bbchausa verticals/052 pilotless airliner

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Would you fly in a pilotless airliner [1] <> Ko za ka shiga jirgin sama da ba shi da matuƙi? [2]

#: Driverless trains and cars are already with usbut how soon before pilotless airliners? [3] <> Ko yau she za'a fara ganin jiragen sama marasa matuƙa? [4]

#: The biggest challenge may be getting passengers on board. [5] <> N/A [6]

#: Have you ever had a panic attack in mid-flight? [7] <> Ko ka taɓa firgita a yayin da jirgin sama ya lula da kai sama? [8]

#: Those that have [9] <> Ga duk wadanda suka taɓa shiga cikin irin wannan yanayi [10]

#: will tell you its not fun. [11] <> zasu shaida maka cewa ba abun dariya ba ne. [12]

#: And there are plenty of reasons that make people panic. [13] <> Kuma akwai dalilai da dama da su ke sa mutane firgita. [14]

#: Some of themirrationally sofixate on the state of the pilot. [15] <> Wasu mutane tun farko dama matsorata ne saboda yanayin matuƙin jirgin, [16]

#: Are they tired? Stressed? [17] <> inda suke tunanin ko matuƙin jirgin yana cikin yanayi na gajiya? [18]

#: Paying enough attention? [19] <> Ko yana lura kuwa? [20]

#: Would these people feel any better if we could get rid of pilots altogether? [21] <> Shin ko irin wadannan mutanen za su fi jin dadi idan aka daina amfani da matuƙa jirgin sama kwata-kwata? [22]

#: The technology already seems to be there[23] <> Tuni dai aka samu wannan fasahar- [24]

#: drones are not a particularly new invention. [25] <> saboda jiragen sama marasa matuƙa ba sabon abu bane yanzu. [26]

#: Armies use drones the size of aeroplanes in war zones, [27] <> Sojoji na amfani da irin wadannan jirage a wuraren da ake fama da yake-yake [28]

#: where they are controlled remotely or loiter flying a pattern. [29] <> inda ake sarrafa su da wata na'urar tafi da gidanka. [30]

#: Even helicopters can be pilotless, like the K-MAX, [31] <> Hatta jiragen sama masu saukar ungulu za su iya kasance wa babu matuƙa, kamar jirgin sama ƙirar the K-MAX, [32]

#: which is as big as a standard helicopter, [33] <> wanda shi ne babban jirgi mai saukar ungulu [34]

#: and delivers aid supplies with stunning precision [35] <> da ake amfani dashi wajen kai kayayyakin agaji [36]

#: to dangerous locations. [37] <> a wuraren da ake bukata wadanda kuma suke da hadari. [38]

#: Aeroplane accidents are rare today, [39] <> Hadurran jiragen sama ba kasafai su ke faruwa, [40]

#: but when they happen, [41] <> amma a duk lokacin da suka faru, [42]

#: they are getting harder and harder to solve, says Tim Robinson, [43] <> su kan yi wahalar shawo kan su, in ji Tim Robinson, [44]

#: editor-in-chief of the Royal Aeronautical Societys magazine Aerospace. [45] <> babban edita mujallar ƙungiyar matuƙa jirgin sama ta Royal Aeronautical Society's. [46]

#: Thats why investigations often [47] <> Wannan yasa binciken da ake gudanarwa [48]

#: focus onhuman factors’, [49] <> ya karkata ta fuskar ajizanci na dan adam [50]

#: identifying psychological and physiological issues as a probable cause. [51] <> a matsayin wasu daga cikin dalilan da kan janyo hadurran. [52]

#: So with pilots relying on autopilots for 95% of today's flights, [53] <> Yayin da matuƙa jirgin sama suka dogara ga amfani da nu'rar da jirgin ke tuƙa kansa a cikin kashi 95 cikin 100 na zirga-zirga ta jiragen sama, [54]

#: the argument goes, [55] <> muhawarar da ake yi ita ce, [56]

#: why not make the final 5% – take-off and landingautomated?” says Robinson. [57] <> ko me zai hana a cike kashi 5 cikin 100 na amfani da wannan na'urar wajen tashi da saukar jiragen? In ji Robinson. [58]

#: Computers fly ultra-precise, repeatable trajectories, [59] <> 'Na'urar kwamfuta na iya tashin jirgin sama tare da bin tsari daidai inda ake so, [60]

#: do not fly drunk, [61] <> amma ba cikin wani yanayi na magiya ba sakamakon shan barasa, [62]

#: do not get tired, do not get distracted [63] <> babu wani tsaiko [64]

#: and so the thinking goes could be safer than human pilots in the future.” [65] <> wanda hakan yasa wasu ke ganin ya fi tuƙin jirgi da mutum zai yi a nan gaba. [66]

#: He says that in a debate at the society earlier this year, [67] <> 'Ya ce a wata muhawara da aka yi a ƙungiyar matuƙa jirgin sama a farkon wannan shekarar [68]

#: with pilots, engineers, scientists and airline representatives debating autonomous planes, [69] <> tsakanin matuƙa jirgin sama da injiniyoyi da masana kimiyya tare da wakilan kamfanonin jiragen sama, [70]

#: the motionthere will be no need for pilots in 40 yearswas carried by approximately 60 votes to 40. [71] <> an kawo ƙudirin cewa ' ba za'a buƙaci matuƙa jirgi ba nan da shekaru 40 masu zuwa' inda aka samu ƙuri'u 60 na goyon baya yayin da 40 basa goyon baya. [72]

#: At the Consumer Electronics Show (CES) in Las Vegas in January, [73] <> A wani bukin baje koli na masu amfani da kayayyakin latoroni da aka yi a Las Vegas a watan Janairu, [74]

#: Chinese company Ehang unveiled the first-ever passenger drone, the electric-powered [75] <> kamfanin ƙasar Sin mai suna Ehang ya fitar da wani jirgin sama na fasinja wanda shine na farko da bashi da matuƙi da ke amfani da wutar lantarki. [76]

#: The Ehang 184 quadrocopter can fit one person with a small backpack, [77] <> Jirgin ƙirar Ehang 184 na daukar mutum daya da jakar hannu guda daya [78]

#: and even has air conditioning and a light. [79] <> kuma yana da na'urar sanyaya wuri da kuma hasken lantarki. [80]

#: To fly, [81] <> Domin tafiya a jirgin, [82]

#: the passenger needs to set up a flight plan, clicktake off[83] <> fasinja na buƙatar tsara wuraren da zai je ya kuma latsa 'tashi' [84]

#: andlandon a tablet, [85] <> da kuma 'sauka' a naurar kwamfuta ta tafi da gidanka [86]

#: and the computer does the rest. [87] <> inda daga nan sai kwamfuta ta ci gaba da sauran. [88]

#: With its propellers folded, the 184 takes up as much room as a small car. [89] <> Yayin da aka nade farfelar sa, jirgin kirar 184 nada fili kamar mutum yana cikin wata karamar mota. [90]

#: There are other similar efforts to develop personal air transport systems. [91] <> Akwai kuma wasu shirye shirye da ake yi na bunkasa hanyar sufurin jirgin sama na kashin kai. [92]

#: In the US, a twin-propeller experimental plane with two passenger seats and two cockpit seats was flight-tested last year. [93] <> A Amurka, bara ne aka yi wani gwajin jirgin sama mai farfela biyu tare da fashinjoji biyu. [94]

#: Made by Aurora Flight Sciences Corp and called the Centaur, [95] <> Jirgin da kamfanin Aurora Flight Sciences Corp ya ƙirkiro mai suna the Centaur, [96]

#: it can be operated by pilots from the cockpit or from the ground[97] <> ana iya tafiyar da shi daga cikin jirgin ko kuma daga waje, [98]

#: and during the test, it successfully flew with no one on board. [99] <> kuma a lokacin gwajin, jirgin ya tashi ya kuma sauka ba tare da kowa ya shiga cikin sa ba. [100]

#: Airbus Group is working on Vahana, [101] <> Kamfani Airbus Group na aiki don ƙera Vahana, [102]

#: an autonomousflying car[103] <> wata mota mai tashi sama kamar jirgi [104]

#: for passengers or cargo, [105] <> domin daukar fasinja ko kuma dakon kayayyaki [106]

#: while in Germany [107] <> yayin da kuma a Jamus [108]

#: the Volocopter project hopes to build ascaled-updrone that can carry one or two people. [109] <> shirin Volocopter ke fatan ƙera wani jirgi da bai da matuƙi da zai iya daukar mutane biyu. [110]

#: Another European endeavour, myCopter, [111] <> Har ila yau, wani ƙokari daga nahiyar turai shine na myCopter, [112]

#: looked into the kind of technologies that would be needed to bring personal transportation into the air. [113] <> wanda ke duba irin fasahar da ake bukata don samar da sufurin jirgin sama ga masu bukata. [114]

#: Researchers who took part in the project, [115] <> Masu bincike da suka yi aiki a wannan shiri [116]

#: from the Max Planck Institute for Biological Cybernetics in Tübingen, [117] <> daga cibiyar Max Planck da ke Tübingen, [118]

#: are still trying to figure out how to make it easier to control, says Heinrich Bülthoff, [119] <> na ci gaba da ƙokarin gano yadda za'a iya sarrafa shi cikin sauki, in ji Heinrich Bülthoff, [120]

#: the managing director of the institute. [121] <> direktan cibiyar. [122]

#: We try to make flying a helicopter as easy as driving a car [123] <> muna ƙokarin muga jirgin sama mai saukar ungulu ya tashi cikin sauki kamar dai yadda ake tuka mota [124]

#: with very little training,” he says. [125] <> ta hanyar samun horo ba mai zurfi ba', inji Heinrich. [126]

#: In the UK, similar research was undertaken [127] <> A Burtaniya an gudanar da wani bincike makamancin wannan [128]

#: by a consortium of public and private companies called Astraea; [129] <> da gamayyar wasu kamfanoni na al'umma da masu zaman kansu da ake kira Astraea; [130]

#: in 2013 they received £62m [131] <> inda a shekarar 2013 aka ware musu Fam miliyan £62 [132]

#: to investigate civilian pilotless aircraft concepts. [133] <> domin su gudanar da bincike akan shirin jirgin sama marasa matuƙa. [134]

#: The aim was toinvestigate the kind of technologies you would need, [135] <> Manufar dai itace binciko irin fasahar da ake bukata, [136]

#: such as sense and avoid, secure communications and so on, [137] <> kamar tunani da kuma sadarwar da sauran su, [138]

#: to integrate UAVs into manned airspace,” says Robinson. [139] <> domin hada su wuri guda- inji Robinson. [140]

#: But be it a plane thats controlled remotely, or by an artificial intelligence system, [141] <> Sai dai kasancewar sa jirgin da ake sarrafa shi da na'ura daga wani wuri [142]

#: whether its just a passenger pressing a button, [143] <> ko kuma fasinja ne zai latsa wani wuri [144]

#: or a ground crew pulling the wireless strings, [145] <> ko kuma wasu ne dake ƙasa zasu riƙa jan zare da zai sarrafa jirgin. [146]

#: one fundamental question hasnt been answered yet: [147] <> Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da har yanzu ba'a kaiga bada amsarta ba. [148]

#: Would we feel at ease flying [149] <> Shin ko za'a iya samun natsuwar yin tafiye-tafiye a jirgin sama [150]

#: if we cant see two smartly dressed pilots at the helm, calmly providing us with weather updates during a storm? [151] <> idan ba'a ganin matuƙa jirgi su biyu suna tafiyar da jirgin tare da yiwa fasinjoji bayanin yanayi a lokacin da hazo ko kuma rashin kyawun yanayi ya yi kamari? [152]

#: These days nobody thinks twice before getting into a lift[153] <> A 'yan kwanakin nan babu wanda ke tunani kafin ya shiga cikin na'urar lifta dake kai mutum saman bene, [154]

#: even though decades ago [155] <> duk da cewa a shekarun baya, [156]

#: theirsafeoperation required an operator [157] <> rashin abkuwar hadarin amfani da Lifta ya danganta ne ga samun mutumin dake sarrafa na'urar a cikin sa. [158]

#: It appears that [159] <> Bisa ga dukkan alamu, [160]

#: people are more comfortable [161] <> jama'a sun fi samun natsuwa [162]

#: with a pilot directly at the controls, and on the plane,” [163] <> idan akwai matuƙin jirgin da ke tafiyar da al'amura kai tsaye a jirgin sama, [164]

#: says aeronautics expert Stephen Rice, [165] <> a cewar masani kan tuƙin jirgin sama Stephen Rice. [166]

#: formerly at the Florida Institute of Technology and now at Embry-Riddle Aeronautical University, who co-authored a 2014 report on public perception of robotic flights. [167] <> N/A [168]

#: But computers also dont suffer the kind of mental stress [169] <> Amma na'urorin kwamfuta basa fuskantar matsaloli [170]

#: which leads to incidents such as co-pilot Andreas Lubitz, [171] <> dake janyo hadurra kamar yadda mataimakin matuƙin jirgi Andreas Lubitz, [172]

#: who in 2015 flew a Germanwings passenger jet into a mountain in the French Alps. [173] <> wanda a shekarar 2015 ya jefa wani jirgin saman fasinja na kasar Jamus kan wani tsauni a Faransa. [174]

#: Unmanned planes could potentially prevent such incidents, thinks Rice. [175] <> Jiragen sama da basu da matuƙa babu yadda za'a yi su iya kaucewa abkuwar irin wadannan hadurran kamar yadda Rice ke cewa. [176]

#: This is not to malign human pilots[177] <> "Ba wai don a nuna rashin kwarewa ba ga matuƙa jirgi, [178]

#: No autopilot today could have landed the plane on the Hudson River. [179] <> babu wata nau'rar dake tuƙa jirgi da zata iya sauke jirgi a Tekun Hudson. [180]

#: But a machine doesnt get tired, doesnt get emotional, [181] <> Koda yake nau'rori basa fuskanta fargaba [182]

#: doesnt let fear or fatigue affect its performance, [183] <> ko gajiya da ka iya shafar aikin su [184]

#: and doesnt make poor decisions. [185] <> kuma basa kuskure wajen zartar da hunkunci, [186]

#: It simply does what its programmed to do. [187] <> na'urori kan yi abun da aka bukace su ne kawai. [188]

#: So, in the long run, I believe they will be safer overall.” [189] <> A don haka nan gaba zasu fi inganci ga kowa kowa da kowa. [190]

#: Michael Clamann, Duke University [191] <> Sai dai a cewar Michael Clamann, na jami'ar Duke, [192]

#: Some complex problems may be difficult to diagnose from the ground, [193] <> zai yi wahala a yi gano tare da magance wasu matsaloli daga kasa [194]

#: without direct access to all the planes systems. [195] <> ba tare samun damar isa ga kowane bangare na jirgin sama ba. [196]

#: But not everyone agrees. [197] <> Amma ba kowa ya amince da hakan ba. [198]

#: Michael Clamann, research scientist at the Humans and Autonomy Lab at Duke University in Durham, North Carolina, [199] <> Michael Clamann, wani masanin kimiyya a jami'ar Duke da ke Durham, arewacin Carolina, [200]

#: thinks the level of safety will be about the same. [201] <> na ganin yanayin kaucewa hadurra kusan duk iri daya ne. [202]

#: While its true that there have been rare cases of pilots purposefully crashing planes [203] <> Yayin da gaskiya ne akwai wasu lokuta ƙalilan da ake samun matuƙin jirgi ya kifar da jirgi da gangan, [204]

#: (or making grave mistakes), [205] <> ko kuma ya yi wani babban kuskure, [206]

#: there are also examples of pilots preventing disasters through creative problem solving. [207] <> akwai kuma wasu misalai da matuƙa jirgi kan hana abkuwar wani bala'i ta hanyar samar da yanayi na warware matsala. [208]

#: Robinson believes that the first step to remove pilots on commercial airliners could be to do it gradually. [209] <> Robinson na ganin matakin farko na janye matuƙa a jiragen sama masu daukar fasinjoji shine a fara sannu a hankali. [210]

#: For instance, a European research project called Across (Advanced Cockpit for Reduction Of Stress and Workload) on future passenger aircraft flight decks [211] <> Misali, wani bincike da ake gudanar wa a nahiyar turai [212]

#: is looking into thereduced crewoperations with just one pilot. [213] <> na duba yiwuwar rage adadin ma'aikatan dake aiki a cikin jirgi tare da barin matuƙi jirgi daya kawai a ciki. [214]

#: Two decades ago, [215] <> Shekaru 20 da suka gabata, [216]

#: it was standard to have three pilots in the cockpit; [217] <> ƙa'ida ne a samu matuƙa su uku a cikin jirgi [218]

#: now the standard is to have two, [219] <> amma yanzu an rage ƙa'idar zuwa matuƙa biyu, [220]

#: says Scott Winter, assistant professor of aeronautics at Florida Institute of Technology. [221] <> in ji Scott Winter, wani mataimakin Farfesa a cibiyar nazarin fasaha dake Florida. [222]

#: Even if it works, [223] <> Koda kuwa ya yi aiki, [224]

#: there will still be one nagging worry: [225] <> akwai wani batu mai cike da sarƙaƙiya, [226]

#: the risk of the unmanned plane getting hacked [227] <> hadarin yiwuwar yin kutse a na'urorin jirgin sama da bai da matuƙi. [228]

#: Ground systems [229] <> Na'urorin da ake da su a ƙasa [230]

#: would have to have highly secure datalinks and potentially military-level cybersecurity, thinks Robinson. [231] <> tilas su kasance akwai kariya ta musamman ta fuskar tsaro kamar yadda Robinson ke cewa. [232]

#: Clamann adds that it would be necessary to have not only preventive [233] <> Clamann ya ƙara da cewa akwai bukatar a samu hayoyin hana abkuwar hakan [234]

#: but also recovery measures[235] <> da kuma hanyoyin kubutarwa [236]

#: to stop an attack from happening [237] <> domin kaucewa kai hari [238]

#: andrescuethe aircraft during a hack. [239] <> tare da ƙwato jirgin idan aka yi kutse a na'urorin sa. [240]

#: So maybe in a few decades, [241] <> A don haka mai yiwuwa nan da wasu shekaru masu zuwa, [242]

#: youll be sipping your wine in the lounge where the cockpit used to be. [243] <> zaka riƙa shan shayi a wurin da matuƙa jirgi kan zauna. [244]

#: Until then, [245] <> Amma kafin lokacin, [246]

#: be prepared to listen to your captains updates, [247] <> ka shirya ci gaba da jin bayanai na matuƙin jirgi [248]

#: and know that [249] <> tare da sanin cewa [250]

#: theyre seeing the same view out of the window as you are[251] <> suna ganin abun da kake gani ta tagar jirgi, [252]

#: but theyre just in the best seat. [253] <> koda yake kujerar da suke zaune ta fi taka. [254]