Talk:permission

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of permission [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar permission:
  1. People were giving themselves permission to spend less time with their children.”
   Iyaye suna ba wa kansu izinin su ba da ɗan lokaci ga ’ya’yansu.” [2]

  2. When he refused, the camp commander contacted Heinrich Himmler, head of the SS (Schutzstaffel, Hitler’s elite guard), and asked permission to execute Dickmann in the presence of all other camp inmates.
   Da ya ƙi, sai shugaban sansanin ya je wajen Heinrich Himmler shugaban SS (Schutzstaffel, rukuni mai girma na masu tsaron Hitler), ya nemi izini ya kashe Dickmann a gaban dukan sauran fursunoni na sansanin. [3]

  3. What do many find it hard to understand about God’s permission of suffering, and what knowledge may help them?
   Menene wasu suka kasa fahimta game da abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, kuma menene zai taimake su? [4]

  4. With her husband’s permission, she traveled about 19 miles (30 km) to Elisha at Mount Carmel.
   Ta nemi izini daga maigidanta kuma ta yi tafiyar kilomita 30 zuwa Dutsen Karmel wurin Elisha. [5]

  5. 3 Let us consider how free will is involved in God’s permission of suffering.
   3 Bari mu yi la’akari da yadda zancen son zuciya ke kunshe cikin kyale shan wahala da Allah ya yi. [6]

  6. 4 After the Noachian Flood, God gave humans permission to eat the flesh of animals but not the blood.
   4 Bayan Ruwan Tufana, Allah ya ba wa mutane izini su ci nama na dabbobi amma ba jininsu ba. [7]

  7. God’s permission of wickedness on earth affords us an opportunity to give a personal answer as to where we stand on the issues of Jehovah’s sovereignty and our integrity.
   Da yake Allah ya ƙyale mugunta a duniya, ya ba mu zarafin nuna ra’ayinmu a batutuwan ikon mallakar Jehobah da kuma amincinmu. [8]

  8. To arouse the interest of her teacher and classmates, she obtained permission to place several Bible publications in the library.
   Don ta ta da marmarin malamanta da ’yan ajin, ta karɓi izini ta saka littattafai na Littafi Mai Tsarki dabam dabam a laburaren. [9]

  9. God’s temporary permission of evil has afforded all of us the opportunity to show him what is truly in our hearts.
   Ƙyale muguntar da Allah ya yi na ɗan lokaci ya ba dukanmu zarafin nuna masa ainihin abin da ke cikin zuciyarmu. [10]

  10. Although he felt hesitant, he asked permission to correct these false claims, and the teacher agreed.
   Ko da yake Luca ya ji tsoro, ya nemi izini daga malaminsa don ya gyara wasu kurakurai da ke littafin, kuma malamin ya yarda. [11]

  11. When she asked her employer for permission to take some days off to attend one of our conventions, he angrily retorted that if she went, he would fire her.
   Sa’ad da ta nemi izini daga wurin shugaban aikinta don ta halarci taron gunduma, ya faɗa da fushi cewa idan ta je, zai kore ta daga aiki. [12]

  12. The class was about to end, so she asked her teacher for permission to give a presentation about her beliefs as one of Jehovah’s Witnesses.
   An kusan tashi ajin koyar da tarbiyya, sai ta gaya wa malamarsu ta ba ta izinin tattauna imaninta a matsayin ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah. [13]

  13. 9 On hearing one of the recorded Bible talks, a householder named Hillary Goslin obtained the publisher’s permission to borrow the phonograph for a week in order to acquaint his neighbors with the Kingdom message.
   9 Sa’ad da wani magidanci mai suna Hillary Goslin ya ji waɗannan jawaban Littafi Mai Tsarki, sai ya karɓi garmaho daga wurin wani mai shela na sati ɗaya don ya yi amfani da shi wajen yi wa maƙwabtansa wa’azi. [14]

  14. So after the missionaries consulted with King Radama I, the king granted permission to adopt the Roman alphabet and use it in place of sorabe.
   Saboda haka, sa’ad da ’yan mishan suka yi magana da Sarki Radama na ɗaya, sarkin ya ba da izinin yin amfani da harafi na Roma maimakon sorabe. [15]

  15. Despite having the right to glean, Ruth asked for permission before doing so.
   Ko da yake tana da ’yancin ta yi kala, Rut ta nemi izini. [16]

  16. 17 God’s temporary permission of hardship has allowed time for others to embrace the truth.
   17 Yadda Allah ya ƙyale wahala na ɗan lokaci ya taimake wasu su sami gaskiya. [17]

  17. How do many feel about God’s permission of suffering?
   Ina yadda mutane dayawa suke ji game da kyalewar shan wahala na Allah? [18]

  18. 13 In Bolivia, a five-year-old girl being raised by Witness parents asked her teacher for permission to be excused from school during the week of the circuit overseer’s visit.
   13 A Bolivia, wata yarinya ’yar shekara biyar da iyaye da suka yi renonta Shaidu ne ta tambaye malamarta ta ba ta hutu na mako ɗaya daga makaranta lokacin ziyarar mai-kula mai-ziyara. [19]

  19. The director gave her permission to visit the rooms of different residents.
   Darektan ya ba ta izini ta ziyarci gidaje dabam dabam da suke wajen. [20]

  20. They do not knowingly buy stolen property or take things without permission.—Exodus 20:15; Ephesians 4:28.
   Basu sayan kayan sata da ganga ba ko kuwa ɗauki wani abu babu izini. —Fitowa 20:15; Afisawa 4:28. [21]

  21. “He asked permission to pray to Jehovah with us.
   “Ya nemi izini ya yi addu’a ga Jehovah tare da mu. [22]

  22. With the teacher’s permission, at the conclusion she asks the student if she knows any others who might enjoy having their own study.
   Da izinin mai nazarin, sai ta tambayi ɗalibar ko ta san wata da za ta so a yi nazari da ita. [23]

  23. 12 God’s permission of suffering has been painful for us.
   12 Kyale shan wahala da Allah ya yi ya kasance ko da ɗaci garemu. [24]

  24. Even so, Brother Young requested a permit for the Camões Secondary School gymnasium, and permission was granted!
   Duk da haka, ɗan’uwan ya nemi izinin yin amfani da ɗakin motsa jiki da ke makarantar sakandare na Camões, kuma aka ba shi izinin yin amfani da wurin! [25]

  25. For example, would it show good manners if we take photos of them without their permission or when they are not aware of it, perhaps when they are eating or doing something else?
   Alal misali, bai kamata mu ɗauki hotonsu ba tare da izininsu ba, ko sa’ad da suke ci abinci ko kuma lokacin da suke yin wani abu. [26]


Retrieved December 5, 2019, 1:37 am via glosbe (pid: 22762)