Talk:praise

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Glosbe's example sentences of praise [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar praise:
  1. Am I inclined to focus primarily on aspects of God’s service that seem to bring recognition and praise?
   A bauta ta ga Jehobah, shin na fi son yin ayyukan da za su sa mutane su lura da ni kuma su yaba mini? [2]

  2. Praising Jehovah is a good reason for us to keep living, and having life is a good reason to praise him.
   Yabon Jehobah dalili ne mai kyau na kasancewa a raye, kuma kasancewa a raye dalili ne mai kyau na yabonsa. [3]

  3. The main purpose of our congregating regularly, both in local congregations and at large conventions, is to praise Jehovah.
   Ainihin dalilin da ya sa muke taruwa a kai a kai, a ikilisiyoyi da kuma manyan taro shi ne don mu yabi Jehobah. [4]

  4. In Ps 148 verse 11, powerful and influential humans, such as kings and judges, are invited to join in the praise.
   A cikin aya ta 11 an gayyaci ’yan adam masu iko da rinjaya, kamar su sarakuna da hukumomi su haɗu a yabon. [5]

  5. Yes, whether we are ‘experts’ or ‘learners,’ all of us can —and should— unite our voices to Jehovah’s praise. —Compare 2 Corinthians 8:12.
   Hakika, ko da mu ‘gwanaye’ ne ko kuma ‘masu koyo,’ dukanmu za mu iya, haɗa muryoyinmu tare don yabon Jehobah.—Gwada 2 Korintiyawa 8:12. [6]

  6. Praise Jah, you people!”
   Hallelujah!” [7]

  7. A lack of humility is disclosed when praise fosters a feeling of superiority.
   Za mu nuna rashin tawali’u idan muka bar yabo ya sa muka fara jin kamar mun fi kowa. [8]

  8. When newcomers see and experience Christian love in action, they may be moved to praise God and join us in pure worship. —Joh 13:35.
   Amma muna bukatar yin hakan a kowane lokaci. Idan sababbi suka ga yadda muke ƙaunar juna, hakan zai motsa su su ɗaukaka Jehobah kuma su soma bauta masa. —Yoh 13:35. [9]

  9. How Can You Praise Jehovah?
   Ta Yaya Za Ku Yabi Jehobah? [10]

  10. • What opportunities are there to praise Jehovah “all day long”?
   • Waɗanne hanyoyi ne za mu yabi Jehovah a “dukan yini”? [11]

  11. Clearly, Jesus and his Father were pleased with the praise of the young boys.
   Hakika, Yesu da Ubansa sun yi farin ciki da yabon ’yan yaran. [12]

  12. Praise “I will praise Jehovah at all times; his praise will be on my lips constantly.” —Psalm 34:1.
   Yabo “Zan albarkaci Ubangiji a kowane loto: yabonsa kuwa za ya zauna a bakina tuttur.”—Zabura 34:1. [13]

  13. And if we followed such practices, would he accept sacrifices of praise from our lips?
   Kuma idan muna bin irin waɗannan hanyoyi, zai karɓi hadayar yabo daga bakinmu kuwa? [14]

  14. (Hebrews 13:15) By using our abilities and resources to offer a sacrifice of praise to Jehovah, whether in the public ministry or in “the congregated throngs” of fellow Christians, we can express heartfelt thanks to our loving heavenly Father, Jehovah God.
   (Ibraniyawa 13:15) Ta wurin yin amfani da iyawarmu da kuma wadatarmu mu ba da hadayar yabo ga Jehovah, ko a hidimar fage ko a “taron jama’a” na ’yan’uwa Kiristoci, za mu furta godiyarmu daga zuci ga Ubanmu na samaniya mai ƙauna, Jehovah Allah. [15]

  15. It is also home to the Swiss National Park, where the area’s natural beauty and rich variety of flora and fauna praise our Grand Creator, Jehovah.
   Akwai wuri mai suna Swiss National Park, inda furanni da dabbobi dabam dabam masu kyau suke yaba wa Mahaliccinmu Mai Girma, Jehobah. [16]

  16. 2 Loud Shout of Praise: To help publishers expand their ministry, a special provision has been made for any who wish to auxiliary pioneer in the month of August.
   2 Yabo da Murya Mai Ƙarfi: Domin a taimaka wa masu shela su faɗaɗa hidimarsu, an ba waɗanda suke so su yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Agusta damar yin awoyi 30 idan suna so. [17]

  17. 7:9, 14) There, they will experience untold blessings as they continue to grow in appreciation for Jehovah, and they will be able to praise him to time indefinite. —Ps.
   Yoh. 7:9, 14) A wurin, za su more albarka masu yawa yayin da suka ci gaba da nuna godiya ga Jehobah, kuma za su iya yabonsa har abada.—Zab. [18]

  18. Such good work brings praise to Jehovah God and is evidence of our “godly devotion [that] is beneficial for all things.” —1 Timothy 4:8.
   Irin wannan nagarin aiki yana kawo yabo ga Jehovah Allah kuma tabbaci ne na ‘ibadarmu wadda tana da amfani ga dukan abu.’—1 Timothawus 4:8. [19]

  19. (Ephesians 5:19) We do our best to praise Jehovah in the field ministry.
   (Afisawa 5:19) Muna yin iyakacin ƙoƙarinmu mu yi yabon Jehovah cikin hidimar fage. [20]

  20. 6:5-8) Being a conscientious worker can also bring praise to our heavenly Father.
   Wanda yake yin aiki da kyau yana sa a yaba wa Ubanmu na samaniya. [21]

  21. “Every breathing thing —let it praise Jah.” —PSALM 150:6.
   “Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji.”—ZABURA 150:6. [22]

  22. Therefore, gratitude for all these good gifts should move us to respect his elevated standards and to praise him with zeal, declaring these “magnificent things” to others.
   Saboda haka, nuna godiya ga dukan waɗannan kyauta masu kyau, ya kamata mu motsa mu mu yi ladabi ga mizanansa masu girma kuma mu yaba masa da himma, muna faɗa wa wasu “ayyuka masu-girma.” [23]

  23. (Psalm 41:13) After considering them, are we not moved to bless, or praise, Jehovah?
   (Zabura 41:13) Bayan mun gama yin la’akari da su, za su motsa mu, mu yabi Jehobah. [24]

  24. (Psalm 119:175, 176) Some who have wandered away from the Christian congregation may still love God and may want to praise him.
   (Zabura 119:175, 176) Mutanen da suka bar ikilisiyar Kirista wataƙila har ila suna ƙaunar Allah kuma suna so su yabe shi. [25]

  25. Jehovah is the rightful Sovereign, worthy of worship and praise.
   Jehobah ne Mai Ikon Mallaka, kuma ya cancanci bauta da yabo. [26]


Retrieved June 21, 2019, 11:09 am via glosbe (pid: 25199)