Talk:agogo

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of agogo [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar agogo:
  1. Idan ka ba wa abokinka agogo mai tsada, mota, ko kuma gida, hakika abokin nan zai yi godiya kuma ya yi murna, kuma za ka samu farin cikin bayarwa.
   If you give a friend an expensive watch, a car, or even a home, that friend will likely be grateful and happy, and you will have the joy of giving. [2]

  2. Sa’ad da kake barci mai zurfi, ka san abin da yake faruwa ne?— Kuma sa’ad da ka farka, ba za ka san ko barcin awa nawa ka yi ba sai ka duba agogo.
   When you are in a very deep sleep, you do not know what is going on around you, do you?— And when you wake up, you do not know how long you have been sleeping until you look at a clock. [3]

  3. 3 Agogo yana bukatar mai-kera agogo.
   3 A watch requires a watchmaker. [4]

  4. Idan yaronka ya roƙa cewa yana son a kara masa minti biyar kuma ka yarda, ka sa agogo ya yi kara idan lokacin da ka kara masa ya cika.
   If your child pleads to stay up an extra five minutes and you want to grant the wish, set an alarm clock to ring in five minutes. [5]

  5. (Esther 9:24-26) Da sauran watanni kafin ranar ta kai, amma hannun agogo yana tafiya.
   (Esther 9:24-26) The day was yet months away, but it was fast approaching. [6]

  6. Alal misali, ina sayan agogo da warwaro da su zobe masu ruwan gwal, sai in sayar da su a kan titi da kuma garejoji a matsayin gwal masu tsada.
   For example, I would buy large quantities of gold-plated watches, bracelets, and rings, mark them as 14-carat gold with an engraver’s stamp, and then sell them on the street and in the parking lots of shopping centers. [7]

  7. Kamar yadda Sulemanu ya lura, babu hikima cikin kasancewa da sha’awar abin da ta faru a dā, babu tantama, ba za mu iya mai da hannun agogo baya ba.
   As Solomon noted, there is no wisdom in unrealistically dwelling on the past, since it is evident that we cannot turn the clock back. [8]

  8. Stavros yana jin daɗin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai har ya mai da dukan agogo da ke gidansa baya da awa guda don kada mu samu jirgi na ƙarshe na koma gida don mu daɗe sosai tare da su.
   Stavros enjoyed studying the Bible so much that he would turn all the clocks in his house back one hour so that we would miss the last train home and have to stay longer. [9]

  9. 4 Idan fa agogo, wanda da sauƙi yake, yana bukatar wanzuwar mai-yin agogo, lallai sarari mai-ban tsoro mai-wuyan ganewa fiye da haka yana bukatar wanzuwar mai-tsari da kuma mai-yi.
   4 If a watch, which is relatively simple, implies the existence of a watchmaker, surely the infinitely more complex and awesome universe implies the existence of a designer and maker. [10]


Retrieved June 23, 2019, 6:11 pm via glosbe (pid: 20462)