UMD NFLC Hausa Lessons/105 Political Unrest in Madagascar

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/105)
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Political Unrest in Madagascar - This is a report about the political situation in Madagascar.
 2. Language: Hausa
 3. Topic: Economics/Politics
 4. ILR Level: 1+/2
 5. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High
 6. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 7. Modality: Reading
 8. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 9. Subject Area: Language
 10. Material Type: LLO
 11. Publication Year: 2009
 12. ObjectID: T8RHA12

Transcript


Original Translation

Me ya sa ake ta da zaune tsaye a kasar Madagascar Cikin shirin yau za mu mai da hankali a kasar Madagascar da ke gabashin Afirka, inda a rana 17 ga watan Maris Marc Ravalomanana, shugaban kasar,ya ba da umarnin rushe gwamnati da kafa kwamitin zartaswa na soja don aiwatar da ikon shugaban kasa. Amma shugaban kwamitin soja ya ce an riga an mika ikon shugaba ga Andry Rajoelina, shugaban 'yan Adawa, yayin da Mista Rajoelina ya yi ikirarin cewa ya riga ya zama shugaban kasar, kuma zai shirya babban zabe cikin shekaru 2. Manazarta na ganin cewa, dalilan da suka sa ake samun fadi-tashi kan harkokin siyasar kasar Madagascar, su ne, da farko, manufar kasar kan tattalin arziki ba ta ba jama'a gamsuwa ba. Bayan da Ravalomanana ya kama mulki a shekarar 2002, ya taba gabatar da taken manufar raya tattalin arziki na "mai dorewa kuma cikin sauri", ta yadda ya samu yabo. Sai dai lokacin da ya yi tazarce a shekarar 2007, ya fito da matakan tattalin arziki wadanda ba su dace da halin da ake ciki ba, sa'an nan ya kasa kyautata halin zaman rayuwar jama'a kamar yadda ya alkawarta. Talaucin da kasar ke fama da shi ya haddasa rashin gamsuwa a cikin jama'ar kasar. Na biyu, shugaba Ravalomanana ya kan yi amfani da mukarabinsa, ta yadda ya kan sa sojojin kasar rashin jin dadi. A watan Oktoba na shekarar 2007, shugaba Ravalomanana ya nada Cecile Manorohanta, 'yar gaban goshinsa wadda ba ta da tushe cikin sojoji, zuwa mukamin ministar tsaron kasar, haka kuma a watan Fabarairu na shekarar bana, ya nada Edmond Rasolomahandry a matsayin hafsan hafsoshin sojojin kasar. Abun ya samu kin amincewa daga sojojin kasar sosai, har ma sun ta da bore, sun zabi hafsan hafsoshin da kansu. Dalili na uku shi ne, sabuwar dokar jam'iyyar siyasa ta sa jam'iyyum wadanda ba su kan kujerar mulki su hada kawunansu. A watan Janairu na shekarar bana, shugaba Ravalomanana ya sa majalisun kasar, inda jam'iyyar TIM da ke kan karagar mulki take da rinjaye, su zartas da kudurin gyara tsarin mulki, da dokar jam'iyyar siyasa. Sa'an nan cikin dokokin, an kayyade cewa, dole ne a shiga zaben kasar bisa matsayin wakilin wata jam'iyya, inda ake da nufin nuna kin amincewa ga Andry Rajoelina, wanda ya ci zabe ya zama magajin birnin Antananarivo,hedikwatar kasar Madagascar, a shekarar 2007, bisa matsayinsa na zaman kansa, inda bai wakilci wata jam'iyya ba. Cikin shekarun da suka wuce, magaji Rajoelina ya samu sabanin ra'ayi da shugaban kasar kan abubuwa da yawa, kamar su raba kayayyakin tallafi, da samar da wutar lantarki da ruwa, da dai sauransu. Da ma jam'iyyun kasar 'yan adawa kowa na kula da aikin kanta, sai dai sabuwar dokar jam'iyyar siyasa ta sa su hada kawunansu don neman rinjaye a majalisa.Sa'an nan an mai da Andry Rajoelina shugaban 'yan adawa. A watan Disamba na shekarar 2008, shugaba Ravalomanana ya ba da umurnin rufe gidajen rediyo da talabijin na Aadry Rajoelina, wannan ya zama dalilin kai tsaye da ya haddasa ta da zaune tsaye a kasar Madagascar. Sabo da goyon baya da sojojin kasar, da 'yan kasuwa, da kuma bangarorin ketare suka nuna masa, Msita Rajoelina yana ta daga murya. Da ma ya ce zai shiga gwamnati, amma yanzu yana neman korar shugaba mai ci, har da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Why There Is Unrest in Madagascar In today’s program, we will focus on the country of Madagascar in East Africa, where, on March 17, President Marc Ravalomanana gave an order to dissolve the government and establish an executive military council to carry out the authority of the president, but the head of the military council said that presidential power had already been transferred to opposition leader Andry Rajoelina, while Mr. Rajoelina announced that he was already president, and that he would plan for general elections in two years. Analysts believed that there are several reasons for the political instability in Madagascar. First, people were disappointed with the country’s economic policy. After Ravalomanana seized power in 2002, he promised to introduce “quick and permanent" policies for economic development, for which he won praise. But when his term was extended in 2007, he did away with economic measures that were not appropriate for the circumstances and failed to improve the people’s standard of living as he had promised. The poverty the country was suffering brought disappointment to its citizens. Secondly, President Ravalomanana made use of his trusted friends in a way that upset the military. In October 2007, President Ravalomanana appointed Cecile Manorohanta, one of his favored associates who had no military experience, to the position of Defense Minister, and in February of last year, he appointed Edmond Rasolomahandry to the post of Army Chief of Staff. This was done without the support of most of the military; because of this, the military officials rose up in rebellion and chose their own chief of staff. The third reason is that a new law regarding political parties united the parties that were not in power. In January of last year, President Ravalomanana pushed the national legislature—where the ruling TIM party held a majority—to carry out a resolution to reform the constitution with a regulation on political parties. This law dictated that an individual had to be a representative of a political party to run in a national election, and seemed to be directed at Andry Rajoelina, who in 2007 won the election to become mayor of Antananarivo, the capital city of Madagascar, based on his status as an independent who did not represent any particular party. In the past year, Mayor Rajoelina has had confrontations with the president on a number of issues, such as the distribution of development aid, the supply of electricity and water, and so forth. In the past, the country's opposition parties had all attended to their own work, but the new law on political parties led them to join forces to seek a majority in the legislature. Then Andry Rajoelina was chosen as opposition leader. In December 2008, President Ravalomanana ordered Andry Rajoelina’s radio and television stations to be shut down, and this became the driving force behind the unrest in Madagascar. With backing from the military, merchants , and foreign factions, Mr. Rajoelina kept raising his voice. In the past, he had said that he would enter the government, but now he was attempting to run the president out of office and even bring him to justice.


Glossary

Hausa Hausa Meaning
ta da zaune tsaye (lit: causing sitting and getting up) unrest
yan adawa (lit: children of opposition) opposition party
fadi-tashi (lit: rise up, fall down) political instability
yar gaban goshinsa (lit: the one who is on the front of his forehead) favored associates
tada bore rose up in rebellion

Bore is spelled properly as bori.

magajin birni (lit: brother of the city) mayor
sabanin ra'ayi had confrontations with
wutar lantarki electricity
yan kasuwa (lit: children of the market) merchants

Notes

1. Political Instability in Madagascar

Since becoming a sovereign nation in the 1960s, Madagascar has had a considerable amount of political instability. Recently, Andry Rajoelina took power from President Marc Ravalomanana with the support of the military, industry, and many politicians. Popular opinion does not see his position as president solidified because he seized power in the same manner that his predecessor did. Rajoelina used his influence as the Mayor of Antananarivo (the center of political and economic power in Madagascar) to overthrow the incumbent president. During the months of political unrest, the country’s economy—which is mainly based on tourism—has taken huge losses.

2. More Information

For more information about the political situation in Madagascar, read Barry Moody’s article “Madagascar Could Face More Instablility” (March 19, 2009), which is published on the Internet by Reuters at the following URL:

http://uk.reuters.com/article/homepageCrisis/idUKLJ228594._CH_.2420