UMD NFLC Hausa Lessons/26 The Refugee Crisis in Africa

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: The Refugee Crisis in Africa - This is a report about refugees in Africa.
 2. Language: Hausa
 3. Topic: Culture/Society
 4. ILR Level: 1+/2
 5. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 6. Modality: Reading
 7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 8. Subject Area: Language
 9. Material Type: LLO
 10. Publication Year: 2009
 11. ObjectID: T8RHA18

Transcript


Original Translation

Hukumar UNHCR na kokarin neman mafita ga dimbin 'yan gudun-hijira

Wani rahoto daga hukumar UNHCR ya ce, tun daga farkon shekarun 1990, an samu tashe-tashen hankula da fadace-fadacen da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin Balkan, da yankin babban tafki na Afirka, gami da kasashen Sudan da Chadi da Iraki, inda dimbin mutane suka bar matsugunansu suka fara gudun-hijira. Akasarin masu gudun-hijira sun tsere zuwa kasashe makwabta, inda suke yin dafifi a yankunan bakin iyaka da sansanonin 'yan gudun-hijira dake yankunan karkara. Ba ma kawai masu gudun-hijira sun haddasa cikas ga muhallin halittu, da albarkatun kasa, da sha'anin samar da guraben aikin yi na wuraren da suke jibgeba, hatta ma suna zama cikin halin tsaka mai wuya. Baligai sun kasa samun guraben aikin yi, yara kanana ba su da damar shiga makaranta, har ila yau kuma an gaza wajen biyan bukatun masu gudun-hijira na yau da kullum. A waje daya kuma, halin kaka-naka-yi da ake ciki a sansanonin masu gudun-hijira ya haddasa matsaloli da dama, ciki har da barkewar cututtuka masu yaduwa, da munanan laifuffukan fasa-kwaurin makamai, da sace yara kanana. Matsalar 'yan gudun-hijira, matsala ce da ta dade tana ciwa kasashen duniya tuwo a kwarya. A wajen taron da aka shirya a wannan rana, firaministan kasar Tanzaniya Mizengo Kayanza Peter Pinda ya gabatar da bayanin yadda kasarsa ke shirin warware wannan matsala, inda ya ce, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su sa kulawa sosai kan gungun mutane masu gudun-hijira, haka kuma kada su manta da irin kokarin da kasashe masu karbar 'yan gudun-hijira suke yi. A hakika dai, bisa kididdigar da hukumar UNHCR ta bayar, an ce, a halin yanzu, kasashe masu tasowa suna kokarin karbar akasarin 'yan gudun-hijira a duniya. Babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun-hijira na MDD, Antonio Guterres ya ce, daidaita matsalar 'yan gudun-hijira yadda ya kamata, nauyi ne dake rataye a wuyan dukkanin kasashen duniya. Ya kamata kasashen duniya su kafa wani tsari na daukar nauyi cikin adalci, a wani yunkurin daukar matakai na bai daya domin warware wannan matsala. Kazalika kuma, hukumar UNHCR ta sake jaddada cewa, tallafawa 'yan gudun-hijira, babban nauyi ne da aka dankawa kowace kasa. UNHCR ta kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara bada tallafin kudi wajen kyautata halin matsugunan 'yan gudun-hijira da samar da agajin jin-kai, domin warware matsalar 'yan gudun-hijira daga dukkan fannoni, da neman mafita ga 'yan gudun-hijira masu tarin yawa.(Murtala)

UNHCR Seeks a Solution for Millions of Refugees

A report from the office of the United Nations High Commissioner for Refugees (UNHCR) notes that, since the beginning of 1990, civil unrest and fighting has enveloped the Balkans, the Great Lakes Region of Africa, and the countries of Sudan, Chad, and Iraq. Millions of people have left their homes and become refugees. The majority flee to neighboring countries, where they are crowded together in border areas and rural refugee camps. Refugees not only have a negative impact on the environment, land quality, and employment dynamics in the areas where they congregate, but they also face difficult living conditions. Adults are unable to find employment, young children do not have the opportunity to attend school, and the refugees’ daily needs remain unfulfilled. Moreover, the dire conditions in refugee camps lead to many problems, including the outbreak of contagious diseases, the serious crime of weapons smuggling, and the kidnapping of children.

The refugee crisis is a problem that the world has struggled with for a long time. At a conference being held today, Tanzanian Prime Minister Mizengo Kayanza Peter Pinda presented an account of how his country was planning to confront this problem. In his presentation, he noted that the international community must pay more attention to refugee populations, and that the efforts being undertaken by countries that accept refugees must not be forgotten. Indeed, according to statistics provided by the UNHCR, it is developing countries that make the effort to accept the majority of the world’s refugees. UN High Commissioner for Refugees Antonio Guterres said that finding an appropriate solution to the refugee problem is a global responsibility. The international community must develop an equitable system for assuming responsibility and take steps to solve this problem accordingly.

In addition, the UNHCR reiterated that helping refugees is a major responsibility for every country. The UNHCR also called on the international community to increase financial aid for improving refugee housing, to provide relief assistance in order to address the refugee problem on all fronts, and to find a solution to the refugee population crisis. (Murtala) [Author’s name]

Glossary

Hausa English Meaning
suka ƙi ci suka ƙi cinyewa (lit: they don't stop consuming) has enveloped
yin dafifi they are crowded together
haddasa cikas have a negative impact
halin tsaka mai wuya difficult living conditions
ciwa ƙasashen duniya tuwo a ƙwarya struggled with for a long time
gamayyar ƙasa da ƙasa the international community
nauyi da ke rataye a wuyan (lit: a weight on everybody's neck) a major responsibility for every country
agajin jin-kai relief assistance

Notes

The UNHCR: The office of the United Nations High Commissioner for Refugees (UNHCR) was created to defend refugees’ and displaced people’s rights worldwide. The agency also assists in the relocation of refugees. For more information about the office of the UNHCR, visit the office’s Web site at the following URL: http://www.unhcr.org