UMD NFLC Hausa Lessons/67 Desertification and Northern Nigeria

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/67)
Jump to: navigation, search

Overview

 1. Lesson Title: Desertification and Northern Nigeria-This is a report about desertification.
 2. Language: Hausa
 3. Topic: Ecology/Geography
 4. ILR Level: 2+/3
 5. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
 6. Modality: Reading
 7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
 8. Subject Area: Language
 9. Material Type: LLO
 10. Publication Year: 2009
 11. ObjectID: T8RHA03

Transcript


Original Translation

Hamada na ƙara zama babbar barazana ga jihohin Arewacin Nigeria.

Jihar Katsina na daga cikin jihohi goma sha ɗaya na arewacin Nigeria waɗanda suka ƙunshi jihohin Borno da Yobe da Kano da Jigawa da Sokoto da Kebbi da Zamfara da Bauchi da kuma Gombe waɗanda ke fama da matsalar kwararowar Hamada. Kowace daga cikin waɗannan jihohi sun ƙaddamar da matakai daban daban na yin kariya ga yaduwar Hamada a yankunan su. Babban abin damuwa ga yaɗuwar Hamada shine irin matsalolin da take haddasawa. A baiyane yake dai cewa matsaloli kama daga ƙarancin ruwan sama da fari da ƙonewar amfanin gona da kuma yaɗuwar yashin Hamada dake rufe gonaki ya hana shuka fitowa na daga cikin tasirin da muke gani ƙuru-ƙuru na matsalolin Hamada. Abin laákari shine ko me yasa Hamadar ke neman zama gagarabadau, matasalar ta gawurta ne yadda ba zaá iya shawo kanta ba ? A jihar Katsina a shekarar 2008 gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya ƙaddamar da katafaren shirin dashen itatuwa a garin Dankama tare da alƙawarin cewa gwamnati zata dasa itatuwa miliyan bakwai a faɗin jihar nan da shekarar ta 2011 domin yin kandagarkin Hamada. Sai dai kuma kamar yadda akan ce ba nan Gizo ke saƙar ba, sau da dama akan yi dashen itatuwa amma daga wannan lokaci baá sake waiwayar su sai wata shekarar idan azo yin wani bikin dashen itatuwan. Sakamakon daɗa gusowar da Hamada ke yi, a kowace shekara akan yi hasarar ƙasar noma mai yawa, a wasu lokutan ma, ya kan zama wajibi jamaá su ƙauracema yankunan su a sabili da matsowar Hamadar. Sare dazuka da kuma dogaro da itace a matsayin makamashin girki na daga cikin abin da ke kawo koma baya ga matakan kariyar Hamada. A nan akwai buƙatar majalisun dokoki na jihohi su sabunta doka mai ƙarfi wadda zata tanadi hukunci mai tsanani akan dukkan wanda ya sare bishiya ba tare da izni ba. Sai dai kuma a waje guda akwai buƙatar gwamnati ta samar da sabbin dabarun makamashi ga alúma domin cimma nasarar wannan manufa. Ko shakka babu ana dai iya shawo kan matsalar Hamada idan aka ɗauki managartan matakan da suka dace kamar yadda wasu ƙasashe irin su Libya da Algeria da kuma Mauritania suka yi.

The Desert is Increasingly Becoming a Major Threat to the States of Northern Nigeria

Katsina State is among the eleven states of northern Nigeria (including the states of Borno, Yobe, Kano, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Bauchi, and Gombe) that are suffering from the problem of the encroaching desert. Each of these states has undertaken different measures to keep the desert from spreading into their districts.

A major concern regarding the spreading desert is the types of problems it is causing. Clearly, problems such as drought, famine, the drying up of agricultural products, and spreading sand that covers farms and prevents seedlings from sprouting are among the obvious effects resulting from the desert [encroachment].

The increasing advancement of desertification in the area has become a problem so great that it seems irresolvable. In 2008 in Katsina State, the Katsina state governor, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, launched an aggressive campaign to plant trees in Dankama village and promised that the government would plant 7 million trees across the state by the year 2011 as protection against the desert.

But as the saying goes, let’s not lay the blame in one direction only. On many occasions, trees are planted, but then no one cares for the trees to make sure they continue growing until the next annual tree planting campaign.

As a result of desertification, much farmland is lost every year and, in some instances, people are forced to abandon their land because of spreading sand.

[Curbing the] cutting down of shrub lands and the reliance on wood as a source of cooking fuel are some of the steps that help hold off the desert. The state legislatures must now revise and strengthen the law to exact harsh punishment on anyone who cuts down trees without permission.

Furthermore, the government should provide a new fuel plan for the public for this policy to succeed.

We can certainly solve the desert problem if we take deliberate and appropriate steps as countries such as Libya, Algeria, and Mauritania have done.

Glossary

Hausa term English meaning
Ruwan sama (lit: water of the sky/heavens) rainfall 

In this text, a drought, or shortage of rainfall, is referred to.

yashin hamada sand, sand dunes formation
ƙuru-ƙuru can be seen, obvious 

ƙuru-ƙuru is usually used to describe a stare, or a wide-eyed look.

ba nan Gizo ke saƙar ba (lit: that is not where the spider builds its web) let’s not lay the blame in one direction only
Sare dazuka (lit: cutting forests) cutting down of shrub lands
makamashin girki a source of cooking fuel
Shakka babu (also babu shakka) certainly, without a doubt
shawo kan (lit: drinking the head) solve, overcome


Notes

1. Desertification

Northern Nigeria borders Niger, a country with about half its land covered by the Sahara desert. The desert is said to be moving to the south, as Nigeria also experiences desertification, which affects the citizens due to threats of hunger and extreme weather conditions. The temperature is often over 85 degrees in Northern states compared to the South, which has a more tolerable weather. As the years go by, farmers find themselves working harder to maintain the same amount of produce annually and with less rain.


2. More Information

a) For more information regarding the impact of desertification on agriculture in Nigeria, please visit the following link:

http://desertification.wordpress.com/2007/03/30/desertification-in-nigeria-african-agriculture/

b) For more information regarding the social impact of desertification in Nigeria and Niger, please visit the following link:

http://africanpress.wordpress.com/2008/11/28/nigeria-desertification-affects-35-million-nigerians/