bbchausa verticals/032 one food

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Could you survive on just one food [1] <> Za ka iya rayuwa da abinci daya kawai? [2]

#: Were constantly told about the benefits of a varied diet. [3] <> A ko da yaushe ana gaya mana muhimmancin cin abinci mai gina jiki (wanda ya kunshi sinadarai daban-daban). [4]

#: But what if you had to survive on just one foodwhat would you keep you alive the longest? [5] <> To amma ya za ka yi idan ka samu kanka a yanayin da abinci iri daya kawai kake iya samu - Me za ka yi da zai sa ka dade a duniya. [6]

#: Man cannot live on bread alone[7] <> Mutum ba zai iya rayuwa ba da biredi kadai, [8]

#: not least because man would develop scurvy about a month or so into that little experiment. [9] <> domin idan ya kasance biredi kawai yake ci, yayin da ya kai kusa da wata daya sama da haka a wannan hali, zai fara samun larurar ciwon gabbai da yankwanewa. [10]

#: The best diets have plenty of variety in them, making sure you get everything from vitamin C to iron to linoleic acid without even having to think. [11] <> Abinci mai kyau yana dauke da sinadaran da jiki ke bukata daban-daban kuma wadatattu. [12]

#: Even fad diets that focus on just a few foods [13] <> Hatta nau'in abinci na musamman da masu bukatar rage kiba suke ci, [14]

#: or on eliminating certain things [15] <> wanda ake cire wasu sinadaran a cikinsa, [16]

#: are usually varied enough to be reasonably nutritious. [17] <> yana dauke da wadatattun sinadaran da jiki ke bukata. [18]

#: Still, [19] <> Duk da haka, [20]

#: in the extremely unlikely scenario [21] <> idan abu ya yi kamari, [22]

#: that you had to live on just one food, [23] <> mutum ya samu kansa a yanayin da abinci daya kawai yake iya samu, [24]

#: are some nutritionally more complete than others? [25] <> to za a iya cewa wani abin cin ya fi wani nau'in kayan gina jiki? [26]

#: Could you get what you need from, say, just potatoes, or just bananas, or just avocados? [27] <> Misali, za ka iya samun dukkanin sinadaran da jikinka ke bukata daga dankali ko ayaba ko wani abu daya? [28]

#: One thing is for sure, the candidates would not include meat or most fruits and vegetables. [29] <> Idan za a yi wannan misali ko gwaji na rayuwa da cin abu daya kawai, ba za a yi maganar nama ko yawanci 'ya'yn itace ko kayan lambu ba, [30]

#: Meat doesn't have fibre, nor does it have key vitamins and nutrients. [31] <> domin nama ba shi da muhimman sinadaran gina jiki irin su bitamin (vitamin), [32]

#: Fruits and vegetables may have vitamins, but they don't have anywhere close to enough fat [33] <> yayin da su kuma 'yayan itace da kayan lambu, ba su da isasshen sinadarin maiko (fat) [34]

#: or protein, [35] <> da kuma mai gina jiki (protein), [36]

#: even eaten in quantity. [37] <> ko da kuwa ka ci su ne da yawa, ba za ka samu isassun wadannan sinadarai ba. [38]

#: The body does not need as much as you might think [39] <> Jiki ba ya bukatar wadannan sinadarai masu yawa kamar yadda kai kake tsammani, [40]

#: to stay alive, [41] <> kafin ya zauna lafiya , ko ya ra yu, [42]

#: but you omit them at your peril. [43] <> amma kuma kana zubr da su a rashin sanin muhimmancinsu. [44]

#: Arctic explorer Vilhjalmur Stefansson [45] <> Mai bincike a kan yankin Tekun Akatik (arctic), Vilhjalmur Stefansson, [46]

#: wrote about a phenomenon among the peoples of northern Canada called rabbit starvation, [47] <> ya yi rubutu a kan wani rashin lafiya da mutanen yankin arewacin Canada suke fama da shi (rabbit starvation), [48]

#: in which those who eat only very lean meat, [49] <> inda mutanen da ke cin 'yan kananan dabbobi kawai, [50]

#: such as rabbit, [51] <> kamar zomo, [52]

#: develop diarrhea in about a week, [53] <> suke kamuwa da wata cuta kamar ta tamowa ko yunwa, [54]

#: with headache, lassitude, a vague discomfort.” [55] <> wadda almunta sun hada da zawayi da ciwon kai da rashin katabus da mutum ke samun kansa cikin kusan mako daya. [56]

#: To avoid death from malnutrition, [57] <> Domin kare mutumin da ya kamu da wannan cuta daga mutuwa a sakamakonta, [58]

#: rabbit starvation sufferers must consume some fat, he writes. [59] <> dole ne maras lafiyar ya rika cin abin cin da ke dauke da sinadarin da ke samar da maiko ga jiki (fat), in ji Stefansson, kamar yadda ya rubuta. [60]

#: It's thought that getting almost all one's calories from protein, [61] <> Masana na ganin idan mutum ya dogara ga nau'in sinadarin abinci daya kamar na protein, [62]

#: and almost none from fat or carbohydrates, [63] <> wajen sama wa jikinsa karfi ko makamashin da yake bukata, ya yi watsi ko ya bar kayan abincin da ke da sinadarin maiko(fat) ko masu ba wa jiki karfi carbohydrates, [64]

#: may overwhelm the liver's ability to process protein. [65] <> wannan zai iya sa hanta ta kai ga ta rasa karfin sarrafa sinadarin na protein. [66]

#: Still, if meat and most vegetables are off the table, [67] <> Idan kuma ya kasance mutum ya rasa nama da yawancin kayan lambu a abincinsa, [68]

#: somewhat surprisingly, potatoes are not as bad an option as you might think, [69] <> to abin mamaki zai iya amfani da dankali [70]

#: says dietician Jennie Jackson of Glasgow Caledonian University. [71] <> in ji masaniya kan abinci Jennie Jackson, ta Jami'ar Glasgow Caledonian. [72]

#: She wrote last year about Australian Andrew Taylor, who [73] <> A shekarar da ta wuce ne ta yi rubutu a kan Andrew Taylor, wani dan Australia da [74]

#: spent a year eating just potatoes as a well-publicised effort to lose weight and build healthier habits. [75] <> ya yi shekara daya ba shi da wani abinci in ban da dankali, domin ya rage kiba da inganta lafiyarsa. [76]

#: The thing that makes potatoes special is that [77] <> Abin da ya sa dankali ya zama daban a tsakanin sauran kayan abinci shi ne, [78]

#: for a starchy food, [79] <> duk da cewa abin ci ne mai bayar da karfi ga jiki, mai dauke da sinadarin sitaci (starch), [80]

#: they have an unusual amount of protein, [81] <> yana da sinadarin protein mai yawan gaske, [82]

#: and that includes a wide variety of amino acids, says Jackson. [83] <> wanda hakan ya sa yake da wasu sinadaran masu matukar muhimmanci ga jiki, in ji Jackson, [84]

#: But he seems to have gotten through his year relatively unscathed. [85] <> wanda hakan ya sa Jackson ya iya yin shekarar cur da cinsa kadai ba tare da ya gamu da wata matsala ba, [86]

#: But beyond pure nutrition, [87] <> Bayan tasiri ko maganar muhimmancinsa ga gina jiki, [88]

#: there are other barriers to narrowing one's diet to a single food. [89] <> akwai kuma wasu matsalolin da za su iya tasowa ko za su hana dogaro ga abinci daya kawai a rayuwar mutum, [90]

#: Humans have built-in mechanisms to avoid just such a situation [91] <> domin shi jikin dan adam yana da tsari ne da ba a yi shi domin haka ba. [92]

#: The more you eat of one thing, [93] <> Idan aka ce ka saba da cin abinci daya ko a kwana a tashi [94]

#: the less you can stomach it. “I call this the pudding scenario,” says Jackson, [95] <> za a kai ga yanayin da zai gundire ka, za ka kasa cinsa in ji Jackson, [96]

#: where you go out for a meal and you're stuffed, you couldn't manage another bite. [97] <> wanda hakan zai kai ga yanayin da za ka kasa cin abincin. [98]

#: Furthermore, [99] <> Haka kuma [100]

#: the logic that [101] <> maganako dabarar cewa [102]

#: it must be possible to eat a single-item diet rather than a varied one, and suffer no ill effects, [103] <> mutum zai iya rayuwa da abinci daya [104]

#: as long as all the vitamin, mineral, and calorie boxes are checked, doesn't quite work out. [105] <> muddin dai, yana dauke da kusan dukkanin sauran sinadaran da jiki ke bukata, ba tare da ya gamu da wata larura ba, ita ma ba ta tabbata ba. [106]

#: Researchers in the early 20th Century [107] <> Domin masu bincike a farkon karni na 20, [108]

#: deprived rats of certain nutrients [109] <> sun gudanar da gwaji a kan wasu beraye, [110]

#: and kept track of whether they got sick or died. [111] <> inda suka rika basu abincin da ba ya dauke da wasu sinadarai, domin su ga ko berayen za su kamu da wani rashin lafiya ko ma za su mutu. [112]

#: This is how we learned about the existence of vitamins, for instance. [113] <> Ta wannan hanya ne muka ma gano wasu sinadaran, wadanda a da ba mu ma san da su ba. [114]

#: It tells you what rats will die without, [115] <> Sannan wannan zai nuna maka abin da bera ba zai iya rayuwa ba tare da shi ba, [116]

#: at least in the short term. [117] <> akalla na wani gajeren lokaci. [118]

#: However, it's likely that [119] <> Sai dai zai iya kasancewa [120]

#: some of the health benefits of a varied diet[121] <> ba za a iya ganin wasu daga cikin alfanun cin abinci mai dauke da sinadarai daban-daban ba, [122]

#: which play out in the long term[123] <> (wanda ake gani a tsawon lokaci), [124]

#: can't be picked up in reductive experiments like this, says Jackson. [125] <> a irin wannan gwaji in ji Jackson ba [126]

#: (And of course, humans are not rats.) [127] <> (domin ko shakka babu mutane ba beraye ba ne). [128]

#: Epidemiological data on people has made it clear [129] <> Bayanai sun tabbatar cewa [130]

#: that a variety of vegetables in one's diet [131] <> abincin da aka sanya wa kayan lambu da yawa [132]

#: is healthier than just a few, for instance, [133] <> ya fi wanda aka sanya wa kadan amfani, [134]

#: but it isn't exactly clear why. [135] <> amma kuma ba a san dalilin hakan ba. [136]

#: Maybe a diet that includes no green vegetables means that somewhere down the line, [137] <> Watakila abincin da ba ya dauke da kayan lambu irin su alayyahu da sauran ganyaiyaki [138]

#: you'll have a higher chance of developing cancer than you might have otherwise. [139] <> zai iya sa mutum ya gamu da hadarin kamuwa da ciwon daji [140]

#: We don't really know which foods are [141] <> Jackson ta ce, ba mu san abincin da za mu iya cewa [142]

#: causing which effects,” Jackson says. [143] <> shi ne ke haddasawa ko haifar da wannan ko waccan matsala ba. [144]

#: So while you could work out what exactly you needed from macro nutrients, [145] <> 'Saboda haka idan za ka iya gano illa ko sinadarin da za ka rasa idan ba ka ci wani abin ci ba, [146]

#: you won't know exactly what you might be missing.” [147] <> ba lalle ba ne kuma ka san abin da za ka rasa daga garesu ba. In ji masaniyar. [148]

#: Cutting down your daily diet to just one ingredient [149] <> Duk da cewa cin abinci daya a kullum [150]

#: might save time [151] <> zai iya sa ka daina bata lokacinka [152]

#: and hassle, [153] <> da kuma rage maka kai kawo wajen neman kayan abinci, [154]

#: but itd be a quick way to get ill as well as bored. [155] <> to amma kuma fa wata hanya ce ta saurin kamuwa da wata cuta da kuma gajiya da abinci daya. [156]