinsa da muka sa ruwa ya fito da ita domin zama aya da darasi ga sauran a tarihi. Abin mamaki a nan shi ne abin da Annabi Musa (AS) ya yi hassashe kan Fir'auna ya wakana a karshen rayuwarsa lokacin day a ga mutuwa ba makawa sai y ace: na yi imani da Allah amma Allah bai karbi wannan imani nasa ba domin bai yi imani ba said a ya ga mutuwa ba don Allah .

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda uku kamar haka; Na farko: a gwagwarmaya da Daguti sai mu yi dogaro da Allah domin ba zai taba barinmu ba duk kunci da wahalar da muka shiga sai kubutar da mu a wannan duniya ko a lahira.

Na biyu: Idan muka yi riko da hanayr Allah da yin tsayin daka za mu ci nasara kan ma'abuta girman kai da danniya.

Na uku: alamaomin mutane da abubuwan da suka wakana a baya a tarihi yana zama darasi ga na gaba.

To masu saurare da wannan ne kuma muka kawo karshen lokacin da aka diba mana a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda kafin mako mai zuwa ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 93-97 (Kashi Na 335)

Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani da bin diddigin nasihohin da galgadin da ke tattare a cikin irin wadannan ayoyin kur'ani mai girma . Har ila yau duk wani wanda zai yi riko da ayoyin kur'ani ko shakka babu ba zai tabe ba duniya da lahira kuma babu wani abu da yafi dacewa mutum musamman musulmi ya yi riko da shi a wannan duniya da samun tsira a gobe kiyama kamar Alkur'ani mai girma da dokaka.Allah ya sa mu kasance daga cikin wasu riko da aiki da kur'ani a kullum kuma a ko da yaushe amin.

Za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 93 a cikin suratul Yunus:

وَلَقَدْ بَوَّأْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مُبَوَّأَ صِدْقٍ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ فَمَا اخْتَلَفُواْ حَتَّى جَاءهُمُ الْعِلْمُ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِي بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ{93}

93- Hakika mun sanya bani-israila a kyakkyawan matsayi na gaskiya, muka kuma arzuta su abubuwa dadada na halal. To kawunansu ba su tashi rabuwa ba har sai lokacin ilimin shara'a ya zo musu. Hakika Ubangijinku zai yi hukunci tsakaninsu ranar alkiyama game da abin da suka kasance suna sabani a kansa.

A wannan ayara Allah yana yin bayani kan ni'imomin day a yi wa bani Isra'ila da cewa: bayan shekaru suna gudun hijira mun bas u yanki mai ruwan sha mai kyau da iskar shaka da abincin da za su ci da mallaka masu arziki amma a maimakon su yi mana godiya da bin umarni Allah sai suka samara da sabani a tsakaninsu to su sani duk hanayr da mutum ya rika zai bada amsa a babbar kotun ranar tashin kiyama.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:A koyarwar Annabawa bayan bangaren ma'anawiya suna kula da bangaren rayuwar mutane ta yau da kullum.

Na biyu: sabani da banbance bambance ya samo asali daga nisantar mutane daga koyarwa ta Allah da kafircewa ni'imomin Allah.

Yanzu kuma sai a saurari ayoyi na 94 da 95

فَإِن كُنتَ فِي شَكٍّ مِّمَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ فَاسْأَلِ الَّذِينَ يَقْرَؤُونَ الْكِتَابَ مِن قَبْلِكَ لَقَدْ جَاءكَ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ{94} وَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِ اللّهِ فَتَكُونَ مِنَ الْخَاسِرِينَ{95}

94- To idan kana tababa game da abin da muka saukar maka to sai ka tambayi wadanda suke karanta littafi gabaninka. Hakika ta zo maka daga Ubangijinka; to kada ka zama daga cikin masu kokwamto.

95- Lallai kuma kada ka kasance daga cikin wadanda suka karyata ayoyin Allah, sai ka zamo daga tababbu.

Wadannan ayoyi na Magana ne ga masu shakku kan gaskiyar ma'aikin Allah da cewa: idan suka yi dubi a cikin littatafan da aka sabkar za su ga labarin ma'aikin Allah da kuma labaran al'ummomin da suka gabata da kur'ani ya ambato hadda labarin bani isra'ila a cikin da hakan zai tabbatar mana da wannan kur'ani littafi ne daga Allah. To ku sani cewa shakku da karyatawa bayan hujjoji zai nisanta mutum daga tafarkin shiriya kuma haramin ne karyatawa bayan gamsuwa kan gaskiyar lamarin.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: shakku wani abu ne na dabi'a da kan iya samin kowa amma abu mia muhimmancin samin yakini bayan shakku .

Na biyu:idan mutum ya dauwama kan shakku da kwankwato zai kai shi ga fadawa kan tafarkin karyata gaskiya.

Sai a kara gyara zama domin sauraren karatun ayoyi na 96 da 97 a cikin wannan sura ta Yunus:

إِنَّ الَّذِينَ حَقَّتْ عَلَيْهِمْ كَلِمَتُ رَبِّكَ لاَ يُؤْمِنُونَ{96} وَلَوْ جَاءتْهُمْ كُلُّ آيَةٍ حَتَّى يَرَوُاْ الْعَذَابَ الأَلِيمَ{97}

96- Hakika wadanda kalmar Ubangijinka ta hau kansu (ta zamansu 'yan wuta) bas a ba da gaskiya.

97- Ko da kuwa dukkanin ayoyi sun zo musu har sai sun ga azaba mai radadi ( Ta saukar mu).

Mutane sun rabu kashi uku wajan banbance gaskiyar addini : gungun farko shi ne wanda bai san gaskiya ba kuma bayan neman saninta.Gungu na biyu shi ne wanda bai san gaskiyar ba amma yana neman sanin ta sai kuma rukuni na uku wanda ya san gaskiyar da cewa addini yana kan gaskiya amma ba a shirye yake ba ya amince da addinin saboda kare manufarsa na jin dadin duniya da tara dukiya da matsayi. To wannan ayar tana Magana ne kan kaso na uku wadanda saboda da jayayya dab akin kafirci zucciyarsu ta kekashe bas u karbar musulunci da yin imani to irin wadannan mutane za su gamu da fushin Allah kuma bas u yin imani da Allah sai sun ga azaba da idanunsu lokacin za su yi imani da mika wuya.Irin wadannan mutane duk wani dalili na hankali bas u saurara matsalarsu it ace son zucciya da ke hana su fahimtar gaskiya da binta.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka; Na farko:Kar mu yi zaton dukan mutane su yi imani domin sabo da fasadi na daga cikin dalilan da ke hana yin imani da karbar gaskiya.

Na biyu: ko ba jima ko ba dade hatta mafi girman kai da kafirci zai yi imani da gaskata abin da yake karyata amma a daidai lokacin da yin hakan ba shi da wani amfani.

To masu saurare da wannan ne kuma muka kawo karshen lokacin da aka diba mana a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda kafin mako mai zuwa ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 98-100 (Kashi Na 336)

Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani da bin diddigin nasihohin da galgadin da ke tattare a cikin irin wadannan ayoyin kur'ani mai girma . Har ila yau duk wani wanda zai yi riko da ayoyin kur'ani ko shakka babu ba zai tabe ba duniya da lahira kuma babu wani abu da yafi dacewa mutum musamman musulmi ya yi riko da shi a wannan duniya da samun tsira a gobe kiyama kamar Alkur'ani mai girma da dokaka.Allah ya sa mu kasance daga cikin wasu riko da aiki da kur'ani a kullum kuma a ko da yaushe amin.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 98 a cikin suratul Yunus (AS) kamar haka:

فَلَوْلاَ كَانَتْ قَرْيَةٌ آمَنَتْ فَنَفَعَهَا إِيمَانُهَا إِلاَّ قَوْمَ يُونُسَ لَمَّا آمَنُواْ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ الخِزْيِ فِي الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَى حِينٍ{98}

Baba wasu mutane na wata alkarya da suka bada gaskiya,sannan imaninsu ya amfane su,sai fa mutanen Annabi Yunusa,lokacin da suka bada gaskiya sai Muka yaye musu azabar wulakanci a rayuwar duniya,Muka kuma jiyar da su dadi har zuwa wani lokaci iyakantacce.

Kamar yadda muka yi bayani a shirye-shiryen da suka gabata cewa sunnar Allah ce ta bawa mutane dama da lokaci da zai kais u da yin tuba da yin nadama da gyara kura-kuransu ta hanyar yin ayyuka na alheri da za su wanke munanan ayyuka da suka aikata a baya.To sai dai abin sani a nan wannan dama da jinkirtawa da Allah yake yi mana, rangwame ne da lokacinsa yana kawo karshe ne da duk lokacin da mutuwa ta riski mutum da lokacin da azabar Allah ta sabka kan mutane ,to a irin wannan lokaci ko yin imani ko yin tuba bas u da wani amfani,Dalili wannan tuba da imani da wani zai yo a wannan lokacin b ata da kima da matsayi domin ta tsoron azaba ba ne ba don Allah da Annabinsa ba,alhali ana son mutum ya yi imani da tuba kan zabinsa ba tilastawa. Wannan sunnar Allah ba wai kawai ta shafi mutum ban e a'a hatta gungu da al'umma haka ne tana shafar su. A tsakanin al'ummomi kawai al'ummar Annabi Yunus (AS) ne lokacin da mutanan lokacinsa suka ga alamun sabkar azaba babu makawa sai suka mika wuya da yin imani da Allah day a bas u wata dama a nan gaba ta su tuba kamar yadda ya zo a tarihi a tsawon shekaru masu yawa da Annabi Yunsu (AS) ya yi yana wa'azi da kokarin shiryar da al'ummarsa da aka turo shi don shiryar da su kawai mutane biyu ne suka yi imani da shi , ganin haka a karshen rayuwarsa guiwar ta yi kasa na burin ganin ya shiryar da mutane sai ya yi addu'ar ganin Allah ya kubutar da shi daga irin wadannan mutane kafirai.Kuma bisa al'ada addu'ar Annabawa (AS) karbabba ce kan haka azaba za ta sabka. Sai dai wani mutum mai hikima masani mai hangen nesa daya daga cikin mutanan biyu da suka yi imani da Annabi Yunus (AS) ganin wannan addu'a ta Annabi Yunus (AS) sai ya tafi gurin mutanan yana ma ice masu: ku saurari sabkar Azabar Allah idan kuna son rahamar Allah ta shafe ku ku fice daga cikin gari zuwa wajensa kuma ku kebe kananan yara daga cikinku kukan rrabuwa da uwayensu da shaukin saduwa da uwayensu mata a dabra da haka ku tuba da yin nadama da ayyukan da kuka aikata a baya da neman afuwar Allah ,la'alla wannan ya sa Allah ya tausaya maku To haka mutane suka yi day a sa Allah ya jinkirta azaba shi ma Annabi Yunus (AS) ya koma cikin al'ummarsa.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu:

Na farko: a tsakanin al'ummomin da suka gabata kawai al'ummar annabi Yunus (AS) ne suka tuba da yin imani a daidai lokacin da azaba ke gaf da sabka.

Na biyu; wannan yana fahimtar da mu cewa; makomar mutane tana hannunsu suna iyawa ta hanyar addu'a da nadamarsu ko aiki da hakan zai kawar da bala'i inda rahamar Allah za ta sabka.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 99 a cikin wannan sura ta Yunus (AS) kamar haka:

وَلَوْ شَاء رَبُّكَ لآمَنَ مَن فِي الأَرْضِ كُلُّهُمْ جَمِيعاً أَفَأَنتَ تُكْرِهُ النَّاسَ حَتَّى يَكُونُواْ مُؤْمِنِينَ{99}

99- Da Ubangijinka Ya so lallai da duk wadanda suke bayan kasa sun bad a gaskiya gada dayansu.Shin kai ne kake tilasta wa mutane har su zama muminai?.

Daya daga cikin abubuwan da Allah ya lazimtawa kansa shi ne shiryar da mutane kan tafarki na gaskiya amma Allah bai zabi ya shiryar da bayunsa ba wannan hanya ta gaskiya da imani da shi ta hanyar tilastawa a'a ya bas u zabi ne ko su bi hanyar shirya da samun tsira ta hanyar yin imani da aikata ayyukan alheri da ganin sakamakon ayyukan da suka aikata duniya da lahira ko kuma su zabi hanyar bata da tabewa duniya da lahira wato hanyar kafirci da shurka da ayyuka mummunan aiki. Kuma haka lamari yake a dabi'ance duk abin da mutun ya aikata da zabinsa shi ne zai girbe da ganin sakamakonsa. Da A ace Allah ya nunawa dan adam hanyar madaidaiciya amma duk da haka ya ba shi zabin zabar hanyar da yaga dama da zabinsa. Idan mutum ya ga dama ya bin tafarkin Annabawa da manzonni ba tare da takura masu ba ko kuma su zabi hanyar kafirci abin kama saboda haka Allah ya ma huduba da cewa: ba dole ba mu yi tsamna da jiran cewa za a tilasta mana bin hanyar imani. Babu tilastawa a bangaren akida.

A cikin wannan aya za mu iya ilmanta da fahimtar abubuwa guda biyu;

Na farko:imani na karkashin zabi shi ne ke da daraja da matsayi ba wai imani da ke karkashin tilasta da matsi ba bai imani na hakika.

Na biyu : ko wane ma'aiki himmarsa it ace shiryar da jama'a da samun kwanciyar hankali daga Allah ta wannan hanya. Da fatar Allah ya bam u ikon shiryar da ko da mutum daya ne a kan tafarkin Allah da manzonsa amin.

Sai kuma aya ta 100:

وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَن تُؤْمِنَ إِلاَّ بِإِذْنِ اللّهِ وَيَجْعَلُ الرِّجْسَ عَلَى الَّذِينَ لاَ يَعْقِلُونَ{100}

100- Ba zai yiwu wani rai ya bad a gaskiya ba said a yardar Allah,yana kuma sanya azaba ne a kan wadanda bas a aiki da hankali.

Suratu Yunus, Aya Ta 101-106 (Kashi Na 337)

Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani da bin diddigin nasihohin da galgadin da ke tattare a cikin irin wadannan ayoyin kur'ani mai girma . Har ila yau duk wani wanda zai yi riko da ayoyin kur'ani ko shakka babu ba zai tabe ba duniya da lahira kuma babu wani abu da yafi dacewa mutum musamman musulmi ya yi riko da shi a wannan duniya da samun tsira a gobe kiyama kamar Alkur'ani mai girma da dokaka.Allah ya sa mu kasance daga cikin wasu riko da aiki da kur'ani a kullum kuma a ko da yaushe amin.

To madallah yanzu kuma za mu fara shirin ne da sauraran aya ta 101 da 102 a cikin suratl yunus kamar haka:

قُلِ انظُرُواْ مَاذَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا تُغْنِي الآيَاتُ وَالنُّذُرُ عَن قَوْمٍ لاَّ يُؤْمِنُونَ{101} فَهَلْ يَنتَظِرُونَ إِلاَّ مِثْلَ أَيَّامِ الَّذِينَ خَلَوْاْ مِن قَبْلِهِمْ قُلْ فَانتَظِرُواْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ{102}

101- Ka ce da su Ku yi tunanin abubuwan da suke cikin sammai da kassai na ayoyi .Ayoyin kuwa da gargadi bas a wadatar da mutanan dab a sa bad a gaskiya.

102 -Ai ba abin da suke saurare sai irin azabar da ta sami.Wadanda suka wuce kafin su .Ka ce da su Sai ku saurara,Hakika ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.

A ayoyin da suka gabata Allah madaukakin sarki na gayyatar makirai da su yi nazari da tunani a cikin halittun Allah a sammai da kassai da ganin alamomin da za su isar da su zuwa ga Mahalicci. To a cikin wannan aya Allah na cewa ne : wadanda ba a shirye suke ba su yi nazari a cikin ayoyin Allah to za su gamu da tsanani da azabar da aka yi masu tanadi saboda haka sunnar Allah take al'umma tamkar daidaikun mutane ne kowa na gamuwa da sakamakon abin da ya shibka kuma hakan ana la'akari ne da yawancin mutanan da ke rayuwa a cikin wannan al'umma. Idan yawancin mutane da ke cikin al'umma na rayuwa cikin tsari da gaskiya da sulhu to al'umma za ta rayu karkashin wannan tafarkin .To haka akasin hakan yake idan yawancin mutanan da ke rayuwa cikin wannan al'umma fasikai ne da aikata banna to al'umma za ta rayuwa cikin banna da fasadi da ganin sakamakon wannan danyan aiki ko da kuwa a cikin wannan al'umma akwai salihan bayu. Babban misali a nan shi ne abubuwan da suka faru a tarihin al'ummomin da suka gabata kamar al'ummar annabawa su Nuhu,Lut da Hudu da abin da ya faru da su ya tabbatar da wannan sunna ta Allah saboda haka manzon Musulunci da Allah ya aiko shi domin shiryar da al'umma da shaidawa mushrikan Makka cewa idan kuka bijire da juyawa wannan shirya daga Allah, to ku kwan da sanin kamarku za ta kasance daya da ta sauran al'ummomin da aka hallaka.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko: Sunnar Allah ba ta canjawa ba tare da banbanci kan wannan al'umma ko wannan mutum.

Na biyu: tarihin wadanda suka gabata madubi da abin daukan darasi ga al'umma mai zuwa.

To yanzu kuma za mu saurari aya ta 103 kamar haka;

ثُمَّ نُنَجِّي رُسُلَنَا وَالَّذِينَ آمَنُواْ كَذَلِكَ حَقّاً عَلَيْنَا نُنجِ الْمُؤْمِنِينَ{103}

-Sannan muka rika tserar da manzanninmu da wadanda suka bada gaskiya da su kamar haka ne ya zama lallai a kanmu Mu tserar da muminai.

Ayar da ta gabata tana magana ne kan sabkar azaba a wannan duniya da ke shafar kowa da kowa kafirai da mumunai ba tare da la'akari da ayyukansu na daidaiku face rayuwarsu ta al'umma amma ita wannan aya ta cewa ne : saidai wani hamzari adalcin Allah yana nan ba zai taba daidaita mai gaskiya da wanda yake kan bata da aiakata banna da sabo ba ko hada su guri daya a gobe kiyama domin yi masu azaba .A'a za a raba wanda ya aikata alheri daga cikin wadanda suka aikata lala da sabo. Duk wata al'umma za ta ganu da sakamakon aikin da ta aikata a gobe kiya kuma azaba a lahira za ta shafi kawai wadanda suka aikata sabo da wadanda suka yi shuru kan haka ba tare da sun yi kokarin hana sub a alhali sunada karfin yin haka to sune azaba da fushin Allah za su shafa . A dabra da haka mumunai za su samu kubuta daga Azaba wannan wani alkawali da tabbatacciyar sunnar Allah ce cewa wutar kunar fasikai da masu banna ba za ta shafi Mumunai ba.

A cikin wannan aya za mu iya fahimta da ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko: Mumuani na hakika hatta a wannan duniya fushin Allah bay a shafarsu domin ta ko ina zai kare su ko da kuwa suna rayuwa ne a cikin al'umma fasika.

Na biyu: makoma tana hannun mumunai ne saboda su masu fasadi hallakakku ne a daidai lokacin guda mumunai su samu tsira.

za mu sauraren aya ta 104 a cikin suratul Yunus (AS) kamar haka:

قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِن كُنتُمْ فِي شَكٍّ مِّن دِينِي فَلاَ أَعْبُدُ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللّهِ وَلَـكِنْ أَعْبُدُ اللّهَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُمْ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ{104}

- Ka ce da su Ya ku mutane ,idan kun kasance cikin kokwanto game da addinina,to ba zan bauta wa wadanda kuke bauta wa ba ba Allah ba,sai dai kuma ni zan bauta wa Allah da yake karbar ranku. An kuwa umarce ni da in zama cikin muminai.

A cikin ayoyin da suka gabata suna magana da bayani ne kan makomar Mushrikai amma ita wannan aya tana cewa ne: idan suna zaton kana shaku kan tafarkin da kake a kai ko kuma suke zaton za ka iya barin wannan tafarki da bautawa wanin Allah ba Allah to to ka tabbatar masu da cewa; ko kusa babbu wanin abin bautawa d azan bautawa face Allah madaukakin sarki kuma har abada ba zantaba yiwa gomakan da kuke bautawa wani abu makamancin haka hatta girmamawa balantana Bauta.Ni ina Bautawa Allan rayuwa da mutuwarku tana hannunsa kuma har abada ba za ku iya kubuta da hakan ba . Bugu da kari gumakan da kuke bautawa ba za su iya kubutar da ku ko tsirar da ku daga mutuwa ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:Shakku da kwankwaton wasu komin yawansu kar ya sa mu yin shakku a kwankwato a kullum mu kasance masu yin riko da hanyar gaskiya da muka yi imani da ita.

Na biyu: babu wanda ya cancanci mu bauta masa sai wanda mutuwa da rayuwarmu ke hannunsa.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 105 zuwa 106 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka;

وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفاً وَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ{105} وَلاَ تَدْعُ مِن دُونِ اللّهِ مَا لاَ يَنفَعُكَ وَلاَ يَضُرُّكَ فَإِن فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذاً مِّنَ الظَّالِمِينَ{106}

105-ma An umarce ni da cewa : Ka tsai da fuskarka ga addinin Allah madaidaici,Kada kuma ka kasance cikin mushrikai.

106-Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba,abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba,to idan kuwa ka aikata haka to hakika daga sannan ka zama cikin azzalumai.

Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa a ci baga da isar da sakon Allah madaukakin sarki ga mutane domin fahimtar mushrikai ya bayyana cewa; dole dole ku yi riko da hanya madaidaiciya wadda babu karkata a cikinta kuma babu bulbudin akidar shirka da kaucewa hanay ta kin gaskiya da nuna kiyayya kuma duk wanda ya yi riko da addinnin Allah zai samu rabo mai yawa .Amma duk wanda ya yi riko da hanyar bata ya zalunci kansa .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:

Na farko :hanya madaidaiciya tana yin daidai da Fidira ta hakika da kuma take tafiya kafada da kafada da dan adam.

Na biyu; masu hankali suna aiki ne don samun sakamako ko kuma kubuta daga cutarwa amma su gumaka bas u amfanarwa bas u kuma cutarwa ko karewa daga cutarwa saboda haka yin shirka babu alheri a cikinsa sai bata lokaci da cutar da mai yinsa.

Da fatar Allah ya kiyashe mud a aikata aikin da na sani amin. Da kuma wannan ne Ni Tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.

Suratu Yunus, Aya Ta 107-109 (Kashi Na 338)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani bayan da muka surari aya ko ayoyi daga cikin ayoyin surorin Alkur'ani mai girma ,domin yin dubi a cikin irin nasihohin da ke tattare da irin wannan ayoyi,kuma shi Kur'ani daga aya ta farko harzuwa aya ta karshe da ke cikinsa nasiha ce illa iyaka mu yi aiki da irin wadannan nasihohi da hakan zai cece mu duniya da lahira ma'ana a wannan duniya mu samu yin rayuwa ta gari cikin sauki da wadata yayin da idan kuma muka mutu da tayar da mu a ranar Kiyama mu samu sakamako na alheri na gidan Aljanna da aka yi wa wadanda suka aika ta alheri tanadi. Da fatar Allah ya sa mu dace duniya da lahira amin.

Yanzu kuma sai sauraran karatun sura ta 107

وَإِن يَمْسَسْكَ اللّهُ بِضُرٍّ فَلاَ كَاشِفَ لَهُ إِلاَّ هُوَ وَإِن يُرِدْكَ بِخَيْرٍ فَلاَ رَآدَّ لِفَضْلِهِ يُصَيبُ بِهِ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَهُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ{107}

107-Idan Allah ya dora maka cuta to ba mai yaye maka ita sai Shi,idan kuma ya nufe ka da alheri ba mai juyar da falalar tasa. Yana bayar da shi ga wadanda Ya so daga bayinsa,Shi ne kuma mai gafara Mai rahama.

A karshen ayoyin da muka karanto a shirin day a gabata Allah ya gawa ma'aikinsa day a fuskanci mushrikai da fada masu gaskiya da akidarsa ta kadaita Allah da bauta babu wani lallashi .To ita wannan ayar ci gaban hakan ne da cewa: arzikin da talauci sauki da wahalarka duk suna hannun Allah ne kuma bayansa babu wani ko wani abu da zai samara maka alheri ko cutar da kai kuma ka sani ba tare da yardarsa ba babu wani da zai iya cutar da kai ko ya cutar da wasu kuma idan Allah ya so a maimakon azabtar da wani sai ya yi masa gabata.

A cikin wannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko :Mushrikai da kafirai su sani gujewa yin imani ba yana nufin sun fice daga dukura da karfin ikon Allah duk abin da Allah ya so shi ne yake wakana.

Na biyu: Duk wani alheri da wadata da za su samu mutum daga falalar Allah ne ba wai don ya cancanta ba ne.

Sai kuma aya ta 108 a cikin suratul ta yunus kamar haka;

قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءكُمُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ فَمَنِ اهْتَدَى فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا وَمَا أَنَاْ عَلَيْكُم بِوَكِيلٍ{108}

108-Ka ce da su: Yak u mutane hakika gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku, duk wanda ya shiriya to ya shirya ne don kansa,wanda kuma ya bace to hakika ya batar da kansa ne Ni kuwa ba mai gadin ku ba ne.

A karshen wannan sura ta Yunus ma'aikin Allah yana Magana da dukan mutane da cewa: nauyin day a rataya a wuyana shi ne isar da sako da wahayin da Allah ya yi mani zuwa gare ku kuma ba ni da ikon tilasta maku yin imani da wannan tafarki na gaskiya.Ko wane daya daga cikinku karkashin zabinsa yana iya yin imani da kaiwa ga shiriya ko kuma ya zabi hanyar bata da tabewa amma ku sani kafircinku ko imaninku ba tasiri a gare ni da kuma Allan day a turo ni kuma lada da cutar imani ko kafircinku yana komawa gare kun e domin Allah baya bukatuwa da ku nima haka na isar da nauyin da aka daura mani na isar da sakonsa zuwa gare ku kuma ya rage naku.

A cikin wannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko : Allah ya kafa hujjarsa kan mutane da nuna masu hanyar gaskiya ya rage mutane su yi imani.

Na biyu:Nauyin da ya rataya kan malamai da masu yada addini shi ne isar da sakon shiriya ba tare da tilastawa ko nuna kama a gare su.

Daga karshe za mu saurari aya ta 109 a cikin wannan sura ta Yunus kamar haka:

وَاتَّبِعْ مَا يُوحَى إِلَيْكَ وَاصْبِرْ حَتَّىَ يَحْكُمَ اللّهُ وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ{109}

109-Kuma ka bi abin da aka yi maka wahayinsa,ka kuma yi hakuri har sai allah ya yi hukunci, Shi ne kuwa Fiyayyen mahukunta.

Wannan ayar na jaddada matsayin ma'aikin Allah da kuma matsayin wadanda suka yi imani da shi sahabbansa da yadda suka yi hakuri da tsayin daka zuwa lokacin da gaskiya ta yi nasara kan bata.Kuma lamari ne da ke a fili dagutu da azzalumai sun kawo cikas da matsaloli masu tarin yawa domin toshe hanayr mumunai amma mumunai suka nuna juriya da tsayin daka da yin hakuri ,Kuma Allah yana sane da ganin abubuwan da suka wakana har zuwa ranar da gaskiya da Aadalci za su yi hukumci a tsakaninsu bugu da kari hatta a wannan duniya masu tsayin daga sune za su yi nasara kan azzalumai.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu muhimmanci da ilmantuwa guda biyu kamar haka;

Na farko : mutane nada zabi ko su yi imani ko su kafirce amma kafircinsu kar ya sanya mana shakku a maimakon haka ya kara mana karfi da juriya da ci gaba da yin riko da umarnin Allah.

Na biyu: mu yi aiki da nauyin day a rataya a kanmu kar mu damu da abin da zai kasance gobe domin gobe tana hannun Allah kuma Shi ne zai yi hukumci kan ayyukan da kowa ya aikata.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani malam Lawali damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.