bbchausa verticals/035 living plants

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Plants can see, hear and smelland respond [1] <> Ko kun san tsirrai na ji da gani da shakar wari ko kamshi? [2]

#: Plants perceive the world without eyes, ears or brains. [3] <> N/A [4]

#: Understanding how can teach us a lot about them, and potentially a lot about us as well [5] <> N/A [6]

#: Plants, according to Jack C Schultz, "are just very slow animals". [7] <> N/A [8]

#: This is not a misunderstanding of basic biology. [9] <> Wannan ba gurguwar fahimta ba ce game da kimiyyar halittu. [10]

#: Schultz is a professor in the Division of Plant Sciences at the University of Missouri in Columbia, [11] <> Schultz farfesa ne a bangaren kimiyyyar nazarin tsirrai a Jami'ar Missouri da ke Kolombiya, [12]

#: and has spent four decades investigating the interactions between plants and insects. [13] <> kuma ya shafe shekara 40 yana gudanar da bincike kan mu'amalar tsirrai da kwari. [14]

#: He knows his stuff. [15] <> Kwararre ne a fanninsa. [16]

#: Instead, [17] <> Sabanin haka ma, [18]

#: he is making a point about common perceptions of our leafy cousins, [19] <> ya bijiro da muhimmin al'amari wajen fahimtar danginmu masu ganye, [20]

#: which he feels are too often dismissed [21] <> wadanda yake ganin an yi watsi da su [22]

#: as part of the furniture. [23] <> tamkar wani yanki na kayan alatun gida. [24]

#: Plants fight for territory, seek out food, [25] <> Tsirrai na fafatawa saboda wurin zama da neman abinci, [26]

#: evade predators and trap prey. [27] <> su farmaki masu kai musu hari da kuma yi wa abincinsu tarko. [28]

#: They are as alive as any animal, [29] <> Suna da rai kamar kowace dabba, [30]

#: andlike animalsthey exhibit behaviour. [31] <> kuma tamkar dabbobi suna nuna dabi'arsu. [32]

#: "To see this, you just need to make a fast movie of a growing plant[33] <> "Don ganin hakan, kana bukatar yin majigin tsirrai da ke girma, [34]

#: then it will behave like an animal," [35] <> ta yadda za su nuna dabi'u irin na dabbobi," [36]

#: enthuses Olivier Hamant, a plant scientist at the University of Lyon, France. [37] <> kamar yadda a cikin zumudi Olivier Hamant, wani masanin kimiyyar nazarin tsirrai daga Jami'ar Lyon, a Faransa ya furta. [38]

#: Indeed, a time-lapse camera [39] <> A gaskiya, kyamara mai daukar hoton wucin gadi [40]

#: reveals the alien world of plant behaviour in all its glory, [41] <> za ta bayyanar da abin da ya boyu a duniyar tsirrai da dabi'u masu kayatarwa, [42]

#: as anyone who has seen the famous woodland sequence [43] <> ta yadda duk wanda ya taba ganin jerin majigin nan na jerin "woodland" [44]

#: from David Attenborough's Life series can attest. [45] <> wanda David Atenborough ya gabarar da shirin tartibin rayuwa (Life series) zai fahimta. [46]

#: These plants are moving with purpose, [47] <> Wadannan tsirrai na yin motsi ne da manufa, [48]

#: which means they must be aware of what is going on around them. [49] <> ma'ana suna sane da abin da ke wakana a kewaye da su. [50]

#: "To respond correctly, [51] <> "Don mayar da martani yadda ya dace, [52]

#: plants also need sophisticated sensing devices tuned to varying conditions," says Schultz. [53] <> tsirran na bukatar managarcin tsari da na'urori da za su yi juyi daidai da mabambantan yanayi," inji Schultz. [54]

#: So what is plant sense? [55] <> Ko me ake nufi da sansanowar tsirrai? [56]

#: Well, if you believe Daniel Chamovitz of Tel Aviv University in Israel, [57] <> Ta yiwu idan ka yarda da batun Daniel Chamovitz na Jami'ar Tel Aviv da ke Isra'ila, [58]

#: it is not quite so different from our own as you might expect. [59] <> babu bambanci da yanayinmu kamar yadda kake sa rai. [60]

#: When Chamovitz set out to write his 2012 book What a Plant Knows[61] <> Lokacin da chamovitz ya kuduri yin rubutunsa a shekara 2012, [62]

#: When Chamovitz set out to write his 2012 book What a Plant Knows[63] <> wato littafinsa mai taken Me tsiro ya sani[64]

#: in which he explores how plants experience the world [65] <> a ciki ya bibiyi yadda tsirrai ke samun fahimtar duniya [66]

#: by way of the most rigorous and up-to-date scientific research[67] <> ta hanyar kai kawo a wajen nazari har zuwa yau a tsarin binciken kimiyya [68]

#: he did so with some trepidation. [69] <> ya yi hakan ne cikin damuwa. [70]

#: "I was incredibly wary about what the response would be," he says. [71] <> "Na yi matukar zakuwar son jin irin martanin da za a samu," inji shi. [72]

#: A Beethoven symphony is of little consequence to a plant, [73] <> Kwarewar kade-kaden Beethoven ba shi da wani tasiri ga tsiro, [74]

#: but the approach of a hungry caterpillar is another story [75] <> amma idan tsutsa mai jin yunwa ta kawo hari, a nan za a ga yadda tsiro zai fafata da ita. [76]

#: His worry was not unfounded. [77] <> Damuwarsa ba za a ce ba ta da tushe ba. [78]

#: The descriptions in his book of plants seeing, [79] <> Al'amuran da ya siffanta na tsirrai game da ganinsu [80]

#: smelling, feeling and, indeed, knowing have echoes of The Secret Life of Plants, [81] <> da sansanarsu da tunaninsu da ma sanin sauti a Sirrin rayuwar tsirrai (The Scret Life of Plants), [82]

#: a popular book published in 1973 [83] <> wani mashahurin littafi da aka wallafa a shekarar 1973 [84]

#: that appealed to a generation raised on flower power, [85] <> wanda ya dauki hankalin al'ummar zamanin game da karfin fure, [86]

#: but contained little in the way of facts. [87] <> amma sai aka tattara shi a 'yar karamar hanya wajen kafa hujoji na gaskiya. [88]

#: The earlier book's most enduring claim, [89] <> Littafin farko ya fito da kwararan bayanai, [90]

#: perhaps, [91] <> wadanda ta yiwu, [92]

#: is the thoroughly discredited idea that plants respond positively to the sound of classical music. [93] <> shi ne ke kunshe da bayanin da ka ki amincewa da shi na cewa tsirrai na mayar da martani yadda ya dace ga karar kidan zamani. [94]

#: But the study of plant perception has come a long way since the 1970s, [95] <> Amma nazarin irin fahimtar tsirrai ya faro tun daga shekarun 1970, [96]

#: and in recent years there has been an uptick of research into plant senses. [97] <> kuma a shekarun baya-bayan nan an samu ci gaba wajen bincike kan yadda tsiro ke sansano abubuwa. [98]

#: The motivation for this work [99] <> Abin da ya zaburar da wannan aikin [100]

#: has not been simply to demonstrate that [101] <> ba wai don a a nuna cewa [102]

#: "plants have feelings too", [103] <> "tsirrai ma suna yin tunani ba," [104]

#: but instead to question why, [105] <> sai dai don neman dalilin da ya sanya, [106]

#: and indeed how, a plant senses its surroundings. [107] <> da yadda aka yi tsiro ke sansano abin da ke kewaye da shi (a mahallinsa). [108]

#: Enter Heidi Appel and Rex Cocroft, colleagues of Schultz at Missouri [109] <> Heidi Appel da Rex Cocroft, wasu abokan aikin Schultz a Missouri sun shiga jerin masu binciken, [110]

#: who are searching for the truth about plant hearing. [111] <> wadanda ke bin kadin gaskiyar lamari kan yadda tsiro ke saurare. [112]

#: "The main contribution of our work has been to provide a reason for why plants are affected by sound," says Appel. [113] <> Gudunmowar kawai tana da manufar bijiro da dalilin da zai tabbatar da tasirin sauti a kan tsirrai," inji Appel. [114]

#: A Beethoven symphony [115] <> Salon kidan Beethoven [116]

#: is of little consequence to a plant, [117] <> tasirinsa kadan ne a kan tsiro, [118]

#: but the approach of a hungry caterpillar is another story. [119] <> amma farmakin tsutsa mai jin yunwa wani sabon labari ne. [120]

#: We have noses and ears, but what does a plant have? [121] <> Muna da hanci da kunnuwa, amma mene ne tsiro ke da shi? [122]

#: Ecological relevance is key. [123] <> Muhimmancin abubuwan da ke kewaye a muhalli su ne mabudi. [124]

#: Consuelo De Moraes of the Swiss Federal Institute of Technology in Zurich, [125] <> Consuelo De Moraes na Cibiyar Tarayyar Swiss ta Kere-kere da ke Zurich, [126]

#: along with collaborators, [127] <> tare da hadin gwiwar abokansa, [128]

#: has shown that as well as being able to hear approaching insects, [129] <> ya nuna cewa iya sauraren karar kwaron da ke tahowa, [130]

#: some plants can either smell them, [131] <> wasu tsirran za su iya sansano su ko su ji kamshi [132]

#: or else smell volatile signals released by neighbouring plants in response to them. [133] <> ko warin hargowar alamunsu daga tsirran da ke makwaftaka da su don mayar da martani gare su. [134]

#: More ominously, back in 2006 [135] <> Babbar barazanar da aka yi nuni da ita a shekarar 2006 [136]

#: she demonstrated how a parasitic plant known as the dodder vine sniffs out a potential host. [137] <> ta nuna yadda tsiro mai cin dan uwansa, [138]

#: The dodder vine then wriggles through the air, before coiling itself around the luckless host and extracting its nutrients. [139] <> nau'in "dodder vine" ya kassara wanda yake zaune a kansa. [140]

#: Conceptually, [141] <> Abin fahimta a nan, [142]

#: there is nothing much distinguishing these plants from us. [143] <> babu bambanci mai yawa a tsakaninmu da wadannan tsirran. [144]

#: They smell or hear something [145] <> Su kan sansano kamshi ko wari ko su saurari wani abu, [146]

#: and then act accordingly, just as we do. [147] <> sannan su mayar da martanin da ya dace, tamkar yadda muke yi. [148]

#: But, of course, there is an important difference. [149] <> Sai dai tabbas, akwai wani muhimmin bambanci. [150]

#: "We don't really know how similar the mechanisms of odour perception in plants and animals are, [151] <> "Ba mu san hakikanin yadda ake da kamaceceniya a tsarin jin wari ko kamshi a tsirrai da dabbobi ba, [152]

#: because we don't know much about those mechanisms in plants," says De Moraes. [153] <> saboda ba mu fahimci al'amura da dama game da tsarin yadda yake a tsirrai ba, inji De Moraes. [154]

#: We have noses and ears, but what does a plant have? [155] <> Muna da hanci da kunnuwa, amma me tsiro ke da shi? [156]

#: The lack of obvious centres of sensory input makes it harder to understand plant senses. [157] <> Rashin sansannun cibiyoyin tattara bayanai kan sansane-sansane ya haifar da wuyar fahimta yadda tsiro ke sansane-sansane (a kafofin jikinsa). [158]

#: For their part, Appel and Cocroft are hoping to track down the part or parts of a plant that respond to sound. [159] <> A nasu bangaren kuwa, Appel da Cocroft suna sa ran bin kadin yadda sassan jikin tsirrai ke mayar da martani ga sauti. [160]

#: Researchers have begun to find repeating patterns [161] <> Masu bincike sun fara maimaita tsare-tsaren [162]

#: that hint at deep parallels with animals [163] <> da ke nuni da yadda aka yi matukar shan bamban da dabbobi. [164]

#: These convert micro-deformations of the kind that sound waves [165] <> Wadannan kananan illoli da karar sauti ke haifarwa [166]

#: can generate as they wash over an object into electrical or chemical signals. [167] <> na iya jefa abu cikin tafiyar lantarki ko motsin sinadarai. [168]

#: They are testing to see whether plants with defective mechanoreceptors can still respond to insect noise. [169] <> Ta yiwu wadanda za a yi gwajin a kansu ne ke tarairayar tsarin sarrafa abinci mai gina jiki a daukacin kwayoyin halittar tsiro. [170]

#: For a plant, it seems, there may be no need for something as cumbersome as an ear. [171] <> A wajen tsiro kuwa, yana yiwuwa babu bukatar wani abu mai tsauri kamar kunne. [172]

#: Another ability we share with plants is [173] <> Wani aikin da muke iya yi daidai da tsirrai [174]

#: proprioception: [175] <> shi ne motsin daidaiku: [176]

#: the "sixth sense" that enables (some of) us to touch type, [177] <> "kafa ta shida" da ke ba mu damar (wasu daga cikin) tabawa [178]

#: juggle, [179] <> da tsalle-tsalle, [180]

#: and generally know where various bits of our body are in space. [181] <> tare da fahimtar inda wasu sassan jimkinmu suke walwala. [182]

#: Because this is a sense that is not intrinsically tied with one organ in animals, [183] <> Saboda wannan ita ce kafa da ke da muhimmanci tattare da kafar jikin dabbobi, [184]

#: but rather relies on a feedback loop [185] <> amma an fi dogaro sakamakon sakar da ke [186]

#: between mechanoreceptors in muscles and the brain, [187] <> tsakanin tsare-tsaren tarairayar nama da kwakwalwa, [188]

#: the comparison with plants is neater. [189] <> wanda kwatantawa da tsirrai ke da matukar kyau. [190]

#: "The overarching idea is the same," says Hamant, [191] <> "Wannan dabarar mamaya iri guda ce," a cewar Hamanta, [192]

#: who co-authored a 2016 review of proprioception research. [193] <> wanda ya yi hadin gwiwa wajen bibiyar binciken daidaikun sassan jiki da suka rubuta a shekarar 2016. [194]

#: "So far, what we know is that in plants [195] <> "Zuwa yanzu dai, abin da muka fahimta shi ne game da tsirrai [196]

#: it is more to do with microtubules [[[structural]] components of the cell], [197] <> ya fi yawa tsarin kwayar halitta, [198]

#: responding to [199] <> wajen mayar da martani [200]

#: stretch and mechanical deformation." [201] <> da motsin tankwarawa." [202]

#: In fact, a study published in 2015 [203] <> Gaskiyar lamari, wani bincike da aka wallafa a shekarar 2015 [204]

#: appears to show similarities that go even deeper, [205] <> ya yi nuni da kamanceceniyar mai yawa, [206]

#: suggesting a role for actina key component in muscle tissuein plant proprioception. [207] <> wadda ta bayyana wani bangaren naman mutum da aikinsa ya yi daidai da nan daidaikun motsin na jikin tsiro. [208]

#: "This is less supported," says Hamant, [209] <> "Wannan hujja ce marar karfi," inji Hamant, [210]

#: "but there has been some evidence that actin fibres in tissue are involved; almost like muscle." [211] <> "amma akwai wasu hujjojin da ke nuni da cewa silin tsiron na 'actin' na aiki kamar yadda nama ke yi." [212]

#: These findings are not unique. [213] <> Wadannan sakamakon binciken ba kebabbu ba ne ba. [214]

#: As research into plant senses has progressed, [215] <> Domin an ci gaba da bincike kan sansane-sansanen tsiro, [216]

#: researchers have begun to find repeating patterns [217] <> masu bincike sun gano tsare-tsaren da ke maimaita kansu, [218]

#: that hint at deep parallels with animals. [219] <> wadanda suka nuna sun yi hannun riga da na dabbobi. [220]

#: Today there are plant researchers investigating such traditionally non-plant areas [221] <> A yau akwai masu binciken tsiro, kan al'amarin al'adun da ba su shafi tsiron ba, [222]

#: as memory, learning and problem-solving [223] <> wadanda suka hada da tunani da koyo da warware matsala. [224]

#: In 2014, a team at the University of Lausanne in Switzerland [225] <> A shekarar 2014. Wani gungun masana daga Jami'ar Lausame ta Switzerland [226]

#: showed that when a caterpillar attacks an Arabidopsis plant, it triggers a wave of electrical activity. [227] <> da farmakin da tsutsa ta kai wa wani tsiron nau'in kabeji (Arabidopsis) ya ingizo da hargowar lantarki. [228]

#: The presence of electrical signalling in plants is not a new idea[229] <> Kasancewar alamun hargowar lantarki a tsirrai ba sabon abu ba ne, [230]

#: physiologist John Burdon-Sanderson [231] <> a cewar masanin sassan jiki John burdon-Sanderson [232]

#: proposed it as a mechanism for the action of the Venus flytrap as early as 1874[233] <> da ya nuna cewa tsarin aiki ne na tsiron Venus flytrap tun a shekarun 1874, [234]

#: but what is surprising is [235] <> sai dai abin mamakin shi ne [236]

#: the role played by molecules called glutamate receptors. [237] <> rawar da sinadari ke takawa, wadda ake kira da mai karbar sinadarin glutamate. [238]

#: Glutamate is the most important neurotransmitter in our central nervous system, [239] <> Sinadarin Glutamate ya fi kowanen muhimmanci wajen aikewa da sakonni a masarrafar kadarkon jijiyoyi, [240]

#: and it plays exactly the same role in plants, [241] <> kuma yana taka irin wannan muhimmiyar rawar a jikin tsirrai, [242]

#: except with one crucial difference: [243] <> sai dai wani abin muhimmin lura [244]

#: plants do not have nervous systems. [245] <> tsirrai ba su da kadarkon jijiyoyin aikewa da sakonni. [246]

#: "Molecular biology [247] <> "Fannin kimiyyar nazarin kwayoyin halitta [248]

#: and genomics [249] <> da juyin kwayoyin halittu [250]

#: tell us that plants and animals are composed of a surprisingly limited set of molecular 'building blocks' [251] <> sun nusar da mu cewa tsirrai da dabbobi suna da kwayoyin halitta da jerin su ke da iyaka 'jigon gina jiki' [252]

#: that are very much alike," says Fatima Cvrčková, [253] <> masu kama da juna," a cewar Fatima Cvrčková, [254]

#: a researcher at Charles University in Prague, Czech Republic. [255] <> wata mai bincike a Jami'ar Charles da ke Prague a jamhuriyar Czech. [256]

#: Electrical communication has evolved in two distinct ways, [257] <> Sakonnin lantarki suna zarya ne ta hanyoyi biyu. [258]

#: "Evolution [259] <> "Bunkasar halittu [260]

#: has led to a certain number of potential mechanisms for communication, [261] <> ta haifar da dimbin tsare-tsaren sadarwa, [262]

#: and while you can get to that in different ways, [263] <> kuma duk da cewa za ka iya kai wa ga haka ta hanyoyi mabambanta, [264]

#: the end point is still the same," says Chamovitz. [265] <> karshen al'amarin dai irin guda ne," inji Chamovitz. [266]

#: The realisation that such similarities exist, [267] <> Fahimtar cewa irin wadannan kamance-kamancen na nan, [268]

#: and that plants have a far greater ability to sense their world than appearances might suggest, [269] <> kuma tsirrai na da karfin sansano abin da ke kewaye da su sabanin yadda ake ganinsu, [270]

#: has led to some remarkable claims about "plant intelligence", [271] <> wannan ya haifar da kyakkyawan ikirarin cewa "tsiro na da basira," [272]

#: and even spawned a new discipline. [273] <> har ta kai ga an fito da sabon fannin nazari. [274]

#: Electrical signaling in plants [275] <> Karkarwar lantarki da ke bijirowa daga tsirrai [276]

#: was one of the key factors in the birth of [277] <> na daya daga cikin jiga-jigan al'amuran da suka haifar [278]

#: "plant neurobiology" [279] <> "kimiyyar sakonnin tsirrai - plant neurobiology" [280]

#: (a term used despite the lack of neurons in plants), [281] <> (mahangar da ake amfani da ita duk da cewa tsirrai ba su da jijiyoyin aikewa da sakonni), [282]

#: and today [283] <> sannan a yau [284]

#: there are plant researchers [285] <> akwai masu bincike kan tsirrai, [286]

#: investigating such traditionally non-plant areas as memory, learning and problem-solving. [287] <> wadanda ke gudanar da binciken kan al'adun da ba su shafi tsirrai ba, wato abubuwwan da suka shafi tunani da koyo da warware matsala. [288]

#: Despite lacking eyes, [289] <> Duk da rashin idanu, [290]

#: plants such as Arabidopsis possess at least 11 types of photoreceptor, [291] <> tsirrai irin su latas din Arabidopsis na da nau'uka 11 na makarbiyar haske, [292]

#: compared to our measly four [293] <> wadda ake kwatantawa da namu nau'uka hudu. [294]

#: This way of thinking has even led to [295] <> Irin wannan tsarin tunanin shi ya haifar wa [296]

#: law makers in Switzerland setting guidelines designed to protect [297] <> yan majalisa a kasar Switzerland suka bullo da wasu ka'idojin kiyaye [298]

#: "the dignity of plants" – whatever that means. [299] <> "martabar tsirrai" - ba tare da la'akari da abin zai haifar ba. [300]

#: And while many consider terms [301] <> Duk da cewa akwai dimbin wadanda ke ganin cewa kalamai [302]

#: like "plant intelligence" [303] <> irin su "basirar tsirrai" [304]

#: and "plant neurobiology" [305] <> da "kimiyyar sakonnin tsirrai" [306]

#: to be metaphorical, [307] <> wata sarkakiyar Magana ce, [308]

#: they have still been met with a lot of criticism, not least from Chamovitz. [309] <> sun sha dimbin suka ba ma kawai daga Chamovitz ba. [310]

#: "Do I think plants are smart? [311] <> "Ko ina tunanin cewa tsirrai masu wayau ne? [312]

#: I think plants are complex," he says. [313] <> Ina jin cewa dai tsirrai na da cukurkudaddun al'amura," inji shi. [314]

#: Complexity, he says, should not be confused with intelligence. [315] <> Cukurkudewar lamura, a cewarsa, ba za a rudu da cewa tana nufin kaifin basira ba. [316]

#: So while it is useful to describe plants [317] <> Duk da cewa yana da alfanu a kwatanta tsirrai [318]

#: in anthropomorphic terms [319] <> da wasu siffofin mutane (irin su soyayya da haihuwa da kyawu da kiyayya da hadama da hikima da sauransu) [320]

#: to communicate ideas, there are limits. [321] <> wajen isar da dabarun sadarwa, suna da iyaka. [322]

#: The danger is that we end up viewing plants as inferior versions of animals, [323] <> Sai dai hadarin da ke tattare shi ne kallon tsirrai a matsayin makaskantan rukunin dabbobi, [324]

#: which completely misses the point. [325] <> wannan ya kauce wa manufa gaba daya. [326]

#: "We plant scientists [327] <> "Mu masana kimiyya da ke nazarin tsirrai [328]

#: are happy to talk about similarities and differences [329] <> muna farin cikin yin magana game da kamanceceniya da bambance-bambancen [330]

#: between the plant and animal lifestyles [331] <> da ke tsakanin rayuwar tsirrai da ta dabbobi [332]

#: when presenting results of plant research to the general public," says Cvrčková. [333] <> a lokacin gabatar da sakamakon bincike ga daukacin al'umma," inji Cvrckova. [334]

#: However, she thinks reliance on animal-based metaphors to describe plants comes with issues. [335] <> Sai dai, tana jin cewa dogaro da sarkakiyar kamanceceniya wajen siffanta tsirrai na tattare da matsaloli. [336]

#: "You want to avoid [[[such]] metaphors], [337] <> "Kana son kauce wa irin wannan (sarkakiyar), [338]

#: unless you are interested in a (usually futile) debate [339] <> sai dai in manufar ta dogara ne kacokam (kan abu mara amfani) [340]

#: about a carrot's ability to feel pain when you bite into it." [341] <> a takaddamar jin zafin ciwon karas idan ka gutsire shi." [342]

#: Plants are supremely adapted for doing exactly what they need to do. [343] <> Tsirrai sun kai makura wajen yin hakikanin abin da suke son yi. [344]

#: They may lack a nervous system, [345] <> Ta yiwu ba su da tsarin jijiyon aikewa da sakonni, [346]

#: a brain and other features we associate with complexity, [347] <> wato kwakwalwa da sauran sassan da muke dangantawa da cukurkudewar al'amura, [348]

#: but they excel in other areas. [349] <> amma sun yi fice a wasu sassan. [350]

#: We are more plant-like than we would like to think [351] <> Mun fi kusa (a kamanceceniya) da tsirrai fiye da yadda muke tsammani. [352]

#: For example, despite lacking eyes, [353] <> Misali, duk da rashin idanu, [354]

#: plants such as Arabidopsis possess at least 11 types of photoreceptor, [355] <> tsirrai irin su latas din Arabidopsis suna da makarbiyar haske nau'ika 11, [356]

#: compared to our measly four. [357] <> in an kwatanta da namu 'yan kadan guda hudu. [358]

#: This means that, in a way, their vision is more complex than ours. [359] <> Wannan na nufin cewa, tsarin ganinsu na da rudarwa fiye da namu. [360]

#: Plants have different priorities, [361] <> Tsirrai na da fifikon bukatu, k [362]

#: and their sensory systems reflect this. [363] <> uma kafofin sansano harkokinsu na nuni da haka. [364]

#: As Chamovitz points out in his book: [365] <> Tamkar dai yadda Chamovitz ya yi nuni a cikin littafinsa cewa: [366]

#: "light for a plant is much more than a signal; light is food." [367] <> "haske a wajen tsiro ya fi gaban walkatawa; haske abinci ne." [368]

#: So while plants face many of the same challenges as animals, [369] <> Saboda haka a lokacin da tsirrai ke fuskantar kalubale irin na dabbobi, [370]

#: their sensory requirements are equally shaped by the things that distinguish them. [371] <> bukatun kafofin sansano abubuwa na tasirantuwa ne da irin al'amuran da suka bambance su. [372]

#: "The rootedness of plantsthe fact that they are unmoving[373] <> "Kafuwar tushen itace[374]

#: means they actually have to be much more aware of their environment than you or I do," says Chamovitz. [375] <> na nufi da gaskiyar lamarin rashin motsinsu shi ke nuna cewa suna sane da abin da ke kewaye da su a muhallinsu fiye da yadda kake yi ko nake yi," inji Chamovitz. [376]

#: To full appreciate how plants perceive the world, [377] <> Don samun cikakkiyar fahimtar yadda tsirrai ke sanin duniya, [378]

#: it is important that scientists and the wider public appreciate them for what they are. [379] <> yana da matukar muhimmmanci ga masana kimiyya da daukacin al'umma su fahimci hakikanin yadda suke. [380]

#: "The danger for the plant people is that if we keep comparing [[[plants]]] with animals [381] <> "Hadarin da ke tattare da mutane game da tsirrai, shi ne idan muka ci gaba da kwatanta tsirrai da dabbobi [382]

#: we might miss the value of plants," says Hamant. [383] <> za mu iya yin watsi da alfanun tsirran," inji Hamant. [384]

#: "I would like to see plants acknowledged more as the amazing, [385] <> "Ina son ganin an fahimci cewa tsirrai na da ban mamaki da ban sha'awa, [386]

#: interesting, exotic living beings they are," agrees Cvrčková, [387] <> tare da karfin jure wa rayuwa," kamar yadda Cvrckova ta tabbatar, [388]

#: "and less as a mere source of human nutrition and biofuels." [389] <> "kuma ta yi kasa a matsayin abincin mutane da makamashinsu." [390]

#: Such an attitude will benefit everyone. [391] <> Irin wadannan al'amura za su amfanar da kowa. [392]

#: Genetics, [393] <> Nazarin kwayoyin halitta [394]

#: electrophysiology [395] <> da gamayyar lantarki [396]

#: and the discovery of transposons [397] <> da kimiyyar ayyukan sassan jiki da gano yadda kwayoyin halitta ke samun sauye-sauye [398]

#: are just a few examples of fields that began with research in plants, [399] <> kadan ne daga cikin misalan wadannan fannoni da aka fara su daga binciken tsirrai, [400]

#: and they have all proved revolutionary for biology as a whole. [401] <> kuma sun bude sabon babi wajen bunkasar kimiyyar nazarin halittu gaba daya. [402]

#: Conversely, the realisation that we have some things in common with plants might be an opportunity to accept that we are more plant-like than we would like to think, just as plants are more animal-like than we usually assume. [403] <> Sabanin haka ma, ganewar da aka yi cewa muna da wasu abubuwa iri guda da tsirrai ta iya zama wata damar amincewa da cewa mu ma tamkar tsirrai muke, muna bukatar yin tunani, tamkar yadda tsirrai suke kamanceceniya da dabbobi fiye da yadda muke tsammani. [404]

#: "Maybe we are more mechanistic than we think we are," concludes Chamovitz. [405] <> "Ta yiwu al'amuranmu sun fi cukurkudewa fiye da yadda muke tsammani," kamar yadda Chamovitz ya karkare. [406]

#: For him, the similarities should alert us to plants' surprising complexity, [407] <> A ganinsa, kamanceceniyar za ta ankarar da mu game da cukurkudaddun al'amura masu ban mamaki na tsirrai, [408]

#: and to the common factors that connect all life on Earth. [409] <> da kuma jiga-jigan al'amuran da suka yi wa daukacin halittun da suke rayuwa a duniya mahada. [410]

#: "Then we can start to appreciate the unity in biology." [411] <> "Daga nan za mu fara sha'awar jin cewa halittu (tsirrai da dabbbobi) na da mahada kamar yadda kimiyyar nazarin halittu ta tabbatar." [412]

#: Join over six million BBC Earth fans by liking us on Facebook, or follow us on Twitter and Instagram. [413] <> Shiga cikin jerin mutum fiye da miliyan shida masoyan shirin Doron kasa na BBC, ta hanyar taba maballin kauna a shafinmu na facebook, ko ka biyo mu a shafinmu na Twitter da Instagram [414]