Talk:spend

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of spend [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar spend:
  1. 13:20) Most pioneers spend considerable time in the ministry with fellow evangelizers.
   13:20) Yawancin majagaba suna wa’azi na sa’o’i da yawa tare da ’yan’uwansu. [2]

  2. People were giving themselves permission to spend less time with their children.”
   Iyaye suna ba wa kansu izinin su ba da ɗan lokaci ga ’ya’yansu.” [3]

  3. However, some husbands and wives spend long periods of time apart —taking separate vacations or being away from each other because of secular work, thus depriving each other of the “due.”
   Amma dai, wasu mata ko miji suna kasancewa su kaɗai na dogon lokaci, suna zuwa hutu su kaɗai saboda aikinsu, kuma da hakan ba sa yin ibadar aure. [4]

  4. Then they may spend a lifetime in vain trying to shore up mistaken beliefs. —Jeremiah 17:9.
   Suna iya ba da rayuwarsu a ƙoƙarin goyon bayan ra’ayoyi da ƙarya ne.—Irmiya 17:9. [5]

  5. On other occasions, we spend time together in wholesome recreation.
   A wasu lokatai, muna yin nishaɗi mai kyau tare. [6]

  6. However, training for that career might severely limit the time you can spend serving Jehovah.
   Amma, yin koyon domin wannan zai iya cin lokacinka ƙwarai da za ka yi amfani da shi a bauta wa Jehovah. [7]

  7. Special pioneers and missionaries spend even more time in Kingdom service.
   Majagaba na musamman da masu wa’azi a ƙasashen waje suna amfani da lokaci da ya fi haka a hidimar Mulkin. [8]

  8. If you have a means of supporting yourself, do you really need to spend time, money, and effort on further education just to realize personal aspirations or those of your parents or other relatives?
   Idan kana da abin biyan bukata, shin kana bukatar ka ɓata lokaci da kuɗi da kuma ƙoƙari wajen samun ƙarin ilimi don ka cim ma burinka ko kuma na iyayenka ko na wasu dangogi? [9]

  9. Having brief meetings for field service will enable all to spend more time in the ministry.
   Yin gajeren taron fita wa’azi zai taimaki kowa ya yi wa’azi na sa’o’i da yawa. [10]

  10. But when we spend too much time on “fun” things at the expense of activities connected with our worship, relaxation becomes a valueless thing, adversely affecting our spiritual well-being.
   Amma idan muka ɓatar da lokaci mai yawa a kan ayyukan “nishaɗi” kuma muka ƙyale ayyukan bautarmu, to nishaɗi zai kasance aikin banza, wanda yake shafan ruhaniyarmu sosai. [11]

  11. And those with similar preferences in recreation often spend much time together.
   Kuma waɗanda suke son nishaɗi irin ɗaya sau da yawa sukan kasance tare. [12]

  12. But she will spend the rest of her life serving Jehovah at his tabernacle in Shiʹloh.
   Ta ƙarasa sauran rayuwarta a mazaunin Jehobah a Shiloh. [13]

  13. They want us to slave to gain money so that we can spend it on newer, better, bigger items.
   Suna so mu riƙa aiki a kowane lokaci don mu samu kuɗi kuma mu kashe su a kan sababbin abubuwa, mafi kyau, kuma manya. [14]

  14. Would you spend your money on such an inferior product?
   Za ka so ka ɓāta kuɗinka a kan irin wannan mummunar ɗinkin? [15]

  15. We may spend more time studying God’s written Word and may make greater effort to apply it.
   Muna iya ƙara ba da lokaci a yin nazarin rubutacciyar Maganar Allah kuma mu yi ƙoƙarin yin amfani da ita. [16]

  16. (Acts 13:48) Presently, Jehovah’s Witnesses spend an average of more than three million hours each day of the year in Kingdom-preaching and disciple-making activity worldwide.
   (Ayyukan Manzanni 13:48) A yanzu, a kowacce rana cikin shekara, Shaidun Jehovah suna ɓatar da sa’o’i fiye da miliyan uku a yin wa’azin Mulkin da kuma almajirantarwa a dukan duniya. [17]

  17. After preaching until mid-afternoon the next day, we looked for a place to spend the night.
   Washegari bayan muka yi wa’azi har tsakar rana, muka nemi inda za mu kwana. [18]

  18. Ask yourself: ‘Over the past month, how much time did I set aside just to spend with my mate?
   Ka tambayi kanka: ‘A watanni da suka wuce, awa nawa ne na keɓe don in kasance da abokiyar aurena? [19]

  19. HOW I HAVE BENEFITED: My reading skills have improved, and I now spend many hours each week helping others learn to read and study the Bible.
   YADDA NA AMFANA: Na iya karatu sosai yanzu, kuma ina amfani da sa’o’i da yawa a kowane mako wajen taimaka wa mutane su koyi karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki. [20]

  20. To spend more time in the field service, an elder needs good personal organization to balance his schedule and to know what to delegate and how to do so.
   Domin ya ƙara ba da lokaci a hidimar fage, dattijo yana bukatar ya tsara abubuwa da kyau don ya daidaita tsarinsa kuma ya san abin da zai ba wasu su yi da kuma yadda zai yi hakan. [21]

  21. Based on that, we discuss in detail how much we can spend.”
   Bisa ga hakan, muna tattaunawa dalla-dalla a kan yawan kuɗin da za mu iya kashewa.” [22]

  22. Parents with practical wisdom spend hours learning and applying Jehovah’s standards, thus fearing his name.
   Hakazalika, iyaye masu hikima suna yin amfani da lokacinsu don su koyi da kuma bi ƙa’idodin Jehobah. [23]

  23. Schedule certain times you will spend together.
   Ka tsara wasu lokatai da za ku shaƙata tare. [24]

  24. After doing that, they soon discovered that they actually enriched their life because they had more time to spend with their families and in Jehovah’s service.
   Bayan sun yi hakan, sun ga cewa sun kyautata rayuwarsu domin a yanzu suna da isashen lokaci na kasancewa da iyalinsu da kuma na yi wa Jehobah hidima. [25]

  25. One can spend a lifetime studying them and still not fully understand them.
   Mutum zai iya yin bincike har zuwa ƙarshen rayuwarsa, amma ba zai fahimce su sosai ba. [26]


Retrieved July 31, 2019, 5:35 pm via glosbe (pid: 17861)