Talk:access

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Glosbe's example sentences of access [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar access:
  1. * This program does not translate the text, but it does help translators to organize their work and easily access reference material.
   * Wannan manhajar ba ta fassara, amma tana taimaka wa mafassara su tsara aikinsu kuma su samu littattafai da za su yi bincike da su da sauƙi. [2]

  2. According to certain estimates, some two billion access it on mobile devices, such as smartphones and tablets.
   Wani ƙirge da aka yi ya nuna cewa wajen mutane biliyan biyu suna shiga Intane ta wayar selula da allon kwamfutar hannu, wato Tablets. [3]

  3. Remember that whoever is on your e-mail contact list also has access to the Internet and is therefore able to look for things of interest without your help.
   Ka tuna cewa duk wanda yana cikin jerin sunayen lambobin mutane da ke na’urarka zai iya shiga Intane. Saboda haka, zai iya neman wani bayani daga Intane ba tare da taimakonka ba. [4]

  4. Ebed-melech evidently was a high-ranking official, for he had direct access to King Zedekiah.
   Ebed-melech babban ma’aikacin sarki ne don yana da ’yancin zuwa wurin Sarki Zedekiya. [5]

  5. They went from a lush estate with easy access to healthful vegetation and fruit to the difficult situation outside the garden of Eden.
   Yanayinsu ya canja daga zama a lambu mai kyau da ke da tsiro da ’ya’yan itace masu kyau zuwa yanayi mai wuya waje da lambun Adnin. [6]

  6. If you have access to a library, you will find it interesting to note what reference books say about holidays that are popular where you live.
   Idan kana iya zuwa laburare, za ka yi farin ciki idan ka duba abin da littattafai suka ce game da ranaku masu tsarki da suka yi fice a inda kake da zama. [7]

  7. As never before, people have access to information on just about any subject.
   Fiye da dā, mutane suna samun labari a kan kowane batu. [8]

  8. Those who loyally meet God’s requirements receive a gracious invitation from Jehovah: They can be guests in his “tent”—welcomed to worship him and granted free access to himin prayer.—Psalm 15:1-5.
   Waɗanda suke cika bukatun Allah da aminci suna samun gayyata mai kyau daga wajen Jehobah, wato: Suna iya sauka cikin ‘tantinsa,’ su bauta masa kuma su yi addu’a ga Allah a kowane lokaci.—Zabura 15:1-5. [9]

  9. What is “the secret place of the Most High,” and how can we gain access to it?
   Menene “mabuyan Maɗaukaki,” kuma yaya za mu samu shiga cikinsa? [10]

  10. (John 14:9, 10) Furthermore, through Jesus’ sacrifice, we gain access to Jehovah when we pray for forgiveness of our sins.
   (Yohanna 14:9, 10) Ƙari ga haka, ta wajen hadayar Yesu, mun samu hanyar zuwa ga Jehovah sa’ad da muka roƙi gafara domin zunubanmu. [11]

  11. Being granted free access to the “Hearer of prayer” is a truly remarkable privilege.
   Da yake an ba mu ’yancin kusantar “mai-jin addu’a” wannan baiwa ce mai girma. [12]

  12. The United States calls on all parties to allow aid workers safe and unhindered access to help communities in need.
   Amurka tana kira ga duk ɓangarin da ke cikin waɗannan rikice-rikicen da su ba masu aikin agaji damar isa wurin al’ummar da ke bukatar taimako cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da an yi musu katsalandan ba. [13]

  13. However, you can remain spiritually strong whether you have access to our Web site or not.
   Duk da haka, za ka iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ko da ba ka shiga dandalinmu. [14]

  14. Ken relates, “It took time to get used to living in a location where you may not have access to warm water, electricity, or telephone service for days.”
   Ken ya ce, “Ya ɗauke mu dogon lokaci kafin mu saba zama a inda ba za mu samu ruwa mai ɗumi ba, wutan lantarki, ko kuma daman yin waya na kwanaki.” [15]

  15. If you have access to the Internet, we encourage you to get acquainted with jw.org.
   Idan kuna shiga Intane, muna ƙarfafa ku ku shiga dandalin jw.org. [16]

  16. We have access to him from any place we may be and at any time we may choose.
   Muna iya yi masa magana a ko’ina muke kuma a kowane lokaci da muke so. [17]

  17. Today tens of millions of Africans – across sub-Saharan Africa – have access to electricity in part because of commitments from more than 140 private-sector partners.
   A yau miliyoyin mutanen Afrika – a fadin yankin sahara – sun samu wutar lantarki saboda yunkurin da kamfanoni masu zaman kan su sama da 140 suka yi wajen tabbatar da haka. [18]

  18. If you do not have ready access to the Internet, explain how the person can use jw.org to find the answer himself.—Go to “Bible Teachings/Bible Questions Answered” or “About Us/Frequently Asked Questions.”
   Idan ba ku da waya ko kuma wata ƙaramar na’ura mai Intane, ku bayyana wa mutumin yadda zai iya samun amsar tambayar da kansa a dandalin jw.org.—Ku danna “Abubuwan da Aka Koyar Daga Littafi Mai Tsarki/Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki” ko kuma “Game da Shaidun Jehobah/Tambayoyin da Ake Yawan Yi.” [19]

  19. Access to the Internet has presented many with a challenge in this regard.
   Intane yana sa mutane da yawa su fuskanci wannan ƙalubalen. [20]

  20. We have access to what help if we find it difficult to open our hearts to our heavenly Father?
   Idan yana mana wuya mu bayyana wa Jehobah ainihin abin da ke damunmu a addu’a, mene ne zai taimaka mana? [21]

  21. 15 After his rebellion, Satan still had access to the heavenly courts, as indicated in the book of Job.
   15 Bayan ya yi tawaye, Shaiɗan yana iya zuwan sama, yadda littafin Ayuba ya nuna. [22]

  22. The answer is stored in a database that any translator can easily access.
   Ana saka amsar a wurin da dukan mafassara za su iya ganinta a duk lokacin da suke so. [23]

  23. How happy we are that we have access to Bible literature in some 600 languages.
   Muna farin ciki cewa ƙungiyar Jehobah ta wallafa littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki cikin kusan harsuna 600. [24]

  24. Even those who have no access to the Bible can still learn much about the true God by observing the things he has made.—Romans 1:20.
   Waɗanda ba su da Littafi Mai Tsarki har ila za su iya koyan abubuwa masu yawa game da Allah ta wajen lura da abubuwan da ya halitta.—Romawa 1:20. [25]

  25. In addition, our Web site, jw.org, is now available to the more than 2.7 billion people worldwide who access the Internet.
   Ƙari ga haka, sama da mutane biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai da ke amfani da Intane za su iya shiga dandalinmu na jw.org. [26]


Retrieved Thu Mar 07 2019 03:40:38 GMT-0500 (EST) via [27]