bbchausa verticals/017 oversharing

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Contents

#: Think before you overshare. Yes, it can get you fired [1] <> Hattara da shafukan sada zumunta. Kar ka yi asarar aikinka [2]

#: Has social media made us less inclined to share our opinions? [3] <> Shin shafukan sada zumunta sun samu fargabar bayyana raayoyinmu? [4]

#: Alvarez, a media sales consultant and mother of two from London, [5] <> Alvarez, mashawarciya kan harkokin talla kuma mahaifiyaryaya biyu da ke zaune a London, [6]

#: isnt a prolific online sharer [7] <> ba ta cika sa hotuna a Facebook ba, [8]

#: so didnt think too much about posting a photo of her toddler with a bare bottom on her page. [9] <> don haka ba ta yi tunanin mai zai biyo baya ba, lokacin da ta sa hoton danta mai ta-ta-ta babu wando a shafinta. [10]

#: The post was a funny, innocent photo,” she says. “Normally my posts receive a good reception.” [11] <> Ta ce: “Hoton na da ban dariya. Kuma na saba samun kyakkyawar tarba idan na saka abubuwa a Facebook.” [12]

#: Mummy shaming? [13] <> Kunyata uwa? [14]

#: But, after initial likes and positive comments, [15] <> Sai dai, bayan da wasu su ka danna maballinsoda kuma sakonni masu dadi da ta fara samu, [16]

#: the criticism started, [17] <> sai kuma suka ta biyo baya. [18]

#: someone responded withVery funny but take this off. [19] <> Wani ya rubutaAbin dariya amma dai ki cire. [20]

#: There are a lot of perverts around.’ [21] <> Akwai masu mugun tunani da yawa.” [22]

#: Then, a barrage of negative comments followed. [23] <> Daga nan sai sakonnin suka su ka yi tuttudowa. [24]

#: Alvarez says it wasnt long before she was stopped in the street by acquaintances asking her to delete her post. [25] <> Alvarez ta ce kafin a jima, abokan huldarta sun fara tsayar da ita akan hanya su na ce mata ta goge hoton. [26]

#: Numerous private messages landed in her inbox from people advising her to take the picture down becauseits not safe,’ despite it being a private post. [27] <> Ta kuma sami sakonnin sirri da dama daga mutanen da ke ba ta shawarar cewa ta cire hoton sabodaakwai hatsari’. [28]

#: I was made to feel I had done something wrong [29] <> Ta ce: “Sai dai aka sa ni jin cewa na tafka wani babban kuskure [30]

#: and it was a reflection on me as a mother,” she says. [31] <> kuma wannan na nuna cewa ni ba uwa ta gari ba ce. [32]

#: I felt judged. Some of them were more about public shaming than giving me advice in my best interest.” [33] <> Mafi yawan sakonnin na cin mutunci ba wai shawara ba.” [34]

#: The experience has made her much more circumspect. [35] <> Wannan lamari ya sa ta shiga taka-tsan-tsan. [36]

#: I would still post things on social media in the future, [37] <> “Zan ci gaba da wallafa abubuwa a shafukan sada zumunta, [38]

#: but Ive learnt my lesson,” Alvarez says. [39] <> amma dai na koyi darasi,” in ji Alvarez. [40]

#: She feels lucky that on that occasion the episode didnt filter through to her colleagues or workplace. [41] <> Ta ce saarta guda labarin kai wa abokanan aikinta ba. [42]

#: Claire Knowles, a partner at law firm Acuity Legal, [43] <> Claire Knowles, wata lauya da ke kamfanin Acuity Legal, [44]

#: says one of her clients was not so lucky. [45] <> ta ce wata abokiyar huldarta ba ta yi dace da irin wannan saar ba. [46]

#: Messages on her clients private Facebook page put her job in jeopardy. [47] <> Sakonta da ta wallafa a shafinta na Facebook ya sa aikinta cikin hatsari. [48]

#: She effectively posted that her manager was an idiot and incompetent in his role[49] <> “Ta rubuta cewa manajanta shashasha ne kuma bai san aikinsa ba[50]

#: potentially a form of cyber-bullying,” says Knowles. [51] <> wannan kuwa abu ne da ya saba wa dokar tozarta mutane a intanet.” In ji Knowles. [52]

#: Word made its way back to her employer, including her manager [53] <> “A hankali labari ya koma ga kamfanin da ta ke aiki har shi kansa manajan ya ji. [54]

#: and disciplinary proceedings for gross misconduct were initiated. [55] <> Hakan ta sa aka ladabtar da ita bisa tuhumar rashin ladabi. [56]

#: All the employer needed to show was that the posts could have caused offence or damaged the companys reputation,” Knowles adds. [57] <> Iyakacin shaidar da ake bukata daga shugabanninta shi ne su nuna cewa rubutun nata ya bata ran manajan kuma ya zubar da kimar kamfanin.” A cewar Knowles. [58]

#: Knowlesclient, who cant be named for legal reasons, [59] <> Abokiyar huldar Knowles, wacce ba za a iya bayyana sunanta ba saboda dalilai na sharia, [60]

#: says she didnt set out to bully her manager [61] <> ta ce ba ta da niyyar tozarta manajanta, [62]

#: and was only venting frustrations. [63] <> kawai dai ta na huce takaicinta ne. [64]

#: The client claims she wasnt aware of a workplace social media policy [65] <> Ta kuma ce ba ta san akwai wata dokar amfani da kafafen sada zumunta a ofishinsu ba, [66]

#: and hadnt received training on it. [67] <> kuma babu wanda ya ba ta horo a kan haka. [68]

#: The employee was given a final written warning[69] <> Daga karshe dai, an ba ta takardar gargadi, [70]

#: the only reason she wasnt dismissed was her length of service and remorse, Knowles says. [71] <> abinda kawai ya hana a kore ta shi ne dadewarta a bakin aiki da kuma nadamar da ta nuna. [72]

#: Think before you share [73] <> Yi tunani kafin wallafawa [74]

#: When colleagues are part of your social media audience [75] <> Idan abokan aikinka na cikin abokan huldarka a shafukan sada zumunta, [76]

#: you must have the same level of self-governance as within any other work environment, be that at your desk, or at the office party, says James Murray, [77] <> wajibi ne ka kasance cikin taka-tsan-tsan kamar a wurin aiki, in ji James Murray, [78]

#: associate director at global recruitment firm Robert Walters. [79] <> mukaddashin darakta a kamfanin daukar maaikata na Robert Walters. [80]

#: So after a brief, naive, free-for-all, [81] <> Bayan sharholiya, da ganganci, na dan gajeren lokaci da muka yi a farkon samuwarsu, [82]

#: is social media steadily silencing us? [83] <> shin a yanzu shafukan sada zumunta na sa mu yi wa kanmu takunkumi? [84]

#: A Pew Research Center study shows [85] <> Wani bincike da Pew Research Center ta gudanar ya nuna cewa [86]

#: it is making us increasingly more inhibited and less likely to express our real views, on current affairs or real life. [87] <> yanzu bamu cika bayyana raayinmu na gaskiya game da alamuran yau da kullum ko sauran shaanin rayuwa ba. [88]

#: This anxiety explains the rise of WhatsApp, [89] <> Wannan fargabar na daya daga cikin dalilan da su ka bunkasa amfani da WhatsApp, [90]

#: where users can message select friends privately, or apps like SnapChat, [91] <> inda masu amfani da su kan aika da sako ga zababbun abokansu, ko kuma SnapChat, [92]

#: where the message self-destructs, rather than the user's reputation, has been fuelled by demand to express opinion without judgement. [93] <> wanda sako ke goge kansa jim kadan bayan aika shi. [94]

#: And be warned just because youreoff the clockfrom your day job doesnt lessen the risk of getting into trouble at work if you do post something that backfires. [95] <> Kuma ku sani, daukar hutu daga wurin aiki ba ya rage muku fuskantar hatsari idan ku ka wallafa wani abu da ya jawo suka. [96]

#: In July The Telegraph reported that a British Council executive [97] <> A watan Yuli, jaridar The Telegraph ta Ingila ta bada labarin cewa wata maaikaciyar hukumar raya aladun Burtaniya, ‘British Council’, [98]

#: Angela Gibbins will face disciplinary action after writing a critical post about HRH Prince George. [99] <> Angela Gibbins za ta fuskanci ladabtarwa bayan da ta soki Yarima George a shafin sada zumunta. [100]

#: The newspaper also reported that an Instagram post about feeding meat to vegan diners in Derby, UK, got head chef Alex Lambert fired. [101] <> Jaridar ta kuma bada labarin cewa an kori wani babban kuku a Derby, UK, Alex Lambert bayan da ya wallafa hoto a Instagram, da ya yi ikirarin ya na sa nama a abincin mutanen da ba sa cin nama. [102]

#: Staff usage of social media reflects on the company even if staff members arent officially managing that organisations social media channels,” [103] <> “Yadda maaikata ke amfani da shafukan sada zumunta na shafar yadda ake kallon kamfaninsu ko da ba sa cikin wadanda ke kula da shafukan kamfanin a zaurukan sada zumunta,” [104]

#: says Chris Lee, head of digital strategy and training consultancy Silvester & Finch in London. [105] <> in ji Chris Lee, shugaban kamfanin ba da horo kan tallata haja a intanet Silvester & Finch da ke London. [106]

#: Employees can easily let slip confidential information, or their opinions could reflect negatively on their firm, he says. [107] <> Ya ce: “Maaikata na iya fitar da bayanan sirri bisa kuskure ko su bayyana raayin da zai bata sunan kamfanin. [108]

#: In 2015 UK firm Game Retail dismissed one of its employees over offensive but non-work related tweets. [109] <> A 2015, wani kamfani a UK, Game Retail ya kori daya daga cikin maaikatansa saboda rubutan cin mutunci da bai dangancin aiki ba, wanda ya yi a shafin twitter. [110]

#: Despite the employee initially winning an unfair dismissal case Game Retail appealed and won. [111] <> Da farin dai maaikacin ya yi nasara a kotu inda ya zargi kamfanin da korarsa ba bisa kaida ba, amma Game Retail ya yi nasara bayan da ya daukaka kara. [112]

#: Recruitment tool [113] <> Hanyar daukar aiki [114]

#: Can your posts also damage your chances of landing that dream job elsewhere? [115] <> Shin abinda ka wallafa a shafukan sada zumunta na iya hana ka samun aikin da ka ke fata? [116]

#: Well, yes. Social media is now an integral part of the vetting process, whether companies admit it or not. [117] <> E. Yanzu haka kamfanoni na amfani da shafukan sada zumunta wurin tantance wadanda za su dauka aiki, koda yake da yawansu ba sa fadar haka. [118]

#: A study by recruiter, [119] <> Wani bincike da kamfanin daukar maaikata, [120]

#: Robert Walters, found half of employers are prepared to research candidates using social media, [121] <> Robert Walters ya gudanar, ya gano cewa rabin masu daukar aiki a shirye su ke da su binciki wadanda za su dauka ta hanyar shafukan sada zumunta, [122]

#: whilst 63% have viewed a job seekers professional social network profile, say social network LinkedIn. [123] <> yayinda kaso 63 na amfani da shafukan sada zumunta na sanaa irinsu LinkedIn wurin tantance masu neman aiki. [124]

#: Anyone can get themselves into hot water [125] <> Mutane na iya cusa kansu cikin masifa, [126]

#: if they don't think before they share, says Steve Nguyen, a leadership and change consultant in Dallas, Texas. [127] <> matukar za su wallafa abu a shafin sada zumunta ba tare da tunani ba, in ji Steve Nguyen, mashawarci a kan shugabanci da kawo sauyi da ke Dallas, Texas. [128]

#: But reflection is sometimes forgotten in the rush to post. [129] <> Sai dai a lokuta da dama ana wallafa babu tunani saboda rige-rige. [130]

#: Because of this first-to-publish mentality, [131] <> “Saboda kowa ya na so a fara ji daga wurinsa, [132]

#: we can see why were less inclined to self-filter because were in such a hurry to produce something thats funny or shocking,” says Nguyen. [133] <> sai ayi ta wallafa babu nazari a kokarin rubuta labarin ban dariya ko kuma tada hankali,” in ji Nguyen. [134]

#: So if we know the risks why do we still do it? [135] <> To idan mun san hakan na iya jefa mu cikin hadari, me ya sa mu ke ci gaba da yi? [136]

#: Disinhibition can happenwhere we cant see ahead to the impact, [137] <> Rashin hangen nesa na iya jawo haka, [138]

#: says Nathalie Nahai, web psychologist and author ofWebs of Influence.’ [139] <> in ji Nathalie Nahai, mai nazarin halayyar mutane a intanet, wacce ta wallafa littafinWebs of Influence.’ [140]

#: Online communication is mediated through a screen creating distance and sometimes anonymity and that leaves us feeling we can comment and post on whatever we want[141] <> Ana sadarwa a intanet ne ta hanyar kafafen da ke iya boye mu, abinda ke sa mu jin cewa zamu iya yin bayani kan duk abinda mu ka so[142]

#: often in a way that we wouldn't in real life. [143] <> bisa sigar da ba zamu iya yi ba a rayuwarmu ta zahiri. [144]

#: Online, the loudest, flashiest self-promoters grab the attention, [145] <> A intanet, wadanda su ka fi zake wa su suka fi jan hankali [146]

#: not necessarily the most accomplished. [147] <> ba wadanda su ka fi kwarewa ba. [148]

#: This approach fragments our identity, say the experts. [149] <> Hakan ya na raba mana hankali, in ji kwararru. [150]

#: We increase the posts that portray us in the image we like to be seen [151] <> Muna kara wallafa bayanan da suka dace da yadda muke son a kalle mu, [152]

#: and decrease the posts that show how wed rather not be perceived. [153] <> sannan mu na rage wallafa bayanan da ba su dace da yadda mu ke son a kalle mu ba. [154]

#: But to be sure, social media has given more than its taken away in the last decade. [155] <> Sai dai, hakikanin gaskiya, shafukan sada zumunta sun bamu damammaki fiye da wadanda suka karbe mana. [156]

#: There is no evidence that social media decreases the quality of our relationships, [157] <> “Babu wata hujja cewa shafukan sada zumunta na rage mana ingancin alakarmu, [158]

#: makes us withdraw, or diminishes our ability to relate and be in the moment,” [159] <> ko sa mu janye jiki, ko kuma su rage mana ikon muamala da abokan huldarmu, [160]

#: says Pamela Rutledge, director of the Media Psychology Research Centre in California. [161] <> in ji Pamela Rutledge, daraktar cibiyar bincike kan halayyar masu amfani da kafafen yada labarai, wacce ta ke California. [162]

#: The key is always balance and monitoring [163] <> Sirrin dai shi ne kullum mu rika laakari da abinda mu ke rubutawa don ganin [164]

#: whether any behaviour is adding to or taking away from your own goals and experience, she says. [165] <> ko ya dace da burin da muka sa a gaba ko kuma bai dace ba. [166]