Quran/51

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Suratul Dhariyat

Category:Quran: Quran/50 > Quran/51 > Quran/52
1


 1. By those [ winds ] scattering [ dust ] dispersing <> Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. = Da iskõki masu naushi. --Qur'an 51:1
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

2


 1. And those [ clouds ] carrying a load [ of water ] <> Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa). = Sa'an nan da giragizai masu daukan ruwa. --Qur'an 51:2
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

3


 1. And those [ ships ] sailing with ease <> Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi. = Masu gudanar da tanadi. --Qur'an 51:3
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

4


 1. And those [ angels ] apportioning [ each ] matter, <> Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah). = Suna masu rabonsu a bisa umurni. --Qur'an 51:4
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

5


 1. Indeed, what you are promised is true. <> Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne. = Lalle abin da aka yi maku alkawari da zuwansa, gaskiya ne. --Qur'an 51:5
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

6


 1. And indeed, the recompense is to occur. <> Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne = Haqiqa ranar sakamako mai aukuwa ne --Qur'an 51:6
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

7


 1. By the heaven containing pathways, <> Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurari da sautin rediyo). = Duk da cewan an halitta sama babu aibi. --Qur'an 51:7
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

8


 1. Indeed, you are in differing speech. <> Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai saɓawa juna (game da Alƙur'ani). = Kuna ta husuma game da gaskiya. --Qur'an 51:8
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

9


 1. Deluded away from the Qur'an is he who is deluded. <> Anã karkatar da wanda aka juyar (daga gaskiya). = Masu karkatawa daga gaskiya su ne masu karkatawa. --Qur'an 51:9
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

10


 1. Destroyed are the falsifiers <> An la'ani mãsu ƙiri-faɗi. = An la'ani maƙaryata. --Qur'an 51:10
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

11


 1. Who are within a flood [ of confusion ] and heedless. <> Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci. = Wadanda suka shagala a cikin zurfin jahilci. --Qur'an 51:11
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

12


 1. They ask, "When is the Day of Recompense?" <> Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?" = Suna ƙalubalantar tsayiwar ranar sakamako. --Qur'an 51:12
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

13


 1. [ It is ] the Day they will be tormented over the Fire <> Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su. = Ranar da za a gabatar da su ga wuta. --Qur'an 51:13
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

14


 1. [ And will be told ], "Taste your torment. This is that for which you were impatient." <> (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa." = (A ce masu): "Ku dandani azaba; wannan shi ne abin da, da kuke qalubalanta. --Qur'an 51:14
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

15


 1. Indeed, the righteous will be among gardens and springs, <> Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari. = Masu taqawa su ne suka cancanci lambuna da maremari. --Qur'an 51:15
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

16


 1. Accepting what their Lord has given them. Indeed, they were before that doers of good. <> Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya su. Lalle , sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya). = Za su debi ladar Ubangijinsu, saboda da sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka. --Qur'an 51:16
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

17


 1. They used to sleep but little of the night, <> Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci. = Ba safai ba suke yin barcin dare dukanta ba. --Qur'an 51:17
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

18


 1. And in the hours before dawn they would ask forgiveness, <> Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri. = Kuma a lokutan asuba suna yin istigfari. --Qur'an 51:18
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

19


 1. And from their properties was [ given ] the right of the [ needy ] petitioner and the deprived. <> Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo. = Kaso a cikin dukiyarsu akwai hakki da suka ajiye saboda masu roqo da matalauta. --Qur'an 51:19
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

20


 1. And on the earth are signs for the certain [ in faith ] <> Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni. = Kuma a cikin qasa akwai ayoyi ga masu yaqini. --Qur'an 51:20
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

21


 1. And in yourselves. Then will you not see? <> Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba? = Da a cikin rayukanku; za ku iya gani? --Qur'an 51:21
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

22


 1. And in the heaven is your provision and whatever you are promised. <> Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari. = A cikin sama arzikinku ke fitowa, da duk abin da ake yi maku alkawari. --Qur'an 51:22
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

23


 1. Then by the Lord of the heaven and earth, indeed, it is truth - just as [ sure as ] it is that you are speaking. <> To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana, = To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da qasa, wannan gaskiya ne, kamar tabbacin gaskiya cewa kuna magana. --Qur'an 51:23
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

24


 1. Has there reached you the story of the honored guests of Abraham? - <> Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka? = Shin, labarin baqinIbrahim, wadanda aka girmama, ya zo maka? --Qur'an 51:24
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

25


 1. When they entered upon him and said, "[We greet you with] peace." He answered, "[And upon you] peace, [you are] a people unknown. <> A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!" = Sa’ad da suka ziyarce shi, suka yi “sallama” ya ce "Salam gare ku mutane baqi!" --Qur'an 51:25
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

26


 1. Then he went to his family and came with a fat [ roasted ] calf <> Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna, = Sai ya sa iyalinsa ta shirya wata maraqi tutturna. --Qur'an 51:26
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

27


 1. And placed it near them; he said, "Will you not eat?" <> Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" = Sa’ad day ya basu, ya ce, "Ba za ku ci ba?" --Qur'an 51:27
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

28


 1. And he felt from them apprehension. They said, "Fear not," and gave him good tidings of a learned boy. <> Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi. = Sai tsoro ya kama shi game da su. Suka ce, "Kada kaji tsoro," sai suka yi masa bishara da (haihuwar) yaro mai ilimi. --Qur'an 51:28
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

29


 1. And his wife approached with a cry [ of alarm ] and struck her face and said, "[I am] a barren old woman!" <> Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!" = Sai matarsa ta yi mamaki. Tana kallon takureren fuskarta: ta ce, "Ni tsohuwa ce bakarariya." --Qur'an 51:29
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

30


 1. They said, "Thus has said your Lord; indeed, He is the Wise, the Knowing." <> Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi." = Suka ce, "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Shi ne Mafi hikimah, Mai ilmi." --Qur'an 51:30
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

31


 1. [ Abraham ] said, "Then what is your business [ here ], O messengers?" <> ( Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" = (Ibrahim) ya ce, "To ina kuka nufa, ya ku manzanni?" --Qur'an 51:31
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

32


 1. They said, "Indeed, we have been sent to a people of criminals <> Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi. = Suka ce, "An aike mu ne zuwa ga mujirimai. --Qur'an 51:32
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

33


 1. To send down upon them stones of clay, <> "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom). = "Domin mu yi masu ruwan duwatsun yumbu. --Qur'an 51:33
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

34


 1. Marked in the presence of your Lord for the transgressors." <> "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin masu ɓarna." = "Wadanda aka yi wa alama daga wajen Ubangijinka, domin masu ƙetare iyaka." --Qur'an 51:34
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

35


 1. So We brought out whoever was in the cities of the believers. <> Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai. = Sa'an, nan Muka fitar da dukan wadanda suke muminai. --Qur'an 51:35
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

36


 1. And We found not within them other than a [ single ] house of Muslims. <> Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi. = Sai dai ba mu samu a cikinta ba, sai gida guda na Musulmai. --Qur'an 51:36
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

37


 1. And We left therein a sign for those who fear the painful punishment. <> Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsoron azãba, mai raɗaɗi. = Muka sa ta zama ayah, ga wadanda ke jin tsoron azaba, mai zafi. --Qur'an 51:37
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

38


 1. And in Moses [ was a sign ], when We sent him to Pharaoh with clear authority. <> Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. = Kuma ga Musa ma (akwai ayah). Sa’ad da Muka aika shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. --Qur'an 51:38
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

39


 1. But he turned away with his supporters and said," A magician or a madman." <> Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!" = Amma sai ya juya baya, a cikin girman kansa, ya ce, "Mai sihiri ne ko kuwa mahaukaci." --Qur'an 51:39
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

40


 1. So We took him and his soldiers and cast them into the sea, and he was blameworthy. <> Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. = Saboda haka, Muka azabta shi tare da rundunarsa. Muka jefa su a cikin teku, alhali kuwa shi ne wanda za a zarga. --Qur'an 51:40
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

41


 1. And in 'Aaden.wiki [ was a sign ], when We sent against them the barren wind. <> Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙeƙasasshiya a kansu. = Kuma ga Adawa ma (akwai ayah). Sa’ad da Muka aika iskar bala'i a kansu. --Qur'an 51:41
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

42


 1. It left nothing of what it came upon but that it made it like disintegrated ruins. <> Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasusuwa. = Ba ta bari kome ba, da ta zo a kanta sai da ta mayar da shi kamar rududdugaggun qasusuwa. --Qur'an 51:42
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

43


 1. And in Thamud, when it was said to them, "Enjoy yourselves for a time." <> Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci," = Kuma ga Samudawa ma (akwai ayah). Sa’ad da aka ce masu, "Ku dan more na dan lokaci." --Qur'an 51:43
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

44


 1. But they were insolent toward the command of their Lord, so the thunderbolt seized them while they were looking on. <> Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsawa ta kama su, alhali kuwa sunã kallo. = Sai suka yi tawaye ga umurnin Ubangijinsu. saboda haka, walƙiyan aradu ta nausa su, sa'ad da suna kallo. --Qur'an 51:44
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

45


 1. And they were unable to arise, nor could they defend themselves. <> Ba su kõ sãmu dãmar tsayawa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman agaji ba. = Ba su ko samu damar tashiwa ba, kuma ba agaza masu ba. --Qur'an 51:45
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

46


 1. And [ We destroyed ] the people of Noah before; indeed, they were a people defiantly disobedient. <> Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fasiƙai. = Da mutanen Nuhu a gabanin haka; su ma mugayen mutane ne. --Qur'an 51:46
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

47


 1. And the heaven We constructed with strength, and indeed, We are [its] expander. <> Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhali kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatawa. = Mun gina sama da hannunMu, kuma Mu ne za mu ci gaba da yalwatata. --Qur'an 51:47
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

48


 1. And the earth We have spread out, and excellent is the preparer. <> Kuma ƙasa Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ, = Kuma Muka sanya qasa ta zama wurin rayuwa; madaidaicin fasali. --Qur'an 51:48
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

49


 1. And of all things We created two mates; perhaps you will remember. <> Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila ku yi tunãni. = Kuma muka halitta kome nau'i biyu (na miji da mace), la'alla ku yi tunani. --Qur'an 51:49
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

50


 1. So flee to Allah. Indeed, I am to you from Him a clear warner. <> Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lallemai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. = Saboda haka, ku gudu zuwa ga ALLAH. Shi ne Ya aiko ni zuwa gare ku, a matsayin mai gargadi bayyananne. --Qur'an 51:50
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

51


 1. And do not make [ as equal ] with Allah another deity. Indeed, I am to you from Him a clear warner. <> Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. = Kada ku sanya tare da ALLAH wani abin bautawa na dabam. Shi ne ya aiko ni zuwa gare ku, a matsayin mai gargadi bayyananne. --Qur'an 51:51
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

52


 1. Similarly, there came not to those before them any messenger except that they said, "A magician or a madman." <> Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabaninsu ba face sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci." = Kamar haka, sa’ad da wani manzo ya je zuwa ga mutanen zamanin da, suka ce, “Masihirci ne,” ko kuwa “Mahaukaci.” --Qur'an 51:52
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

53


 1. Did they suggest it to them? Rather, they [ themselves ] are a transgressing people. <> shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai. = Shin, ba sun qulla yarjejeniya wa juna ba? Lalle, su masu girman kai ne. --Qur'an 51:53
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

54


 1. So leave them, [O Muhammad], for you are not to be blamed. <> Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne. = To, ka ƙyale su; ba za a zarge ka ba. --Qur'an 51:54
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

55


 1. And remind, for indeed, the reminder benefits the believers. <> Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai. = Kuma ka tunatar, domin tunatarwa tana amfanin muminai. (Dalilin Rayuwarmu) --Qur'an 51:55
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

56


 1. And I did not create the jinn and mankind except to worship Me. <> Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. = Ban halitta aljannu da mutane domin kome ba sai dai su bauta Mini Ni kadai. --Qur'an 51:56
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

57


 1. I do not want from them any provision, nor do I want them to feed Me. <> Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni. = Ba Na bukatan wani arziqi daga gare su, Ba Na kuma bukatan su ciyar da Ni. --Qur'an 51:57
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

58


 1. Indeed, it is Allah who is the [ continual ] Provider, the firm possessor of strength. <> Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi. = ALLAH, Shi ne Mai azurtawa, Mai ikon yi, Mai cikakken qarfi. --Qur'an 51:58
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

59


 1. And indeed, for those who have wronged is a portion [ of punishment ] like the portion of their predecessors, so let them not impatiently urge Me. <> To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggawa. = Wadanda suka qetare iyaka sun jawo wa kansu irin masakin abokansu; saboda haka kada su qalubalanta. --Qur'an 51:59
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio:

60


 1. And woe to those who have disbelieved from their Day which they are promised. <> Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari. = Bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta, daga ranar da ke jiransu. --Qur'an 51:60
  Arabic Audio:
  Saheeh International Translation Audio: