bbchausa verticals/033 avoiding surveillance

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: How what you wear can help you avoid surveillance [1] <> Ka san yadda za ka iya layar-zana? [2]

#: Designers [3] <> Masu zayyanar tufafi [4]

#: are inventing new ways to stay under the radar, [5] <> sun fara kirkiro sabbin hanyoyin da mutum zai kauce wa yadda za a iya ganinsa, [6]

#: including textile patterns that baffle facial recognition software. [7] <> abin da ya hada da zane-zane a tufafi ta yadda za ka iya yi wa hatta na'urori ko manhajojin gane fuskar mutum baddabami, su kasa gane ka. [8]

#: Bel Jacobs takes a look at stealth fashions. [9] <> Bel Jacobs ya yi mana nazari. [10]

#: Imagine youre living in a dystopian future. [11] <> Ka dauka cewa yau ga shi kana rayuwa a wani lokaci da komai ya baci, inda ake aikata abubuwa na rashin gaskiya da makamantansu. [12]

#: Surveillance cameras [13] <> Ga na'urorin daukar hoto na tsaro [14]

#: scan the streets [15] <> a ko'ina a tituna, [16]

#: to recognise and record the faces of passersby[17] <> suna daukar hotunan mutanen da ke kai-kamo, [18]

#: but youre wearing a HyperFace scarf. [19] <> amma kuma kai kana sanye da wani hirami ko mayafi da ka yafa a fuskarka, [20]

#: Amid a kinetic assortment of grid-like structures printed on the fabric, [21] <> wanda yake da zane na musamman da aka tsara domin batar da kama, ta yadda wannan zane-zane zai susuntar da hatta na'urar daukar hoton tsaro a wuraren. [22]

#: black squares suggest tiny eyes, [23] <> Wannan salo na zane-zane na mayafin yakan batar da kanannan ido [24]

#: noses [25] <> ko hanci [26]

#: and mouths. [27] <> ko bakin mutum, [28]

#: The camerasfacial recognition algorithms are confused. [29] <> wanda ta hakan ta yi bad da kama, [30]

#: Your identity is secure; your privacy, protected. [31] <> ka sirrinta kanka tare da samar da kariya. [32]

#: Unveiled in January, the HyperFace textile print was designed by the Berlin-based artist Adam Harvey [33] <> A watan Janairu na wannan shekara ta 2017 ne mai zayyana Adam Harvey, da ke birnin Berlin na Jamus [34]

#: and Hyphen-Labs, an international, all-female design team [35] <> tare da hadin guiwar dakin bincike na kimiyya na Hyphen-Labs da wasu kwararrun mata masu zayyana ko zane-zanen gyale da mayafi ko gyale [36]

#: formed [37] <> suka hadu [38]

#: to explore meeting points between technology, art and science. [39] <> inda suka kaddamar da irin wadannan kaya masu dauke da fasahar batar da kama. [40]

#: Harvey has formed an anti-surveillance design; [41] <> Harvey ya kirikiro zayyan da tsare-tsare [42]

#: a previous project, CV Dazzle, envisaged hair and make-up designs that would foil facial recognition software [43] <> da ado ko shafe-shafen fuska da gyaran gashi masu susuntar da manhajojin gane fuskar mutum, [44]

#: and heat-reflecting garments that deter drones. [45] <> da kuma tufafi ko kayan sawa da ba sa daukar zafi, wadanda kananan jirage marassa matuka, na leken asiri ba sa iya ganowa. [46]

#: When worn, HyperFace [47] <> Ita wannan fasaha ta zayyana tana susuntar da kwamfuta ne, [48]

#: gives a computer about 1,200 possible facial options[49] <> inda take gabatar mata da fuskokin mutum kusan 1,200[50]

#: Harvey was inspired by false colouration in the animal kingdom. “Instead of imagining camouflage as a means to reduce personal visibility,… [51] <> Harvey ya samu wannan fasaha ne daga irin halitta ko baiwar da wasu dabbobi ko halittu suke da ita ne ta sauya kama ko rikidewa domin boye kansu idan suna fuskantar wani hadari ko barazana. [52]

#: Surveillance is a topic that has been top-of-mind at Hyphen-Labs for some time now,” says Hyphen-Labs member Ashley Baccus-Clark, [53] <> Daya daga cikin ma'aikatan dakin binciken kimiyya na Hyphen-Labs, da suke aikin fasahar, Ashley Baccus-Clark, [54]

#: speaking about the projects inspiration. “It started with thinking through issues of security, privacy, and visibility as it relates to black women and black communities. Then, as the events of the past few months have unfolded, our message became more global.” [55] <> Kuma hakan yana da danganataka ne da yadda al'amura ke kasancewa a 'yan watannin da suka gabata, game da tsaro da sirri da kuma fita a bainar jama'a, musamman a kan mata bakaken fata da kuma al'ummomi bakaken fata. [56]

#: The election of US president Donald Trump [57] <> Zaben Shugaban Amurka Donald Trump [58]

#: has made liberal-minded creatives, among others, twitchy. [59] <> ya sanya masu kirkira na bangaren masu sassaucin ra'ayi bullo da hanyoyi da tsare-tsare na batar da kama ga jama'a. [60]

#: Our political climate is making it necessary for us as [61] <> “yanayin yadda siyasa take a yanzu, ya tilasta su [62]

#: artists, [63] <> masu zayyana [64]

#: researchers, [65] <> da masu bincike [66]

#: and creators to explore themes of surveillance,” [67] <> da kuma masu kirkire-kirkire su gano wasu hanyoyin sanya ido ko tsaro.” [68]

#: While celebrities [69] <> Duk da cewa akwai fitattun mutane [70]

#: like Kim Kardashian [71] <> irin su Kim Kardashian [72]

#: make a careerand arguably an artof increasing personal visibility, [73] <> wadanda suka yi fice a duniya ta hanyar sana'ar da ta shafi bayyana kansu ga jama'a, [74]

#: many of us would prefer to stay under the radar. [75] <> da yawanmu, mun fi kaunar sakaya kanmu daga idon jama'a. [76]

#: And while the internet abounds with tips on protecting digital security, [77] <> Kuma duk da cewa intanet na dauke da hanyoyi da dama na samar da tsaro, [78]

#: designers [79] <> masu zayyanar tufafi da sauran abubuwan amfanin jama'a [80]

#: are coming up with protecting a new battleground: the body. [81] <> na bullo da wasu hanyoyi na kare siffa ko jikin mutum, [82]

#: The inventions are potent mixes of fashion, art [83] <> wadanda hanyoyi ne da suka kunshi ado [84]

#: and technology [85] <> da fasaha, [86]

#: that tell us a lot about the world in which we live. [87] <> wanda hakan ke nuna mana irin yanayin duniyar da muke ciki a yau. [88]

#: Surveillance [89] <> Tsaro [90]

#: has been high on the news agenda since mid-2013, [91] <> na daga cikin abubuwan da aka ba wa muhimmanci a fannin watsa labarai tun tsakiyar shekarar 2013, [92]

#: when the US National Security Agency contractor Edward Snowden [93] <> lokacin da jami'in Hukumar Tsaro ta Amurka Edward Snowden [94]

#: blew the lid on just how much the NSA could find out about us. [95] <> ya yi tonon silili kan yadda hukumar tsaron ta Amurka take tattara bayanai cikin sirri a kan jama'a. [96]

#: Since then, [97] <> Tun daga wannan lokacin [98]

#: revelations have come thick and fast: Facebook, Google and Microsoft [99] <> aka samu bayanai kan yadda Facebook da Google da kuma Microsoft [100]

#: have handed over customer data under secret NSA programmes; [101] <> suka rika mika wa hukumar tsaron ta Amurka bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shafukansu. [102]

#: Gemalto, one of the worlds largest manufacturers of Sim cards, [103] <> Daya daga cikin manyan kamfanonin duniya da ke kera layukan wayar salula Gemalto, [104]

#: has also said it believes its systems were hacked US and UK cyber-surveillance agencies. [105] <> shi ma ya ce ya yi amanna hukumomin tsaro na Amurka da Birtaniya sun rika satar shiga taskarsa. [106]

#: Artists have been quick to respond: [107] <> Wannan ne ya sa kwararru da dama da suka hada da kamfanoni irin su Project KOVR [108]

#: Dutch design duo Project KOVR [109] <> Project KOVR na Holland [110]

#: has focused on ways to shield the library of personal information people carry about with them on a day-to-day basis. [111] <> suka karkata wajen nemo hanyoyin da jama'a za su rika amfani da su a kullum wajen kare bayanansu, ko kuma su rika tafi-da-gidanka da bayanasu, ta yadda za su tabbatar da tsaronsu. [112]

#: The ability to choose when and how to divulge information about ourselves [113] <> Damar da muke da ita, a matsayinmu na mutane, ta yadda za mu bayyana wani bayani a kanmu da kuma zabar lokacin bai kamata mu yi hakan ba, [114]

#: is one of the things that make us human, [115] <> na daya daga cikin abubuwan da suka sa muka tabbata mutane, [116]

#: argues graphic designer Leon Baauw, [117] <> kamar yadda mai zayyana Leon Baauw, [118]

#: who co-founded Project KOVR with performance artist Marcha Schagen. [119] <> wanda na daya daga cikin wadanda suka kirkiro shirin KOVR tare da Marcha Schagen. [120]

#: He says their research[121] <> Ya ce bincikensu [122]

#: was based upon the question [123] <> ya ta'allaka ne a kan maganar cewa, [124]

#: what does it mean for a human being to always be visible’? [125] <> 'menene tasirin kasancewar mutum a bayyane a ko da yaushe?' [126]

#: How would we change the way we behave?” [127] <> Ta yaya za mu sauya yadda muke tafiyar da al'amuranmu ko dabi'armu? [128]

#: The possibilities of clothing are transforming, says Baauw, [129] <> Baauw ya ce; yuwuwar amfani da tufafi [130]

#: from those of decoration, expression and shelter from the elements to ones of maintaining privacy and ultimately, individuality. [131] <> wajen tabbatar da tsaro maimakon ado da kariya kadai ga mutum na kara tabbata. [132]

#: He goes on to say [133] <> Ya kara da cewa [134]

#: Clothing has always protected us against possible threats from the biosphere; [135] <> “Abu ne sananne tufafi a ko da yaushe tufafi suna ba mu kariya daga illa ko barazanar muhalli, [136]

#: why not the infosphere, that nearly invisible network of connectivity in which we are proven to be vulnerable?” he asks. [137] <> to amma me zai hana su ba mu kariya kuma wadda ta shafi bayanai? [138]

#: Its motivating to see more and more projects emerge with the goal of [139] <> “Daga irin wadannan kayayyaki na zamani abubuwa ne da suka shafi ado da kuma al'ada, [140]

#: protecting us as well as reminding us that our data and therefore our personality is out there and up for grabs by anyone or anything.” [141] <> wadanda ke zaman hanyoyin tabbatar da tsaro da sirrin jama'a da ake neman gani zamani ya zo da su. [142]

#: Each of Fabricas pieces provoke a sensory reaction that will [143] <> Kowanne daga cikin irin wadannan kayayyaki na Fabrica, yakan [144]

#: attract the wearers attention, suddenly changing brain activity. [145] <> ja hankalin wanda ya sa shi, ta wata siga, abin da ke shafar aikin kwakwalwa ko ya kan sauya aikin kwakwalwar. [146]

#: So if brain scanning were ever to become reality, [147] <> Saboda haka idan har nazarin hoton aikin kwakwalwa zai kasance gaskiya, [148]

#: they would offer a way to keep your thoughts from being read. [149] <> hakan zai samar da hanyar da za a iya nazari ko sanin tunaninka. [150]

#: Prototypes, crafted out of laser-cut felt and wood, [151] <> Daga cikin irin wadannan abubuwa da aka yi na gwaji, [152]

#: include a hat [153] <> har da malafa [154]

#: that transmits sound pulses through the skull, [155] <> wadda ke mika sako ta hanyar kokon kan wanda ya sanya ta, [156]

#: a collar [157] <> da kwalar riga [158]

#: that administers [159] <> da ke sadarwa [160]

#: a gentle electric shock and a mask that distracts the user with flashing lights. [161] <> tsakaninta da mutumin da ya sanya rigar ta hanyar wani dan motsi na lantarki, da kuma fuskar batar da kama, wadda ke daukar hankalin wanda ya sanya ta da wani dan hasken fitila da ke haskawa ya dauke lokaci zuwa lokaci. [162]

#: The idea of neuroimaging surveillance technology [163] <> Tunanin kirkiro wadannan abubuwa na tsaro da kare sirri [164]

#: still seems like science fiction [165] <> har yanzu na zaman kamar wani abu na mafarki ko wanda ba zai yuwu ba a zahiri, [166]

#: but Fabricas designs, as well as the work of Harvey and Project KOVR, [167] <> amma tsare-tsaren wadanda Fabrica da Harvey da kuma ayyukan Project KOVR, [168]

#: express genuine concerns among designers [169] <> na nuna muhimmanci da damuwar da masu zayyana ke da ita [170]

#: about just what the future may look like. [171] <> kan yadda abubuwa za su iya kasancewa a nan gaba. [172]

#: Harvey, for example, [173] <> Misali shi ne, Harvey, [174]

#: is keen to point out that HyperFace [175] <> ya nuna cewa fasahar HyperFace, wadda ake sanya wa a fuska, [176]

#: isonly an introduction to a larger project about computer vision camouflage”. [177] <> wata alama ce ta yadda za a kai ga yi wa kwamfutar da ke gane fuskar mutum, layar zana. [178]

#: When it comes to new technologies, [179] <> 'Idan ana maganar sabbin fasahohi, [180]

#: some consumers rightfully feel that [181] <> wasu mutanen suna ganin [182]

#: most tech companies fail to implement security and privacy measures,” [183] <> yawancin kamfanoni ba sa daukar matakan bayar da kariya da sirrinta bayanan jama'a, [184]

#: says Mano ten Napel, managing editor of fashion technology website FashNerd. [185] <> Editan shafin fasahar tufafi na FashNerd Mano ten Napel ya ce; [186]

#: This has ignited a need to protect ourselves[187] <> wanda hakan ne ya sa muke bukatar ganin an samu yanayi na bayar da kariya garemu, [188]

#: which logically translates into the design of the technology we wear. [189] <> wanda hakan a takaice yake nufin ya kamata a ga hakan a tufafi ko kayan da muke sanya wa a jikinmu. [190]

#: Its easy [191] <> Abu ne mai sauki [192]

#: to imagine a future [193] <> a yi tsinkaye ko tunanin yadda a nan gaba [194]

#: where staying connected will not automatically violate our privacy.” [195] <> mu'amullarmu da intanet ba za ta zama tamkar wata hanya ta bayyana sirrinmu ba. [196]