bbchausa verticals/062 pyramid in mountain

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: The giant pyramid hidden inside a mountain [1] <> Gagarumar dalar da aka boye cikin tsauni [2]

#: This temple at Cholula dwarfs the Great Pyramid at Giza, [3] <> Dalar Cholula ta kere wa babbar dalar da ke Giza, [4]

#: yet it went unnoticed by Spanish invaders. Why? [5] <> amma turawan mulkin mallaka na Spaniya ba su lura da ita ba. Me ya sa haka? [6]

#: They arrived in their thousands. Hardened by months of war with ferocious natives, near-starvation and exotic diseases, Hernan Cortez and his Spanish army marched into the great city of Cholula expecting a fight. [7] <> Lokacin da Hernan Cortez ya jagoranci dubun dubatar dakarun Spaniya zuwa babban birnin Cholula, bayan fama da baraden mayaka da yunwa da kuma cututtuka, ya yi zaton zai fuskanci gagarumar rundunar yaki. [8]

#: But this was a sacred city. [9] <> Sai dai kuma birnin, cibiyar addini ne. [10]

#: Instead of investing in weapons, [11] <> Maimakon makamai, [12]

#: its inhabitants built temples; [13] <> mazaunansa dakunan ibada su ka tanada; [14]

#: it was said they had a holy pyramid for every day of the year. [15] <> an ce sun gina dalar bauta adadin kwanakin shekara. [16]

#: After such generosity, their gods would surely protect them. [17] <> Don haka sun yi Imani allolinsu za su iya kare su daga kowanne sharri. [18]

#: October 12th 1519 was a bloodbath on an unprecedented scale, leaving 10% of the citys population dead [19] <> 12 ga Oktoban 1519 mummunar rana ce a tarihin Cholula domin kuwa sai da aka kashe kaso 10% na mazaunan birnin. [20]

#: This was a grave error indeed. [21] <> A nan kam sun tafka kuskure. [22]

#: As the army stormed its streets, [23] <> Rundunar ta sojojin Spaniya ta mamaye birnin [24]

#: religious treasures were looted [25] <> tare da wawashe dakunan bautarsu [26]

#: and the precious pyramids went up in smoke. [27] <> da kuma rushe dalolin da su ka gina. [28]

#: Within three hours they had murdered 3,000 people. [29] <> Cikin sa'o'i uku, Spaniyawa sun hallaka mutane 3,000. [30]

#: Eventually the Spaniards settled in Cholula [31] <> Daga nan ne Spaniyawa su ka karbe birnin Cholula [32]

#: (now part of Mexico), [33] <> (wanda yanzu ya ke cikin Mexico), [34]

#: erecting enough of their own buildings [35] <> inda su ka yi na su gine-ginen [36]

#: that the city is now known for having a church for every day of the year. [37] <> har birnin ya zama ya na da coci-coci adadin kwanakin shekara. [38]

#: The final touch[39] <> Abu na karshe da su ka yi[40]

#: a symbol of their Christian conquest[41] <> wanda ke alamta Kiristanci ya yi nasara a birnin[42]

#: is the Iglesia de Nuestra Señora de los Remediosa, [43] <> shi ne gina cocin Iglesia de Nuestra Señora de los Remediosa, [44]

#: built on what they thought was a large hill. [45] <> a bisa abinda su ka yi tsammanin wani babban tudu ne. [46]

#: But not all is as it seems. [47] <> Sai dai ba haka lamarin ya ke ba. [48]

#: Beneath the tiny church, [49] <> Karkashin mitsitsin cocin, [50]

#: hiding under tufts of grass, trees and soil, [51] <> a boye a cikin turbaya da ciyayi, [52]

#: is an ancient pyramid of truly gigantic proportions. [53] <> akwai wani tsohon ginin dala mai matukar girman gaske. [54]

#: Standing 450 metres wide and 66 metres tall, from end to end the Great Pyramid of Cholula [55] <> Babbar Dalar Cholula mai fadin mita 450 da tsayin mita 66 [56]

#: is equivalent to nine Olympic sized swimming pools. [57] <> ta kai girman kwamin ninkaya irin wanda ake gasar Olympics a ciki har guda tara. [58]

#: For an obscure temple no ones heard of, Cholula holds an impressive array of records: [59] <> Boyayyar dalar Cholula, wacce mafi yawan mutane ba su ma san da zamanta ba, [60]

#: its the largest pyramid on the planet, [61] <> ita ce ginanniyar dalar da tafi kowacce girma a duniya, [62]

#: with a base four times larger than the Great Pyramid at Giza and nearly twice the volume. [63] <> inda ta nunka Babbar Dalar da ke Giza sau hudu a fadi, kuma sau biyu a tsayi. [64]

#: Never mind the largest pyramidits the largest monument ever constructed anywhere, by any civilisation, to this day. [65] <> Kai bar ta dala - babu wani gini a duniya, da aka yi a kowanne irin zamani, har yau din nan da ya kai girmanta. [66]

#: To locals its aptly known as Tlachihualtepetl ("man-made mountain”). [67] <> Mutanen garin kan kira ta Tlachihualtepetl ("tsauni ginin-mutum"). [68]

#: Thanks to the church on top, [69] <> Sakamakon cocin da aka gina a samanta, [70]

#: its also the oldest continuously occupied building on the continent. [71] <> kuma ita ce ginin da aka fi dadewa ana amfani da shi a gaba daya nahiyar Amurka. [72]

#: The story goes that until the locals began construction of an insane asylum in 1910, nobody knew it was a pyramid. [73] <> Ba wanda ya san da zaman dalar, sai da aka fara ginin asibitin mahaukata a 1910. [74]

#: Certainly, by the time Cortéz and his men arrived, [75] <> Ko a lokacin da Cortez da dakarunsa suka isa Cholula, [76]

#: it was already a thousand years old [77] <> dalar tafi shekaru dubu guda [78]

#: and entirely concealed by vegetation. [79] <> kuma ciyayi sun rufe ta ruf. [80]

#: Early excavations [81] <> Da aka fara hakarta, [82]

#: revealed a series of gruesome findings, [83] <> an ga abubuwan tashin hankali ciki [84]

#: including the deformed skulls of decapitated children. [85] <> har da kawunan yaran da aka sassare. [86]

#: Where did it come from? [87] <> Menene asalin dalar? [88]

#: And why did it stay hidden for so long? [89] <> Kuma me ya sa ta dade a boye? [90]

#: Despite its enormous size, [91] <> Duk da wannan makeken girman na ta, [92]

#: very little is known about the pyramids early history. [93] <> babu tartibin bayanin asalin dalar. [94]

#: Its thought construction began around 300 BC; [95] <> Ana jin dai an fara gina ta shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa; [96]

#: by who exactly remains a mystery. [97] <> wa ya gina ta? Nan fa daya! [98]

#: According to myth it was built by a giant. [99] <> Mutanen Cholula na cewa wani katon mutum ne ya gina ta. [100]

#: Most likely, [101] <> Abinda zai fi karbuwa shi ne, [102]

#: the citys inhabitantsknown as the Cholutecawere a cosmopolitan mix. [103] <> mazaunan birnin a shekaru aru-aru sun fito ne daga sassa daban-daban. [104]

#: It appears to have been multi-ethnic, [105] <> "Da alamu akwai kabilu da yawa, [106]

#: with a great deal of migration,” [107] <> tare da yawan kaura," [108]

#: says David Carballo, an archaeologist at Boston University, Massachusetts. [109] <> in ji David Carballo, mai nazarin kayayyakin mutan da a jami'ar Boston da ke Massachusetts. [110]

#: Whoever they were, [111] <> Ko ma dai su waye su ka gina dalar, [112]

#: they probably had a lot of money. [113] <> da alama su na da tarin kudi. [114]

#: Cholula is conveniently located in the Mexican highlands and was an important trading post for thousands of years, [115] <> Cholula na kan tsaunukan Mexico ne kuma cibiyar cinikayya ce tun shekaru masu nisa, [116]

#: linking the Tolteca-Chichimeca kingdoms in the North with the Maya in the South. [117] <> inda ta zama zango tsakanin daulolin Tolteca-Chichimeca da ke arewa da Maya da ke kudu. [118]

#: Cortez called it "the most beautiful city outside Spain”. [119] <> Cortez ya kira Cholula "birnin da yafi kowanne kawai a wajen kasar Spaniya". [120]

#: By the time he arrived, [121] <> A lokacin da ya isa birnin, [122]

#: it was the second-largest city in the Aztec empire, [123] <> shi ne na biyu a girma a daular Aztec, [124]

#: though it had already exchanged hands numerous times. [125] <> ko da yake dauloli dabam-daban sun mulki birnin a baya. [126]

#: And here there are even more surprises. [127] <> Wani kuma abin karin mamaki game da dalar shi ne [128]

#: In fact its not one pyramid at all, [129] <> ba gini daya bane kadai. [130]

#: but a great Russian doll of a construction, consisting of no less than six, [131] <> Dalar guda shida ce; [132]

#: one on top of the other. [133] <> wata a cikin wata, [134]

#: It grew in stages, as successive civilisations improved on what had already been built. [135] <> inda 'ya'ya ke kara gini akan abinda su ka tarar na iyayensu. [136]

#: They made a conscious effort to maintain and [137] <> "Sun yi kokarin su ga sun kare gine-ginen baya [138]

#: in some cases display previous construction episodes. [139] <> inda su ke dora na su ba tare da rushe wancan ba. [140]

#: This is pretty novel, and shows deliberate efforts to link to the past,” says Carballo. [141] <> Wannan sabon abu ne a tarihin gini a duniya, wanda ke nuna yadda su ke danganta kansu da tarihin baya," in ji Carballo. [142]

#: According to legend, when they heard the conquistadors were coming, [143] <> An ce wai lokacin da mutanen birnin su ka ji labarin dakarun Spaniya sun musu tsinke, [144]

#: the locals covered the precious temple with soil themselves. [145] <> sai su ka lullube dalar da turbaya. [146]

#: In fact it may have happened by accident. [147] <> Sai dai masana na ganin, kasa ta rufe ginin ne kadan da kadan. [148]

#: Thats because, incredibly, the largest pyramid in the world [149] <> Saboda kuwa, abin mamaki shi ne, wannan dalar da tafi kowacce girma a duniya, [150]

#: is made of mud. [151] <> da tabo aka yi ta. [152]

#: Adobebricks are made by mixing mud with other materials such as sand or straw, and [153] <> Tubalin da aka yi ginin na tabo ne da aka cakuda da harawa, [154]

#: baking it hard in the sun. [155] <> sannan aka gasa a rana. [156]

#: To make the pyramid, [157] <> A lokacin ginin dalar, [158]

#: the outer bricks were smoothed with more earth [159] <> an shafa wa tubalan waje turbaya [160]

#: to create a painting surface. [161] <> domin su yi santsi su yi luwai-luwai. [162]

#: In its prime, the temple was covered in red, black and yellow insects. [163] <> Haka kuma an yi wa dalar ado da kwari jajaye, da bakake da kuma ruwan dorawa. [164]

#: In dry climates, [165] <> A busassun kasashe, [166]

#: mud bricks are extremely durable[167] <> tubulin kasa na dadewa sosai[168]

#: lasting thousands of years. [169] <> inda ya kan kai dubunnan shekaru. [170]

#: In humid Mexico, the mud creation was a fertile platform for tropical jungle. [171] <> A kasar Mexico, mai laima kuwa, ginin na tubulin tabo sai ya zamo mafakar ciyayi. [172]

#: It was abandoned sometime in the 7th or 8th Century CE. [173] <> "A cikin karni na 7 zuwa na 8 na kalandar Kirista ne aka daina amfani da dalar. [174]

#: The Choluteca had a newer pyramid-temple located nearby, [175] <> Mutanen Cholula sai suka gina wata sabuwar dalar a kusa da wurin, [176]

#: which the Spaniards destroyed,” says Carballo. [177] <> wacce dakarun Spaniya su ka rusa," in ji Carballo. [178]

#: The pyramid also had topography in its favour; [179] <> Haka kuma dalar ta yi dacen matsuguni; [180]

#: the pyramid rests on a natural platform in an area which is almost completely mountainous. [181] <> domin kuwa an gina ta ne a cikin kwarin da ke tsakanin wasu manyan tsaunuka. [182]

#: Today the city has reclaimed their pyramid, [183] <> Yanzu dai mutanen birnin sun sake tono dalarsu, [184]

#: which can be explored via over five miles of tunnels [185] <> wacce akan ziyarce ta ta hanyar amfani da ramuka masu nisan fiye da mil biyar, [186]

#: constructed in the early 20th Century. [187] <> wadanda aka haka a farkon karni na 20. [188]

#: Nearly 500 years after the colonial conquest, [189] <> Kimanin shekaru 500 bayan mamayar dakarun mulkin mallaka, [190]

#: the city must contend with a new invasion: tourists. [191] <> yanzu birnin na fama da wasu maziyartan: 'yan yawon bude ido. [192]