bbchausa verticals/048 expensive drink

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Chinas ancient bushes of Da Hong Pao produce one of the most expensive teas in the world, [1] <> Itatuwan Da Hong Pao na kasar China na samar da ganyen shayin da yafi kowanne tsada a duniya, [2]

#: astonishingly costing more than 30 times its weight in gold. [3] <> wanda farashinsa ya nunka na zinariya sau 30. [4]

#: In 2002, a wealthy purchaser paid 180,000 yuanalmost $28,000[5] <> A 2002, wani mai kudi ya biya yuan 180,000kusan $28,000[6]

#: for just 20g of China's legendary Da Hong Pao tea. [7] <> domin sayen giram 20 na ganyen shayin Da Hong Pao na kasar China. [8]

#: Even in a culture thats valued tea drinking as an art form for around 1,500 years [9] <> Ko da yake shayi na da daraja a aladar China tun kimanin shekaru 1,500, [10]

#: the price was astonishing. [11] <> farashin ya isa abin mamaki. [12]

#: Original Da Hong Pao doesn't just cost its weight in gold[13] <> Ganyen shayin Da Hong Pao na asali ya nunka zinariya daraja sau 30, [14]

#: almost $1,400 for a single gram, [15] <> inda giram daya ya kai $1,400, [16]

#: or well over $10,000 for a pot. [17] <> wato tukunya daya ta zarta $10,000. [18]

#: Its one of the most expensive teas in the world. [19] <> Hakika ya na daga cikin ganyen shayi masu tsada a duniya. [20]

#: It looks fit for a beggar, but it's priced for an emperor and has the heart of the Buddha,” [21] <> “A ido kamar abin banza, amma farashinsa sai dai sarki, darajarsa sai dai Buddha,” [22]

#: said Xiao Hui, a tea maker in Wuyishan, a misty riverside town in Fujian, southern China. [23] <> in ji Xiao Hui, wata mai shayi a garin Wushiyan da ke bakin ruwa a jihar Fujian, da ke kudancin China, [24]

#: She showed me the dark, tangled, unfinished-looking Da Hong Pao leaves [25] <> yayinda ta ke nuna min ganyen Da Hong Pao masu duhu wanda ta tsinko [26]

#: from her family's tea gardens in Wuyishan. [27] <> daga lambun shayin gidansu. [28]

#: Xiao and her family, tea makers for many generations, [29] <> Xiao dayan uwanta, wadanda suka gaji sanaar shayi daga iyaye da kakanninsu [30]

#: still go into the mountains every spring [31] <> na ci gaba da ziyartar tsaunukan gari a duk damina, [32]

#: to call on the tea god, Lu Yu, to bring new shoots. [33] <> inda su ke rokon ubangijin shayi, Lu Yu, ya samar da sababbin ganyen shayin. [34]

#: Wuyishan's startling karst landscape has been famous for tea for centuries. [35] <> Garin Wuyishan ya shahara da noman shayi tsawon daruruwan shekaru. [36]

#: The rain that pours down the limestone gorges and karst pinnacles, [37] <> Ruwan saman da ke gangarowa daga tsaunukan farar kasa [38]

#: flooding the narrow mountain streams and tumbling waterfalls, [39] <> ya Malala a koramun garin, [40]

#: is heavy with minerals that impart flavor. [41] <> na cike da sinadiran da ke bai wa shayi dandano. [42]

#: Today, every other shop in Wuyishan has a tea-tasting table set [43] <> A yanzu haka duk kantin da ke Wuyishan ya na da teburin dandana shayi [44]

#: for the ritual of gong fu cha (kung fu tea) – [45] <> domin gudanar da aladar shan shayi tagong fu chan’, [46]

#: and shelves stacked with a gaudy selection of tea leaves. [47] <> sannan kuma ya na cike da ganyayen shayi iri-iri. [48]

#: Travelling to Wuyishan, I discovered that many Da Hong Pao teas are surprisingly affordable. [49] <> Da na kai ziyarar Wuyishan, na gano cewa da akwai samfuran ganyen shayin Da Hong Pao da dama da basu fi karfin talaka ba. [50]

#: Though aged or antique versions can sell for extremely high prices, [51] <> Ko da ya ke na asalin na da matukar tsada, [52]

#: a Da Hong Pao of reasonable quality can cost around $100 per kilo in Wuyishan. [53] <> ana iya sayar da Da Hong Pao mai kyau akan $100 duk kilo daya a Wuyishan. [54]

#: But every genuine Da Hong Pao [55] <> Sai dai duk wani Da Hong Pao na gaskiya [56]

#: originates with a cutting from a single group of mother trees. [57] <> ya samu asali ne daga dashen reshen bishiyun da su ka fito daga gona guda. [58]

#: And it's these original trees that produce the rare and sought-after original tea. [59] <> Kuma wadannan bishiyun na asali su ne ba su da yawa kuma ganyen shayinsu ya ke dan karen tsada. [60]

#: The original Da Hong Pao is so expensive because there are hardly any of the original tea trees left,” [61] <> “Da Hong Pao na asali na da matukar tsada ne saboda bishiyun asalin da su ka rage sun yi karanci kwarai,” [62]

#: explained local tea master Xiangning Wu. [63] <> in ji malamin hada shayi na Wuyishan, Xiangning Wu. [64]

#: But it's not just the Chinese who value Da Hong Pao. [65] <> Ba mutanen China ne kadai ke darajanta ganyen shayin Da Hong Pao ba. [66]

#: In 1849, British botanist [67] <> A 1849, wani masanin tsirrai daga Burtaniya, [68]

#: Robert Fortune came to the Wuyishan mountains on a secret mission, [69] <> Robert Fortune ya ziyarci tsaunukan Wuyishan a asirce [70]

#: part of the agro-industrial espionage at which the colonial East India Company excelled. [71] <> bisa umarnin kamfanin mulkin mallaka na East India Company domin satar basirar noman shayin Da Hong Po. [72]

#: Britons were, then, as now, obsessed with tea, [73] <> A lokacin, kamar yadda ya ke a yanzu, mutanen Birtaniya mayun shayi ne, [74]

#: and Chinafrom where the Brits also bought silk and porcelain ­– was the only place they could get it. [75] <> kuma a China ne kawai su ke iya samo shayin kamar dai yadda a can su kan samo alharini da tangaran. [76]

#: But Britain made little that China wanted, [77] <> Ga shi kuma babu wani abu da ake yi a Birtaniya da mutanen China su ke bukata, [78]

#: creating a massive trade deficit. [79] <> don haka sai ya zamo su na sayan abubuwa da yawa daga China ba tare da sun sayar da komai nasu a China ba. [80]

#: An obvious way of resolving the balance of trade was to [81] <> Hanyar da zaa magance wannan matsalar ita ce [82]

#: do what the East India Company had done with other valuable plants: [83] <> a yi abinda East India Company ya saba yi game da wasu shuke-shuken masu daraja: [84]

#: steal the seeds (or, better, cuttings) and grow them elsewhere. [85] <> a sace iri ko dashe a shuka wani wurin. [86]

#: If Britain could make its own tea in India, [87] <> Idan har Burtaniya za ta iya samar da shayinta a India, [88]

#: the nation would be that much less dependent on China. [89] <> ke nan za ta rage dogaro da China. [90]

#: But Britain couldn't. [91] <> Sai dai kuma hakan ya kasa yiwuwa. [92]

#: The tea seeds that previous spies had sourced from Guangdong simply would not grow in India. [93] <> Irin dayan leken asiri su ka samo daga yankin Guangdong a China yaki fitowa a India, [94]

#: and the native Indian tea bushes just didn't taste right. [95] <> kuma ganyen shayin India na asali sam ba shi da dadin dandano. [96]

#: Enter Fortune. [97] <> Wannan shi ne dalilin zuwan Fortune. [98]

#: His aim was to track down China's best teaDa Hong Pao[99] <> Aikin da aka ba shi, shi ne ya samo ganyen shayin da yafi kowanne daraja a ChinaDa Hong Pao[100]

#: and to learn how to grow it. [101] <> tare da koyo yadda ake shuka shi. [102]

#: And since almost all of China was closed to foreigners on pain of death, [103] <> Da yake a lokacin kusan baki dayan China ba a bari baki su shiga, wanda kuma duk ya shiga a bakin ransa, [104]

#: disguise was essential. [105] <> bad-da-kama ta zama dole. [106]

#: Fortune hired a servant, cut his hair, affixed a purchased pigtail and embarked for Wuyishan in search of Da Hong Pao. [107] <> Sai Fortune ya yanke gashin baransa, ya makala a kansa ya yi wa Wuyishan tsinke da zimmar neman Da Hong Pao. [108]

#: Just as they do today, [109] <> Kamar yadda su ke a yanzu, [110]

#: tea gardens clambered up [111] <> lambunan shayin a kan tsaunuka su ke [112]

#: and around the mountains, squeezed into the narrowest of gorges and perched on the steepest of slopes. [113] <> da cikin kwaruruwan da ke kewayensu. [114]

#: And just like today, [115] <> Kuma kamar yadda su ke yanzu, [116]

#: a handful of precious bushes balanced in a brick terrace in a vertiginous limestone face, [117] <> ya tarar dayan shukoki kadan kan wani tsaunin farar kasa [118]

#: with three Chinese characters carved in scarlet: Da Hong Pao. [119] <> wanda aka zana alamomin rubutun China guda uku a jikinsa da launin farar kasa: Da Hong Pao. [120]

#: The nameBig Red Robereferences a scarlet blanket that a mythical emperor donated long ago in thanks for a miracle cure. [121] <> Sunan, Jar alkyabba babba, ya samo asali ne daga wani jan bargo da wani sarkin China ya bayar shekaru aru-aru sakamakon warkewa daga cutar da aka yi zaton ba za ta kyale shi ba. [122]

#: Fortune took up residence in the Tianxin Yongle Temple below Da Hong Pao, [123] <> Fortune ya tare a dakin bauta na Tianxin Yongle da ke kasan Da Hong Pao, [124]

#: andamid leisurely discussions as to whether shoots picked by monkeys or virgins made the best teathe botanist acquired seeds, seedlings and the secrets of their cultivation. [125] <> inda ya shige cikin masu bauta har sai da ya samu iri da dashen shayin da kuma dabarun kula da tsironsu. [126]

#: When they reached India, [127] <> Wannan irin da ya kai India [128]

#: these seeds, merged with indigenous Indian tea, [129] <> aka hada shi da shayi dan kasa, [130]

#: would form the beginnings of an industry now worth billions of dollars a year. [131] <> shi ne tushen kasuwancin da a yanzu ya kai darajar biliyoyin dala a kowacce shekara. [132]

#: Or, as Zhe Dao, now abbot of Tianxin Yongle told me: [133] <> Kamar yadda Zhe Dao, limamin dakin bauta na Tianxin Yongle na yanzu ya shaida min: [134]

#: In the 19th Century, [135] <> “A cikin karni na 19, [136]

#: some plant hunter came and took the seeds. [137] <> wani mai farautar iri ya zo ya sami irin shayin, [138]

#: But he didn't know how to make the tea [139] <> amma bai san yadda zaa kula da shi ba [140]

#: so he needed the masters to teach him how.” [141] <> don haka ya zauna ya koya daga kwararru.” [142]

#: Tianxin Yongle was founded in 827AD. [143] <> A shekarar 827 kididdigar Kirista aka kafa dakin bautar Tianxin Yongle. [144]

#: In 1958, during the Mao era, [145] <> A 1958, lokacin mulkin Mao, [146]

#: the monks were forced out, taking their tea-making knowledge with them. [147] <> aka kori masu bautar tare da iliminsu na hada shayi. [148]

#: When Zhe arrived from the ancient city of Suzhou in 1990, [149] <> Lokacin da Zhe ya dawo daga tsohon birnin Suzhou a 1990, [150]

#: what little remained of the temple was home to peasants. [151] <> abinda ya rage na dakin bautar ya zamo gidan talakawa. [152]

#: Back then it was just me,” Zhe explained. [153] <> “Da fari ni kadai ne kurum,” in ji Zhe. [154]

#: Now I have a lot of disciples, [155] <> “Yanzu kuwa ina da almajirai da dama, [156]

#: so five or six years ago we started to make tea.” [157] <> don haka shekaru biyar zuwa shida da su ka wuce muka fara yin shayi.” [158]

#: The original Da Hong Pao trees sat on temple land, [159] <> Shukokin Da Hong Pao na asali su na gonar dakin bautar ne, [160]

#: but Zhe left their management to the government. [161] <> amma gwamnati ke kula da su. [162]

#: Production was tightly controlledthe few hundred grams [163] <> ‘Yan ganyayen da ba su fi daruruwan giram ba [164]

#: the trees yielded every year were reserved for the state[165] <> da shukokin ke samarwa na karkashin ikon gwamnati ne, [166]

#: and until recently, the trees were under constant armed guard. [167] <> kuma har ya zuwa shekarun baya-bayan nan sojoji ke gadinsu da muggan makamai. [168]

#: I walked past the monastery's vegetable gardens [169] <> Na zarta lambun kayan marmari na dakin bautar [170]

#: and up and along the narrow, winding mountain paths to the original Da Hong Pao. [171] <> na bi wani siririn burtali da ya nausa kan tsauni har zuwa inda shukokin Da Hong Pao na asalin su ke. [172]

#: The trees looked tired and spindly. [173] <> Shukokin sun bayyana alamar gajiya. [174]

#: Estimates of their age vary widely, [175] <> Babu takamaiman kiyasin shekarunsu, [176]

#: although 350 years gels with Fortune's account. [177] <> amma dai in aka tuni da labarin Fortune, tabbas sun fi shekaru 350. [178]

#: It was hard to imagine these straggly bushes bursting with new growth. [179] <> Zai yi wuya wadannan shukokin su ci gaba da fitar da ganyen shayi. [180]

#: On 1 May, soon after the tea harvest begins, [181] <> A ranar 1 ga Mayu, da zarar an fara girbe ganyen shayi, [182]

#: a red carpet will be rolled out to mimic the emperor's gift. [183] <> zaa shimfida jar darduma domin tunawa da kyautar tsohon sarki. [184]

#: Beautiful women dressed in traditional costume will ascend the mossy steps and perform a ritual. [185] <> Kyawawan mata sanye da kayan gargajiya za su gudanar da wata ibada a wurin. [186]

#: But there will be no harvest. [187] <> Sai dai babu wani girbi da zaa yi musu. [188]

#: These precious, ancient bushes, last harvested in 2005, [189] <> Rabon da wadannan shukoki masu daraja su samar da ganye tun 2005, [190]

#: will likely never make tea again. [191] <> kuma mai yiwuwa ba za su sake bayar da ganyen shayi ba. [192]

#: Which means the scattered few grams collectors are lovingly storing, [193] <> Hakan na nufin kwayakin ganyayen da su ka rage hannun mutane, [194]

#: drying them each year [195] <> wadanda kan shanya su duk shekara [196]

#: to mature their flavour, [197] <> domin kara ingantan dandanonsu [198]

#: will be more valuable than ever before. [199] <> za su ci gaba da kara hauhauwa a farashi. [200]

#: Perhaps as expensive as diamonds, given time. [201] <> Mai yiwuwa ne ma wata ran darajarsu ta kai darajar duwatsun daimon! [202]