bbchausa verticals/063 living in darkness

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: How it feels to live in darkness [1] <> Yadda ake rayuwa cikin makanta [2]

#: The Dialogue in the Dark exhibition in Israel [3] <> Nunin rayuwa cikin makanta mai taken Dialogue in the Dark da ake gabatarwa a Isra'ila [4]

#: aims to bridge the understanding between sighted and blind people. [5] <> na da burin kyautata alaka tsakanin mutane masu ido da kuma makafi. [6]

#: BBC Future visits the museum to learn about the ways the brain can adapt to life without vision. [7] <> Wakiliyar BBC Tiffanie Wen ta ziyarci cibiyar da ake nunin domin koyon hanyoyin da kwakwalwa kan sauya domin rayuwa ba idanu. [8]

#: I know there isnt one dot of light, [9] <> Na san ba ko digon haske, [10]

#: but I frantically scan the pitch-black area surrounding me out of habit nonetheless. [11] <> amma duk da haka na shiga lalube cikin bakin duhu saboda sabo da yi. [12]

#: As I shuffle slowly through the carpeted hallway, [13] <> A lokacin da nake tattakawa a hankali cikin dakin da ke shimfide da darduma, [14]

#: clumsily swinging my long cane in a small arch [15] <> tare da dogara sandata [16]

#: the way the guide instructed a minute ago, [17] <> irin yadda jagoranmu ya koya min minti guda da ya wuce, [18]

#: I can hear the sounds of exotic birds, [19] <> ina iya jin saututtukan tsuntsaye, [20]

#: the rustle of wind through the trees [21] <> da motsin iska na karkada ganyaye tare [22]

#: and a babbling brook just around the corner. [23] <> kuma da kwararar korama a kusa da ni. [24]

#: After stumbling through a doorway, [25] <> Bayan da na yi tuntube da dokin kofa, [26]

#: the flat carpet suddenly gives way to a hill covered in rocks. [27] <> sai nai sallama da darduma na fito wani fili mai kwazazzabo. [28]

#: The breeze hits my face [29] <> Wata kakkarfar iska ta fara bugun fuskata [30]

#: and the cacophony of an artificial forest is everywhere. [31] <> yayin da saututtukan daji su ka kewaye ni ta ko'ina. [32]

#: Okay kids! [33] <> "To yara! [34]

#: Were in the nature now. [35] <> Yanzu mun shigo daji. [36]

#: What can you find?” [37] <> Me ku ke iya ganowa a nan?" [38]

#: says our guide, [39] <> in ji jagoranmu, [40]

#: 45-year-old Meair Mattityahu, [41] <> Meair Mattityahu, dan shekaru 45, [42]

#: who lost his sight shortly after birth. [43] <> wanda ya makance jim kadan bayan haihuwarsa. [44]

#: I found a tree!” [45] <> "Na gano bishiya!" [46]

#: shouts an 11-year old girl visiting with her family from New York. [47] <> in ji wata yarinya 'yar shekara 11 wacce ta zo tare da iyayenta daga New York. [48]

#: Im still lagging behind the group, standing a few feet from the entrance on the bumpy mound that imitates earth, trying to get my bearings. [49] <> Ni dai ina can sun bar ni a baya, ina laluben hanya. [50]

#: Now that I know there are obstacles, [51] <> To kuma tun da na ji cewa akwai bishiyu a wurin [52]

#: Im worried that if I take another step Im going to walk directly into a tree. [53] <> sai na shiga fargabar in na kara taki daya zan iya karo da bishiya. [54]

#: This is just the first room of seven [55] <> Wannan dai shi ne daki na farko cikin bakwai [56]

#: at the Dialogue in the Dark exhibition at the Childrens Museum in Holon, Israel, more commonly referred to as theblind museum.” [57] <> na cibiyar nunin rayuwa cikin makanta da ake gudanarwa a gidan adana kayan tarihi na Holon da ke kasar Isra'ila. [58]

#: The World Health Organization [59] <> Hukumar lafiya ta duniya (WHO) [60]

#: estimates that 38 million people are blind around the world, [61] <> ta kiyasta cewa akwai makafi miliyan 38 a fadin duniya, [62]

#: with an additional 110 million having low vision and at great risk of becoming blind. [63] <> da kuma karin mutane miliyan 110 da ba sa gani sosai kuma su ke fuskantar barazanar makancewa. [64]

#: Like the dark dining concept, where visitors eat in a restaurant that is in complete darkness, this exhibition, [65] <> Manufar wannan nunin dai, [66]

#: which started in Germany in 1988 [67] <> wanda aka kirkira a Jamus a 1988, [68]

#: and has franchises in several countries, [69] <> kuma ake yadawa zuwa kasashe da dama, [70]

#: is designed to bridge understanding between sighted and blind people, [71] <> ita ce kyautata fahimta tsakanin masu gani da makafi, [72]

#: and give visitors a taste of what it feels like to be blind. [73] <> ta hanyar bai wa maziyarta damar dandana yadda rayuwar makafi ta ke. [74]

#: Mattityahu says that hes witnessed all kinds of initial reactions to the exhibit. Some people panic, [75] <> Mattityahu ya ce wasu maziyartan kan firgice, [76]

#: some start screaming as if others wont be able to hear them in the dark, [77] <> su fara ihu kamar ba za'a iya jin su a cikin duhu ba tare da sun daga murya ba. [78]

#: others laugh. [79] <> Wasu kuma su kan kyalkyale da dariya. [80]

#: At least one has fainted. [81] <> An ma taba samun wanda ya sume. [82]

#: Some people become so disoriented and unfocused that they cant tell left from right,” he says. [83] <> Ya ce "wasu mutane su kan rude su kasa gane dama da hagu. [84]

#: Ill tell them to use their left hand to find the wall, and they cant do it.” [85] <> Idan na ce musu su yi amfani da hannun hagu domin su lalubo bango, sai su kasa." [86]

#: By the end of our 90-minute tour, [87] <> A cikin ziyarar ta minti 90 dai, [88]

#: we will have ridden on a boat, [89] <> mun shiga kwalekwale, [90]

#: wandered through a house, [91] <> mun kewaya wani gida, [92]

#: walked down a public street, [93] <> mun yi tafiya a kan titi, [94]

#: shopped for fruit and vegetables at a grocery store [95] <> mun sayi kayan marmari a shago, [96]

#: and drank soda in a bar, all in complete darkness. [97] <> sannan kuma mun sayi lemon kwalba a kanti, duk a cikin duhu dundum! [98]

#: Though its terrifying at first, [99] <> Duk da yake ziyarar na da firgitarwa da farko, [100]

#: it is also enlightening. [101] <> lallai ta na da wayarwa. [102]

#: About half-an-hour in, [103] <> Bayan kimanin rabin sa'a da farawa, [104]

#: I find that my other senses are more focused, primarily hearing and touch, including the telling bumps beneath my cane, [105] <> sai ji na, na kunne da na tabawa su ka karu. [106]

#: and it becomes increasingly easy and more natural to navigate through each room. [107] <> Sai lalube cikin duhun ya fara sauki a lokacin da na ci gaba da kutsawa daga daki zuwa daki. [108]

#: Our brains are, after all, enormously adaptable to make the most of what they are given. [109] <> An shirya kwakwalenmu ne ta yadda za su yi cikakken amfani da duk abinda aka ba su. [110]

#: For sighted people, [111] <> Ga masu idanu, [112]

#: the areas of the brains cortex devoted to visual processing [113] <> bangaren kwakwalwar dake lura da gani [114]

#: has more neurons than those processing hearing and touch combined, [115] <> yafi bangarorin da ke lura da ji da tabawa yawan jijiyoyi, [116]

#: allowing our eyes to quickly analyse our surroundings. [117] <> abinda ke sa idanunsu gane wurararen da su ke cikin hanzari. [118]

#: In the absence of sight, however, [119] <> Ga wadanda ba sa gani kuwa, [120]

#: our others senses may pick up the slack. [121] <> sai jijiyoyin su tattara a bangaren kwakwalwa mai kula da ji da tabawa. [122]

#: Research on blindness and neuroplasticity [123] <> Bincike akan dangantakar makanta da kwakwalwa, [124]

#: have even shown that being blind can change the way the brain processes information, [125] <> ya gano cewa makanta kan sauya yadda kwakwalwa ke aiki, [126]

#: with studies demonstrating that [127] <> inda masana su ka gano cewa [128]

#: early-blind individuals use their occipital cortex in auditory, verbal processing and/or tactile processing. [129] <> mutanen da suka makance kan yi amfani da bangaren kula da gani na kwakwalensu wurin sarrafa ji da tabawa, [130]

#: says Patrice Voss, a postdoctoral fellow at McGill University. [131] <> kamar yadda wani mai bincike a jami'ar McGill, Patrice Voss ya bayyana. [132]

#: Vosss research has shown that early-blind people [133] <> Binciken na Voss ya kuma nuna cewa mutanen da su ka makance tun da kuruciya [134]

#: outperform sighted people [135] <> sun fi masu gani [136]

#: at locating sounds on a horizontal plane when limited to one ear, [137] <> iya gano ta inda sauti ke fitowa musamman idan ta bangaren kunne daya ne. [138]

#: while other studies have shown blind people [139] <> Haka kuma wasu masanan sun gano cewa makafi [140]

#: outperform sighted people on other nonvisual tasks like recognising voices and verbal memory. [141] <> sun fi masu gani gane muryoyi da kuma hadda. [142]

#: Though people who lose their sight later in life [143] <> Koda yake mutanen da su ka makance da girmansu ma, [144]

#: still exhibit behavioral changes, [145] <> kan samu sauyi a yadda kwakwalwarsu ke aiki, [146]

#: Voss says that early or congenitally blind individuals [147] <> Voss ya ce wadanda su ka makance tun da kuruciya [148]

#: typical benefit from more reorganisation of visual areas than people who lose their sight in adulthood. [149] <> sun fi samun sauyin aikin bangaren gani fiye da wanda su ka makance da girmansu. [150]

#: Our brain is less plastic as we age, [151] <> Ya ce "Kwakwalwa ma ta na tsufa. [152]

#: so theres less room for change. [153] <> Don haka muna girma ikonta na sauya tsarin aikin sassanta na raguwa. [154]

#: But early experience also drives the connections that our brain forms,” he says. [155] <> Amma wanda ya makance tun da wuri, kwakwalwarsa kan samu kwarewar sarrafa abubuwan da basu shafi gani ba a sassan da ya kamata su sarrafa ganin." [156]

#: People also often refer to Ray Charles and Stevie Wonder [157] <> Mutane kuma kan bada misali da Ray Charles da Stevie Wonder [158]

#: as examples of blind individuals with superior musical abilities [159] <> a matsayin makafin da su ka yi matukar kwarewa a fannin kida. [160]

#: and there is some research to back the claim that [161] <> To akwai binciken da ya nuna cewa [162]

#: early blindness could lead to superior auditory skills. [163] <> makanta kan kara karfin ji da kuma sarrafa sauti. [164]

#: One study from 2004 for example found that [165] <> Ga misali, wani bincike da aka yi a 2004 ya gano cewa [166]

#: the percentage of musicians who possess absolute pitchthe ability to identify and recreate a musical notewas significantly higher in a blind population of musicians than in a sighted population of musicians. [167] <> makada makafi sun zarta takwarorinsu masu ido kwarewa wurin nakaltar sautin kida tare da maimaita shi ba tare da kuskure ba. [168]

#: People always say that if they had to give up their sight, they would die. [169] <> A cewar Mattityhau "Mutane da yawa na daukar rashin gani a matsayin mutuwar tsaye. [170]

#: But thats not the case,” said Mattityahu. [171] <> Amma ni a wuri na ji yafi gani amfani. [172]

#: I cannot see, [173] <> Ba na iya gani, [174]

#: but I can hear, [175] <> amma ina iya ji, [176]

#: remember, [177] <> in rike magana, [178]

#: communicate, [179] <> in isar da sako, [180]

#: walkI function regularly.” [181] <> in yi tafiya - wato dai ina cikakkiyar rayuwa tamkar kowa." [182]

#: Mattiyahu says that in addition to empathising with the blind, [183] <> Mattityahu ya ce baya ga fahimtar yadda rayuwar makafi take kuma, [184]

#: one of the hopes of the exhibit [185] <> daya daga cikin manufar shirya nunin, [186]

#: is that visitors will learn to judge blind people [187] <> shi ne maziyarta su rika kimanta makafi [188]

#: based on their abilities rather than merely their blindness. [189] <> bisa kwarewarsu ba wai su rika kallonsu a matsayin nakasassu ba. [190]

#: I wish that in the light, my life would be more like in the exhibit,” he said. [191] <> Ya ce "Zan so a ce rayuwata a waje za ta yi daidai da ta wurin nunin nan. [192]

#: Nobody saw me before you came here [193] <> Babu wanda ya taba ganina cikinku kafin zuwa nan, [194]

#: and everyone very quickly learned how to trust me. [195] <> amma duk kun amince da jagorancina. [196]

#: But if you had met me in the light, [197] <> In da kuwa a cikin haske muka hadu, [198]

#: no one would consider the possibility of getting help from a blind person. [199] <> ba wani daga cikinku da zai tunanin neman taimako daga makaho. [200]

#: And Im thinking, why not? [201] <> Na kan tambayi kai na ko me yasa haka? [202]

#: The same way I could guide you here, [203] <> Yadda na iya jagorantarku a cikin duhu, [204]

#: I could also tour you in the light.” [205] <> zan iya jagorantarku a cikin haske." [206]

#: Its not just the physical world that can pose challenges for blind people; [207] <> Ba wai rayuwar zahiri ce kawai ke zama kalubale ga makafi ba, [208]

#: they also have to learn to navigate the digital world. [209] <> har ma da duniyar fasahar zamani. [210]

#: How does it feel to use technology as a blind person? [211] <> Ko yaya makafi ke amfani da fasahar zamani? [212]

#: You may not realise it, [213] <> Ba mamaki ba ku sani ba, [214]

#: but its likely that your smart phone and computer have settings that make them useable without sight. [215] <> amma mafi yawan wayoyin komai-da-ruwanka da kwamfutoci su na da tsarin da ke bada damar a yi amfani da su ba tare da gani ba. [216]

#: Android phones have a series of settings you can enable [217] <> Wayoyin Android suna da manhajar da za ta sarrafa su ta hanyar magana [218]

#: including Talk Back and Explore by touch, as well as Vlingo, a Siri-like voice command software; [219] <> irinsu Talk Back da Vlingo ko kuma ta hanyar tabawa kamar Explore by touch. [220]

#: while Apple devices have an accessibility setting called VoiceOver. [221] <> Wayoyin Apple kuma su na da manhajar VoiceOver. [222]

#: Furthermore, apps like the LookTel Money Reader and the Color Identifier by GreenGar Studio [223] <> Haka kuma, akwai manhajojin LookTel Money Reader da Color Identifier, [224]

#: uses the camera to identify and speak the names of currency from all over the world and colors respectively. [225] <> wanda ke amfani da kyamarar wayar salula wurin gane takardun kudi da kuma launuka. [226]

#: Other apps like the Ray App by Project Ray simplify the interface of Android phones and orientates options on the phone based on where you initially touch on the screen. [227] <> Akwai kuma Ray App mai saukaka tsarin wayoyin Android domin amfanin makafi. [228]

#: I used my iPhone on its VoiceOver setting for a week. [229] <> Na yi amfani da wayar iPhone bisa tsarin VoiceOver na tsawon mako guda. [230]

#: Switching it on was easy enough, but after that I was at a loss, even while looking at the phone, since VoiceOver uses a completely different set of gestures. [231] <> Sai dai nan take na rikice saboda amfani da waya bisa manhajar VoiceOver ya sha bamban da yadda na saba. [232]

#: For example, swiping up and down in VoiceOver doesnt move the page up or down, swiping with two fingers do. I decided to get a lesson from an expert. [233] <> Misali, shafar fuskar waya daga sama zuwa kasa da dan yatsa daya, ba ya sa shafin da ake karantawa ya yi sama, sai dai in an yi amfani da yatsu biyu. Don haka sai na yanke shawarar neman taimakon kwararru. [234]

#: Liran Frank worked as a computer technician before he lost his sight to a congenital degenerative condition called retinitis pigmentosa. [235] <> Liran Frank injiniyan kwamfuta ne kafin ya makance sanadiyyar ciwon ido. [236]

#: Its not that blind people only use assistant technology,” he says. [237] <> Ya ce "Ba fasahar taimako kadai makafi ke amfani da ita a wayoyin salula ba. [238]

#: We use all the apps sighted people use [239] <> Muna amfani da duk manhajojin da masu gani ke amfani da su [240]

#: like Netflix, Google Maps, Moovit, Whatsapp, et cetera. [241] <> irin su Netflix, Google Maps, Moovit, Whasapp, da sauransu. [242]

#: Using VoiceOver is so simple; you just have to get the hang of it. [243] <> Amfani da VoiceOver na da matukar sauki da zarar ka gane yadda ya ke aiki. [244]

#: I use my phone at the speed of a sighted person.” [245] <> Ina amfani da wayata kamar yadda mai gani ke amfani da ta sa." [246]

#: Drawing the digital curtain [247] <> Jan labulen fasaha [248]

#: After a quick lesson with Frank, [249] <> Bayan kwarya-kwaryar darasi a wurin Frank, [250]

#: who teaches blind people how to use smart phones [251] <> wanda ke koyawa makafi yadda za su yi amfani da wayoyin komai-da-ruwanka [252]

#: and computers and creates instructional podcasts about VoiceOver, [253] <> da kuma na'urorin kwamfuta tare da samar da darussan sauraro na dabarun amfani da VoiceOver, [254]

#: I began using my phone on VoiceOver [255] <> sai na fara amfani da manhajar VoiceOver [256]

#: with a digital curtain drawn so that the screen perpetually looked as if the phone was off. [257] <> a wayata tare da jan labulen fasaha wanda ya mayar da fuskar wayar dundum kamar a kashe ta ke. [258]

#: Within a day, [259] <> Cikin yini guda, [260]

#: using my phone when it was black was surprisingly intuitive. [261] <> sai hannuna ya fada kan amfani da wayar da take dundum. [262]

#: Various sounds indicating certain things help orientate you and become instinctive. [263] <> Saututtuka daban-daban da wayar ke bayarwa su na taimakawa kwarai wurin sarrafata. [264]

#: For example telltale sounds will indicate that you cant erase anymore in a text field, [265] <> Misali akwai sautin da ke nuna ka gama goge rubutun da ka ke gogewa, [266]

#: that youve successfully opened something [267] <> akwai mai nuna ka bude abinda ka ke son budewa [268]

#: or that you are off the parameters of the screen. [269] <> ko kuma ka fita daga kan iyakar fuskar wayar. [270]

#: Various one- to four-finger gestures, like swiping, tapping, double tapping, triple tapping and a motion calledscrubbinghelp navigate and give commands to the phone quickly. [271] <> Ana kuma sarrafa wayar ne ta hanyar shafarta da 'yan 'yatsu daga daya zuwa hudu ta sigogi dabam-daban. [272]

#: For example, you can double tap anywhere on the screen to stop a talk-back of something, [273] <> Misali, kwankwasar fuskar wayar sau biyu na tsayar da karatu, [274]

#: for example if the screen is reading a text message or email that youve heard before. [275] <> kamar idan wayar na karanta wani sako da ka riga ka saurara. [276]

#: Theres even a virtual rotor that you can activate by twisting two fingers on the screen as if turning a dial, [277] <> Haka kuma idan ka mintsini fuskar wayar sai ta baka jerin abubuwan da zaka iya yi cikin manhajar [278]

#: which gives more options relevant to the page or app you are on, like producing a list of links, [279] <> da ka bude kamar lissafo sauran shafukan da ke cikin gidan da ka shiga [280]

#: or having words spoken to you, character by character, [281] <> ko kuma karanto maka bakaken rubutun da ka yi daya bayan daya [282]

#: so you can check the spelling of something. [283] <> domin tabbatar da cewa ka rubuta kalmomin daidai. [284]

#: I was able to check my email, send and listen to text messages both by typing and using dictation, [285] <> Ta kai ina iya duba sakonnin i-mel, aikawa da sauraron rubutattun sakonni, [286]

#: surf the Internet on Safari, [287] <> bude shafukan intanet, [288]

#: make phone calls and play music. [289] <> kiran waya da kuma sauraron wakoki. [290]

#: After listening to Franks podcast and with some practice, [291] <> Bayan kuma na saurari darasin Frank, [292]

#: I was even able to use Google Maps. [293] <> ina iya amfani da Google Maps. [294]

#: But that doesnt mean there arent frustrations. [295] <> Hakan ba ya nufin ban fuskanci matsaloli ba. [296]

#: In addition to the initial learning curve that includes sending messages like the one below, [297] <> Baya ga lokacin da na dauka wurin koyon amfani da manhajar, [298]

#: there are often challenges when an app is updated. [299] <> akan samu kalubale duk lokacin da aka sake inganta wata sabuwar manhajar wayar salula. [300]

#: While some apps and websites are accessible by design, its clear that some are only well-suited for use with VoiceOver or other screen-reading software by chance. [301] <> Yayinda ake tsara wasu manhajojin domin su dace da tsarin VoiceOver, wadansu manhajojin kan dace ne ba tare da sanin masu kirkirarsu ba. [302]

#: Frank says he used a popular public transportation app with VoiceOver [303] <> Frank ya ce akwai wata manhajar motocin sufuri da ya ke amfani da ita akan tsarin VoiceOver [304]

#: until an update made the app significantly graphic and therefore inaccessible. [305] <> amma da aka kara ingantata sai ya zama an dora ma ta abubuwan da VoiceOver ba zai iya dauka ba. [306]

#: A group of us wrote them a letter,” he said. [307] <> "Muka hada kai mu ka rubuta mu su wasika. [308]

#: They wrote us back telling us that they had no idea that blind people used their software and that they wanted it to be accessible. [309] <> Sai su ka aiko mana cewa ba su taba sanin makafi na iya amfani da manhajar ta su ba amma tun da haka ne za su so makafi su ci gaba da amfani da sabuwar manhajar. [310]

#: So they worked with us to hire a programmer to go through the code and make it totally accessible again.” [311] <> Don haka su ka hada kai da mu, mu ka dauko wani mai shirya manhajar salula ya yi wa sabuwar manhajar ta su tsarin da za ta iya ci gaba da aiki a VoiceOver." [312]

#: Frank believes its more worthwhile to spend energy and resources making apps that already exist more accessible [313] <> Frank na ganin zai fi kyau a mai da hankali wurin tsara manhajojin da masu gani ke amfani da su ta yadda makafi ma za su iya amfani da su [314]

#: rather than create interfaces or phones specifically for blind users. [315] <> maimakon a ce za'a kirkiro wa makafi wayoyinsu na dabam. [316]

#: Those phones are typically more limited and dont give you all the functions of the normal device,” he says. [317] <> "Irin wadannan wayoyin yawanci ba sa iya yin komai da komai da sauran wayoyi ke yi. [318]

#: I think its a bit condescending [319] <> Ina ganin hakan kamar raini ne [320]

#: since were smart enough to learn how to use the normal phones [321] <> domin kuwa muna da basirar da zamu iya amfani da wayoyin yau da kullum [322]

#: with accessible websites and apps, and it gives us more capabilities.” [323] <> matukar a ka dora musu manhajojin da za su ba makafi damar amfani da su. Kuma wannan yafi bamu damar a dama da mu." [324]

#: And while getting private companies to be concerned about accessibility may continue to be an ongoing challenge, [325] <> Koda yake karkatar da tunanin kamfanonin wayar salula izuwa samar da manhajojin da makafi za su iya amfani da su babban kalubale ne, [326]

#: many in the blind community say it is just another issue that they will learn to navigate. [327] <> makafi da yawa na ganin wannan na daya daga cikin abubuwan da ya kamata su sa a gaba. [328]

#: As for me, I wouldve liked to try using an app to guide me [329] <> Ni kuwa, zan so a ce akwai wata manhajar salula da za ta yi min jagora [330]

#: through the dark exhibit. [331] <> wurin ziyarar nunin rayuwa cikin makanta. [332]

#: Perhaps its an element organisers [333] <> Zan so a ce masu shirya nunin [334]

#: will add to the experience in the future. [335] <> za su yi tunanin samar da wannan manhaja nan gaba. [336]

#: But the most revealing part was leaving the exhibit. [337] <> Amma abinda yafi ba ni mamaki shi ne barin wurin nunin. [338]

#: After spending a couple hours in the dark tuning my other senses, [339] <> Domin kuwa bayan kwashe sa'o'i a cikin duhu tare da kara saitin ji na, [340]

#: I was completely bombarded by visual information [341] <> abubuwan da idona ke gani bayan na fito cikin haske sai su ka yi min yawa [342]

#: and felt more comfortable closing my eyes on the drive home. [343] <> har sai da na runtse idanuna lokacin da nake komawa gida. [344]

#: I then realised both how much most of us depend on our sight[345] <> A sannan ne na fahimci irin tsananin dogaron da mafi yawanmu muka yi akan gani[346]

#: and how rich the world can be without it. [347] <> da kuma irin yadda rayuwa za ta iya yin armashi ba tare da ganin ba. [348]