UMD NFLC Hausa Lessons/113 Local Government

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Local Governments
 2. This is a discussion with current and former members of local government councils in Nigeria about the controversial management of local government funds and the influence of state governors.
 3. Language: Hausa
 4. Topic: Economics/Politics
 5. ILR Level: 2+/3
 6. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
 7. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 8. Modality: Listening
 9. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 10. Subject Area: Language
 11. Material Type: LO
 12. Publication Year: 2007
 13. ObjectID: HAUS_11905

Transcript


Original Translation

Local Government

A: Ɗaya daga cikin haƙidojin dimukuraɗiyya shi ne bayar da ƴancin cin gashin kai, ga matakai uku da suka yi murhun dai tallafa salon mulkin watau matakan tarayya, da na jihohi da kuma ƙananan hukumomi. Sai dai akwai koke-koken cewa wannan tsari ba ya tafiya daidai tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi a Nijeriya, musamman ta fuskar sarrafa ikon dukiyoyinsu kamar dai yadda yake a tsakanin matakan tarayya da na jihohi. Wasu shugabanin ƙananan hukumomi sun sha kukan cewa gwamnatocin jihohin su suna yawan tsoma musu baki akan yadda za su sarrafa ƙasansu na dukiyan ƙasa da suke samu daga gwamnatin tarayya, bayan su jihohin ana ba su ikon sarrafa nasu ƙasan ba tare da tsoma baki ba. Wasu da muka yi hira da su sun ce ya kamata gwamnoni su ji tsoron Allah, su ƙyale shugabannin ƙananan hukumomin jihohinsu, su yi wa jama’ar da suka zaɓe su aiki.

B: Sunana Idriss Garba Anguwan Rimi shugaban ƙaramar hukumar Tofa. Na farko dai muna roƙon gwamnonin da suke wannan su ji tsoron Allah, su sani cewa za su je su ta yadda Allah, na biyu kuma ya kamata a riƙa bin dokar ƙasa da bin tsarin mulki na ƙasa domin a launi muke na dimukuraɗiyya.

C: Sunana Ɗan Kaka Alhaji Usaini Bebeji, shugaban ƙaramar hukumar Bebeji. To, hanya guda ɗaya ce su gwamnonin ya kamata su dubi Allah, su yadda cewa tun da gwamnati kashi uku ce akwai gwamnatin sama akwai ta tsakiya, su ke nan, akwai kuma ta ƙasa can ita ce ƙaramar hukuma, to ya kamata a ce kowa ya karɓi ƴancin kansa ya ci gahin kansa domin Nijeriya ta tafi bai ɗaya kuma a samu a yi wa jama’ar ƙasa aiki.

D: Sunana Abubakar Abdullahi shugaban ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano. Mukan tattauna da su kuma suna gaya mana irin halin ƙuncin da suke ciki wanda koma ba su faɗa ba muna gani … muna ganin irin {pressure [English]} da suke ciki da kuma irin yadda ba sa iya gudana da ayyuka wanda {directly [English]} zai je ga talakawa wanda suka yi zaɓen domin su

A: Shugaban ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Ƙwanƙwaso ya ce shi ganau ne ba jiyau ba na wasu jihohi da ba sa tausaya wa ƙananan hukumominsu. Kana da bayanin daga ƴan’uwanka shugabannin ƙananan hukumomi na waɗansu jihohin dangane da irin wannan matsala?

E: Ƙwarai kuwa ga ma kusa da ni nan {((--))} Ibrahim Gwamna Turaki ina tara da waɗansu daga cikinsu, wanda kawai kuɗaɗa ake bayarwa na akwati da sauran waɗansu ƴan kuɗaɗen? Sannan kuma akwai a Kaduna da sau … duk … duk Nijeriya nake gaya maka ba inda ake zakka kuɗin ƙananan hukumomi ba tare da an ɗiba musu kuɗi ko an ba an ba da umurni ba. Ko jiya na gani a jarida gwamna na Ekiti, ƙungiyar shuwagabannin ƙananan hukumomin nashi sun faɗi cewar an ɗebe musu wasu kuɗaɗe sama da biliyan goma sha ɗaya, wanda an karkata da su ne ba bisa oda ba. Saboda haka ina gaya ma ba wai na duk Nijeriya babu gwamna da yake ba ƙananan hukumomi kuɗinsu akan lokaci.

A: Gwamnonin dai sukan shiga aljihun ƙananan hukumomi su yi facaka ta hanyoyi daban-daban, wasu sukan ce a haɗa guyiwa a aiwatar da ayyukan raya ƙasa tare, a ƙarshe kuma, sai ka tara duk da cewa gwamnonin ne sukan bayar da kwangilar, kuma su karɓe ɗan hasifin da ƴan kwangila kan baiwa wanda ya ba su aiki, gaba ɗayan kuɗin aikin ƙaramar hukuma ce take biya. Ga shi kuma ƙaramar hukuma ba ta da ikon magana. Ko da kuwa an yi amaja a aikin, wasu kuma sukan tura ɗan kwangila ga shugabannin ƙananan hukumomi da zaran sun samu ƙasansu na wata, su ce a ba su aiki. Kuma shugaban ƙaramar hukuma, ba shi da ikon cewa a’a. Waɗannan masu ɗan sauƙin ke nan. Akwai gwamnonin da sukan karɓe duk abin da ƙananan hukumominsu suka samu, su ɗan tsakura musu abun da bai fi yin albashin ma’aikata ba, idan mutum ya yi magana kuma yanzun nan sai a cire shi. Wani tsohon shugaban ƙaramar hukuma a jihar Bauchi, Alhaji Muhammadu Mai Auduga ya ce wannan hallaya da ke hanawa ƙananan hukumomi aikin da suke bukata yana matuƙar sosa rai.

F: Wannan … ai ba zargi ba ne abu ne wanda ya tabbata tun da ba wai jama’a ne kaɗai suke yin wannan magana ba, akwai hukumomi na gwamnatin tarayya kamar misalin {AFCC [English]} wadda ita da kanta ta fito ta yi maganganu akan cewar akwai wasu gwamnoni na wasu jihohi wadda sun riga sun juya akalen asusun ƙananan hukumominsu ya zama kama na gwamnatocin jiha, suna amfani da shi, sabida haka wannan ba zargi ba ne, abu ne wanda ya tabbata ana yin sa kuma ya zama kaman ruwan ɗare gama duniya ne kusan akasari a Nijeriyan nan, kuma idan ba an yi maganinsa ban a tabbatar maka da cewar za a daɗe, ba a samu ci gaba a ƙananan hukumomin Nijeriya ba.

A: Abun da masu fashin baƙin al’amuran ƙasa suke faɗa shi ne, tsarin mulki Nijeriya ya saka ƙananan hukumomi a aljihun jihohi inda ya ba su damar yin amfani da majalisun jihohinsu su cire shugaban ƙaramar hukuma ko da kuwa bai aikata wani laifi ga ƙasa ko al’umma da suka zaɓe shi ba. Ɗan majalisar wakilai a Nijeriya mai wakiltar mazaɓar ɓaɓar da garkin jihar Jigawa, Alhaji Nasiru Garba Ɗan Tiye, shi ma yana jimamin halin da ƙananan hukumomi ke ciki:

G: Idan akwai abun ɗaya gurgunta da wannan dimukuraɗiyya, shi ne wannan tsarin mulkin da sojoji suna gagawa suka zo suka bayar, aka ɗauki iko da mulki na ƙananan hukumomi aka danƙara su ga hannun gwamnatin jiha. Gwamnatin jiha shi ne majalisa jihohi da ƙarƙashin gwamna. Wannan abu ba ƙaramin illa ba ne ga dimukuraɗiyya, za kaga gwamnonin nan, ba kuɗin da suke amfani da shi inla kuɗin jiha da kuɗin ƙananan hukumomi. Sun hana ƙananan hukumomi su zauna su yi aiki, saboda ba za ka yi aiki ba aiki dai wannan abun da ake kira aiki …

A: Mhhmm

G: Ba za ka yi shi ba, na gwamnati sai da kuɗi. Idan babu kuɗi babu yanda za ka yi kowane sai an hanƙura, akwai jihar ma da na tabbatar tsakani na da Allah ba a ba su {up to twenty percent of [English]} abun da suke abu nan. Ba wanda ya isa ya yi magana, ba wanda ya isa ya yi magana saboda kai {chairman [English]} ba ka isa ba, saboda haka wannan abun in ba gyara shi aka yi ba, aka duba tsarin mulki na Nijeriya aka gyara shi, gwamnoni ba su bar dimukuraɗiyya ta yi ba saboda suna cinye kuɗin ƙananan hukumomi, suna cinye kuɗaɗensu kuma sun maida kansu alloli, sun maida kansu kaman ba ƴan Nijeriya ba ne, kaman ba zaɓensu aka yi ba. Wannan abu dole ne a yi gyara a Nijeriya in ana son a sami yadda biyan bukata na dimu- … ah … ah … abun da ake kira {dividend [English]} na dimukuraɗiyya.

A: To, ina mafita? Yawancin malaman da muka yi wa wannan tambaya dai, sun ce mafita ɗaya ita ce ta gyara tsarin mulki domin ya baiwa ƙananan hukumomi cikakken ƴanci daga tsoma bakin gwamnatocin jihohinsu. Wasu kuma suka ce tun da fari badaƙalar da ƙananan hukumomi suka riƙa yi da dukiyoyin ƙananan hukumominsu, shi ne ya jefa su cikin halin da suka shiga a halin yanzu. Babbar magana dai in ji waɗansu ita ce gwamnoni su ji tsoron Allah, su yi wa ƙananan hukumominsu adalci. In an bi ta ɓarawo, a bi ta mabi sau in ji bahaushe. Kamar yadda masu sharhi suke ta faman faɗa idan kowa zai yi wa kansa da sauran jama’a adalci, to kome zai inganta.

Local Government

A: One of the rights of democracy is to give freedom of argument. There are three levels that go into providing for the pattern of authority, that is the federal level, those of the states, and also the local governments. But there are the complaints that this system doesn’t work well between the states and the local governments, especially regarding control over their wealth, such as it is between the federal and state levels. Some local government leaders have complained bitterly that their state governments have interfered a great deal in how they would control their share of the country’s revenue that they get from the federal government, while states have been given control over their own land without interference. Some that we have spoken with say that governments should fear God, allow the local government leaders freedom to operate in their states, to work for the public that elected them.

B: My name is Idriss Anguwan Rimi, head of Tofa Local Government. First of all, we are asking that governments here be God-fearing, and realize that they will eventually face God’s judgment. And secondly, one should follow the laws of the land and the country’s hierarchy of authority because we are in a democratic system.

C: My name is D’an Kaka Alhaji Usaini Bebeji, the chairman of Bebeji Local Government. Well, the number one approach is that those in government must look to God, and agree that since government has three divisions – there is upper and middle government here, and there is also the lower government there, that is the Local Authority. So we should say that each one should accept its independent responsibility to take up its own tasks so that Nigeria works together for the population.

D: My name is Abubakar Abdullahi, chairman of Wudil Local Government in Kano State. We have been discussing it with them and they tell us about the difficult position they’re in, which we understand even without them saying it. We understand the kind of pressure that they are in as well as the fact that they can’t administer the system whereby it might go directly to the common people who have elected them.

A: The chairman of Madobi Local Government in Kano State, Alhaji Musa Iliyasu K’wank’waso, says that he is a witness to the contentious relationship in which some states have no sympathy for their local governments. Do you have an illustration from your fellow Local Government heads and their states relating to this kind of problem?

E: Indeed, right here next to me, Ibrahim Gwamna Turaki. I was meeting with some of them, who had been paid a box of money from other moneyed interests. And then in Kaduna and elsewhere … all over … all over Nigeria I’m telling you, there’s no place that local government taxes are collected where there’s not also embezzlement from them, regardless of laws in place. Just yesterday I read in the newspaper about the governor of Ekiti, a group of Local Government heads of his said that more than eleven billion had been embezzled from them, and diverted without any permit. So I’m telling you that throughout Nigeria there’s no governor who gives the Local Governments their money on time.

A: Governors regularly raid the pockets of Local Governments to squander money in different ways; some of them conspire to carry out development activities together, but in the final analysis, it’s the governors that are awarding the contract, and they accept a small kick-back that the contractors give to the one who gives them work, and all at once the operating budget comes from the Local Government. And the Local Government doesn’t have the authority to talk about this. Even if there’s sloppy work being done, some just direct the contractor to the Local Government heads with orders that they be given contracts. And the Local Government head doesn’t have any authority to say no. Those are the cheap ones. There are governors who take everything their Local Governments receive, by skimming off a little at a time, leaving them only workers’ wages, but if anyone says anything about it he’s immediately fired. One former Local Government chairman in Bauchi State, Alhaji Muhammadu Mai Auduga, said these habits that prevent local government from working for their people as needed, are disturbing.

F: This … alas, it’s not just an accusation, it’s something that we’re certain of, since it wasn’t only the public who were talking about it. There are a few federal government agencies such as the EFCC, which came out on its own to publicize the fact that certain governors of certain states had already transformed their local governments’ funding so as to become like that of the state governments to use. So it’s not an idle accusation, it’s something that’s certainly being done, and it’s becoming like an unrestrained disaster [night-time rains that flood the world] in most parts of Nigeria, and if this is not resolved, I assure you it will take a long time before Nigeria ever progresses.

A: What those who are well-versed in the country’s affairs are saying is this: The structure of power in Nigeria puts the local governments in the pocket of the states when it gives them the opportunity to use their state legislatures to depose a local government head, even though he has done no harm to the country or to the public who has elected him. Member of the Federal House of Representatives representing Jigawa State, Alhaji Nasiru Garba D’an Tiye, discusses briefly the nature of local governments there.

G: If there is one thing that is crippling this democracy, it is this power arrangement that the military has quickly established, whereby local governments’ power and authority were taken up and concentrated into the hands of state government. State government is the state legislative body under the governor. This is no small weakness in a democracy, as you will see these governors, whose only source of finance is the state and local government treasuries. They prevent the local governments from getting down to work, because you can’t do your work, or what passes for work …

A: Mhhmm.

G: You cannot do government work without money. If there’s no money, there’s nothing you can do, whatever patience one has. There is a state that I swear to God was not given up to twenty percent of what they needed. No one dared discuss it, no one dared to talk about it because you, the chairman, will not dare. So if this thing doesn’t get fixed, by looking at the power structure in Nigeria and fixing it, the governors won’t let democracy work, because they’re spending the local governments’ funds, they’ve changed themselves into fetishes, they’ve changed themselves as if they’re not Nigerians, as if nobody had elected them. This must be fixed in Nigeria if we want to find out how to fulfill the needs of democra-- … ah … ah … what’s called the dividend of democracy.

A: Well, where’s the way out? Most of those we questioned said the only way out is to correct the power structure so that it gives local governments complete freedom from interference by their state governments. Others point out that giving the local governments the right to spend freely was the beginning of the problem initially. The most important points according to some is that those governors should fear God and be fair to their local governments. According to the Hausa, in order to trace the thief, follow the footprints of those chasing the thief. And as the commentators are at pains to point out, if everyone would be fair to himself and the rest of the public, then everything will work out.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
Tsoma masu baki Suna yin tasiri bisa tafiyar da abubuwa da ba nasu ba ta wurin magana. To interfere in the handling of matters that do not concern one directly by speaking
Su ta yadda Allah ( Su tarda da Allah) Wannan magana ce da akan yi anfani da ita cikin hirar addini; tana nufin tuna wa mutun da ya yi kome da gaskiya domin a ƙarshe zai fuskanci Allah kuma ya ba shi lissafin ayyukansa ko ayyukanta. They will face God; this saying is usually stated in a religious context to remind people that they will give an account of their deeds to God, and therefore they should be honest.
Ganau ne ba jiyau ba. Wannan magana tana nufin mutunen ya ga abinda yake magana a kai, ba ya ji ba kawai. This expression implies that a person has witnessed what he or she is talking about, and has not only heard it. It reflects the veracity of a statement or the reality of a fact.
Shiga aljihun... A nan ana nufin aiki da kuɗin da suka fito daga wani ma'aji wanda ba na mutun ba. This expression means spending money that comes from sources other than one's own pocket.
Haɗa guyiwa a aiwatar da... A yi aiki tare domin a biya wata bukata. Make a joint effort to carry out something
An yi amaja a aikin... An yi aiki wanda ba nagari ba. A yi aiki da ha'inci, ko cikin raggonci. This expression means to slacken at a job, or do something wrong at work.
Yana matuƙar sosa rai. Abu ne wanda yana bada damuwa dayawa. This expression means something that is of great concern to somebody.
Ruwan dare gama duniya. Wannan karin magana ne na hausawa kuma ana nufin wani abu da yake shafa jama'a ko fannoni dayawa. This is a hausa proverb which means that something has reached a general scale. It describes something that is common or an ordinary act.
In an bi ta ɓarawo, a bi ta mabi sau.. Wannan karin magana ne na hausawa wanda yake nufin a bi hanyoyi daban-daban domin a gano da inda matsirin matsala yake kuma a yi gyara. This is a hausa proverb that means looking at things from differrent angles to find a cause and a solution.

Note

Hausa Note English Note

Rashawa, babban magana ce cikin siyasar Nijeriya, kuma lokacin da Obasanjo ya hau mulki a 1999, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ya fara shi ne kafa wata hukuma da ake kira 'Economic and Financial Crimes Commission' (EFCC), wadda ke hukuntar mayyan ma'aikata, kuma ta dawowa da kuɗaɗe da aka ko shugabanai suka sata. Ita wannan hukumar ta ƙayyadar da cancantar 'yan takarar zaɓe na 2007 cikin hali wanda shike rashawa ta kawo rashin yarda da shugabanni ga jama'a.

Corruption has been a prominent issue in Nigerian politics, and when Obasanjo came to power in 1999, one of his first actions was to set up the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), which persecuted many high-ranking officials and recovered stolen funds. In a situation where corruption has undermined the leadership's public accountability in the eyes of the people, the commission played a major role in the qualification of candidates for the 2007 elections.

XML<activity>
  <finishtl>Yaya shugabannin gwamnatin tarayya ke iya tsaida gwamnonin jiha daga ci wa ma'aikatan ƙananan hukuma da burga domin su kare kansu?</finishtl>
  <finish>In your opinion, how can federal authorities stop state governors from seeking to protect themselves by intimidating other workers into covering up their mismanagement of public funds?</finish>
  <finishtl>Yaya kuke ganin za a iya tsaida irin wannan ɓata kuɗin jama'a da gwamnonin jiha suke yi?</finishtl>
  <finish>How do you think state governors could be stopped from squandering public funds?</finish>
  <finishtl>Cikin irin wannan halin kuna ganin canji tsarin mulkin Nijeriya na iya sa jama'a su yi aiki tare cikin gaskiya? Ta yaya?</finishtl>
  <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
  <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
  <problemset>
   <problem correctindex="2">
     <choices>
      <opt>
        <eng-response>In this report, current and former chairmen of Nigerian local government councils address the deplorable interference of state authorities in local budget management, an interference that has caused fear and helplessness. Sharing stories of state governors who take money for their own use from local government treasuries, they denounce the failure of the federal government to tackle a general problem that will not stop unless regulations are changed, and the country develops a unified system that returns financial autonomy to local authorities. They call upon governors to put their religion first, and to be honest and work in a democratic way in order to obtain economic stability for their people and for the country in general.</eng-response>
        <response>A cikin wannan rahoton shugabannin ƙananan hukumomin Nijeriya na da da na yanzu, suna magana bisa yadda gwamnatocin jiha ke malakar sarrafawa kuɗinsu, da kuma irin halin tsoro da wannan ya kawo . Sun bada bayyanai da suka daidaita da juna, bisa ga yadda gwamnonin jihan ke anfani da kuɗin ƙananan hukumomi domin muradin kansu kuma, da kasawar gwamnatin tarayya don tattalin yin maganin matsalar da ƙarewarta ya danganta da canjin wasu ƙa'idodi, da haɗin kan ƙasa ga ba ƙananan hukumomin cikkaken yanci na tsara kuɗinsu. Sun yi kira ga gwamnonin, da su sa addininsu gaba da komi, su zama masu gaskiya, kuma su yi aikinsu bisa ƙa'idodin dimukkuraɗiya, domin a samu tabbatacewar tattalin arzikin jama'a da ƙasa gabaɗaya.</response>
        <fdbk>Ba daidai ba ne. Wannan zaɓen bai dace ba saboda wasu magangannun ba daidai yadda masu maganan suka faɗesu ba ne cikin bayyanai da suka bada bisa yadda gwamnoni suke ɓata kuɗi, da kuma yadda wannan aikin tsorata da ƙananan hukumomi, sai kuma maganar kasawar gwamnatin tarayya. A ƙara saurara rahoton. Wane irin tsoro ne suke magana a kai, kuma yaya suke kawo zancen gwamnatin tarayya ciki bayyanansu?</fdbk>
        <eng-fdbk>Incorrect. This is not the best choice because some comments, such as fear in local authorities and “failure of the federal government,” are not quite what the speakers said in describing the unethical management of local funds by governors, and the impact of such practices. Please listen again to the report. What kind of fear is mentioned and what is their approach to the federal government?</eng-fdbk>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>The main point of this report is that, contrary to democratic principles, state governors in Nigeria control financial activities of local governments, bringing local economies to a state of helplessness and decay. Rampant corruption makes it difficult for business people to succeed and for civil servants to help their communities because funds are mismanaged or stolen by high-level, influential authorities. The local government chairmen express their concern, calling for changes in mentality, behavior, regulations, and leadership in order to give all Nigerians the right to participate in the development of their country. They suggest that democracy should be taken into account in every aspect of public funds management.</eng-response>
        <response>Mahimmi bayyanin wannan rahoto shi ne a Nijeriya gwamnonin jiha ne suke faɗi a ji bisa yadda za a yi anfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, abin da ka'idodin dimukuraɗiyya ba su ce a yi ba; ta haka kuma suna sa cikas ga tattalin arzikin ƙasa.
Yaɗuwar rashawa ta zama matsala ga albarkatuwar 'yan kasuwa, da taimakon ma'aikatan gwamnati ga jama'a saboda ana rashin gaskiya cikin tafiyar da harakokin kuɗin, ko kuma masu babban matsayi suna sata. Shugabanni na ƙananan hukumomin sun nuna damuwarsu wajen kira da suke yi na canjin yadda ake ɗaukar aiki, da dokoki, da kuma shugabanci, domin a ba dukan 'yan Nijeriya 'yancin su shiga cikin aikin tattalin arzikin ƙasa. Sun bada shawarar a yi harakar kuɗi dangance da yadda dimukuraɗiyya ke so a yi.</response>
        <eng-fdbk>Incorrect. This is not the best choice because it does not reflect some important elements of the report, such as the solutions suggested by the speakers—for example, the reform of the constitution. Think about the different comments on how governors should behave. What other specific solutions do they suggest?</eng-fdbk>
        <fdbk>Ba daidai ba ne.Wannan zaɓen bai dace ba saboda ba a bayyana hanyoyin da masu maganar suka bayyana ba don yin maganin rashin gaskiya wajen tafiyar da harakar kuɗi. Ku ƙara tunani bisa ra'ayoyi akan yadda ya kamata halin gwamnoni ya zama. Wane irin gyara suka shawarta?</fdbk>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>This report discusses the implication of Nigerian state governors in corrupt practices that disregard democratic principles, paralyzing the capacity of local authorities to sustain their localities. A journalist and various current and former chairmen of local government councils contend that state-level authorities embezzle or squander local government funds, whether by forming contract arrangements, taking away commissions, or stealing outright. Some think that the constitution inherited from military governments, as well as the authorities’ despotic rule, have together given governors the power to control local finances. They suggest that changes should come through reform of the constitution, fear of God, and transparency.</eng-response>
        <response>Wannan rahoto ne bisa shigar gwamnonin jiha na Nijeriya cikin ayyukan rashawa da rashin yin hankali da ka'idodin dimukuraɗiyya, wannan tabi'a ce da take gurguntar da ƙoƙarin ƙananan hukumomi na tabbatar da cikakken biyan bukatar harabansu. Wani ɗan jarida da shugabannin ƙananan hukumomi daban-daban, na halin yanzu da na da, sun yarda da cewa mayyan hukumomin jiha suna yin zamba, ko suna ɓatar da kuɗin jama'a ta wurin tsara kwangila don a ɗauki kuɗi, ko kuma wani lokaci ɗaukar kuɗin musamman. Wasu suna ganin tsarin mulkin da mulkin soja sun yi a baya, da kuma kama karyar hukuma sun ba gwamnonin iko bisa asusan kanannan hukumomi, saboda haka duk canji da za a yi sai ya bi ta gyaran tsarin mulkin, da tsoron Allah, da kuma adalci.</response>
        <fdbk>Daidai ne. Cikin wannan taƙaitawar akwai bayyanin mahimman abubuwa da suke sa a fahimci kan magana, ga ƙarfin rashin gaskiyar gwamnoni cikin sarrafar da kuɗin jama'a, kuma da yadda wannan ke shafar tattalin arzikin jama'ar da ƙasa. Ana kuma bada shawarwarin waƙilan hukumomi masu son ganin ƙarshen wannan rashawar.</fdbk>
        <eng-fdbk>Correct. This choice reflects the main aspects of the report in the sense that it helps convey the magnitude of the state governors' mismanagement of local government funds, and its social and economic impacts. It also reflects the reactions of concerned officials and their various suggestions for ending rampant corruption.</eng-fdbk>
      </opt>
     </choices>
   </problem>
  </problemset>
  <finish>In the current situation, could reforming the Nigerian constitution bring people to work together in a transparent way? How?</finish>
</activity>