bbchausa verticals/044 scar tissue vs normal skin

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Why is scar tissue different to normal skin [1] <> Me ya sa fatar tabo ta bambanta da mai lafiya? [2]

#: A scar tells the world of injuries pastbut why does scar tissue look and feel so different? [3] <> Tabo alama ce da ke shaida wa duniya mun samu miki a baya, amma me ya sa fatar wurin ke bambanta da sauran jiki? [4]

#: When I was 10 or 11 years old, [5] <> Lokacin ina da shekaru 10 ko 11, [6]

#: I hurt my knee at summer camp when I fell running around a gravel-covered walkway with some of my bunkmates. [7] <> na ji ciwo a gwiwata lokacin da nake 'yar tsere da abokaina a wani wurin wasa mai cike da kananan tsakuwoyi. [8]

#: I fell hard enough that a few tiny pieces of gravel actually embedded themselves under the skin that covered my kneecap. [9] <> Faduwar da na yi ta jawo har tsakwankwani sun nutse karkashin fatar gwiwata. [10]

#: In the infirmary, [11] <> Da aka kai ni asibiti, [12]

#: after the nurses wiped away the blood [13] <> bayan da ma'aikatan jiyya su ka wanke jinin, [14]

#: and washed the gravel bits out of the skin, [15] <> su ka kuma cire tsakwankwanin, [16]

#: they placed a bucket under my leg and poured rubbing alcohol over it. [17] <> sai suka sa magani su ka wanke mikin. [18]

#: It hurt, but at least I didn't get an infection. [19] <> Na ji zafi, amma hakan ya sa babu wata kwayar cuta da samu shiga. [20]

#: What I did get, however, was a nice scar. [21] <> Sai dai na samu tabo. [22]

#: Then there was the time I stabbed my hand with a knife while attempting to open boxes in my college dorm room. [23] <> Akwai wani lokaci kuma da na cake hannuna da wuka a kokarin bude wasu akwatuna a dakinmu na jami'a. [24]

#: Despite my best efforts, that, too, [25] <> Duk da kokarin neman maganin da na yi, [26]

#: resulted in a scar on my left hand, in the space between my thumb and first finger. [27] <> a wannan karon ma sai da na samu tabo a hannun haguna tsakanin babban dan yatsa da mai yatsan farko. [28]

#: Nearly everyone has a good scar story (or two, or three) they can tell in an effort to one-up their friends' stories. [29] <> Kusan duk wanda na sani ya na da tabo daya ko biyu a jikinsa. [30]

#: But what exactly is scar tissue anyway? [31] <> Amma tambayar anan ita ce: menene tabo? [32]

#: For one thing, a scar is a virtual certainty following a wound of any sort, at least to some degree. [33] <> Da fari dai, tabo, wani abu ne da kan biyo samuwar rauni kowanne iri ne. [34]

#: That's because a scar is the natural outcome of the body's normal healing process as it works to repair the skin or another of its organs. [35] <> Saboda shi ne abinda jiki ke haifarwa a lokacin da yake gyara inda rauni ya lalata. [36]

#: However, animals that regenerate parts of their bodies, [37] <> Sai dai kuma sauran dabbobi da kan sake samar da sassan jikinsu da su ka gutsure, [38]

#: like limbs or tails, can do this without scarring. [39] <> kamar jela ko kafa, ba sa yin tabo a wurin da sabuwar gabar ta fito. [40]

#: After a wound, burn, or injury, the first thing the body does is bleed. [41] <> Bayan samun rauni, kuna, ko miki, abu na farko da jiki zai yi shi ne zubar da jini. [42]

#: The second thing the body does is form a blood clot. [43] <> Na biyu shi ne daskarar da jinin. [44]

#: The very top layers of the clot dry out and harden to form a scab, [45] <> Bangaren da ke saman daskararren jinin, shi ne ke kekashewa ya zama bawo [46]

#: which protects the wound from additional disturbances. [47] <> domin kare raunin daga abubuwan da za su iya cutar da shi. [48]

#: Protected from the external world, the lower portion of the clot becomes host to cells called fibroblasts, [49] <> To a karkashin wannan bawon ne, wasu kwayoyin halitta da ake kira fibroblasts ke taruwa, [50]

#: whose job in part is to replace the scab with scar tissue. [51] <> wadanda aikinsu shi ne maye gurbin bawon da tabo. [52]

#: But while the tissue that makes up a scar is made of the same stuff as normal skina protein called collagen, primarilyit looks and feels different. [53] <> Kodayake ana yin fatar tabo da irin sinadiran protein mai suna collagen, wanda ake yin lafiyayyar fata da shi, tabo ya kan bambanta da sauran fatar jiki a ido da kuma wurin tabawa. [54]

#: In a 1998 paper in the Bulletin of Mathematical Biology, University of Warwick mathematicians John C Dallon and Jonathan A Sherratt explained why. [55] <> Masana lissafi a jami'ar Warwick ta Ingila John C Dallon da Jonathan A Sherratt sun bayyana dalilin haka a wani bincike da su ka wallafa sakamakonsa a 1998. [56]

#: "In humans and other tight-skinned animals," they wrote, [57] <> Su ka ce: "a jikin mutane, da sauran dabbobi masu matsattsiyar fata, [58]

#: "collagen has a cross-weave structure in normal tissue, [59] <> ana shirya sinadirin collagen ne a karkace a lafiyayyar fata, [60]

#: whereas in scar tissue it is aligned parallel to the plane of the skin." [61] <> a kuma jera shi a mike a fatar tabo". [62]

#: It's actually quite reasonable, from an evolutionary perspective. [63] <> Wannan ba karamar hikima ba ce idan mu ka lura. [64]

#: An open wound leaves the body susceptible to all sorts of problems, from intense pain to infection. [65] <> Budadden ciwo na ba da damar cutar da jiki ta hanyoyi da dama. [66]

#: So rather than slowly build skin the usual way, [67] <> Don haka, maimakon a gina fatar da za ta rufe ciwo a hankali kamar yadda ake samar da ragowar fata, [68]

#: scars are the work of the body's rapid response team. [69] <> sai halittu masu agajin gaggawa a jiki, su kai dauki a kan kari. [70]

#: Think of it this wayif you've got a hole in your roof and it's raining, [71] <> Kamar kai ne rufin gidanka ya ke zuba da damina. [72]

#: it's not worth waiting for the best carpenter in town if the second-best carpenter is available. [73] <> Ba bukatar jiran kafintan da yafi kwarewa a garinku idan za ka iya samun wanda bai kai shi a nan take. [74]

#: Especially if he can get the job done in half the time for half the price. [75] <> Musamman ma idan wanda bai kai shin ba, zai gudanar da aikin a rabin lokacin da kwararren zai dauka kuma a rabin farashi. [76]

#: It's better to protect the body from the outside world as soon as possible, even if the handiwork is a bit sloppy. [77] <> Gaggawar kare jikin ita ce tafi muhimmanci fiye da samar da kyakkyawar fata. [78]

#: While some scars are a source of pride, others might be aesthetically displeasing. [79] <> Kodayake wasu kan yi alfahari da tabonsu, wasu kuwa kyamarsa su ke yi. [80]

#: And though there aren't any methods to completely avoid scarring, there are ways to minimise their formation or appearance. [81] <> Babu wata hanya ta magance afkuwar tabo kwata-kwata, amma akwai hanyoyin rage shi. [82]

#: That's why doctors so often use stitches. [83] <> Wannan ne dalilin da ya sa likitoci kan dinke bakin ciwo domin rage fadin tabo. [84]

#: If a scar is particularly unsightly, [85] <> Idan kuma tabon ya yi muni da yawa, [86]

#: a dermatologist might recommend "revising" the scar. [87] <> likitan fata kan yade shi, [88]

#: In this process, the scar is entirely removed and the skin is re-stitched. [89] <> ya sake dinkin wurin ta yadda wani sabon tabon da bai kai na farkon muni ba zai maye gurbinsa. [90]

#: Because scars are unavoidable, a new one will form, but the doctor can work to make it less obvious. [91] <> Saboda ba za'a iya hana tabon baki daya ba. [92]

#: Other forms of treatment, [93] <> Sauran hanyoyin da ake bi wurin rage tabo [94]

#: like chemical peels or dermabrasion work by removing the outermost layers of skin. [95] <> sun hada da daye fatar sama ta hanyar amfani da sinadirai. [96]

#: The skin then heals from this kind of controlled assault, [97] <> Fatar kan warke daga wannan sabon raunin, [98]

#: and as a result the newer, younger skin could appear more uniform. [99] <> kuma sabuwar da za ta maye gurbinta ta kan fi waccan kyan gani. [100]

#: But while each of these methods may result in an improved appearance for some folks under some conditions, [101] <> Sai dai duk da yake wadannan hanyoyin za su iya rage tsananin tabo, [102]

#: none of them actually remove scars entirely. [103] <> babu wata dabara da za ta iya cire tabo dungurumgun. [104]

#: Only a skin graft can completely remove a scar, [105] <> Abinda kawai ke kawar da tabo shi ne dashen fata, [106]

#: and even then a new scar will appear along the edges of the graft. [107] <> wanda zai rufe tabon asali, amma kuma shi ma yakan haifar da wani sabon tabon. [108]

#: So until medical science comes up with something better, the majority of us will simply have to remain content with trading scar stories. [109] <> Don haka kafin lokacin da likitoci zasu samo hanyar kawar da tabo, babu abinda za mu iya yi akai sai dai bada labaran yadda aka yi muka samu namu tabon. [110]