Talk:3

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of three [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar three:
  1. Within three months, 30,000 troops appeared on the scene, led by the Roman governor of Syria, Cestius Gallus.
   Amma, sojojin Roma suka ɗauki mataki nan da nan. [2]

  2. It is a very meaningful prayer, and a consideration of its first three petitions will help you to learn more about what the Bible really teaches.
   Addu’a ce mai ma’ana ƙwarai, bincika abubuwa uku da ya roƙa da fari za ta taimake mu mu koyi abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. [3]

  3. This was to be in at least three ways: the number of years the temple was in existence, who taught there, and who flocked there to worship Jehovah.
   Hakan zai kasance ta hanyoyi uku: shekarun da haikalin ya yi, da wanda ya koyar a wurin, da kuma waɗanda suka je wajen don su bauta wa Jehobah. [4]

  4. In high school I won three successive titles in the yearly national athletic contests.
   A shekaru uku na ƙarshe kafin in kammala sakandare, na ci kofi sau uku a jere a gasar wasanni na ƙasa da ake yi kowace shekara. [5]

  5. 5:32; 7:6) Their three sons grew up and married, bringing the family up to “eight souls.”
   5:32; 7:6) Yaransu maza uku suka yi girma kuma suka yi aure, hakan ya sa adadin waɗanda suke cikin iyalin ya kai “masu-rai takwas.” [6]

  6. Let us consider three things you can do to shepherd your children —know them, feed them, and guide them.
   Bari mu tattauna abubuwa uku da za ku iya yi don ku kula da yaranku: Ku san su da kyau, ku koyar da su, kuma ku ja-gorance su. [7]

  7. “I was on a three-person phone call.
   MICHAEL ya ce: “Mu uku muna magana ta waya. [8]

  8. We will learn a lot more about these men later on, since all three of them were close friends of Jesus.
   Za mu koyi abubuwa da yawa game da waɗannan mutanen a gaba, tun da dukansu uku abokane ne na kud da kud da Yesu. [9]

  9. Twenty years ago, Selmira’s husband was gunned down in a robbery, leaving her with three young children to rear.
   Shekara ashirin da ta shige, ’yan fashi da makami sun kashe mijin Selmira, aka bar ta da kula da yara uku. [10]

  10. 6:19-22) We owned three homes, land, luxury cars, a boat, and a motor home.
   6:19-22) A lokacin, muna da gidaje uku da filaye da motoci masu tsada da kwalekwale mai inji da kuma mota mai kayan ɗaki a ciki. [11]

  11. Three young men who refuse to worship a towering image are thrown into a superheated furnace, yet they survive unsinged.
   An jefa samari uku da suka ƙi bauta wa wani gunki mai tsawo a tanderu mai ƙuna, duk da haka sun tsira babu wani taɓo. [12]

  12. So from 1970 to 1990, three buildings were purchased and remodeled in Manhattan to provide suitable meeting places.
   Saboda haka, daga shekara ta 1970 zuwa 1990, mun saya gidaje uku a birnin Manhattan da za mu riƙa taro a wurin kuma mun gyara su. [13]

  13. DOMESTIC AND SEXUAL VIOLENCE: “One in three women has been a victim of physical or sexual violence by an intimate partner at some point in her lifetime,” reports the United Nations.
   WULAƘANTA MATA DA KUMA CIN ZARAFINSU: Wani rahoto na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce: “Kashi ɗaya cikin mata uku suna fama da wulaƙanci da kuma cin zarafi daga wurin mazansu.” [14]

  14. “I started teaching my son when he was three years old,” says a mother in Mexico named Julia.
   “Na soma koya wa ɗana sa’ad da yake ɗan shekara uku,” in ji wata uwa a ƙasar Mexico mai suna Julia. [15]

  15. The husband and his wife were spending up to three hours each day commuting to and from work.
   Matar da mijinta suna ɓad da sa’o’i uku da rabi a tafiya da kuma dawowa daga aiki kowacce rana. [16]

  16. These young boys would be trained for three years.
   Za a horar da su har shekara uku. [17]

  17. We were assigned to Korea, though three years of war had just ended in the summer of 1953, leaving that country devastated.
   An aika mu hidima a Koriya, ko da yake bai daɗe ba da yaƙin da aka yi shekara uku a ƙasar ta ƙare a cikin rani ta shekara ta 1953, kuma hakan ya ɓata ƙasar. [18]

  18. Dye makers combined these with salt and exposed the mixture to the open air and the sun for three days.
   Masu yin rina suna haɗa waɗannan sassan da gishiri sa’an nan su bar haɗin ya sha iska da kuma rana na tsawon kwanaki uku. [19]

  19. One writer estimates that “each fruit-bearing [palm] tree will have yielded two or three tons of dates as tribute to its owners in the course of its lifetime.”
   Wani marubuci ya kimanta cewa “kowane itacen dabino zai iya yin ’ya’ya har tan biyu ko uku na dabino da mai shi zai samu riba sa’ad da take raye.” [20]

  20. Among the 166,518 delegates at three “Godly Devotion” conventions held in Poland in 1989 were large numbers of delegates from what were then the Soviet Union and Czechoslovakia, and from other Eastern European countries.
   A shekara ta 1989, ’yan’uwa 166,518 sun halarci taron gunduma na “Godly Devotion” [“Ibada ga Allah”] a ƙasar Folan wanda aka yi a wurare uku. Mutane da yawa sun zo daga ƙasar Rasha ta dā da Czechoslovakia da kuma wasu ƙasashe da ke Gabashin Turai. [21]

  21. Posters reminded people of the promises of the last three governments.
   Hotuna kuma suna tuna wa mutane abubuwan da gwamnatoci uku da suka shige suka yi alkawari. [22]

  22. There I was sentenced to three years in prison on Yíaros (Gyaros), an island about 30 miles (50 km) east of Makrónisos.
   A wurin aka yanke mini hukuncin shekara uku a kurkukun Yíaros, wani wurin da ke bakin teku mai nisan mil 30 daga gabashin Makrónisos. [23]

  23. (2 Chronicles, chapters 34, 35) Daniel and his three Hebrew companions in Babylon never forgot their identity as servants of Jehovah, and even under pressure and temptation, they kept their integrity.
   (2 Tarihi, surori 34, 35) Daniyel da Ibraniyawa uku a Babila ba su taɓa mantuwa ba cewa su bayin Jehobah ne, sun riƙe amincinsu cikin matsi da gwaji. [24]

  24. Consider three reasons:
   Ka yi la’akari da waɗannan dalilan guda uku: [25]

  25. 5 As we learned in Chapter 1 of this publication, the request “Let your name be sanctified” is one of three petitions in Jesus’ model prayer that have to do with Jehovah’s purpose.
   5 Kamar yadda muka koya a Babi na 1na wannan littafin, roƙon nan “A tsarkake sunanka” ɗaya ne cikin roƙo uku da ke cikin addu’ar Yesu ta misali da suka shafi nufin Jehobah. [26]


Retrieved June 25, 2019, 11:14 pm via glosbe (pid: 3862)