UMD NFLC Hausa Lessons/34 Differences Between Abacha's and Obasanjo's Children

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/34)
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Differences Between Abacha's and Obasanjo's Children-This publication compares the roles that the children of Obasanjo and Abacha play in the Nigerian society.
 2. Language: Hausa
 3. Topic: Culture/Society
 4. ILR Level: 2+/3
 5. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 6. Modality: Reading
 7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 8. Subject Area: Language
 9. Material Type: LO
 10. Publication Year: 2007
 11. ObjectID: HAUS_12030

Transcript


Original Translation

Differences Between Abacha's and Obasanjo's Children

Bambancin ‘Ya’yan Abacha Da Na Obasanjo

Kusan shekara ɗaya ke nan da ’ya’yan shugaban ƙasa Obasanjo suka fara samun damar ganin hotunansu a shafunan farko na jaridun ƙasar nan, duk kuwa da rashin dacewar abin da suke yi. Tun daga lokacin shugabancin Sir.Abubakar Tafawa Ɓalewa har zuwa yanzu, ba a taɓa yin shugaban ƙasar da ’ya’yansa suka riƙa yi wa al’amuran rayuwar mu shigar-kutse ba kamar ’ya’yan shugaba Obasanjo.

Kada ma ku haɗa su da ’ya’yan janar Abacha, waɗanda Obasanjo ke ta farauta har yau. Su ’ya’yan Obasanjo daga ka ga mai bin ɗan takarar shugaban ƙasa yankar fom na takara, sai masu zaɓar Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa domin samun wani babban hasafi.

Je ka an ji ’ya’yan Abacha suna yin kasuwanci na biliyoyin nairori,amma dai daga cikinsu babu wanda ya taɓa yin gangancin zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa ko mataimakinsa, kai ko a harkar kasuwancin ma, duk abin da ’ya’yan Abacha suka yi, su ma na Obasanjo sun yi.Yau ka ga ’ya’yan Obasanjo suna taimakawa kamfanin jirgin Virgin ya kafu a Nijeriya, sai sayen katafaren gidaje da kadarori a Amurka,sai kuma mallakar kadadar man fetur da suna haɗin gwiwa da abokan hada hadar kasuwanci. To amma ba kamar ubansu ba, su ’ya’yan Obasanjo sun fahimci wa’adin babansu ya zo ƙarshe, sun saurara, an daina jin ɗuriyar yawancinsu.

Sai dai a yau, na fi damuwa da babbar ɗiyarsa, wata mai suna Dakta Iyabo Obasanjo. Ta riƙe muƙamin kwamishina a gwamnatin Gbenga Daniel, gwamnan da Obasanjo ya wa ’yan jiharsa ta haihuwa ɗauki ɗora. Shi kuma gwamna Gbenga Daniel, sai ya bata kwamishina ne don ya nuna wa Obasanjo godiyarsa ta maguɗantar masa da kujerar gwamna. Hausawa dai sun ce ramuwar maɗi masakin kanya.

Ita kuma Iyabo, daga samun tukuicin muƙamin kwamishina, sai ta ɗauki mayafin kankanba da tinƙaho da ɗagawa ta yafa.

Kafin a jima sai Iyabo ta riƙa hangen ga ta can akan kujerar Sanatan yankin da ta fito. Madan Iyabo kenan! Ba abin mamaki ba ne don ta yi tunanin hawa kujerar Sanata musamman tunda ga mahaifinta Obasanjo, wanda ya ɗauki muƙamin shugaban majalisar dattawa ya bai wa wanda bai ci zaɓen sanata ba, kun ga ai abu ne mai sauƙi ga Iyabo ta sami Sanata ko? Zurfin tunanin da Iyabo ke yi fa shi ne idan ta ci zaɓen 2007, to ita ce za ta zama shugabar majalisar dattawa kenan, domin a bisa dukkan alamu, daga yankin jihohin yammacin ƙasar nan za a zaɓi shugaban majalisar. Ya fa riga ya bai wa shiyyarsu muƙamin shugaban kwamitin amintattun dattawan jam’iyya, muƙamin da zai riƙe idan ya sauka.

Ita fa Iyabon nan da nake magana ta ɗan sha kutsawa cikin manyan ƙasa tana halartar taron ministoci, ga shi dai ko ta wace hanya ba ta cancanta ba.’Ya’yan Abacha kuwa ba su yin haka.Ana nan wata rana sai ta ji labarin cewa mutumin nan wanda ya taka rawa wajen gina Guaranty Trust Bank, mai suna Fola Adeola, shi ma yana neman Kujerar sanata ɗin da Iyabo ɗin ke nema. Ai nan da nan Iyabo ta kiɗime inda ta riƙa sabbatu tamkar mai rawar sanyin zazzaɓi, a cikin wata tattaunawa da ta yi da jaridar The Sun a shekarar da ta gabata inda ta riƙa furta cewa ƙaryar duk wani mai neman ƙwace kujerar sanata da ga gareta. Wai ita ce ta sha wahalar neman zama, kuma sai ita kaɗai ce zata tsaya takara.

A hirar da ta yi, ta riƙa yin wasu kalamai na barazana da ke nuni da cewa da Fola Adeola ta ke. Iyabo ta riƙa yin abubuwa irin na shagwaɓaɓɓun yaran da aka ƙwacewa ’yar bebin da suke wasa da ita. Ya aka yi, oho! Sai dai kawai muka ji wai shugaban ƙasa ya cire Fola a muƙaminsa na babban manajan darektan kamfanin Transcorp da kuma shugabancin da ya ke yi wa hukumar Pensions Commission of Nijeriya. Da wannan ne suka sare masa gwiwar neman takarar sanatan da ya fito yana yi. Ta haka ne Obasanjo ya samar mata tikitin hawa kan hanyarta ta zama shugabar Sanatoci. To wadda aka yi wa haka kuwa, ta ya sunanta zai fito a cikin jerin waɗanda karnukan EFCC suka ciza?Ko da sunan nata ya fito kamar yadda na gwamna Segun Agagu, Sanata Ibrahim Mantu da sauran ’yan barandan Obasanjo, shi shugaban ƙasar tuni zai kankare sunayen na su. A taƙaice dai aka shawarci kowa ne ɗan takara ya janye daga neman kujerar Sanatan Ogun ta tsakiya.

Amma ina, sai wani tsageran mutum wai shi Lanre Tejuoso, ɗan jinin sarautar Egbaland, ya nunawa Iyabo iyakarta, ya fito a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP. Lanre dai ya fi ta magoya baya ɗari bisa ɗari. To ita baya ga Baba, su wa ke son ta? Sati uku da su ka shuɗe, cikin dare wasu baƙi suka kai masa ziyara a Otal ɗin da yake zaune a garin Abeokuta. Kowanensu ɗauke da shanda-shandaman bidigogi. Bayan sun gaisa, suka gabatar da kansu a matsayin ’yan ku-kashe-a-biya ku. Masu karatu kuna ji ko? Makasan da harshen yarbanci su ke magana. Cikin firgita, laure ya ɗauko naira miliyan biyu ya ba su, don shi a tunaninsa ko ’yan fashi da makami ne.sai suka ce da Lanre don me zai rage ma su daraja? Su fa ba fashi suke yi ba, kashe wa suke ana biyan su,

Ci gaba a shafi na 15

Differences Between Abacha's and Obasanjo's Children

It’s been nearly a year since President Obasanjo’s children started seeing their photos on the front pages of the country’s newspapers, despite the inappropriateness of such publications. From the time of Sir Abubakar Tafawa Balewa’s administration up to the present, we have never had a president whose children kept on bursting in on the affairs of our lives like Obasanjo’s children.

Don’t even compare them to the children of General Abacha whom Obasanjo continues pursuing to this day. Among Obasanjo’s children, you find one who escorts a presidential candidate to buy the registration forms while his other children are inaugurating Goodluck Jonathan to the position of vice presidential candidate in order to receive a substantial payoff.

Even if we assume that Abacha’s children are making business deals worth billions of naira, at least none among them has ever acted recklessly enough to inaugurate a candidate for president or vice president. Business wise, everything that Abacha’s children did, those of Obasanjo did as well. Today you see Obasanjo’s children are helping Virgin Airlines become established in Nigeria, then buying huge houses and properties in the U.S., then owning oil shares in cooperation with their so-called financial partners. But unlike their father, Obasanjo’s children understand that their father’s term is coming to an end, and so we no longer hear much news about most of them.

But today, I’m more concerned about his eldest daughter, the one named Doctor Iyabo Obasanjo. She held the position of commissioner in the government of Gbenga Daniel, the governor that Obasanjo had hand-picked on behalf of the people in his home state. And Governor Gbenga Daniel then appointed her commissioner to show Obasanjo his thanks for hastening him to the governor’s seat. The Hausa have a saying: Repaying a debt is like a large ebony calabash of sweet drink.

On her part, this Iyabo, soon after receiving a gift of the position of commissioner, she took off the cloak of modesty and started putting on airs.

Before long, Iyabo set her sights on a seat in the Senate for the district that she came from. What a modern girl, this Iyabo! It was not surprising that she thought of mounting a campaign for a seat in the Senate, especially given that her father Obasanjo had given the position of Senate president to someone who didn’t win the senatorial election; so you see what an easy thing it is for Iyabo to join the Senate? Iyabo’s thinking was that if she were victorious in the 2007 election, she would become Senate president, because by all indications, the Senate president would be chosen from the western states. Obasanjo had already allocated the chairmanship of the board of party elders to his region, a position that he had saved for himself once he stepped down from the presidency.

And it is this Iyabo that I have been speaking about who has bulldozed her way into ministerial meetings where she had no business being. Abacha’s children never did this. And so, one day, she heard the news that the person who had played a role in building the Guaranty Trust Bank, by the name of Fola Adeola, was also seeking the Senate seat that Iyabo was after. Well, at once Iyabo was upset and started babbling like someone delirious with a fever. In an interview she had with The Sun newspaper last year, she kept on mentioning that it’s a nasty trick for anyone to try to snatch the Senate seat from her. That is, it was she who suffered to seek the legislative seat; as such she’s the only one who deserves to be senator and no one else.

In the interview that she did, she kept on using threatening words that showed she was speaking about Fola Adeola. Iyabo kept doing things like spoiled children tend to do when someone snatched away a little toy that they had been playing with. And how one achieved the objective, nobody cared! Suddenly we heard that the president had fired Fola from his position as executive managing director of Transcorp and also from the chairmanship of the Pensions Commission of Nigeria. With this, they undercut his quest for the Senate. This was how Obasanjo secured the senatorial seat for his daughter, thereby putting her on her way to becoming Senate president.

So how does the name of someone this powerful ever appear on the list that the EFCC dogs might be after? Even if her name appeared there like those of Governor Segun Agagu, Senator Ibrahim Mantu and other ardent supporters of Obasanjo, the president would simply have her name removed. Briefly, all other candidates were thus intimidated enough to withdraw from seeking the senatorial ticket for Ogun’s Central zone

But then along came a brave man who cannot be easily intimidated named Lanre Tejuoso, a blood relation to the chiefdom of Egbaland, to show Iyabo her limits, and appearing under the banner of ANPP [All Nigeria Peoples Party]. Lanre exceeded her in supporters by one hundred percent. For her, besides Daddy, who wanted her? Three weeks later and in the middle of the night some gun-totting strangers paid him a visit at the hotel where he was staying in Abeokuta.

After they exchanged greetings, they introduced themselves to as “hired guns,” Are you following me, my dear readers? The killers were speaking in Yoruba language. In fear, Lanre brought two million Naira and gave it to them, since he was under the impression that they were armed robbers. Then they said to Lanre, why would he begrudge them their status? They were not robbing him, they were professionals who killed and got paid for it, and

Continued on page 15

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
ɗauki ɗora A aza mutun bisa wani matsayi ko bai cancanta ba ya sameshi, kuma ba tare da shawarar jama'a ba. To impose or place a person in a position (usually political) based on a relationship or influence rather than merit.
ramuwar maɗi masakin kanya Girbe abun da aka shibka ko mai kyau ko ba mai kyau ba. One good turn deserves another (give a reward in return for something good done for a person). This could be for good or bad.
Kiɗime Ruɗewa ko jin kunya ko idan mutun na cikin halin da bai san abun da zai yi ba saboda an tona mishi asiri. Confused/embarrassed. (In a state of not knowing what to do or say, could be due to embarrassment, due to someone unveiling something not expected to be unveiled).
rawar sanyin zazzaɓi Wannan na kwatamta irin rawar jiki idan mutun bai da lafiya. Comparing an act of trembling or shivering as a result of cold or when suffering from fever.
Ku kashe a biyaku Mu tane da ake haya don su alkata kissa a ɓoya a biya su. Hired killers or assasins.
Tukuici La'ada da ake ba mutun don nuna jin daɗi ko godiya. Rewarding someone in appreciation for a favor, this could be given directly to the person who gave the favor or a member of his family.
mayafin kankanba da tinƙaho da dagawa ta yafa Sai ta zama mai girman kai. Immediately became arrogant (took a veil of pride and veiled herself with it).
Kutsawa ƙoƙarin shiga inda bai kamata ba ko matsatse wuri. Forcing oneself into a place he/she is not supposed to be in, or squeezing oneself through a small space.
Sare masa gwiwa An kashe masa jiki To discourage someone.
Waɗanda karnukan EFCC suka ciza Waɗanda EFCC ta kama da laifi. People proved or found guilty by the anti-corruption tribunal (EFCC).
Shagwaɓaɓɓun yara Yaran da aka ɓata, suna samun duk abun da suke so. Spoiled children who have everything at their disposal and are allowed to do whatever they want.

Notes

Hausa Notes English Notes

Kamar yawancin shugabannin Afrika, ana ganin cewa ƴaƴan shugabannin Nijeriya na da ƴancin yin duk abun da suke so cikin ƙasa ba tare da an huƙuntasu ba saboda matsayin su. Abacha ya yi mulkin Nijeriya a shakara ta 1993 sai ya rasu a sanadiyar ciwon zuciya a shekara ta 1998. Abdusalam ya gaje shi kuma daga shi sai Obasanjo ya hau mulki bayan kason da Abacha ya sa shi. Obasanjo da Abacha sun haifi ƴaƴa da yawa kuma bayan Abacha gwamnatin Obasanjo ta kama babban ɗan Abacha da laifin zamba da satar ƙuɗin ƙasa. A ƙarshe gwamnatin da iyalin Abacha sun sasanta da cewa za'a yafe ma Mohammed laifufukan idan sun maida ma gwamnatin Nijeriya tamanin bisa ɗari na ƙadarorin su. Obasanjo ya yi mulkin Nijeriya sau biyu kuma tsohon soja ne. Ana samun ƴaƴanshi ko'ina cikin Nijeriya, Ingila da Amurka kuma suna da hannun jari cikin harakokin kasuwancin da yawancin manyan kamfafonin Nijeriya guda 500 da wani babban kamfani mai suna 'Aladja steel complex' da 'Nigerian transcorp'. http://people.africadatabase.org/en/profile/1992.html http://en.wikipedia.org/wiki/Olusegun_Obasanjo http://www.hollerafrica.com/showArticle.php?catId=1&artId=210&PHPSESSID=ebdb55779f4f01e5584badec5e02e8ea

Like most Presidents in Africa, the children of the Nigerian Presidents are believed to have the right to enjoy their father's tenure by doing whatever they want in the society without being penalized. Abacha ruled in 1993 and died unexpectedly of a heart attack in 1998 according to a Nigerian official report. He was replaced by Abdusalam Abubakar who was succeeded by Obasanjo, a former Abacha detainee. Like Obasanjo, Abacha had many children and his oldest son Mohamed was arrested by Obasanjo's government in 1999 on charges of fraud, money laundering and embezzlement. A deal between the government and his family was later made to drop all charges against him if they return 80% of their liquid assets. Obasanjo was a career soldier before serving twice as Nigeria's head of State, once as a military ruler and once since 1999 as an elected President. He has children throughout Nigeria, United Kingdom and the United States. Obasanjo and his children own controlling shares in Aladja steel complex and in many of the fortune 500 companies in Nigeria like the Nigerian transcorp. http://people.africadatabase.org/en/profile/1992.html http://en.wikipedia.org/wiki/Olusegun_Obasanjo http://www.hollerafrica.com/showArticle.php?catId=1&artId=210&PHPSESSID=ebdb55779f4f01e5584badec5e02e8ea

CONTENT SOURCE: Sam Nda-Isaiah (2007 February 22). Differences Between Abacha's and Obasanjo's Children. N/A: Leadership Newspapers Group Limited.

Objective: Demonstrate your core comprehension.

Content description: This publication compares the roles that the children of Obasanjo and Abacha play in the Nigerian society.

XML<activity>
  <problemset>
   <problem correctindex="1">
     <choices>
      <opt>
        <eng-response>According to the author, Obasanjo's children have done everything Abacha's children did and both were involved in using Nigeria's natural resources and income for their business purposes. Obasanjo's children have also realized that their father's tenure is almost over and are getting ready for the hand over, except his daughter who is still using her father's power and influence to threaten her political opponents. The author showed concerns about Iyabo Obasanjo who strives for the position of a senator, and described Obasanjo's acts towards his children's opponents as unjust.</eng-response>
        <eng-fdbk>This is incorrect because the author did not explain the source of Abacha's children's income for their business. Think about the best answer that describes the main interest of both sets of children.</eng-fdbk>
        <fdbk>Wannan ba daidai bane saboda marubucin bai yi bayani ba akan hanyar samun kuɗin yin kasuwanci ba. Yi tunani amsa da ta fi bayyana abin da dukan yaran ke sha'awar yi</fdbk>
        <response>Marubucin ya bayana cewa ƴaƴan Obasanjo sun aikata duk abubuwan da ƴaƴan Abacha suka taɓa yi kuma dukansu sun yi anfani da tattalin arziki ko kuɗin Nijeriya wajan aiwatar da kasuwancin su.Ƴaran Obasanjo sun fahimci wa'adin babansu ya zo ƙarshe kuma suna shirye-shiryen saukar shi daga kujerar mulki, banda wata ɗiyarshi wadda ke ta amfani da ikon babanta don tsoratar da ƴan adawarta masu takarar matsayin da take so na Senata. Marubucin ya nuna damuwarshi da Iyabo mai neman matsayin Senata kuma ya kwatamta rashin gaskiyar Obasanjo wajen kare 'ya'yan shi daga 'yan adawar siyasar su.</response>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>This publication discusses the difference between Obasanjo's and Abacha's children, with more emphasis on Obasanjo's children. While both were engaged in family businesses, Obasanjo's children went beyond building houses in America and making fortunes out of Nigeria's natural resources (petroleum). They are also involved in politics, especially his daughter Iyabo Obasanjo who receives support for her political ambitions mainly from her father. The author concluded that since Sir Abubakar Tafawa Balewa's regime, Obasanjo's children are the only children who incurred people's lives and political ambitions in Nigeria.</eng-response>
        <eng-fdbk>Correct! The summary encapsulates the main differences between Obasanjo's and Abacha's children, including the author's tone in revealing some of the children's injustice towards the Nigerian public.</eng-fdbk>
        <fdbk>Wannan daidai ne! Taƙaitawa ta ƙunshi banbancin ƴaƴan Obasanjo da na Abacha da kuma ra'ayin marubucin wajen bayyana rashin adalcin ƴaƴan ga jama'ar Nijeriya.</fdbk>
        <response>Wannan rubutu na bayyani akan banbancin 'ya'yan Obasanjo da 'ya'yan Abacha masanman labarin 'ya'yan Obasanjo. 'Ya'yan shugabanin biyu duka sun yi harakokin kasuwanci kuma 'ya'yan Obasanjo sun wuce gona da iri wajen gina gidaje da suka yi a Amurka da yi ma kansu arziki da man Nijeriya. Sun kuma sa kansu cikin harakokin siyasa masanman wata ɗiyar shi mai suna Iyabo Obasanjo wadda ke samu yawancin goyon bayanta daga babanta.Marubucin ya kamala da cewa tun daga lokacin shugabancin Sir Abubakar Tafawa Balewa har zuwa yanzu ba'a taɓa yin ƴaƴan shugaban ƙasa da suka riƙa shiga harakokin rayuwar ƴan Nijeriya da buƙatun su na siyasa irin 'ya'yan Obasanjo.</response>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>In this publication, the author expresses his concern about Obasanjo's children and reveals to the readers some of their dangerous activities including invading the privacy of the Nigerian people. Unlike Obasanjo's children, Abacha's children were not involved in running for any political office in Nigeria. Also, they did not attend any Nigerian Ministers' meetings or any official meeting that does not concern them. The author concludes that Nigeria will continue to experience injustice if the people allow Iyabo to win the seat of a senator in the 2007 elections.</eng-response>
        <eng-fdbk>This is incorrect because the summary describes Iyabo's success as a sign of failure in Nigeria. Think about the author's opinion regarding the children's political desires.</eng-fdbk>
        <fdbk>Wannan ba daidai bane saboda taƙaitawa ba ta bayyana cewa nasara Iyabo zata zama alamar rashin ci gaba a Nijeriya. Yi tunanin ra'ayin marubucin bisa begen ko marmarin siyasa da yaran ke da.</fdbk>
        <response>Marubucin wannan labari na bayyani ne akan damuwarshi da ƴaƴan Obasanjo da irin abubawan da suke yi masu hatsari ga jama'a kamar shiga cikin al'amuran rayuwar jama'ar Nijeriya. Ƴaƴan Abacha basu sa kansu ba cikin takara wani matsayi cikin siyasa Nijeriya ba kamar ƴaƴan Obasanjo ba kuma ba'a ganin su cikin taruwar da bata shafesu ba kamar taruwar ministocin Nijeriya. marubucin ya kamala da bayyanin cewa Nijeriya za ta ci gaba da fusƙantar rashin adalci idan jama'a suka bar Iyabo ta samu kujara senata wajen zaɓen dubu biyu da ɗari bakwai .</response>
      </opt>
     </choices>
   </problem>
  </problemset>
  <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
  <instr type="target">Umurni:
Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
  <finish>How do you think previous Nigerian Presidents' children contributed to the society?</finish>
  <finish>Who do you think should be held responsible for the roles played by the Presidents' children in Nigeria? Why?</finish>
  <finish>How can the Nigerian Government protect the country's resources from misuse by Presidents and their families?</finish>
  <finishtl>A ganinku yaya ƴaƴan tsohin shugabannin Nijeriya suka bada gudunmuwasu cikin ƙasar?</finishtl>
  <finishtl>Wa ya kamata a ba laifin abubuwan da ƴaƴa shungabannin Nigeriya suka yi ?Don mi?</finishtl>
  <finishtl>Yaya Gwamnatin Nigeriya ke iya tsare arzikin ƙasa daga hannun shugabannin ƙasa da iyalansu?</finishtl>
</activity>