bbchausa verticals/016 recruiters on fb

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Contents

#: How recruiters are stalking you on Facebook [1] <> Yadda masu daukar aiki ke bibiyarku a Facebook [2]

#: Social media platforms like Facebook are an ideal place for recruiters to look for candidates. [3] <> Shafukan sada zumunta irin su Facebook na taimakawa masu daukar maaikata neman irin mutanen da su ke so. [4]

#: But can powerful targeting tools allow companies to discriminate? [5] <> Sai dai kuma anya hanyoyin kebance masu ganin talla a shafukan ba za su bai wa kamfanoni damar nuna wariya ba? [6]

#: Almost four months ago, [7] <> Kusan watanni hudu da su ka wuce, [8]

#: Lisa Dorahy was scrolling through Facebook when she saw a job advert pop up in her news feed. [9] <> Lisa Dorahy ta ga wani tallan neman maaikata a shafinta na Facebook. [10]

#: She wasnt really looking for a new job, [11] <> Ba ma aiki ta ke nema ba, [12]

#: and it was one of the rare times the mother-of-three had time to use social media. [13] <> kuma ba ta cika duba shafin Facebook ba, [14]

#: But the post advertising for a part-time assistant at a recruitment agency seemed perfect for her. [15] <> amma aikin mataimakiyar rabin lokaci a kamfanin daukar maaikata ya bata shaawa. [16]

#: She followed the link to apply, [17] <> Kamar wasa sai ta danna tallan, [18]

#: had an interview three days later, and a job with New Zealand agency, Human Connections Group by the following week. [19] <> cikin kwanaki uku an kira ta ganawa, bayan mako guda kuma aiki ya samu a kamfanin daukar maaikata na Human Connections Group da ke kasar New Zealand. [20]

#: Dorahy now realises the ad was specifically targeted to find heror someone like her. [21] <> Daga baya ne Dorahy ta gano cewa dama an shirya tallan ne domin ya riske ta ko kuma dai mata irinta. [22]

#: The ability to hyper-target candidates for specific jobs could also allow some recruiters to discriminate based on age, ethnicity, religion or gender [23] <> N/A [24]

#: Facebook ads are not a new phenomenon[25] <> Talla a Facebook ba bakon abu ba ne[26]

#: no doubt youve seen similar ads in your news feed. [27] <> tabbas kun saba ganinsu a shafukanku. [28]

#: But you may have also seen job advertisements appear for roles and industries that are outside your regular line of work. [29] <> Sai dai kuma mai yiwuwa kun taba ganin tallan aikin da ba ya cikin abubuwan da ku ka saba yi a baya. [30]

#: This is likely the result of [31] <> Hakan na faruwa ne saboda [32]

#: recruiters [33] <> masu neman maaikatan [34]

#: looking for someone with your specific skills, [35] <> na bukatar mutane masu irin kwarewarku, [36]

#: based off information that Facebook has learnt about you from your behaviour on the site. [37] <> sakamakon bayananku da ku ka wallafa a shafin Facebook da kuma dabioinku a shafin. [38]

#: As more recruiters begin to use the tool, [39] <> Yayin da masu neman maaikata da yawa ke tururuwar tallata gurabe a Facebook, [40]

#: some warn the ability to hyper-target candidates for specific jobs [41] <> masana na gargadin cewa damar da shafin ke bayarwa na aika sakonnin talla ga wasu kebantattun mutane [42]

#: could also allow some recruiters to discriminate based on age, ethnicity, religion or gender. [43] <> zai iya bai wa wasu kamfanonin damar nuna wariya bisa ga dalilin shekaru, kabilanci, addini ko jinsi. [44]

#: When BBC Capital contacted Facebook [45] <> Lokacin da BBC ta tuntubi Facebook, [46]

#: it declined to comment on the practise of targeted recruitment on the platform. [47] <> kamfanin ya ki amincewa ya mai da martani game da tsarin aika tallan neman aiki ga wasu kebantattun mutane. [48]

#: It works like this: [49] <> Ga yadda tsarin ya ke: [50]

#: Facebook Ads is a service which allows businesses to [51] <> tallan Facebook wani tsari ne da ke bai wa kamfanoni [52]

#: pay to place advertisements on and around peoples Facebook feeds. [53] <> damar tallata hajarsu a shafukan masu amfani da Facebook. [54]

#: When placing an advert, [55] <> Lokacin da za su bada tallan, [56]

#: the business can choose the exact type of person they want to see it, [57] <> kamfanonin na iya zabin irin mutanen da su ke son su ga tallan, [58]

#: based on their age, sex, interests, race, religion and much more. [59] <> ta hanyar bayyana shekarunsu, jinsinsu, launin fatarsu, addininsu, abubuwan da su ke shaawa da ma sauran bayanai da dama. [60]

#: Facebook is not the only social media network to allow targeted advertising[61] <> Ba Facebook kadai ne shafin zumuntar da ke bai wa masu talla damar zabin wadanda su ke son su ga tallan na su ba[62]

#: any platform that collects data on its users can offer a similar service. [63] <> duk wani shafi da ke tattara bayanan abokan huldarsa ma zai iya hakan. [64]

#: For example, Google+ and Facebook-owned Instagram also offer hyper-targeted advertising, [65] <> Misali Google+ da Instagram, mallakar Facebook su ma su na bada wannan damar, [66]

#: while LinkedIn allows recruiters to create targeted ads based on age or gender, [67] <> yayin da LinkedIn ke bai wa masu neman maaikata damar zaben wadanda za su ga tallansu bisa laakari da shekaru ko jinsi [68]

#: but not on race or sexual preference. [69] <> amma ban da launin fata ko dabiar jimainsu. [70]

#: A billion potential candidates [71] <> Maaikata biliyan guda [72]

#: Founder of London-based digital marketing agency Link Humans [73] <> Mutumin da ya kafa kamfanin Link Humans da ke London, wanda ke tallace-tallace a Intanet, [74]

#: Jorgen Sundberg estimates 10% of the UKs almost 20,000 recruitment agencies are now using Facebook advertising. [75] <> Jorgen Sundberg ya kiyasta cewa kaso 10 na kusan kamfanonin daukar maaikata 20,000 da ke Burtaniya na yin talla a shafin Facebook. [76]

#: Facebook has the most data on anyone, arguably, out of all the tech companies,” he says. [77] <> Ya ce: “Facebook yafi kowanne kamfanin fasahar zamani tattara bayanai game da abokan huldarsa.” [78]

#: A Facebook spokesman says the company could not share data on the number of recruiters using the tool, and declined to comment further. [79] <> Wani mai magana da yawun Facebook ya ce kamfanin ba zai iya bayyana adadin kamfanonin daukar maaikata da ke talla a shafin ba. [80]

#: With 1.13 billion daily active users, Facebook is a place where you can find candidates for all sorts of jobs, [81] <> Babu irin maaikatan da ba za ka samu a Facebook ba, saboda fiye da mutane biliyan guda ne ke ziyartar shafin a kullum, [82]

#: says founder of UK social media agency Social-Hire Tony Restell. [83] <> in ji mutumin da ya kafa kamfanin Social-Hire mai daukar maaikata ta hanyar shafukan sada zumunta, Tony Restell. [84]

#: Venture capitalists are as likely to want to keep up with friends as truckers [[[are]]], so Facebook has a massive penetration across sectors.” [85] <> “Yadda masu hada-hadar kudi ke bukatar hulda da abokansu, haka masu aikin karfi su ke da wannan bukata, don haka babu irin wanda babu a Facebook.” [86]

#: This huge variety of people on Facebook means advertisers need to be specific and accurate in their targeting. [87] <> Kasancewar akwai mutane mabambanta a Facebook, ya zamo dole masu tallata guraben aiki su zabi wadanda su ke so su ga tallansu. [88]

#: When theyre not, we end up seeing those job adverts that are laughably irrelevant to us. [89] <> Idan ba haka ba kuwa, zamu yi ta ganin tallan guraban aikin da babu abinda ya hada mu da su. [90]

#: But Facebook wont stand for too much error, he says. It rewards advertisers with lower fees if the audience is interested in the advert, and punishes with higher fees it theyre not. [91] <> Baya ga haka Facebook na cajar masu talla kudi kalilan idan mutanen da aka tallatawa sun nuna shaawarsu, amma su na cajin kudi da yawa idan mafi yawan wadanda aka tallatawa ba su nuna shaawarsu ba. [92]

#: Bang for your buck [93] <> Zabi ka darje [94]

#: Human Connections Group founder and recruiter Emily Richards [95] <> Wacce ta kafa rukunin kamfanonin Human Connections Group, Emily Richards [96]

#: now uses Facebook to fill one in every three jobs. [97] <> na amfani da Facebook wurin cike daya daga cikin uku na guraben aikin da ta ke da su. [98]

#: The New Zealand-based recruiter says she will spend NZ$20 ($14) [99] <> Mai daukar maaikatan, da ke New Zealand ta ce ta kan batar da $14 [100]

#: to reach up to 10,000 people, depending on the demographicwhich she says is a cost-effective option. [101] <> domin tallanta ya isa ga mutane 10,000, abinda ta ce babu tsada idan aka kwatanta da sauran kafafen yada labarai. [102]

#: But the recruiter is alsoacutely awareof [103] <> Sai dai kuma ta na sane da cewa [104]

#: companiesabilities to use the targeting function for discrimination. [105] <> ana iya amfani da Facebook wurin nuna wariya lokacin daukar aiki. [106]

#: I think if put in the wrong hands it could be incredibly detrimental to gender equality, [107] <> Ta ce: “Ina ga mutanen banza za su iya amfani da wannan damar wurin kawo nakasu ga daidaiton jinsi [108]

#: racial equality and all of that stuff weve worked so hard to get to a point that it doesnt happen," Richards says. [109] <> da launin fata da ma duk wani adalci da mu ka kwashe shekaru muna kokarin ganin ya tabbata.” [110]

#: Wanted: Single male. Vegans need not apply [111] <> Muna nema: Saurayi, mai cin nama [112]

#: For the purposes of testing just how targeted a job ad could be, [113] <> Domin gwajin yadda ake zaben masu ganin tallace-tallace a Facebook, [114]

#: BBC Capital attempted a test job advertisement on Facebook. [115] <> BBC ta bayar da tallan gurbin aiki a shafin. [116]

#: First, we chose to target only males between the ages of 18 and 25, living in New York. [117] <> Da farko mun zabi samari masu shekaru 18-25, da ke zaune a New York. [118]

#: We then opted toexcludeall men who were parents or in a relationship. [119] <> Daga nan kuma sai mu ka ce ban da mazan da su ke dayaya ko aure ko ma su ke da budurwa. [120]

#: One could even exclude by race. [121] <> In da mun so ma da zamu iya kebe wani launin fata. [122]

#: We then excluded all vegans, vegetarians and men wholikechocolate. [123] <> Sai kuma muka ce ban da duk wadanda ba sa cin nama da kuma wadanda ke son alawar cakulati. [124]

#: The resulting super-targeted job ad for aSocial Media Superstarwas soon approved by Facebook and ready to goheading out to 430,000 young, single, childless, meat-eating men. [125] <> Ba da jimawa ba kuwa Facebook ya amince da tallan, inda aka shirya nuna shi ga samari, mara sayaya, maciya nama da ke birnin New York su 430,000. [126]

#: Davida Perry, the managing partner of New York law firm Schwartz & Perry, says targeting specific job candidates through Facebook advertising could amount to a breach of several laws. [127] <> Davida Perry, shugabar kamfanin aikin lauya na Schwartz & Perry da ke New York, ta ce tallata guraben aiki ga wasu kebantattun mutane a Facebook zai iya sabawa dokoki da yawa. [128]

#: In the US, federal human rights laws forbid recruiting in a way that discriminates against people based on age, race, religion, gender, pregnancy, disability or sexual orientation. [129] <> A Amurka, doka ta haramta nuna bambanci wurin daukar aiki bisa dalilin shekaru, launin fata, addini, jinsi, daukar ciki, nakasa, ko halayyar jimai. [130]

#: In the UK, its illegal to discriminate when recruiting based on age, gender, pregnancy, sexuality, religion or marital status. [131] <> A Burtaniya, haramun ne a nuna bambancin shekaru, jinsi, daukar ciki, halayyar jimai, addini, ko aure a wurin daukar aiki. [132]

#: Where you advertise can be discriminatory as well[133] <> Ana iya kama ka da laifin nuna wariya ma idan aka yi laakari da wurin da ka tallata gurbin aikin[134]

#: for example, if you were to advertise a role only in mens magazines. [135] <> misali, talla a mujallar maza kadai. [136]

#: So even though the targeted advertisements themselves might not appear discriminatory, the process of targeting them to some people and excluding others can be. [137] <> Don haka duk da cewa su tallace-tallacen babu alamun wariya a cikinsu, tsarin da ake bi wurin zaben wadanda za su gansu zai iya keta dokokin haramta wariya. [138]

#: Although the process used to post some job ads could be illegal, thesefailure to hirecases arevery, very hard to prove”, Perry says. “Its hard enough to prove discrimination against someone in the workforce”. [139] <> Duk da haka, “zai yi matukar wuya a kama masu tallan da cikakkiyar hujjar da za a iya hukunta su,” in ji Perry. [140]

#: But, she says, if the recruiter has publicised the targeting, it could open them up to legal repercussions like a fine or court order. [141] <> Amma ta ce, da masu neman maaikatan za su tallata matakan da su ka bi na kebe wadanda za su ga tallace-tallacensu da kuwa za su iya haduwa da fushin kotu. [142]

#: Facebooks advertising policy states advertisements [143] <> Kaidar talla a Facebook dai ta bukaci duk masu bada talla da [144]

#: must not use targeting options to discriminate against, harass, provoke, or disparage users”, [145] <> su kauce wanuna bambanci, muzganawa, tsokana, ko wulakanta abokan hulda,” [146]

#: and advertisers on Facebook are obliged to make sure their ads comply with the law. [147] <> kuma wajibi duk wanda zai ba da talla a shafin ya tabbatar ya cika wannan kaidar. [148]

#: Facebook declined to comment on the practise of targeted recruitment on the platform. [149] <> Mun so jin ta bakin Facebook game da ware mutanen da zasu ga talla amma ya yi gum. [150]

#: A force for good [151] <> Alheri ne [152]

#: Despite the risk, [153] <> Duk da barazanar wariya da ke cikin tallan Facebook, [154]

#: online recruitment specialists urge people not to think the worst. [155] <> kwararru a kan harkar daukar maaikata ta intanet na shawartar mutane da su daina musu mummunan zato. [156]

#: Link HumansSundberg uses the analogy ofthe forcein Star Wars: targeted ads can be used by the dark side, but they can also be used for good. [157] <> Sundberg na kamfanin Link Humans ya ce tabbas zaa iya amfani da tallan Facebook domin kitsa sharri amma kuma zaa iya amfani da su domin tabbatar da alheri. [158]

#: Theres always rogue players out there, but on the whole its all legit. If youre a recruiter or an agency recruiter everyone is screaming out for diversity, so I dont see why you would use it to discriminate.” [159] <> Ya ce: “A kullum baa rasa mutanen banza, amma dai mafi yawa na amfani da tsarin ne bisa doka. Idan kai sanaarka nema wa kamfanoni maaikata, duk inda ka juya ana tunatar da kai bukatar budawa kowa ya samu, don haka babu dalilin da za ka yi amfani da Facebook don kawo wariya.” [160]