UMD NFLC Hausa Lessons/39 Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/39)
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor: The political and social changes that mark the history of Nigeria are discussed in this interview with Alhaji Inuwa Wada, Mayor of Kano, Nigeria.
 2. Language: Hausa
 3. Topic: Culture/Society
 4. ILR Level: 2+/3
 5. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 6. Modality: Reading
 7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 8. Subject Area: Language
 9. Material Type: LO
 10. Publication Year: 2007
 11. ObjectID: HAUS_12110

Transcript


Original Translation

Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor

Ya kamata matasa su daina garaje -Magajin Garin Kano

NOTE: ”Q” represents the Hausa hooked ”K” “X” represents the Hausa hooked “D” “V” represents the Hausa hooked “B”


Alhaji Inuwa Wada shi ne mai riqe da sarautar gargajiya ta Magajin Garin Kano. A hira ta musamman da yayi da jaridar Aminiya a gidansa da ke cikin garin Kano, Magajin Gari ya bayyana faxi-tashin da yayi a rayuwa da kuma irin rawar da ya taka a fagen siyasarsu ta da. Kuma ya ba da labarin irin yadda rayuwar da ta bambanta da ta yanzu. A sha karatu lafiya: Masu karatu za su so jin taqaitaccen tarihinka?

Magajin Gari: Tarihina taqaitacce ne amma kuma ba taqaitacce ba ne. Ya danganta da irin me kake so ka sani, tambaya za ka yi, na ba ka amsa.

Abin da nake so in tambaya shi ne kamar irin makarantar da ka yi da kuma irin gwagwarmayar da ka sha a rayuwa?

Magajin Gari: A nan Kano na fara makaranta a lokacin ana kiranta ‘Shahuci Elementary School’ tun ba ta zama ‘Primary School’ ba, to daga nan ne muna cikinta aka yi ‘Middle Schools’ a jihohin Arewa. Da aka yi‘Middle School’ aka gina wannan tamu da ake kira Rumfa, muka fara tarewa a cikinta, to na zauna a Rumfa na yi makaranta, daga nan na tafi Katsina ‘Higher College’ inda na samu shekara biyar aka hore ni, na zama malami na dawo ita wannan’Middle School’ da na bari na koyar a cikinta kamar shekara tara ko goma.

To yanzu kamar ka sami shekara nawa ke nan da haihuwa?

Magajin Gari: Yanzu Alhamdulillahi, na samu shekara casa’in da xan wani abu. In an bi lissafin watanninmu na sama na haura shekara casa’in, in ko an bi shekaru na turawa mai kwanaki xari uku da sittin, ita kuma wataqila a ce shekarata casa’in dai-dai ko kuma tamanin da tara. Tun da zan iya cewa an haife ni shekarar 1917.

Ka tava shiga cikin harkokin siyasa?

Magajin Gari: Kwarai kuwa, siyasa ta farko da aka fara a Arewa, da mu aka fara ta. Wato wadda aka fara yi da sunann Jam’iyyar Mutanen Arewa, ba ta siyasa ba. Daga baya ma da ta zama ta siyasa duka ina cikinta.

Waxanne irin muqamai ka riqe a rayuwarka zuwa yanzu?

Magajin Gari:To haka ne, a cikin ita wannan jam’iyya da aka yi kamar yadda na gaya maka cewa mu ne muka fara ta, yadda aka kafa tushenta a gurare da dama, to a nan Kano ma mu ne waxanda muka kafa ta. To da ma kuma mu ne muka kafa ta har muka shigo cikinta, har takai na zama babban Sakataren ita wannan Jam’iyya ta Mutanen Arewa.

Me ya sa kamar a yanzu ba a jin xuriyarka, me ke faruwa?

Magajin Gari: Babu abin da ke faruwa sai lafiya in ji Hausawa. Ni dai daman tun daga tashina har zuwa quruciyata kawo ya zuwa yanzu ni ba mai son rigima ba ne, ba na son in shiga cikin duk wani abu da yake da rikici a cikinsa. Shi ya sa ba a ji na.

Banda muqamin da ka riqe a siyasa, waxanne muqamai ka riqe walau a aikin gwamnati ko kuma sarautar gargajiya?

Magajin Gari:To bayan na gama makaranta a Katsina, na dawo na zama malamin makaranta in da na koyar a ‘Middle School’, to ina cikin koyarwa ne harkar ‘Scouting’ ta zo wannan qasa wato nan yankin Arewa, to ina xaya daga cikin waxanda suka shiga harkar, har na zama ‘Scout master’ anan Kano, daga nan sai ya zama su ‘Scout’ xin suka nemi su xauke ni don na taimaka musu harkar ‘Scouting’ xin ta daxa bunqasa, to na zama aka naxa ni kwamishina na ’yan ‘Scout’ wato ‘Travilling Scout Commissioner’ na Arewa baki xaya. To na yi wannan ’yan shekaru da dama.

Yanzu da ake cikin harkokin siyasa, wace shawara za ka baiwa matasan ’yan siyasa na wannan zamani?

Magajin Gari: Shawarar da zan ba su shi ne, su yi qoqari su yi tambaya su ji mu yaya muka fara siyasar? Yawancinmu duk da muka fara siyasa har shugabanninmu na wannan lokaci, waxanda suka rasu kamarsu Sardaunan Sakkwato, da Sir Abubakar Tafawa Valewa, Alhaji Muhammadu Ribaxu, Makaman Bidda, Madakin Ilori, Shatima Kashim, na Barno, dukkaninsu waxannan su ne kamar yayinmu a harkar siyasa. To babu wanda ya shiga siyasa ba yana da sana’a takamaimai, wadda yana kanta ba, kuma ta isa ta riqe shi da harkar gidansa da iyalinsa da komai. To shawarar da zan ba wa mutanen yanzu, siyasa ba aba ce wacce za a shiga saboda neman kuxi ba, a’a, siyasa duk inda take abu ce ta ra’ayi. Kuma kana so ka yi abu bisa ra’ayinka, ya kamata a ce kana da abin da ya isheka ba sai ka je ka jingina da wani kan ka ci ko ka sha ba.

Bari in xan koma baya, banda sarautar Magajin gari wace sarauta ka riqe?

Magajin Gari: Na riqe muqamai amma a lokacin da ake kiran qaramar hukuma N.A, na riqe muqamin babban magatakardan Ciroman Kano, a lokacin Alhaji Muhmmadu Sunusi, shi kuma shi yake kula da harkokin hakiman waje, to ni kuma na zama ni ne babban malaminsa, duk abin da zai vullo ta kaina yake bi ke nan sannan a je gare shi. To kuma daga wannan na riqe waxansu muqamai a harkar N.A xin dai, na riqe muqamin babban jami’i mai watsa labarai, na riqe muqamin babban jami’i mai kula da ilimin yaqi da jahilci, saboda ni na fara futo da harkar yaqi da jahilci a nan Jihar Kano, har muna koya wa mutane rubutu da karatu wato irin yadda ake cewa lanqwasa xin nan. Bayan wannan na kuma riqe ofishin ma’aikata gaba xaya na Kano N.A. Duk na yi waxannan kafin na bar duk wani aiki na koma aikin ‘Scout’ xin nan da na ce maka na yi a baya.

Mutane za su so jin wai ita sarautar Magajin Gari me ta qunsa ne?

Magajin Gari: Magajin gari sarauta ce da aka yi ta a Kano, abin da ya sa ba a san ta a Kano ba, don ba a yi ta da yawa ba. Kamar ni ne magajin gari na uku da aka yi a Kano. An yi magajin gari Mamudu, qanen Sarkin Kano Alu, an yi Magajin Gari xan Fanisau, shi kuma xan’uwa ne ga Sarkin Kano Alu, don xan Sarkin Kano ne Abdullahi Maje-karofi. To daga nan shi ne aka dakata, don ba a qara naxa Magajin Gari ba sai da aka zo kaina, aka naxa ni Magajin Gari.

Mene ne ainihin aikin Magajin Gari?

Magajin Gari; Aikin da na fara yi shi ne aikin harkar qasa, shi ne fulotai, da gidaje da gonaki, duk dai qasa wacce take qarkashin N.A a lokacin, ni kuma ni ne xan majalisar sarki wanda yake kula da wannan harka.

Kamar ina da ina ka je a ciki da kuma wajen Nijeriya?

Magajin Gari: A nan gida Nijeriya da waje, na yi tafiye-tafiye da yawa. Don a lokacin siyasa, na zama minister a qarqashi Firayinminista Sir Abubakar Tavawa Valewa, ministan da na fara yi shi ne Ministan ayyuka da safiyo, to da na zamo ministan nan saboda hanyoyi qasar nan da gine-gine, sannan kuma ga safiyo baki xaya , na sami dama babu inda ban sanya qafata a qasar nan ba. A qasashen waje kuma, bayan an yi juyin mulki, mun bar gwamnati, shi ma na samu damar yin yawo wurare da dama. Na je Esha da Ostireliya da Amurka ta Arewa da Amurka ta Kudu da Yurof, balantana ma Ingila da zan ce muna tare da su.

Ta yaya za ka kwatanta siyasar irin taku ta da da ta yanzu?

Magajin Gari: Yadda zan kwatantata shi ne siyasa tamu Ta yaya za ka kwatanta siyasar irin taku tad a da ta yanzu?

Magajin gari: Yadda zan kwatantata shi ne siyasa tamu ta da, akwai manyana waxanda na xauka tamkar iyayena ko kuma yayuna, to mu mun yi siyasa da ganin girman juna da kula da haqqin juna. Babu iskanci a ciki, babu ashararanci.

Wace shawara za ka ba wa matasan yanzu?

Magajin Gari: Wannan haka yake, domin tun iyayenmu da kakanninmu dama cewa ake yara manyan gobe. To amma yara ba sa zama manyan gobe sai sun zauna da manya yau, sun koyi kyawawan abubuwa na zaman duniya da manya ke yi. To abin da zan ce wa yara na yanzu shi ne su riqa yin haquri su daina garaje. Domin garaje idan ba a yi sa’a ba, ba ya haifar da alheri. Sai a je a faxi ko ma a ruguje. Shawarar da zan baiwa shugabani na yanzu shi ne su riqa yin adalci da gaskiya.

Matanka da ‘ya’yanka nawa?

Magajin Gari: ’Ya’yana takwas ne masu rai, amma abin da na haifa su ne ’ya’ya tara. Na auri mata biyu da farko amma yanzu duk Allah ya karvi ransu, da fatan Allah ya gafarta musu. Sai wacce nake tare da ita guda xaya munanan muna haquri da juna. Jikokina idan ba su kai talatin ba , to za su kai arba’in.

Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor

Alhaji Inuwa Wada holds the traditional position of Magajin Gari [roughly translated as “Town Administrator”] of Kano. In an important conversation he had with Aminiya newspaper at his home in Kano, the Magajin Gari explained his life’s struggles as well as the many roles he had played in the political arena of the past. He also recounted how life in the past was different than it is now. We hope you enjoy reading this: Readers would like to hear a short summary of your background. Magajin Gari: My background is brief, but in a way it’s not. It depends on what kind of things you’d like to know. Ask me a question and I’ll respond. What I want to ask about is the kind of schooling you had and also the kinds of struggles you have endured in life.

Magajin Gari: I started school here in Kano. It was called “Shahuci Elementary School” at that time, before it became a “Primary School”; from then on we were there, when they built “Middle Schools” in the Northern states. It was when they established these “Middle Schools” that they built this one of ours, called Rumfa, and we moved there. Well, I stayed at Rumfa for my education, after which I went to Katsina Higher College, where I spent five years in training, until I became a teacher and came back to this same “Middle School” that I had left, and I taught there for nine or ten years. So, about how old are you now? Magajin Gari: Now, alhamdu lillahi (thank God), I’m ninety-some years old. If you follow our system of counting up months, I’m more than ninety, but if you follow the European year of three hundred and sixty days, perhaps you could say that I’m exactly ninety or eighty-nine. I can say that I was born in the year 1917. Have you ever entered into politics? Magajin Gari: Yes, indeed: the first political group that was started in the North, it was we who started it. That is, what we started out with, called the Northern People’s Party [NPP], it wasn’t really a political party. But after it became a party for all, I was in it. What types of positions have you held in your life up to now? Magajin Gari: Well, in that party that was established, which I told you we started it, we set up chapters in lots of towns, well, here in Kano as well. We were the ones who founded it. And it was we who founded it and joined its ranks, up to the point when I became Secretary General of the NPP. So why is it that we don’t hear any news about you these days? What’s happening? Magajin Gari: There’s nothing happening, everything’s fine, as the Hausas say. For me, it has always been the case, even when I was growing up right from the time when I was young up to now, that I have always tried to avoid controversy, so I didn’t want to get involved in anything that involved conflict. That’s why you don’t hear about me. Besides the position that you held in politics, what other positions have you held, say, in government work or traditional office? Magajin Gari: Well, after I finished my education at Katsina, I came back to be a school teacher where I taught at “Middle School,” and while I was teaching, the scouting movement arrived in this country, including here in the Northern region. I was among those who became involved in the movement, until I eventually became a scout master here in Kano. At that point, it so happened that scouts sought to appoint me to help those in the scouting movement to further its development, and I was appointed commissioner of scouts, that is, Traveling Scout Commissioner for the entire North. This I did for many years. Now that we are in the midst of political affairs, what advice would you offer to rising politicians of the current era? Magajin Gari: The advice I would offer to them is this: they should try to talk to us and listen to how we started in politics. Most of us who started in politics, even our leaders at that time, the ones who have passed away, such as the Sardauna of Sokoto, and Sir Abubukar Tafawa Ɓalewa, Alhaji Muhammadu Ribaɗu, the Makami of Bidda, the Madaki of Ilorin, Shatima Kashim of Borno: all of them had the same style as us in political affairs. Not one of them entered politics without a certain trade that he was in charge of and that was sufficient to maintain him and his household affairs and his family and everyone. So, the advice that I would offer to people today is, that politics is not something one should enter for the money. No, politics, wherever it may be, is about ideas. And you want to take action based on your ideas, so you must have enough to sustain yourself and not need to rely on others in order to eat and drink. Let me go back a bit and ask, besides the office of Magajin Gari, what other traditional title do you hold?

Magajin Gari: I have held another position but back when it was called the Native Administration or N.A.: I held the position of senior clerk for the Ciroma of Kano, during the period of Alhaji Muhammadu Sunusi; it was he who attended to the affairs of the district heads from outside the emirate. I was his main teacher; everything came through me before it went to him. Then I went on to become a top official in the broadcasting service, where I held the position in charge of adult literacy education, because I had started to come out with literacy materials here in Kano State, so that we could teach people to read and write this kind of cursive script. After that I worked in the office overseeing the entire Kano N.A. workforce. All these things I did before leaving and returning to the scout work that I told you I had done previously. People would like to hear about the functions of this traditional title of Magajin Gari. What does it involve?

Magajin Gari: The Magajin Gari is an official position that we have in Kano, but the reason it’s not well known in Kano is that it hasn’t been used very much. Such as it is, I am only the third Magajin Gari that we’ve had in Kano. We had Magajin Gari Mamudu, the younger brother of Emir Alu of Kano; then we had Magajin Gari ɗan Fanisau, who was also a brother of Emir Alu, since the Emir’s son was Abdullahi Maje-Karofi” From then on, that’s it, and there was a stretch during which no further Magajin Gari was appointed, until I was approached and appointed Magajin Gari. What is the actual job of the Magajin Gari? Magajin Gari: The work that I started to do involved land affairs: plots, housing, farms, and all the land that had been under the N.A. at that time. I’m the member of the Emir’s council who looks after these matters.

And what are some of the places that you’ve visited inside and outside of Nigeria? Magajin Gari: Both here within Nigeria and abroad, I’ve done a lot of traveling. Because during my time in politics, I was minister under Prime Minister Sir Abubakar Taɓawa Ɓalewa; the ministry that I first headed was the Ministry of Public Works and Surveying, and in that capacity and due to the ubiquitous poor highways in the country, I found myself traveling everywhere. As for foreign countries, after the change in administration, we quit the government, and this was when I got the chance to go to a great many places. I’ve been to Asia, Australia, North and South America, and Europe, not to mention England, with which we have such close relations. How would you compare your kind of politics in the past to that of today?

Magajin gari: The way I would compare it is that in our politics in the past, there were some of our major political figures whom I regarded as my parents or elder brothers, and we conducted our politics by respecting each other and looking out for each other’s rights. There was no recklessness in it, and no foul language.

What advice would you offer to today’s young people? Magajin Gari: This is how it is: our parents and our grandparents have been saying for a long time that children are tomorrow’s adults. But children will not become tomorrow’s adults unless they sit with the elders of today, and learn the wonderful things about living in the world that adults have learned. So what I would say to the children of today is that they should keep being patient and take it easy. Because haste, if one is unlucky, often does not lead to greatness. One in a hurry could fall or even collapse. The advice that I would give to the leaders of today is that they should be just and truthful. How many wives and children do you have? Magajin Gari: Eight of my children are alive, but I fathered nine altogether. I married two women at first, but now God has accepted both their lives, with hope that God may be merciful to them. It’s just the one that I am with now, and we are patient with each other. I have at least thirty grandchildren, if not forty.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
sarautar gargajiya Cikin tsarin mulki na Hausa wasu matsayai ana ganin kamar sarauta, wanda yake riƙe da matsayin kuma aka kira shi sarkin...har a ce ma shi ranka ya daɗe don ban girma. In traditional Hausa social structure and administration, higher posts are referred to as kingships and officials are, to some extent, respected like royalty.
faxi-tashin da yayi a rayuwa Wannan ya nufin iyakar muhimman abubuwan da ya yi ko kuma abubuwan da suka faru da shi cikin rayuwar shi. This implies an overview of his personal life, struggles and career. The Mayor gives an autobiography.
fagen siyasarsu ta da Wannan magana ce bisa halin tafiyar siyasa da gudunmawar Magagin gari cikin gudanar harakar ta a lokacin da. Political field. In this context, the journalist refers to the mayor's early achievements in the political field.
ba a jin xuriyarka Ba a jin labarinka. Cikin wannan halin ana ganin kamar a manta da Magagin garin domin ba a san abin da yake ciki ba. This saying means to be out of sight, or when a person is not mentioned in local chats, in this case referring to the mayor.
Babu abin da ke faruwa sai lafiya in ji Hausawa Wannan salon magana yana nufin babu wata matsala da take damuwar mutun, komi lafiya ne. This Hausa expression means everything is going well.
daxa bunqasa Ƙara ƙarfin wani abu cikin ƙara bayyana shi ga mutane, kamar harkar Scout da ake magana kai a nan. To develop, to spread. The Scout activities are promoted in the region and beyond.
yayinmu a harkar siyasa Mai wannan maganar yana zancen mutane waɗanda sun shafa ayukanshi da tunaninshi a zamanin da ya wuce; suna kamar malamai da sun koyar da shi. This statement illustrates the influence of the contemporary political leaders referred to by the speaker as his mentors.
babban jami’i mai kula da ilimin yaqi da jahilci Wannan matsayi ne da ake iya kira shugaba kuma. This is a title which could be considered Press Director in the case of the speaker.
fulotai Fili; a matsayinshi na Magagin garin, yana kula da yankin ƙasar da mutane su kan iya saye domin gina gida ko masana'anta. Plots of land. The speaker, who is a Mayor in this context, is in charge of public land management.
balantana wannan wata hanya ce ta cewa balle... This word is synonymous to "balle" which means 'let alone' in this context.
ganin girman juna ɗaukar juna da daraja. This expression means mutual respect.
yara manyan gobe Wannan karin magana ne da Hausa, kuma yana nufin ana ganin yara na yanzu sune za su canji datiɓai ko kuma shugabanin yanzu lokacin da sun girma. This Hausa saying refers to youth as people who will take over the leadership of a community or a nation in the future to replace the elders.
sun koyi kyawawan abubuwa na zaman duniya da manya ke yi. mai maganar yana nufin matasan su tasa da tarbiyya nagartatta, wadda za ta zama alheri ga dukan rayuwarsu ta wurin sauraren abin da mayan suke faɗa ko nunawa. In this context, the statement is like a sermon to young people from a respected and experienced elder, to call them to follow elders' footsteps in order to acquire knowledge and wisdom.
...ba ya haifar da alheri Ba ya kawo alheri. Its outcome is not positive; in this context, this saying refers to possible negative results that haste can bring about.
...ko ma a ruguje. Wannan yana nufin lalacewa, ko rashin ƙarko.Mai maganar yana nuna yadda ƙarshen wani abu zai iya zama maras kyau idan an aikata abin ciki hamzari da rashin tsari. This expression means to ruin. The speaker illustrates the consequences of rushing to take action in situations when wise planning is necessary or the action would be doomed to fail completely.
Allah ya karvi ransu Yana magana ce mai ladabi da Hausawa suke anfani da ita lokacin da suke cewa mutun ya mutu. God has taken them back; it is a polite way of saying that a person has passed away, or died.
munanan muna haquri da juna Wana magana ce da take nuna yadda mutane biyu ko fiye da biyu suke zaman rayuwa da juna cikin kamna da kula. This is a Hausa expression that applies to two or more people living together in a family relationship, friendship, or work-related interaction; it means accepting one another and caring for one another.
Gwagwarmaya Faɗi tashin rayuwa. One's struggles in life
ƙuruciya Yarintaka- Lokacin da mutum yake yaro. Childhood

Notes

Hausa Notes English Notes

Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor

Kano jiha ce da take a Arewa ta Yamma ƙasar Nijeriya. Ta kasance cikin yankin Arewa da ake kira ' Northern Region' har shekara ta 1967 lokacin da ta zama jiha a ƙarƙarshin ikon Bagaudawa da ake gani sun ci nasara bisa mazamnata kuma sun haɗa su daga baya. Suna da shirin iko da suke kira sarauta. Cikin gargajiya shugabanci a jihohin Hausa yana danganta da gado daga kakanni. Birnin Kano shi ne hedkwatar jihar kuma birni mai girma a Arewa wadda mafi yawa mutanen Hausa-Fulani ne kuma Musulmi. A nan akan yi tarzomai manya da suke farawa da sunan addini kuma wani lokaci su zama sanadin gaba da faɗa tsakanin ƙabiloli.

http://hrw.org/reports/2005/nigeria0505/6.htm#_Toc 103668154 www,kanoonline.com http://www.kanostate.net

Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor

Kano is a state located in the northwestern part of Nigeria. It used to be part of the northern region, until 1967 when it was created under the Bagaudawa, who conquered its inhabitants and later engaged in unifying the communities under the Sarauta (kingship) system. Traditionally, leadership in Hausa states was based on ancestry. Kano, the capital, is a large city in the North, and is predominantly Hausa-Fulani and Muslim. There, deadly clashes between religious groups sometimes turn into ethnic confrontations.

For more information, refer to the following links: http://hrw.org/reports/2005/nigeria0505/6.htm#_Toc 103668154 www.kanoonline.com http://www.kanostate.net

CONTENT SOURCE: Abubakar Haruna (2007 March 16). Youths Should Take It Easy - The Kano State Mayor. Abuja, NIigeria: Media Trust Limited (AMINIYA NEWSPAPER). http://www.dailytrust.com/maza.htm

Objective: Demonstrate your core comprehension.

Content description: The political and social changes that mark the history of Nigeria are discussed in this interview with Alhaji Inuwa Wada, Mayor of Kano, Nigeria.

XML<activity>
  <problemset>
   <problem correctindex="0">
     <choices>
      <opt>
        <eng-response>This interview with Alhaji Inuwa Wada, Mayor of Kano and a prominent figure in the state’s history, presents us with insight into the political and social changes that have marked the city’s past and present over the course of his long life.  From student to teacher in one of the state’s first schools, from the alphabet to Scout, his teaching ability goes beyond civil service to a leadership career that has positively contributed to the political progress of the North. The calm patriarch calls upon young politicians and future leaders to follow their predecessors’ footsteps in order to act wisely, respectfully, and patriotically. Politics should not be a business, but rather, an ideology, and a politician should be financially self-sufficient with a primary stable career, he remarked.</eng-response>
        <response>Wannan ganawa da Alhaji Inuwa Wada, Magajin Garin Kano, wanda shike kuma mashahuri ne ga tarihin jihar, tana ba mu basira bisa canji na zaman jama'a da siyasa a zamanin da, da yau, biye da tarihinshi. Daga lokacin da ya yi zaman ɗalibi, zuwa zaman malami, daga yaƙi da jahilci, zuwa Scout, sai a ce iyawarshi ta wuce bautar ƙasa, ta kai ga halin shugabanci wanda ya shafa ci gaban siyasa Arewan. Shi dattijon yana kira ga matasa ƴan siyasa, su bi hanyar mutanen da domin su samu koyi mai kyau na aiki, da ban girma da kuma hikima. Ya ce siyasa ba sana'a ba ce, harkar ra'ayi ce , kuma ya kamata ɗan siyasa ya iya riƙe kanshi da iyalinshi, ya zama kuma da riƙaƙƙar sana'a da farko.</response>
        <eng-fdbk>Correct! You followed the mayor's answers, which support the journalist's introduction and the main idea of the text.You also noticed how the journalist used subtle questions to get an authentic autobiography from the mayor.</eng-fdbk>
        <fdbk>Daidai ne! Kun lura da yadda amsoshin Magajin Garin sun daidaita da gabatarwar ɗan jaridar wadda ita ce kan maganan ganawar.Ku yi lura kuma da yadda ɗan jaridar ya yi tambayoyi waɗanda suka kawo Magagin garin ga bada ainihin tarihin kanshi.</fdbk>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>A journalist depicts an interesting profile of Kano’s mayor, Alhaji Inuwa Wada, in this interview. Wada’s predominantly political career has taken him through periods of apprenticeship and then leadership as the state has gone through its own social, economic, and political changes. Young politicians must listen to and learn from their elders, because, he said, young people are the future, and their lives should reflect patience, respect, and wisdom like their forefathers’. He does not appear on the political scene because of his calm nature. Old principles are not respected by young politicians who act irresponsibly, he mentions. The different posts he held in the administration contributed to his being nominated for his present post.</eng-response>
        <response>Wani ɗan jarida yana bada bayyani bisa tarihin Magajin Garin Kano, Alhaji Inuwa Wada, cikin wannan ganawa. Aikin Magajin Garin da ya yawaita a fannin siyasa, ya kai shi daga halin koyo, zuwa shugabanci yayinda jihar ita ma tana gusawa a wajen fanni tattalin arziki, zaman jama'a, da siyasa.Ya cancanta matasan ƴan siyasa su saurare dattijai, su koya daga garesu saboda, ya ce su ne shugabannin gobe, kuma ya kamata rayuwarsu ta kwatamtu da ta mutane da. Ba ya hawa bisa fagen siyasa saboda halinshi na rashin rigima, kuma matasa ba su ganin darajar tarbiyya irin ta da, sai dai aikata rashin hikima ya ce. Maƙamai da ya rika cikin hukuma sun danganta da naɗa shi ga matsayinshi na yanzu.</response>
        <fdbk>Ba daidai ba ne! Wannan zaɓen bai dace ba saboda akwai magana da ba a bayyana ba a cikin ganawar, amma an nuna ta cikin taƙaitawar. Ku yi tunani bisa ayyukan Magajin Garin da matsayinshi.
Akwai bayyanin dangantaka tsakanin ayyukanshi da ba shi wannan matsayi?</fdbk>
        <eng-fdbk>Incorrect! This choice is not correct because it states that the mayor's work experience was the basis for his nomination, whereas the text does not clearly mention that. Think again about his past positions and the post he now holds. Is there any mention of that link?</eng-fdbk>
      </opt>
      <opt>
        <eng-response>This is an interview with the mayor of Kano, who tells about his career, his state’s history, and his concerns about young Nigerians and politics. Alhaji Inuwa Wada reflects on the many administrative and political posts he has held over the years, contented with his achievements and especially with the way politics once was. He states that politicians should not get involved with the goal of making money, but should have financial stability before getting involved in politics. He expresses his respect for some other political figures that influenced him, reminding young politicians that they should follow their example in order to become good leaders. He condemns young people’s lack of respect for traditional values, and politicians’ lack of transparency and leadership.</eng-response>
        <response>Wanna ganawa ce da Magajin Garin Kano wanda yana magana bisa aikinshi, tarihin jihar, da kuma damuwar shi a kan matasa ƴan siyasa na Nijeriya, game da siyasa. Alhaji Inuwa Wada ya riƙe maƙamai dayawa a wajen hukuma da kuma siyasa
cikin shekaru dayawa da yake zanawa da jin daɗi saboda gudumawarshi da kuma musamman yadda ake tafiyar da siyasa a lokacin. Ya ce bai cancanta ba ƴan siyasa su shiga cikinta da burin samun kuɗi, amma su zama da wadata kafin su shiga. Ya nuna ban girma ga wasu ƴan siyasa na da waɗanda ya samu tasiri daga garesu, yana tuna wa matasan ƴan siyasan da yi kamar su domin su zama nagartattun shugabanni. Ya yi Allah waddai da rashin ban girman matasa ga al'adu, da rashin gaskiya da shugabanci na ƴan siyasa.</response>
        <eng-fdbk>Incorrect! This choice is not correct because it changes the mayor's statement about youth and politicians. Please read the parts that address his advice to those groups of people. What is his opinion?</eng-fdbk>
        <fdbk>Ba daidai ba ne! Wannan amsa ba daidai take ba saboda a canji bisa maganar Magajin Gari, kan matasa da ƴan siyasa. Minene ra'ayinshi?</fdbk>
      </opt>
     </choices>
   </problem>
  </problemset>
  <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
  <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
  <finishtl>Yaya tarihin Magajin Garin yake nuna banbancin rayuwar da da ta yanzu</finishtl>
  <finish>How does the mayor's biography distinguish between past and present lifestyles?</finish>
  <finishtl>A ganinku Magajin Garin ya iya canza ra'ayin matasa idan a ce ya koma ga karantarwa. Ku bada dalili ko dalilai.</finishtl>
  <finish>Would the Mayor bring about a change of attitude in young people if he were to go back to teaching? Why or why not?</finish>
  <finishtl>Minene ra'ayinku kan wannan Magajin Garin?</finishtl>
  <finish>What do you think of this mayor?</finish>
</activity>