Talk:admire

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Glosbe's example sentences of admire [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar admire:
  1. They appreciate its account of Israel’s history and admire its beautiful poetry.
   Sun ɗauki tarihin Isra’ila da kuma labarai masu daɗi da ke cikinsa da muhimmanci. [2]

  2. There will always be those who have material possessions that we admire or who in one way or another seem to be more successful than we are.
   Da akwai waɗanda suke da abin duniya da muke so ko kuma waɗanda a wasu fanni kamar sun yi nasara a rayuwa fiye da mu. [3]

  3. I admire these people for their strong will and wise use of the Bible.
   Ina son waɗannan mutane don gaba gaɗinsu da amfani da kyau da suke yi da Littafi Mai tsarki. [4]

  4. The director told her: “I admire those who unselfishly devote their time to others.”
   Darektan ya ce mata: “Waɗanda suke ba da kansu don su taimaki mutane suna burge ni sosai.” [5]

  5. We admire God’s qualities and do whatever we can to live in harmony with his purposes.
   Muna son halayen Allah kuma muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi rayuwar da ta jitu da manufofinsa. [6]

  6. I admire their love and their courage.
   Ina sha’awar ƙaunarsu da gaba gaɗinsu. [7]

  7. It is as though he held them up high for all to admire.
   Kamar dai ya ɗaga su sama ne domin kowa ya gani ya yi sha’awa. [8]

  8. 10 A husband writes concerning his wife, a mother of grown children: “The qualities I admire most in Susan are her intense love for God and for people, as well as her understanding, empathy, and honesty.
   10 Wani maigida ya rubuta game da matarsa, uwar yara da sun yi girma: “Halin da na fi so wurin Susan shi ne ƙaunarta na ƙwarai ga Allah da kuma mutanensa, da fahiminta, jinƙai, da kuma yin gaskiya. [9]

  9. We admire the glory reflected in the face of Jehovah’s Son and anointed King, Jesus Christ, and we imitate his example.
   Muna yaba wa ɗaukakar da Ɗan Jehobah kuma shafaffen Sarki, Yesu Kristi yake nunawa,kuma muna yin koyi da misalinsa. [10]

  10. When you have a friend whom you admire and respect, you try to be like him.
   In kana da aboki da ka ke sha’awa kuma ka ke ba wa daraja, za ka yi ƙoƙari ka zama kamar shi. [11]

  11. Do we not admire her courage and faith?
   Gaba gaɗinta da bangaskiyarta sun burge mu, ko ba haka ba? [12]

  12. (Job 34:19; 2 Corinthians 5:14) So if we are going to please Jehovah and serve him shoulder to shoulder, we must not show favoritism or ‘admire personalities for our own benefit.’—Jude 4, 16.
   (Ayuba 34:19; 2 Korinthiyawa 5:14) Saboda haka, idan za mu faranta wa Jehovah rai kuma mu bauta masa da zuciya ɗaya, ba za mu nuna son kai ba ko kuma ‘mu yi tara domin ribar kanmu.’—Yahuda 4, 16. [13]

  13. How can we help but admire her courage, her industriousness, her hospitality, and her humility?
   Ba abin da za mu ce sai da mu yaba mata don ƙarfin halinta da ƙwazonta da karimcinta da kuma tawali’unta, ko ba haka ba? [14]

  14. “Some think that I have wasted my talents,” she relates, “but they recognize that I am happy, and they admire the principles by which I live my life.
   Ta ce: “Wasu suna ganin na yi watsi da ilimina, amma sun gane cewa ina farin ciki, kuma suna son ƙa’idodi da ke ja-gorar rayuwata. [15]

  15. But do we admire Jonathan only because he was loyal to David?
   Amma, shin muna son Jonathan domin ya kasance da aminci ga Dauda ne? [16]

  16. I respect and greatly admire the other members of the Branch Committee.
   Ina daraja sauran ’yan mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshen sosai. [17]

  17. If we love and respect those who take the lead among us but refuse to ‘admire personalities for our own benefit,’ we bring joy to Jehovah.
   Idan muna ƙauna kuma muna daraja waɗanda suke ja-gora a tsakaninmu amma mun ƙi ‘mu so mutane don namu riba,’ za mu faranta wa Jehovah rai. [18]

  18. It was not “the external braiding of the hair” or “the putting on of gold ornaments or the wearing of outer garments” that caused others to admire Ruth.
   Ba “kwalliyar kitso” ba ce, ko kuma saka “kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa” ya sa mutane suka yi sha’awar Rut. [19]

  19. “Like most people, you probably admire the beauty in nature.
   “Kamar mutane da yawa, babu shakka kana yin sha’awar kyaun halitta. [20]

  20. BATHED in the warm light of sunset, a few longtime friends enjoy an outdoor meal together, laughing and talking as they admire the view.
   MANOMI ya dubi gonarsa ya yi murmushi domin hadari ya haɗu kuma ruwan fari yana saukowa a kan irinsa da suke da bukatar ruwa. [21]

  21. 3 We usually admire people who are loyal.
   3 Muna son mutane masu aminci. [22]

  22. They swam a little farther out to admire the reef below.
   Sun yi iyo da ɗan nisa don su kalli ƙarƙashin tekun. [23]

  23. Is it identified with some well-known entertainer—someone I admire?
   Wata shahararriya ce aka san ta da ita—wata da nake so? [24]

  24. Second, Jesus has qualities that we can admire and imitate.
   Na biyu, Yesu yana da halaye masu ban sha’awa da za mu iya koyi da su. [25]

  25. WE TEND to imitate those whose personality and ways we admire.
   MUKAN so mu zama kamar mutanen da suke burge mu. [26]


Retrieved Thu Mar 07 2019 21:41:09 GMT-0500 (EST) via [27]