UMD NFLC Hausa Lessons/130 Corruption in Niger's National Assembly

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Overview

Lesson Title: Corruption in Niger's National Assembly

This is an interview with a political analyst about issues political scandals in Niger.

 1. Language: Hausa
 2. Topic: Economics/Politics
 3. ILR Level: 2+/3
 4. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
 5. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 6. Modality: Listening
 7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 8. Subject Area: Language
 9. Material Type: LLO
 10. Publication Year: 2009
 11. ObjectID: T8LHA04

Transcript


Transcript Translation

Abun da kundun tsarin mulkin Niger ya ce game da rushe majalisa dokoki


A: Na tattamna da Asumana Malam Isa mai fashin bakin al’amuran yau da kullum, don…, watau, a kasar ta Jamhuriyar Nijer, domin mu ji abin kundin tsarin mulkin Nijer ya ce game da rusa majalisar dokoki. Amma kan nan, na bukaci Asumana Malam Isa ya mana, matashiya game da laihuhhukan da ‘yan majalisar dokokin kasar ta Nijer suka yi, wadanda suka halasta, watau wadanda suka hasala talakawa, har suke kiran shugaban kasar Tandja Mammadou ya rusa majalisar dokokin.


B: E! hujjoji dai wa’yanda suke mutane suke sawa a gabansu suke zancen cewa a rusar da wannan majalisar dokokin, ta farko dai kina tune da cewa dangance da albashin da ake ba ma ‘yan majalisar dokoki sun dauki wani kudiri wanda ake cema E! {delebirashin [French]} wanda suka…ya suka ba kansu damar su samu albashinsu dangance da abinda ya kamata a ba su na wata, milyan daya da jakka dari hudu, ko kusan jakka dari hudu. To sai ya kasance wannan {delebirashin [French]} din ba ita ce ya kamata ta ba su damar daukar wannan albashin ba. Doka ce ya kamata su dauka. To a lokacin da abin ya kawo jaye-jayayya sai aka tambayi ra’ayin {kot konshinel [French]} wadda ta ce e’e lallai bassu da gaskiyar daukar wa’yan nan kudin. To bayan ma an huddo wannan kudirin na {kot konshinel [French]} sai suka cigaba da nuna cewa kamar wannan ‘yancinsu ne har ya kasance cikin E! E! kasafin kudi na bana na dubu biyu da tara suka maido wadannan kudaidanin nasu. Shi ya sa lokacin da kungiyoyin farar hula suka tashi suka ce nan kai sun taka doka, kuma baicin ma sun taka doka an ba su ra’ayin {kot konshinel [ French]} ba su yi aiki da shi ba. Ke nan laifi ne babba cikin tahiyar da demokrasiyya a cikin kasa, har ya kasance shugaban kasa ya maido musu wannan kasafin, ya ce a’a sai su kara sake shi, su cancanja su maida shi dangance da abin da {kot konshinel [French]} ta ce a yi aiki da shi. Wannan laifi ne na daya. Laifi na biyu, E! kin san da E! yau lokacin da aka yi {moshon de sonsol [French]} ta karshe, har aka tada shugaban {gobanimar [French]} wanda kowa ya sani, Hamma Amadou cewa da an kai yana da hannu cikin wannan e! {ansar kai [French]} wadda aka ci kudin ‘yan makaranta hiye da milyar hudu, wadda ake cema {ansar nema [French]}. To sai aka gano cewa da akwai difitoci da yawa wa’yanda sunannakinsu, sun hito cikin binciken da aka yi. To a halin yanzu sai {gobanimar [French]} ya ce a! ku ‘yan majalisar dokoki ku tube ma wannan defute uku rigunansu saboda kundin tsarin mulki ya ba su ‘yancin cewa ba a iya ayi musu wani abu in su na tahiyar da aikinsu. To wannan rigar sai an hidda ta, sai in kuma su ‘yan majalisar dokoki sun hudda, sai suka zo suka yi wannan {seshon estaradiner [French]} ta su aka kwana aka tashi, suka ce su ba su hidda wannan saboda zaben da an ka yi bai samu rinjaye yadda kundin zabe ya ce a yi ba in ana son a hudda wannan rigar. Kin ga wannan talakawa duk ba su ji dadin shi ba don duk wa’yanda suka ba da ra’ayoyinsu sun nuna cewa da kenan an hudda ma shi Firaministar, kuma sun dauko Minista biyu sun tura su gaban kotu, me yasa za su hana tunda dai saurarensu ne za a yi, su tura wadannan difitocin mutum uku aje a saurare su, su ba da ra’ayoyinsu in su na da abinda za su kare kansu su kare kansu. To wannan rashin bada damar kotu ta yi aikinta shi ne talakawa ba su ji dadin shi ba, shi ne hujjoji na biyu. Hujja ta biyu, wadda dai mutane suke ganin da sun yi laifi kuma ba karamin laifi ba.


A: Ko za ka iya gaya mana abinda kundin tsarin mulkin kasar jamhuriyar Nijer ya hwadi gameda rusa majalisar dokoki?


B: To kundin tsarin mulki Halima, lallai a kudirin shi na hamsin ba biyu, arba’in da takwas ke nan ya ba ma shugaban kasa ’yancin ya rusa {assembly [English]} amma bayan ya tuntubi Firaminista da {president din assembly nationale [French]} a ce bayan ya tuntube su, yana iya ya rushe {assembly [English]}. Amma kudirin zab…wannan kudirin bai bada ba wane hujjoji ne za su tura shugaban kasa na ya rushe {assembly [English]} amma yana da wannan ’yanci.


A: Yawwa to! daga karshe Asumana Malam Isa a tattamnawar da, ko kuma in ce a martanin da dan majalisar dokoki Zilli ya maida ya nuna cewa kungiyar kare hakkokin jama’a tunda kamar siyasa take kawai ta zo ma ta zama jam’iyyar siyasa. A ganin ka, wannan kungiya tana iya zama siyasa, a! jam’iyar siyasa, kuma tana da ‘yancin yin haka?


B: Magana ce ita, irin ta bacin rai. Kamar shi Zilli yana son ya nuna bacin ranshi ne dangance da su wadannan kungiyoyi na farar hula sun tashi sun yi tsaye tukuru sun nuna cewa duk abinda {assembly [English]} take nan ga yi wanda ba na kwarai ba, bai kamata a bari tana yin shi ba. Bai kamata ba shi matsayinshi na dan majalisar dokoki, ba ma shi dai ba, ai har {president din kwamishin nationale [French]} wanda ake ce ma Alma Oumarou. A matsayinshi na {president commission nationale [French]} kuma a matsayinshi na wakilin talakawa, bai kamata su hito suna cece-kuce da kungiyoyin farar hula ba. Da Zilli da shi {president [English]} da duka defute wa’yanda suke hitowa su na nuna bacin ransu, kan su bata ransu ya kamata su yi nadama. Su ce lallai sun yi kuskure tunda dai har da aka maido masu kasafin kudin sun yarda sun kawo gyaran huska. Ke nan, sun yarda da sun yi kuskure. Sai su ce ma talakawa mun yi kuskure a yafe mu, su nemi gafara ga talakawa ba ga shugaban kasa ko ga wani ba, ga talakawa ya kamata su nemi gafarar cewa, da sun yi kuskure, saboda mun yi imani da cewa akwai da yawa cikinsu basu san abinda ya auku ba. Amma sai su huto su na wani cece-kuce, su na cacar-baki da ‘yan kungiyoyin farar hulla. Kuma Alla Ya nuna mana yau a rana tsaka da sun hisu gaskiya, ‘yan farar hullar ma in ba da sun ka yi tsaye ba da wannan, wannan mugun abu na fannin cin kudin kasa da sun ka soma da ba a san lokacin da zai tsaya ba. Ke nan, bai kamata su na irin wa’yan nan magunguna ba. Na farko, na biyu kuma sun ma kansu nafiza ne, yau duk abinda ya kamata wani ya gayi, musamman ma irinsu su da suke fadi a saurare su ya kamata ya kasance abu ne wanda mutane za su koyo gare shi. Ni yau kin bani daman ma in gayi wani abu da Zilli ya gayi wanda ban ji dadin shi ba a wani {deba- [French]} da sun kai a nan Nijer. Ya ce shi wannan {kwansitushen [French]} ta Nijer babu ruwan shi da ita, a matsayin shi na dan majalisar dokoki, kuma dan babu, a cikin babu ruwanshi da ita, ana ba shi kudi da sunan wannan kundin zaben yana ci. A matsayinshi na dan majalisar dokoki ba a iya a ci mai mutunci saboda ita wannan kundin zaben ya kare shi. To yana da ‘yancin ya huto a huskar {telebishen [French]} na duniya ya ce ma mutane shi ba ruwanshi da {konshitushen [French]} din Nijer? Ba ya aiki da ita ((alarika)) yana nan yana amfani da ita. Wa’yan nan maganganuwa ne wa’yanda bai kamata ba dattijawa kuma shugabanni irinsu Zilli irin wa’yanda duk ‘yan majalisar dokoki su hito su na fadi. Saboda Allah da Annabi. Abinda ya kamata mu nema shi ne kowa ya yarda da cewa ya yi laihi, ko kuma kowa ya yarda cewa ko mutum ya yi laihi ana iya ayi ma shi gafara in ya nemi gafara, ba a zo ai ta jaye-jaye ba har kwarya ta barke.


A: To fa kun ji abubuwan da ‘yan majalisar dokokin kasar ta Nijer suka yi wa wa’yanda suka hasala talakawan kasar.

The Issue of the Constitutional Right to Dissolve the National Assembly


A: I spoke with Alumina Malam Isa, a current affairs analyst, to . . . that is, in the Republic of Niger, so that we might understand what the constitution of Niger says about dissolving the National Assembly. But first, I asked Asumana Malam Isa to remind us of the offences committed by members of the National Assembly that have shamed, or rather angered, the public to the point that they were calling on President Tandja Mammadou to dissolve the National Assembly.


B: Yes, the reasons that people put forth, in saying that this National Assembly should be dissolved were, first of all, as you recall, related to the salary being paid to National Assembly members. They adopted a resolution, called a deliberation, whereby they-they awarded themselves monthly stipends of nearly 1.4 million CFA francs [about 2,800 USD as of December 2008]. Well, then it turned out that this délibération didn’t necessarily give them the right to receive such a stipend. They must follow the law. So, when push came to shove , they sought the opinion of the Constitutional Court, which said that they had absolutely no right to receive this money. Well, after this decision by the Constitutional Court was handed down, they continued to argue that they were entitled to it, so, in last year's budget [2009], they restored this benefit. This led civil rights organizations to stand up and say that they had disregarded the law and that they had also disregarded the law when they were given the Constitutional Court’s opinion and refused to accept it. This was a major assault on this country’s democratic process, so the president sent this budget back to them and demanded that they make additional changes and restore it to what the Constitution Court had said they must accept. That’s the first offense. The second offense, as you now know, was when the final censure motion was passed against a government leader that everyone knows, Hama Amadou, who was involved in a scandal known as the “MEBA affair”, in which more than 4 million [CFA francs] in educational funds were embezzled. Well, then an investigation uncovered that several deputies [National Assembly members] had been involved in this. So, then, at that point, the government told the members of the National Assembly to remove the deputies’ immunity before taking any legal action against them because the constitution code gives them immunity in the course of their work. So the dismissal order was announced, and the members of the National Assembly met again and held their special session. After several days, they said they would not carry out the dismissal because it had not received the majority of votes required under the voting rules in order to carry out such a dismissal. And this, you see, is what the public was unhappy about because everyone who expressed their opinion on the matter indicated that even the prime minister had been deposed, and they had taken two ministers to court. So why would they prevent these three deputies from testifying, and, if they had anything to defend themselves with, providing a defense? This lack of regard for the court doing its job was what the public was upset about. That was the second reason—the second reason why the public felt they had misstepped, and it was no small misstep at that.


A: So, could you tell us what the constitutional code of the Republic of Niger says about dissolving the National Assembly?


B: Well, Halima, in fact, Article 48 of the Constitution gives the president the right to dissolve the National Assembly, but only after consulting with the prime minister and the president of the National Assembly, and it says that once he has consulted with them, he can dissolve the Assembly. But the regulation on elect— this regulation doesn’t provide any reasons that would compel the president to dissolve the National Assembly, but he has the right to do so.


A: I see. Well, finally, Asumana Malam Isa, in a previous conversation, National Assembly member Zilli responded by indicating that when a civil rights group is involved in politics, it starts to become a political party. In your view, can such a group become political—a political party, and does it have the right to do so?


B: It comes down to frustration. Zilli wanted to express his frustration with these civil rights groups when they stood firm and claimed that the National Assembly shouldn’t be allowed to do all of the things it was there to do, which wasn’t much. He mustn’t do this in his position as a member of the National Assembly, nor should the president of the National Commission [sic, Parliamentary Finance Commission), Alma Oumarou. In his position as president of the National Commission, and in his position as a representative of the people, they shouldn't come out and have angry exchanges with civil rights groups. Zilli, the president, and all of the deputies that came out and expressed their frustration should apologize for their outbursts. And they should say that they were mistaken when their budget was returned to them, and they agreed to bring reform. They should admit their error. Then they should say to the public, “We made a mistake, forgive us,” and seek the forgiveness of the people, not the president or anyone else. [They should] seek forgiveness for their mistakes from the people because we believe that there are many among them who don't know what happened. But then they came out and were squabbling and trading insults with the people from the civil rights groups. And God showed us clearly that the civil rights groups had the truth on their side. And if people from the civil rights group don’t stand up to this, who knows when this terrible problem of embezzling from the state coffers will stop. They shouldn't have these kinds of protections. That's the first point. And secondly, this is something they should know: These days, when someone says something, those who are listening should try to learn from it. Today, you have given me the opportunity to talk about something that Zilli said that I'm not happy about, which has caused a big uproar here in Niger. He said that the constitution of Niger was of no concern to him in his position as a National Assembly member and an obstructionist, and in his disregard for it, he is being given money and spending it in the name of voting rules. He cannot be humiliated in his position as an assembly member because the voting rules protect him. So does he have the right to appear on television all over the world and tell people that the constitution of Niger is of no concern to him? He doesn’t accept it, but he is here, and he uses it. These are not words that respectable men and leaders like Zilli or any member of the National Assembly should say. For the sake of God and the Prophet. What we must strive for is for everyone to accept that they have done wrong, and for everyone to agree that even though a person has erred, he can be forgiven if he seeks forgiveness, so that the situation does not escalate into a larger conflict.


A: Well, you’ve heard what members of the National Assembly of Niger have done to anger the public.

Glossary

Items Explanations
a kwana a tashi push came to shove
tsaye tuƙuru stood firm
MEBA (French) MEBA is a French acronym for Ministère de l'Éducation de Base et de l'Alphabétisation, which means "Ministry of Basic Education and Literacy Training Program."
lattizawa (also, dattijai) (lit: important person) member of the National Assembly
a rana tsaka (lit: in the middle of the day) clearly
babu ruwanshi da ita no concern to him
Saboda Allah da Annabi for the sake of God and the Prophet
kwarya ta ɓarke (lit: the calabash cracks) escalate into a larger conflict

Notes

1. Niger’s Political History

Niger, originally a French colony, became a sovereign nation in 1960. Niger has had periods of political instability throughout its history, including periods of constitutional change and military rule. Most recently, Prime Minister Hama Amadou was ousted by the National Assembly because of his involvement in the Affaire MEBA, a scandal that involved the embezzlement of education funds by government ministers.

2. The National Assembly

In 1999, under the new constitution, the National Assembly became the legislative branch of the Nigerien government, though the president retains the constitutional right to dissolve the National Assembly. The National Assembly is currently made up of 113 members; each member is elected to serve a term of five years. The members of the National Assembly have political immunity when they are in office; this protects them from being charged with crimes. When several members of the National Assembly were implicated in the MEBA scandal, the public called for a suspension of the political immunity held by the assembly members. At the same time, the National Assembly was found to have illegally allocated themselves stipends; some civil rights groups called for the dissolution of the National Assembly because of this.