bbchausa verticals/028 olympians struggle

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Many Olympians struggle just to make ends meet [1] <> Mafi yawan 'yan wasannin Olympic talakawa ne [2]

#: All Olympic athletes all have lucrative sponsorship deals, right? [3] <> kana zaton cewa duka 'yan wasannin Olympics attajirai ne? [4]

#: Wrong. Many have to take side jobs just to get by. [5] <> Sam ba haka ba ne. Da daman su suna neman ayyukan da za su riƙe kan su. [6]

#: When Serena Williams takes to the court at the Rio Olympics this month, [7] <> Yayin da Serena Williams ta shiga filin wasannin Olympics a birnin Rio a watannan, tauraruwar ta wasan tennis [8]

#: the US tennis star wont really be alone. [9] <> 'yar Amurka ba ita kadai ta shiga fili ba. [10]

#: She will have arrived at the Games with an entourage of paid staffers, [11] <> Ta je wasannin ne da tawagar ma'aikata da ta ke biya albashi, [12]

#: coaches [13] <> da masu horar da ita, [14]

#: and sponsors whove helped her every step of the way. [15] <> da masu ɗaukar nauyin ta, wadan da suke taimaka mata a duk motsin da ta yi. [16]

#: Worth an estimated $150m in 2016 [17] <> 'Yar wasar wacce ta ke da kudin da ya kai dala miliyan 150, [18]

#: (more than any other female athlete, according to Forbes), [19] <> (hakan ya sa ta zarce duk wata 'yar wasa kudi a duniya) [20]

#: Williams trains upwards of 30 hours per week, [21] <> ta na yin atisaye na sa'a talatin a kowane mako, [22]

#: but has never had to work a second job to get by and pay her way in sport. [23] <> to amma fa banda wannan ba ta da wani aiki da take dan neman albashi. [24]

#: Shes one of a small minority of Olympians. [25] <> Irin su dai ba su da yawa a cikin 'yan wasannin Olymipcs. [26]

#: More likely, walking through the athletes village in Rio, [27] <> Idan kana yawo a birnin Rio da ake wasannin Olympics, [28]

#: youd find people like Canadian Donna Vakalis. [29] <> wataƙila ka yi kiciɓis da mutane irin su Donna Vakalis 'yar ƙasar Canada. [30]

#: To compete in the modern pentathlon, she trains a minimum of 30 hours per week in fencing, [31] <> Tana yin atisaye na sa'o'i 30 a kowane mako dan fafatwa a wasan shallaken sanda a kan dawaki, da wasan lanƙwaya, [32]

#: shooting, [33] <> da wasan jifa, [34]

#: swimming, [35] <> da nunƙaya, [36]

#: horse riding [37] <> da tseren dawaki, [38]

#: and cross-country running. [39] <> da kuma gudun yada ƙanin wani. [40]

#: And when shes not training, [41] <> A duk lokacin da ba ta atisaye kuwa [42]

#: the 36-year-old is pursuing a PhD [43] <> yar wasan mai shekaru 36 tana ci gaba da ƙoƙarin samun digiri na uku ne [44]

#: in civil engineering [45] <> a ɓangaren fasahar gine-gine [46]

#: at the University of Toronto [47] <> a jami'ar Toronto, [48]

#: and juggling a handful of jobs just to support her Olympic dreams. [49] <> sannan kuma ta na wasu 'yan aikace-aikace dan samun kuɗin da za ta cimma burinta na wasannin Olympics. [50]

#: Vakalis estimates that it costs about CAD$50,000 ($39,000) a year [51] <> Vakalis ta ƙiyasta cewa tana buƙatar kuɗin Canada dala dubu hamsin ($39,000 US) a shekara [52]

#: to train and compete in the modern pentathlon. [53] <> don yin atisayen wasan shallaken sanda a kan dawaki na zamani, [54]

#: there is a major funding gap between what she receives in government supportCAD$4,500 ($3,450) last yearand what she needs to get by. [55] <> domin abinda ta ke samu daga gwamnati bai wuce dala dubu hudu da ɗari biyar ba a kudin Canada ($3,450 US). [56]

#: We pay the coaches ourselves, [57] <> "Da kanmu mu ke biyan masu horar da mu, [58]

#: we pay for the athletic centre access ourselves, [59] <> mu mu ke biyan kudin cibiyar wasannin da kan mu, [60]

#: we pay for the physio [61] <> mu ke biyan masu kula da lafiyar mu, [62]

#: and the massage ourselves, [63] <> da masu yi mana tausa, [64]

#: and that means that there is a higher financial burden,” she says. [65] <> hakan na nufin akwai nauyi sosai a kan mu". A cewar ta. [66]

#: This has left Vakalis scrambling to scrape together funds [67] <> Hakan dai ya sa Vakalis ta ke ta fafutukar neman kuɗi [68]

#: through part-time work as a teachers assistant, [69] <> ta hanyar koyarwa ta ɗan wani lokaci, [70]

#: research assistant, [71] <> da taimakawa masu bincike, [72]

#: motivational speaker [73] <> da kalaman ƙarfafa gwiwa, [74]

#: and producer for a university YouTube channel. [75] <> da kuma kula da shafin YouTube na wata jami'a. [76]

#: She also applies for athlete grantswhich can be up to CAD$6,000 ($4,620) – [77] <> Ta na kuma neman tallafi na kuɗin da aka ware wa wasannin Olympics [78]

#: and puts together creative crowdfunding campaigns, like an onlineathlete registry[79] <> da ma kuma sauran hanyoyi na samu kuɗi daban-daban ciki kuwa har da amfani da shafukan Internet, [80]

#: where supporters can buy gear for her the way one might help a newlywed purchase housewares. [81] <> inda ta ke sayar wa magoya bayanta kayayyaki domin taimaka mata. [82]

#: Vakalis is hardly alone in her financial predicament. [83] <> Ba wai Vakalis ce kaɗai ke cikin irin wannan mawuyacin halin ba, [84]

#: A recent report [85] <> wani rahoto na baya-bayannan [86]

#: found that elite Canadian athletes [87] <> ya gano cewa 'yan wasannin Olympics na Canada [88]

#: have annual expenses that are CAD$14,920 ($11,395) [89] <> na kashe kimanin dala 14,920 ta Canada, [90]

#: more than they earn from their sport through federal and provencial funding, [91] <> sama da abin da su ke samu daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin shiyya. [92]

#: with 20% of athletes indebted an average of CAD$40,000. [93] <> Kuma kashi 20 daga cikin su na fama da bashin da ya kai dala 40,000 na kuɗin Canada. [94]

#: Athlete families in the US have, in the past, [95] <> A baya, iyalan 'yan wasan Olympics a Amurka [96]

#: filed for bankruptcy protection when debts from [97] <> sun nemi gwamnati ta kai musu ɗauki kan mummunan talaucin da su ke fama da shi, [98]

#: training, [99] <> da bashin kuɗaɗen horarwa, [100]

#: travel and other costs have gone sky high. [101] <> da tafiye tafiye. [102]

#: There are more than 100 Olympic hopefuls from Mexico to Libya with current campaigns on crowdfunding website GoFundMe. [103] <> Akwai 'yan wasannin Olympics sama da su 100 a ƙasashen duniya da dama da suke neman tallafi daga jama'a ta shafin internet na GoFoundMe. [104]

#: And a surprising number of Olympic-bound competitors trained for Rio [105] <> Haka kuma akwai 'yan wasannin Olympic da su ka yi atisaye domin wasannin Rio, [106]

#: while simultaneously balancing non-athletic careers. [107] <> yayin da a ɓangare ɗaya kuma su ke ci gaba da wasu harkokin na neman kudi. [108]

#: These Olympians may leave Rio in a few weeks as temporary global celebrities, [109] <> Yan wasan dai za su bar birnin Rio nan da 'yan kwanaki a matsayin gwaraza na duniya, amma fa na ɗan wani lokaci. [110]

#: but many of them enter the Games as ordinary people riddled with extraordinary debts. [111] <> To amma da daman su sun shiga wasan ne a matsayin mutane gama gari da bashi ya yi wa kanta. [112]

#: Australian swimmer Matthew Abood was 0.02 seconds short of qualifying for the London Olympics in 2012. [113] <> Ƙasa da daƙiƙa ɗaya ta ragewa ɗan wasan kurmanu na ƙasar Australia Mattew Abood ya samu cancantar shiga wasannin Olympics cikin 2012 a birnin London. [114]

#: Not only did the promising athlete miss out on his dream, [115] <> Ba wai gaza shiga gasar kawai ɗan wasan ya yi ba, [116]

#: but he suddenly found himself with zero funding from the Australian government. [117] <> ya ma rasa samun tallafi daga gwamnatin Australia. [118]

#: I remember asking myself: [119] <> "Na tuna tambayoyin da na ringa yi wa kaina, [120]

#: What am I doing? [121] <> Me ya kamata in yi? [122]

#: I dont have a job [123] <> Ba ni da aiki, [124]

#: Im not studying. [125] <> kuma ba karatu na ke ba, [126]

#: I dont have any work experience’,” Abood recalls. [127] <> ni ba wani aiki na iya ba" In ji Aboot. [128]

#: So he approached Australias Commonwealth Bank witha four-year plan[129] <> Ya tunkari baban bankin Australia da wani tsari da ya yi na shekara hudu, [130]

#: to not only bounce back and make it to Rio [131] <> ba wai dan cimma burin sa na shiga wasanni a Rio ba kawai, [132]

#: but also build a career that could support his training. [133] <> har ma domin ya samu wata sana'a da zai dogara da ita. [134]

#: Abood has worked about two days per week for the past four years as a business development analyst for Commonwealth Bank. [135] <> Abood ya na aikin kwanaki biyu a mako a matsayin masani kan bunƙasa kasuwanci ga babban bankin na Australia tsawon shekaru huɗu. [136]

#: He says the steady income helped fund a training regimen that has propelled the 30-year-old to Rio, [137] <> Ya ce kuɗin da ya ke samu ya taimaka masa wajen samun horon da ya bashi damar shiga wasan kurmanu a Rio, [138]

#: Big dreams, harsh realities [139] <> buri ne dai da ya daɗe yana son cimmawa, sai dai ya cika burin sa da gumin goshi. [140]

#: Unlike athletes in most other countries, [141] <> Ba kamar 'yan wasan Olympics na sauran kasashe ba, [142]

#: US Olympians receive no direct support from the federal government. [143] <> yan wasan Olympics na Amurka ba sa samun tallafin kuɗi kai tsaye daga gwamnati. [144]

#: Instead, they must rely on indirect support from the privately funded governing boards of their respective sports. [145] <> Hakan ya sa sai dai su dogara kan tallafi daga hukumomin gudanarwar wasannin su daban-daban. [146]

#: The US Athletic Trust, a donor-matching agency [147] <> Asusun tallafawa 'yan wasannin motsa jiki na Amurka [148]

#: estimates that individual out-of-pocket costs for coaching, equipment and transportation to worldwide events [149] <> ya ce idan mutum yana so ya ɗauki nauyin kan sa zuwa wasannin Olympics, [150]

#: can cost US Olympians between $12,000 and $120,000 per year, depending on the sport. [151] <> zai iya kashe dala dubu 12 zuwa dala dubu 120 a shekara, domin horarwa, da kudin sufuri, da sayen kayayyaki. [152]

#: Yet, it calculates that just 10% of the total expenses of the US Olympic Committee (USOC) are in direct support of US athletes. [153] <> A Amurka ana neman talafin kudi dan 'yan wasannin Olympics, wanda wata hukuma ta ke kula da su. [154]

#: The money hasnt trickled down to the athletes [155] <> "Ba wai 'yan wasan na Olympics ake bawa kuɗaɗen ba [156]

#: to the extent it should so they can feed themselves, [157] <> har tsawon rayuwar su, domin su ci abinci, [158]

#: have a car, [159] <> su sayi motoci, [160]

#: and not live month to month,” [161] <> sannan su ci gaba gudanar da rayuwar su" [162]

#: says Augie Wolf, a former Olympic shot-putter and founder of the US Athletic Trust. [163] <> A cewar Augie Wolf, wani tsohon ɗan wasannin Olympics na Amurka, wanda kuma ya kafa asusun tallafawa 'yan wasannin na Olympics. [164]

#: Wolf says a lot of elite Olympic athletes in the US are merely in survival mode, [165] <> Ya ce mafi yawan 'yan wasan a Amurka suna rayuwa ne cikin ƙunci, [166]

#: begging and borrowing money [167] <> suna bara, suna rancen kudi, [168]

#: or relying on the philanthropy of others. [169] <> ko kuma su dogara kan kuɗin jin ƙai da wasu ke samarwa. [170]

#: Many of these guys are cobbling together a life, [171] <> Wolf ya ce "Mafi yawan 'yan wasan suna rayuwar taimake ni-in taimake ka ne, [172]

#: living with three other athletes in a two-bedroom apartment,” he says. [173] <> za ka ga mutum uku na zaune a gida mai ɗaki biyu". [174]

#: Those who dont make enough money from their athletic career to survive [175] <> Wanɗanda suka gaza samun isasshen kuɗin da zai ishe su gudanar da al'amuran yau da kullum, [176]

#: typically find flexible work that will allow for odd training hours and frequent travel to competitions. [177] <> suna neman wasu ayyukan da za su iya basu damar yin atisaye a wasu lokutan daban. [178]

#: Other US Olympians have trained while working at places like McDonalds, [179] <> Wasu 'yan wasan na Olympics kuwa suna yin atisaye ne a lokacin da suke aiki a wurare kamar su McDonalds, [180]

#: selling real estate [181] <> da dillancin gidaje, [182]

#: or serving in the US Army. [183] <> da kuma aikin soja. [184]

#: The golden opportunity [185] <> Muhimmiyar Dama. [186]

#: Though many first-time Olympic athletes have a rough time sustaining themselves while qualifying for the Games, [187] <> Duk da ya ke waɗanda suka shiga wasannin Olympics karon farko suna matuƙar shan wahala, [188]

#: things have actually improved in recent decades, [189] <> a 'yan shekarun nan abubuwa na inganta, [190]

#: says sports historian Mark Dyreson, a professor of kinesiology at Pennsylvania State University in the US. [191] <> a cewar masanin tarihin wasanni Mark Dyreson, kuma farfesa a jami'ar Pennsylvania ta Amurka. [192]

#: Now you have multimillionaire Olympic athletes like Jamaican sprinter Usain Bolt and US swimmer Michael Phelpsthe latter with a net worth in excess of $55 million [193] <> A yanzu kana da 'yan wasannin Olympics kamar ɗan tsere Usani Bolt na Jamaica, da kuma ɗan Kurmanu Michael Phelps na Amurka na samun miliyon kudade daga ɗaukar nauyin sa da ake yi da kuma tallace tallace. [194]

#: For young athletes, [195] <> Ga matasa masu shiga wasannin Olympics, [196]

#: just getting to the Olympics[197] <> samun damar zuwa gasar ma kawai na iya sa wasu su dauki nauyin ka, [198]

#: not to mention landing on a podium to secure a sponsorship deal[199] <> ba ma a ma ganar ke shiga fili. [200]

#: is a daunting ordeal. [201] <> Hakan dai wata babar dama ce. [202]

#: Not only is it a years-long personal and financial commitment, [203] <> To amma fa gwaji ne kawa za a yi ko za a dace. [204]

#: but its a risky investment with no guaranteed return. [205] <> Domin tamkar kasada ce, kuma ba ka da tabashin cewa haƙarka za ta cimma ruwa. [206]

#: The opportunity to make money for many first-time Olympic athletes wont come until after the Games are over. [207] <> Kuɗi ba ya samuwa ga 'yan wasannin Olympic, sai bayan an kammala wasannin. [208]

#: This is the time when they can capitalise on their new-found fame with lucrative sponsorship opportunities and a speakers circuit ripe for tales of Olympic glory. [209] <> Wannan ne lokacin da suke bibiyar mutanen da suka ƙulla wata magana da su, dan ɗaukar nauyi da kuma bada labaran irin muhimmiyar rawar da suka taka a lokacin wasannin na Olympic. [210]