bbchausa verticals/021 job advice

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search


Contents

#: Cant find a job Try this simple advice [1] <> Ka kasa samun aiki? To ga shawara [2]

#: There's a lot you can do to boost your chances of landing your dream job. [3] <> Akwai abubuwa da yawa da za ka yi wadanda za su fadada damarka ta samun aikin da kake cike da burin yi. Amma kuma mutane da yawa ba kasafai suke jarraba abubuwan ba. [4]

#: University graduation has come and gone [5] <> Karutan jami'a ya zo ya tafi, [6]

#: and despite all the talk of it being the hottest job market in years for new graduates, [7] <> kuma duk irin roman-bakan da ke tattare da shi na zama wata muhimmiyar hanyar samun aiki ga sabbin wadanda suka kammala jami'a, [8]

#: you're still on the sidelines. Still, nothing. [9] <> har yanzu kana gefe guda, aikin bai samu ba. [10]

#: You've sent out dozens of CVs and submitted countless applications. [11] <> Ka aika da takardar neman aiki sau shurin-masaki. [12]

#: Still, nothing. [13] <> Amma har yanzu shiru kake ji, kamar ka shuka dusa. [14]

#: Panic sets in. [15] <> Daga nan hankalinka ya fara tashi. [16]

#: You start to think all that study was for nothing. [17] <> Ka fara tunanin cewa duk wannan shekaru da ka kwashe kana karatu, abin ya tafi a banza? [18]

#: With little real experience on your resume, what can you do to increase your odds of landing your dream position and to make yourself more attractive to employers? [19] <> Ka duba ka gani idan za ka iya kokari ka samu wani horo ko 'yar kwarewa ta aiki da za ka kara a takardarka, wannan zai iya kara ba ka damar samun aikin da kake fata, domin zai sa masu daukar aiki su ga cewa ka dace. [20]

#: Treat it like a job [21] <> Ka dauka kamar kana da aiki. [22]

#: The best advice is simple, [23] <> 'Shawarar da ta fi kyau mai sauki ce, [24]

#: but job seekers rarely follow it,” said Ginger Porter, [25] <> amma masu fafutukar neman aiki ba kasafai suke binta ba, in ji Ginger Porter, [26]

#: managing director of the Dallas and Atlanta offices at global communications firm Golin, in an email. [27] <> manajar darektar ofisoshin Dallas da Atalanta na kamfanin sadarwa na Golin. [28]

#: Start every day like it's your work day.” [29] <> Ta kara da cewa, Ka soma kowace rana kamar ranar aikinka ce. [30]

#: Dont lounge around in your PJs all day while binge-watching your favourite shows. [31] <> Kada ka je ka zauna a daki kana ta kallon finafinai duk tsawon rana. [32]

#: Get dressed in the morning with the idea that you have somewhere you need to be: looking for a job. [33] <> Ka yi wanka ka sa kayanka masu kyau kamar daman kana da inda za ka je: neman aiki. [34]

#: Porter suggests writing a list of every person you know, [35] <> Shawarar Porter ita ce, ka rubata jerin sunan duk mutumin da ka sani, [36]

#: or can think of in your chosen field. [37] <> ko kake iya tunawa a fannin aikin da kake so. [38]

#: These should be people you can approach who might be able to help with your job search. [39] <> Mutanen su kasance wadanda za su iya taimakawa ne game da bukatarka ta neman aiki. [40]

#: Ask each one of them for short coffee dates, or even a brief phone chat or email response. [41] <> Ka nemi kowannensu damar wani dan zama da shi (na shan gahawa), ko 'yar tattaunawa ta waya ko ta wasikae email. [42]

#: Dont ask for a job. [43] <> Kada ka tambaye shi aiki. [44]

#: Talk to each of them about what you're looking for, [45] <> 'Ka gaya wa kowanne daga cikinsu abin da kake nema, [46]

#: and be specific: [47] <> kuma ka fayyace musu ainahin abin da kake son, [48]

#: I'm looking for a position with this kind of employer where I can use my skills in XYZ. [49] <> misali ina neman matsayi kaza a ma'aikata iri kaza, inda zan yi amfani da kwarewata a fanni kaza da kaza. [50]

#: Do you have any advice for me?’” said Porter. [51] <> Akwai wata shawara da za ka iya ba ni? In ji Porter, [52]

#: People will make the time to give advice, [53] <> ta kara da cewa, ta haka mutane za su ba ka shawara, [54]

#: and its better than booking their time to ask for a job.” [55] <> kuma yin hakan ya fi a ce kana neman ganawa da su domin ka nemi aiki a wurinsu. [56]

#: If you're meeting in person, [57] <> Idan za ka yi ganawa ta keke-da-keke ne da mutumin, [58]

#: present yourself professionally[59] <> to ka gabatar da kanka yadda ya kamata wato kamar ma'aikaci, [60]

#: after all, you're asking for help and possibly a personal referral. [61] <> domin kana neman taimako ne, kuma kila ma ya tura ka wurin da za a dauke ka aikin. [62]

#: Arrive prepared with examples of how youve successfully used your skills in the past, [63] <> Ka je a shirye, da misalan yadda ka yi amfani da kwarewar da kake da ita a baya, [64]

#: whether it was for a school project or an internship. [65] <> walau a rubutun da ka yi na kammala digirinka ne ko a wurin sanin makamar aiki ne. [66]

#: Your aim is to impress. [67] <> Manufarka a nan ita ce ka burge shi, ka nuna ka cancanta. [68]

#: Before you leave, [69] <> Kafin ka tafi daga wurinsa, [70]

#: ask the person if there is anyone to whom they might be able introduce you. [71] <> ka tambaye shi ko akwai wurin wanda zai iya hada ka da shi. [72]

#: Follow the same process with those people. [73] <> Ka yi haka da dukkanin sauran mutanen. [74]

#: It's an exponential effect,” said Porter. [75] <> Porter ta ce, wannan mataki ne da zai iya daukar ka lokaci mai tsawo, [76]

#: You could potentially talk to 100 people this way, [77] <> domin karshenta za ka kai ga magana da mutane 100 ta wannan hanya, [78]

#: and I guarantee that out of that group of people, [79] <> kuma ina tabbatar maka cewa daga cikin mutanen [80]

#: someone has the perfect job that fits your skills.” [81] <> akwai wanda yake da aikin da ya dace da kwarewarka. [82]

#: Outside your comfort zone [83] <> Aikin da ba shi kake bukata ba [84]

#: If you are getting interviews [85] <> Idan ana gayyatarka ganawar daukar aiki, [86]

#: but they are outside the field you studied [87] <> amma kuma ba aikin da kake da kwarewa a kai ba ne, [88]

#: and not really of any interest to you, [89] <> kuma ba wanda kake sha'awa ba ne, [90]

#: take time to gain more work experience in your field, [91] <> to ka yi kokarin samun karin kwarewa a fanninka, [92]

#: according to Prague-based Oliver Donoghue, managing director of the Nonstop Recruitment Schweiz AG talent agency. [93] <> in ji manajan darektan kamfanin daukar ma'aikata na Nonstop Recruitment Schweiz AG, wanda ke Prague, Oliver Donoghue. [94]

#: And that may mean taking a position slightly different than you hoped for. [95] <> Ka ga wannan na nufin kenan kila ka samu matsayin da ma ya dandara wanda kake sa rai. [96]

#: It doesnt have to be anything game-changing. [97] <> "Ba wai sai horon ya kasance wani babba ba. [98]

#: Even a brief stint at a relevant organisation [99] <> Ko da na dan lokaci ne a wurin aikin da ya dace da abin da ka karanta, [100]

#: will be enough to show employers that youre serious about your career [101] <> domin zai nuna wa masu daukar aiki cewa lallai ka ba aikinka muhimmanci, [102]

#: and want to gain some professional experience,” he said. [103] <> kuma kana da burin samun kwarewa, ya ce. [104]

#: Presenting yourself on paper [105] <> Gabatar da kanka a takarda [106]

#: If you did any internships while in school [107] <> Idan har ka yi wani zama na sanin makamar aiki a wani wuri a lokacin da kake makaranta, [108]

#: that were related to your field of interest, dont just list them. [109] <> wanda yake da nasaba da fannin da ka karanta, kada ka rubuta shi kawai, [110]

#: Instead, showcase them through a portfolio of the work you did while at the job, [111] <> ka yi bayani a kan shi da kyau, ta hanyar irin aikin da ka yi, a lokacin da kake wurin aikin, [112]

#: suggested Payal Vasudeva, a managing director in Accentures Strategy division in the London office. [113] <> in ji Payal Vasudeva, manajar darektar a ofishin kamfanin Accenture Strategy da ke Landan. [114]

#: Being able to demonstrate specific job skills, [115] <> Ta ce, "nuna irin kwarewar da ka samu a wata ma'aikata ko wurin aiki, [116]

#: whether through an internship, [117] <> walau ta hanyar neman sanin makamar aiki ne, [118]

#: volunteer work or extracurricular activities, [119] <> ko ta hanyar aikin sa-kai da makamantansu, [120]

#: increases your chances of landing that job,” she said in an email. [121] <> hakan na kara maka damar samun aiki. [122]

#: If you need to improve your CV, [123] <> Idan kana bukatar kara darajar takardar bayanin karatunka da kwarewa (CV), [124]

#: consider volunteering or taking vocational courses [125] <> to ka duba yadda za ka yi wani kwas na samun horon koyon aikin hannu [126]

#: that boost your skill set to match the demands of the jobs youre applying for. [127] <> wanda hakan zai kara maka kwarewa a fannin karatun da ka yi, kuma samunn wannan karin kwarewa wata dama ce a gare ka ta samun aiki, kamar yadda [128]

#: Employers will be looking for any signs [129] <> Masu daukar mutane aiki za su rika duba wata alama ce [130]

#: that youve gone above and beyond the call of duty to improve your skill set, and gaining additional experience can make a world of difference,” said Donoghue. [131] <> da za ta nuna cewa ka dora a kan iya abin da ka nazarta a makaranta kamar yadda Donoghue ta ce. [132]

#: Theres a simple way to do this: [133] <> Akwai hanya mai sauki ta yin haka: [134]

#: take training courses in digital and productivity tools, [135] <> ka yi kwas a fannin fasahar zamani [136]

#: even if you arent going into a digital field. [137] <> ko da kuwa ba a fannin fasahar zamanin za ka yi aiki ba. [138]

#: These tools are crucial now and into the future [139] <> Wannan ilimi na da muhimmanci a zamanin yau da kuma gaba, [140]

#: and therefore essential to master, [141] <> saboda haka yana da muhimmanci ka lakance wannan ilimi, [142]

#: according to Austin, Texas-based Sharon Schweitzer, an etiquette and cross-cultural consultant. [143] <> kamar yadda Sharon Schweitzer kwararre a harkar daukar aiki a Texas da ke Amurka ya ce. [144]

#: We understand you know how to use Pokémon Go, [145] <> Schweitzer, ya ce, mun fahimci cewa ka san yadda za ka yi amfani da Pokémon Go, [146]

#: but employers want to know if you have social media skills in other areas, [147] <> amma masu daukar ma'aikata na son sanin ko kana da kwarewa a kan wasu shafukan sada zumunta da muhawara na intanet, [148]

#: such as Instagram, Tumblr, YouTube, and Twitter,” said Schweitzer. [149] <> kamar su Instagram da Tumblr da YouTube, da kuma Twitter. [150]

#: Polish your technical skills.” [151] <> Ka bunkasa kwarewarka. [152]

#: Once youve done so, show them off when it comes to your own online presence. [153] <> To da zarar ka yi wannan, ka nuna kwarewarka idan dama ta samu. [154]

#: You are the digital natives [155] <> 'Kana cikin 'yan zamani [156]

#: who turn to smartphones and social media for everything, [157] <> wadanda suke amfani da wayar komai-da-ruwanka da shafukan sada zumunta da muhawara wajen yin kusan komai, [158]

#: from talking to friends to shopping,” said Accentures Vasudeva. [159] <> daga magana da abokai zuwa siyayya, in ji Vasudeva. [160]

#: As you enter this next chapter of your life in the professional world, [161] <> "Yayin da ka kai wannan matsayi a fannin aikinka, [162]

#: check out job listings on career board apps. [163] <> to ka rika duba jerin ayyukan da ake neman ma'aikata ta hanyar manhajojin tallata ayyuka. [164]

#: Use LinkedIn and other social channels to network [165] <> Ka rika amfani da shafin Likedln da sauran shafukan sada zumunta na intanet, [166]

#: and show off your expertise and industry knowledge.” [167] <> kuma ka nuna kwarewarka ta wannan fanni da kuma ta sanin aiki. [168]

#: Lots of skills, little experience [169] <> Kana da tarin ilimi amma ba ka da kwarewa mai yawa ta taba yin aiki [170]

#: If you dont have any real work experience, consider switching to a skills-based CV, [171] <> Idan ba ka taba yin aiki ba a wata ma'aikata , to ka yi kokari ka koma fannin da za ka samu kwarewa ta hannu, [172]

#: suggested UK-based Sally Walker, [173] <> kamar yadda Sally Walker ta shawarta, [174]

#: an international career coach with SW Career Coaching, in an email. [175] <> kwararriya a fannin horar da ma'aikata ta kasa da kasa da ke Landan. [176]

#: Use the first page to lay out up to five transferable job skill headings [177] <> Ka yi amfani da shafin farko, ka jera tare da bayar da bayyana fannoni zuwa biyar da ka samu horo na zahiri a cikinsu, [178]

#: relevant to the role for which you are applying. [179] <> wadanda duk suna da alaka da aikin da kake nema. [180]

#: Under these headings, create bullet-pointed achievement statements which provide evidence of the skill. [181] <> Ka fito da irin nasarorin da ka samu da wanna ilimi. [182]

#: If you are still coming up empty, consider careers on thefringeof your area of study [183] <> Idan har yanzu kana ganin ba ka koshi ba, to ka yi kokarin samun kwarewa a fannonin bangaren da ka yi karatu. [184]

#: Try to include the key action that you took [185] <> 'Ka sanya muhimman abubuwan da ka yi [186]

#: as well as quantifying the results wherever possible,” said Walker. [187] <> da kuma nuna irin nasarar da ka samu in har za ka iya nuna hakan, in ji Walker. [188]

#: For example, underOrganisation and Planning,” you could include organising a charity event during university. [189] <> Misali za ka iya nuna irin aikin agajin da ka shirya a lokacin da kake jami'a. [190]

#: Describe it in a way that highlights your achievements. [191] <> Ka nuna yadda za ta fito da cigaba da ka samu karara. [192]

#: Networking never out of style [193] <> Ka kulla dangantaka ta zamani [194]

#: Networking is still a great way to get on the radar of potential employers, said Donoghue. [195] <> Kulla alaka da mutane da yawa har yanzu muhimmiyar hanya ce ta yadda masu neman ma'aikata za su same ka in ji Donoghue. [196]

#: But if you dont have the timeor inclinationto attend in-person events, [197] <> Amma idan ba ka da lokacin da za ka halarci taron da kanka, [198]

#: it can also be done online through platforms such as LinkedIn and Xing. [199] <> za ka iya aiwatar da shi ta hanyar intanet kamar ta LinkedIn da Xing. [200]

#: Make sure your profile is up to scratch before looking to engage with firms and hiring managers [201] <> Ka tabbatar komai na bayaninka ka sabunta shi kafin ka fara kokarin kulla alaka da kamfanoni ko manajoji. [202]

#: But, be warned that there is no substitute for meeting someone face-to-face [203] <> Amma fa ka kwana sanin cewa babu wata hanya da tafi ta ganawa da mutum gaba da gaba, [204]

#: and you'll have to get out there at some point. [205] <> kuma dole ne a wani lokaci ka je ka samu mutum da kanka in ji Donoghue. [206]

#: Make sure your profile is up to scratch before looking to engage with firms and hiring managers and that it covers your full job history and any additional experience or skills that you may have gained,” said Donoghue. [207] <> 'Ba lalle ba ne damar aikin da za ta zo maka a ce ta shafi abin da ka karanta kai tsaye, kuma wani lokaci dole sai ka karkata zuwa wani fannin daban da na karatunka, kafin ka cigaba a fannin aikin naka, in ji shi. [208]