bbchausa verticals/047 the village that survived a war

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: The village that survived a war [1] <> Kauyen da ya tsira a yaki [2]

#: Although many people still view Bosnia with trepidation, its dramatic landscapes and [3] <> Koda yake mutane da yawa na yi wa Bosnia kallon dar-dar, yanayin kasarta da kuma [4]

#: singular history are making it an increasingly popular destination. [5] <> tarihinta sun sa ta na samun karbuwa wurinyan yawon bude ido. [6]

#: This is the bridge where the war started,” [7] <> “A nan aka fara yakin,” [8]

#: said Mustafa as we crossed over the sparkling Miljacka River [9] <> in ji Mustafa a yayinda muke tsallaka kogin Miljacka [10]

#: that divides the Bosnian city of Sarajevo. [11] <> wanda ya raba birnin Sarajevo na Bosnia gida biyu. [12]

#: I had walked over this bridge before, [13] <> A baya na tsallaka wannan gadar, [14]

#: just to admire the view, [15] <> a yawon da nake na kallon gari, [16]

#: but had not realised its significance: [17] <> amma ban san muhimmancinta ba: [18]

#: on the afternoon of 6 April 1992, [19] <> A yammacin 6 ga Aprilun 1992, [20]

#: this is where snipers mowed down two young women [21] <> ‘yan bindiga su ka harbe wasuyan mata biyu [22]

#: as they joined a peace march. [23] <> a lokacin da su ke wata zanga-zangar lumana. [24]

#: Multi-ethnic strife disintegrated into full-blown war [25] <> Wannan harbin shi ya haddasa rikicin kabilancin da daga bisani ya koma cikakken yaki [26]

#: as Serbs laid siege to Sarajevo [27] <> lokacin da Sabiyawa su ka zagaye Sarajevo [28]

#: and began killing Muslims and Croats as they tried to carve out a Serb Republic. [29] <> su ka shiga hallaka Musulmi da Kuroshiyawa a kokarinsu na kafa jamhuriyar Sabiya. [30]

#: And on this day, it was the starting point of my journey with a man, [31] <> Kuma a wannan ranar, ita ce mafarin kewaye na da wani mutum, [32]

#: who like most Bosnians, has spent the two decades since the war reconstructing his peace. [33] <> wanda kamar sauran Bosniyawa, ya shafa shekaru 20 tun bayan yakin ya na kokarin samar da zaman lafiya. [34]

#: Mustafa, my guide, was only 17 when the Bosnian War began, [35] <> Mustafa, jagorana, na da shekaru 17 lokacin da yakin Bosnia ya barke, [36]

#: but he still defended his Sarajevo neighbourhood [37] <> amma dai ya shiga cikin dakarun da su ka kare unguwarsu a Sarajevo [38]

#: when Serbian forces began shelling his apartment building. [39] <> lokacin da rundunar Sabiyawa ta fara yi musu luguden wuta. [40]

#: A Bosniak, or Bosnian Muslim, [41] <> A matsayinsa na Musulmi, [42]

#: he fought alongside the Catholic Croats and Orthodox Serbs of Sarajevo [43] <> Mustafa ya hada kai da Kuroshiyawa masu addinin katolika da Sabiyawa masu kiristancin gargajiya [44]

#: against Serbian nationalists who wanted to take over all these lands to create a Greater Serbia. [45] <> domin kare kai daga Sabiyawa masu kokarin mamaye yankin domin kafa kasarsu. [46]

#: With his blue eyes, [47] <> Shudayen idanunsa, [48]

#: close-cropped hair [49] <> askakken kansa, [50]

#: and Balkan good looks, he could be his own action hero. [51] <> da kyaun halittarsa na mutanen yankin Balkan sun sa shi kama da jarimin fina-finai. [52]

#: He studied to be a dentist after the war, [53] <> Bayan yaki ya yi karatun aikin likitan hakora, [54]

#: but the cost of setting up his practice was prohibitive. [55] <> amma ya rasa jarin bude asibitinsa. [56]

#: Instead, [57] <> A madadin haka [58]

#: he became a tour guide [59] <> sai ya zama jagoran masu yawon bude ido [60]

#: who makes his living sharing the stories of war and the places of peace that his exquisite country has to offer. [61] <> inda ya kan bada labaran abubuwan da su ka faru da kuma wuraren zaman lafiya da su ka wanzu a kasarsu. [62]

#: We were headed 111km southeast of Sarajevo into the highlands to Lukomir, [63] <> Mun shirya tafiya mai nisan kilomita 111 daga Sarajevo zuwa kauyen Lukomir, [64]

#: Bosnias highest and most remote village and a little window into the countrys past. [65] <> da ke can cikin tsaunuka domin ganin rayuwar gargajiyar alummar Bosniya. [66]

#: Here, villagers still wear traditional hand-knitted clothing and tend their flocks as they have for centuries. [67] <> Har yanzu kauyawan na sanya kayan gargajiya sakar hannu kuma su na kiwon dabbobinsa bisa tsarin kaka da kakanni. [68]

#: The village was one of only two in these highlands [69] <> Kauyen na daya daga cikin kwaya biyu tak [70]

#: that survived the razed-earth offensive of the Serbian forces, [71] <> da su ka tsira daga balain dakarun Sabiya, [72]

#: who destroyed 13 such villages in the region. [73] <> wadanda su ka lalata irin wadannan kauyuka 13 a yankin. [74]

#: Lukomir meansharbour of peace”– [75] <> Sunan Lukomir na nufintudun-mun-tsira” – [76]

#: a name that has remained relevant in the historically contentious Balkan country. [77] <> sunan da ya dace da tarihin kauyen cikin yankin Bosniya mai fama da rikici. [78]

#: Its been 21 years since the end of the violence unleashed by the disintegration of the former Yugoslavia, [79] <> Shekaru 21 ke nan bayan kammala tashin hankalin da ya biyo bayan rugurgujewar tsohuwar kasar Yugoslavia, [80]

#: but the war remains a central theme for visitors and locals alike. [81] <> amma yakin shi ne babban abin tattaunawa a tsakanin mazauna kauyen da maziyartansu. [82]

#: Although many people still view the country with trepidation, [83] <> Duk da yadda mutane da yawa ke yi wa kasar kallon dar-dar, [84]

#: its dramatic landscapes [85] <> kyawun yanayin kasar [86]

#: combined with its singular history [87] <> da kuma tarihinta [88]

#: are making it an increasingly popular destination. [89] <> na sa wa a hankali masu yawon bude ido na kara tururuwa zuwa kasar. [90]

#: In fact, Mustafas bright green T-shirt said it all: [91] <> Rubutun jikin rigar Mustafa ya dunkule wannan batu inda aka rubuta: [92]

#: Have you ever heard a boring person say, ‘Lets go to Bosnia’?” it said on the front. [93] <> “Ka taba jin mara shiga hada-hada ya ce, ‘mu je Bosnia’?” [94]

#: On the back, the tongue-in-cheek response: [95] <> A bayan rigar kuma sai aka rubuta: [96]

#: Exactly. Bosnia-Herzegovina: Are you brave enough?” [97] <> “Haka ne. Bosnia-Herzegovina: Jarumtarka ta kai ka je?” [98]

#: Mustafa is one of the collaborators of Green Visions, [99] <> Mustafa na daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin jagorar masu yawon bude ido na Green Visions, [100]

#: Green Visions played a key role in the creation of the nearly 2,000km-long Via Dinarica. [101] <> Green Visions ya taka muhimmiyar rawa wurin samar da wani burtali mai tsawon kilomita 2,000 da ake kira Via Dinarica. [102]

#: This mega trail runs from Albania to Slovenia [103] <> Burtalin ya tashi ne daga Albania zuwa Slovenia [104]

#: traversing the regions principle range, the dramatic Dinaric Alps. [105] <> inda ya ratsa tsaunukan da ake kira Dinaric Alps wadanda su ka keta kasashen gabashin Turai. [106]

#: Id planned to hike a section of the trail to Lukomir, [107] <> Na so in daba sayyada akan wannan burtali zuwa Lukomir, [108]

#: but due to weather and time restraints, we opted to drive instead. [109] <> amma yanayin damina da karancin lokaci su ka tilasta min amfani da mota. [110]

#: Soon after leaving Sarajevo, [111] <> Ba mu jima da barin Sarajevo ba, [112]

#: Mustafa and I entered a pine and hardwood forest alive with wildflowers and dense, verdant growth. [113] <> ni da Mustafa mu ka shiga wani daji mai duhuwa da kyawawan furanni. [114]

#: We passed through Babin Do, [115] <> Mu ka wuce Babin Do, [116]

#: the Olympic ski resort [117] <> wato sansanin wasannin zamiyar kankara na gasar Olympics, [118]

#: where the United Nations had one of its bases during the war. [119] <> inda majalisar dinkin duniya ta kafa sansaninta lokacin yaki. [120]

#: In 1984, Mustafa told me, [121] <> Mustafa ya shaida min cewa a 1984, [122]

#: the mountains near Sarajevo were the site of the Winter Olympics, [123] <> an gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu a wadannan tsaunuka da ke kusa da Sarajevo, [124]

#: including the massif that was our destination, Bjelašnica Mountain. [125] <> ciki har da tsaunin da muka nufa wato Bjelašnica. [126]

#: Mustafa told me; Lukomir and one other, Čuhovići, which lies behind it, were the only ones to survive. [127] <> Mustafa ya shaida min cewa Lukomir da wani kauye da ke bayansa, Čuhovići, ne kawai su ka tsira. [128]

#: the Bosnian army was able to stop the Serbs on their destructive march through the region [129] <> Sojojin Bosnia sun yi nasarar tsayar da na Serbia [130]

#: before they reached Lukomir. [131] <> kafin su isa kauyukan. [132]

#: We seemed to be entering the clouds as we ascended, and finally, the tiny town emerged into view. [133] <> Hawan da mu ke yi kan tsaunin kamar muna shiga cikin hadari har dai kauyen ya bayyana. [134]

#: small stone-and-wood houses hugged the ground[135] <> Gidajen na duwatsu da itatuwa ne tare da rufin kwano[136]

#: Mustafa took me to meet a pair of the village elders[137] <> Mustafa ya kai ni wurin wasu tsofaffi a kauyen. [138]

#: indeed they are all elders here, [139] <> Tsofaffi ne dai zalla su ka rage a kauyen [140]

#: as the younger generations have gone away to the cities to seek jobs and a more modern way of life. [141] <> domin kuwa duk matasa sun shiga birane domin neman aiki da kuma rayuwar zamani. [142]

#: Fewer than 20 people live here permanently now. [143] <> Mazaunan kauyen na dindindin a yanzu ba su kai 20 ba. [144]

#: Rahima, her weathered face beaming under a knotted scarf, invited us into her small home with a smile; [145] <> Rahima, ta yi mana maraba cikin murmushi [146]

#: she wore the loose, black wool trousers and colourful knitted socks traditional to this region. [147] <> sanye da bujen wando na sakakken ulu da doguwar riga da mayafi da safar hannu. [148]

#: Her husband, Vejsil, rose to greet us; [149] <> Mijinta, Vejsil ya mike mu ka gaisa; [150]

#: he wore a black beret and orange-and-green knitted socks. [151] <> shi kuma ya na sanye da bakar hular sanyi da safa mai launin kore da ruwan goro. [152]

#: The sheepskin on the wall was a warm reminder of their shepherd past. [153] <> Buzun da ke rataye a bangon dakinsu alama ce mai nuna su makiyaya ne a baya. [154]

#: Rahima busied herself at her old cast-iron stove making traditional Bosnian coffee [155] <> Rahima ta hada mana kofi a kan rishonta na karfe [156]

#: as she and Mustafa shared stories of their children. [157] <> yayinda ita da Mustafa ke tattaunawa game dayayansu. [158]

#: She and Vejsil told us about the winters there, [159] <> Ita da Vejsil sun shaida mana cewa lokacin hunturu, [160]

#: when the deep snows render the village completely inaccessible for up to six months. [161] <> dusar kankara kan katse hanyar kauyen ba-shiga-ba-fita har tsawon watanni shida. [162]

#: For the last couple of years, [163] <> A shekarun baya-bayan nan [164]

#: theyve gone down to spend winters with their children in Sarajevo. [165] <> su kan tafi wurinyayansu a Sarajevo ne da zarar dusar kankara ta fara sauka. [166]

#: They told of the years during the war, when they were isolated for long stretchestimes were hard, but now they content themselves with the gentle rhythms of village life. [167] <> Sun ce mata lokacin yaki sun sha wuya, inda su ka yi fama da karancin kayan masarufi. [168]

#: Soon it was time for prayers, [169] <> Jim kadan lokacin sallah ya yi, [170]

#: and Vejsil excused himself to wash and prepare. We bade our farewells and passed under the Arabic blessing inscribed on the lintel. [171] <> Vejsil ya yi alwala ya yi mana sallama yayinda ya nufi masallaci. [172]

#: Rahima gave us a sweetbread and homemade feta cheese for the road. [173] <> Rahima kuma ta bamu gurasa da cukui kafin ita ma ta shiga alwala. [174]

#: We climbed up to the precipice where steccitombstone monuments of the old Bosnian kingdom [175] <> Daga nan mu ka kara hawa saman tsaunin zuwa ga kaburburan tsohuwar daular Bosnia, [176]

#: that were recognized this year as a Unesco World Heritage Sitehave lain since medieval times. [177] <> inda hukumar Unesco ta mayar daya daga cikin muhimman wuraren tarihi na duniya. [178]

#: Mustafa described to me the faraway vistas he has seen on blue-sky days, then grew quiet. [179] <> Mustafa ya ce min ya na cika da farin ciki duk lokacin da ya ziyarci wurin. [180]

#: Sometimes when the hikers are doing their thing, [181] <> “Wani lokacin idan na rako masu yawon bude ido, [182]

#: Ill just come out here and watch the clouds go by[183] <> na kan zo nan in zurawa gajimare ido[184]

#: just for the pleasure of it,” he said. [185] <> kawai domin jin dadi. [186]

#: This is my place of peace.” [187] <> Nan wurin shi ne kwanciyar hankalina.” [188]