Talk:afternoon

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of afternoon [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar afternoon:
  1. In accord with prophecy, “at the ninth hour [about three o’clock in the afternoon] Jesus called out with a loud voice: ‘Eli, Eli, lama sabachthani?’
   Markus ya gaya mana cewa a sa’a ta tara, wato, wajen ƙarfe uku na rana, Yesu ya kira da babbar murya: “Eloi, Eloi, lama sabachtani? [2]

  2. 1:28) Could you rehearse with your little child such greetings as “good morning,” “good afternoon,” “good evening,” or whatever is customary where you live?
   1:28) Shin za ku iya gwada da ƙananan yaranku gaisuwa kamar su “barka da safiya” da “barka da rana” da “barka da yamma” ko kuma irin gaisuwa da ta fi dacewa a yankinku? [3]

  3. Well, one afternoon an angel appears to him and says: ‘God is pleased with you, and he is going to answer your prayers.
   To, wata rana mala’ika ya bayyana masa ya ce: ‘Allah ya yi farin ciki da kai, kuma zai amsa addu’o’inka. [4]

  4. Early Friday afternoon Jesus is nailed to a stake.
   Ranar Jumma’a da rana aka rataye Yesu a kan gungume. [5]

  5. After preaching until mid-afternoon the next day, we looked for a place to spend the night.
   Washegari bayan muka yi wa’azi har tsakar rana, muka nemi inda za mu kwana. [6]

  6. I first met Sabina one afternoon while she was patiently attending to demanding customers at her sister’s store.
   Na fara haɗuwa da Sabina ne da rana a shagon ’yar’uwarta tana ta sayar da kaya ga waɗanda suke son su saya. [7]

  7. Imagine Ruth noticing that the afternoon shadows had lengthened, then looking at her mother-in-law and wondering if it was time to find a place to rest for the night.
   Ka ɗan yi tunanin yadda Ruth ta ji sa’ad da ta lura cewa dare ya fara yi, sai ta kalli surukarta tana mamaki ko lokaci ya yi da za su nemi masauki. [8]

  8. Amazed to hear this, we decided to hold a meeting that very afternoon.
   Mun yi mamaki da muka ji haka, sai muka yanke shawarar yin taro da rana. [9]

  9. ON Tuesday afternoon, Nisan 11, 33 C.E., Jesus’ disciples raised a question that has profound meaning for us today.
   RANAR talata da rana, 11 ga Nisan, shekara ta 33 A.Z., almajiran Yesu sun yi tambaya da take da ma’ana sosai a gare mu a yau. [10]

  10. Late in the afternoon, Elijah’s turn came.
   Da yamma ta yi kusa, lokacin Iliya ya yi. [11]

  11. One sultry afternoon when we are about to finish our study, we read a Bible text that jolts Kojo like the blow from an opponent’s powerful kick.
   Wata rana kafin mu gama nazarinmu, sai muka karanta wata sura a cikin Littafi Mai Tsarki da ta girgiza Kojo kamar naushi mai ƙarfi daga abokin faɗa. [12]

  12. A fellow pioneer in the same congregation added: “Getting companions in the afternoon is a real problem.”
   Wani majagaba da ke ikilisiyar su Bobbi ya ce: “Samun ɗan’uwan da zai fita wa’azi tare da mu da tsakar rana yana da wuya sosai.” [13]

  13. The brothers contacted the sheriff, and he came in the afternoon with two horses to take us to town.
   ’Yan’uwan suka samu ɗan dokar garin, sai ya zo da rana tare da dawaki guda biyu don ya kai mu cikin gari. [14]

  14. For instance, if the house-to-house ministry is productive on Saturday mornings, could you have your Bible study in the afternoon or in the evening?
   Alal misali, idan ana samun mutane sosai sa’ad da ake wa’azi gida-gida a ranar Asabar da safe, za ka iya shirya ka yi nazari da ɗalibanka da rana ko da yamma. [15]

  15. Imagine the many things that must have occupied the mind and heart of Jesus on the afternoon of his death.
   Ka yi tunanin abubuwa da suka cika wa Yesu zuciya a ranar mutuwarsa da rana. [16]

  16. Later that afternoon, Jesus died, and a great earthquake occurred.
   Can da rana, Yesu ya mutu, kuma aka yi muguwar girgizar ƙasa. [17]

  17. Imagine the late afternoon breeze ruffling Abel’s hair as he turned his gaze upward and thought about his Creator.
   Ka yi tunanin iska mai daɗi na maraice da ke hura sumar Habila, yayin da yake kallon sama kuma yake tunanin Mahaliccinsa. [18]

  18. 7 Upon arriving at the temple on Monday, Nisan 10, Jesus acts on what he saw the preceding afternoon.
   7 Da ya isa haikalin ranar Litinin 10 ga watan Nisan, Yesu ya aikata a kan abin da ya gani da rana a ranar da ta shige. [19]

  19. 6 A great impetus to the Kingdom-proclamation work came on Sunday afternoon, July 26, 1931, when a resolution was adopted, first at a convention in Columbus, Ohio, U.S.A., and thereafter around the world.
   6 An yi wani babban ƙari a aikin shelar Mulkin Allah a ranar Lahadi da rana, 26 ga watan Yuli a shekara ta 1931, sa’ad da aka ɗauki alkawari a taron guduma ta farko a Columbus, Ohio, a Amirka, daga baya kuma a duniya gabaki ɗaya. [20]

  20. One Sunday afternoon, Kenneth and Filomena, who live in Curaçao, went to visit a married couple with whom they were conducting a Bible study.
   Kenneth da matarsa Filomena da suke zama a ƙasar Curaçao, sun je wurin wasu ma’aurata da suke nazarin Littafi Mai Tsarki da su a ranar Lahadi da rana. [21]

  21. His body was offered as a perfect sacrifice, and his blood was poured out the next afternoon of the same Jewish day, Nisan 14.
   Ya ba da jikinsa kamiltaccen hadaya, da jininsa da aka zubar washegari da rana a ranar 14 ga Nisan na Yahudawa. [22]

  22. How he must have reproved himself when Jesus died that afternoon after hours of torment!
   Babu shakka ya tsauta wa kansa sosai sa’ad da Yesu ya mutu da ranan bayan sa’o’in azaba! [23]

  23. However, he worked hard to overcome the problem, and on one Sunday afternoon in 1927, at the age of 14, he announced to his father that he was ready to accompany him in the door-to-door preaching activity.
   Amma dai, ya yi ƙoƙari sosai don ya shawo kan matsalar, kuma da yake ɗan shekara 14, a wata ranar Lahadi da rana a shekara ta 1927, ya sanar wa mahaifinsa cewa yana shirye ya fita wa’azi na gida gida tare da shi. [24]

  24. And this is what happens: Peter and John are going into the temple in Jerusalem one afternoon.
   Ga abin da ya faru: Wata rana Bitrus da Yohanna suna shiga cikin haikali a Urushalima da rana. [25]

  25. One afternoon in 1941, when I was 15, an elderly man and his wife came to our home.
   Wata rana a shekara ta 1941, sa’ad da nake ɗan shekara 15, wani mutum dattijo da matarsa sun zo gidanmu. [26]


Retrieved June 23, 2019, 12:11 pm via glosbe (pid: 7777)