UMD NFLC Hausa Lessons/106 Rising Ocean Levels

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/106)
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Rising Ocean Levels
 2. This is a report on the impact of global warming on Africa.
 3. Language: Hausa
 4. Topic: Economics/Politics
 5. ILR Level: 1+/2
 6. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High
 7. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 8. Modality: Reading
 9. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 10. Subject Area: Language
 11. Material Type: LLO
 12. Publication Year: 2009
 13. ObjectID: T8RHA16

Transcript


Original Translation

Matsalar sauyawar yanayi ta kawo babbar barazana ga zaman rayuwar mutanen da ke gabobin teku a Afrika


Sakamakon zama tamkar ruwan da matsalar sauyawar yanayi ta yi a duniya, ana ci gaba da samun dumamar yanayi da rikidar ruwan teku da narkewar kankara a duniya. Kwararru sun yi kashedin cewa, dukkan mummunan tasiri da matsalar sauyawar yanayi ta kawo zai iya janyo babbar barazana ga zaman rayuwar mutanen da ke gabobin teku a Afrika. Kwararre mai kula da tsarin kimanta yanayin ruwan teku a Afrika Geoff Brundritt ya yi gargadi da cewa, rikidar ruwan teku a duniya za ta iya kawo babbar barazana ga rayuwar kifaye, kana kuma za ta iya lahanta zaman rayuwar masu kamun kifaye na duniya, musamman ma na kasashen Afrika. Hukumar abinci da aikin gona ta M.D.D ta bayyana cewa, mutane na kasashe masu tasowa da ke gabobin teku na Afrika, mutane ne da suka fi fama da radadi a zaman rayuwarsu. Ba su da damar samun kyakkyawan ilmi, kana kuma ba su iya samun kyakkywan aikin kiwon lafiya da dai manyan ayyuka ba. Ban da rikidar ruwan teku, matsalar sauyawar yanayi ta kara haddasa dumamar yanayi a duniya. Masani a sashen nazarin gabobin teku da tekuna na jami'ar Cape Town na kasar Afrika ta kudu Larry Hutchings ya bayyana cewa, ko da yake, dumamar yanayin ruwan teku bai yi babban tasiri ga rayuwar kifaye ba, sai dai kawai zai iya janyo kifaye su yi kaura zuwa wurare masu sanyi. Amma, domin tabbatar da rayuwarsu, kamata ya yi masu kamun kifaye a gabobin teku na Afrika su je wurare masu nisa domin kamun kifi. Mataimakin shugaba mai kula da ruwan teku na sashen yawon shakatawa da yanayin kasa na Afrika ta kudu, Mondle Mayekiso ya bayyana cewa, yanzu kifin Sardine na yin kaura zuwa sauran wurare, ko da yake babu kwararrun shaidu da ke nuna cewa, wannan na da alaka da dumamar yanayin teku a duniya, amma a ganina, gaskiya, kamar yadda muka ce, "Ruwa ba ya tsami banza." Ko da yake a karkashin ruwan teku, yanayin wuri na da sanyi, amma da kyar za a iya kamun kifaye a wurin, kuma ba a iya sayar da irin wadanan kifaye da aka samu kamar yadda ake sayar da kifin sardine ba. Yayin da kasar Afrika ta kudu take fama da raguwar kifaye, kasashen yammacin Afrika na gamuwa da matsalar hauhawar ruwan teku da matsalar sauyin yanayi ta kawo, kwararrun da abin ya shafa sun yi nuni da cewa, lalle, matsalar sauyawar yanayi ta sa gabobin teku na kasashen Senegal da Kamaru su canja sosai, kuma kasashen da sukr fama da wannan matsala su ne Nijeriya da Gambiya da Burkina Faso da Ghana. Haka kuma kwararrun sun bayyana cewa, ruwan teku na kara hauhawa da saurinsa ya kai centimita 2 a ko wace shekara, lalle zai iya kawo rudani ga kasashen da ke gabobin kasashen Afrika.

Climate Change Threatens the Livelihood of Africa's Coastal Communities

Climate change is having an effect on global water resources, and increasing temperatures are changing the oceans and melting ice around the world. Experts warn that all of the adverse effects from climate change could pose a major threat to the livelihood of people living along Africa’s coasts.

The Chairman of the Global Ocean Observing System in Africa, Geoff Brundrit, warns that changes in the world’s oceans could pose a major threat to the survival of fish, which could in turn endanger the livelihoods of fishermen all over the world, especially those living in Africa.

According to the UN Food and Agriculture Organization, people who live in the coastal areas of developing countries are the most vulnerable. These people do not have the opportunity to receive a high level of education, and they lack access to quality healthcare facilities and infrastructure.

In addition to altering sea levels, climate change has brought about an increase in global warming.

Larry Hutchings, a scholar at the Department of Coastal and Oceanic Studies at the University of Cape Town in South Africa notes that, although the warming of ocean water has a minimal impact on the survival of fish, and it may only cause them to migrate to colder areas, fishermen in coastal areas of Africa must venture farther to catch fish in order to assure their own survival.

The deputy director general of the South African Department of Environmental Affairs and Tourism, Monde Mayekiso, explains that sardines are now migrating to other areas. Although scientists have so far been unable to demonstrate that this is due to the rising temperature of the world's oceans, in his opinion, as the saying goes, “There must be something in the water.”

Although the temperature of the deeper oceanic waters remains cold, it is more difficult to catch fish in those areas, and the kinds of fish that are available are not marketable, unlike sardines.

While South Africa suffers from a decreasing fish supply, the countries of West Africa are dealing with the problem of rising sea levels brought on by climate change. Experts in this matter claim that, in fact, climate change has already considerably altered the coastal areas of Senegal and Cameroon, and that countries such as Nigeria, Gambia, Burkina Faso, and Ghana are also threatened by this problem. Moreover, experts explain that the sea levels are rising at a rate of 2 cm per year, and that this is bound to bring chaos to countries along the African coast.

Glossary

Hausa English Meaning
rikidar ruwan teku changing the oceans
ba su da damar samun do not have the opportunity to
aikin kiwo lafiya healthcare facilities
kwararrun shaidu demonstrate
ruwa ba ya tsami banza (lit: water doesn't go bad without a cause) there must be something in the water
rudani chaos

Notes

1. Natural Resources in Africa

In general, natural resources are vital for development in Africa. Most of Africa’s population is dependent on rain for agricultural production. The oceans are an important source of food and transportation. Water resources are often limited in landlocked countries. Global warming is gradually affecting the fast growing population of Africa. Urbanization, deforestation, and lack of adequate technology hold back the continent’s economic growth. Increasing food shortages, land degradation, pollution, and loss of wildlife challenge governments to provide sustainable development.