bbchausa verticals/068 quietest place

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Contents

#: Inside the quietest place on Earth [1] <> Ka san dakin da ya fi shiru a duniya? [2]

#: Microsoft has built a chamber so quiet, [3] <> Kamfanin Microsoft ya gina wani daki da yake shiru ba a jin karar komai, [4]

#: you can hear the grind of your bones[5] <> ta yadda hatta kasusuwan jikinka ma za ka ji motsinsu. [6]

#: and its helping to fine-tune the next-generation of electronic goods. [7] <> Kuma dakin na taimaka wa wajen kirkiro kayan laturoni da za a bullo da su nan gaba. [8]

#: If LeSalle Munroe stands still for a few moments in hisoffice”, [9] <> Idan LeSalle Munroe ya tsaya cik na dan wani lokaci a cikin ofishinsa, [10]

#: something unsettling can happen[11] <> wani abu mai tsoratarwa yakan faru. [12]

#: he can hear the blood rushing around his body [13] <> Zai iya jin karar tafiyar jininsa a cikin jikinsa [14]

#: and his eyes squelch as they move in his skull. [15] <> da motsin idanuwansa a cikin kwarminsu. [16]

#: While many people work in places filled with the tip-tap of keyboards, the hubbub of chatter from colleagues and a constant hum of computers, [17] <> Yayin da wasu mutanen ke aiki a wurin da ke cike da karar kwamfuta da sauran na'urori da surutai da kai-kawo na abokanan aiki, [18]

#: Munroe is surrounded by almost total silence. [19] <> Munroe yana cikin wurin da babu wani motsi ko kara. [20]

#: His office is the quietest place on the planet. [21] <> Ofishinsa shi ne wurin da ya fi shiru a duk duniya. [22]

#: The specially constructed chamber [23] <> Shi dai wannan daki na musamman [24]

#: is hidden in the depths of Building 87 [25] <> yana boye ne can a karkashin Gini na 87 [26]

#: at Microsofts headquarters in Redmond, Washington, [27] <> a hedikwatar kamfanin Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, [28]

#: where the firms hardware laboratories are based. [29] <> inda dakunan binciken kimiyya na manhajar kamfanin suke. [30]

#: Products like the Surface computers, Xbox and Hololens have all been developed here. [31] <> A nan ne aka kirkiro fitattun kwamfutoci da manhajar kamfanin irin su Surface computers da Xbox da Hololens. [32]

#: Microsofts engineers built the roomknown as an anechoic chamber[33] <> Injiniyoyin kamfanin ne suka kirkiro tare da gina dakin ( anechoic chamber), [34]

#: to help them test new equipment they were developing [35] <> domin ya taimaka musu wurin gwajin sabbin na'urorin da suka kirkiro. [36]

#: in 2015 it set the official world record for silence [37] <> Kuma a shekarar 2015 dakin ya kafa tarihin zama wurin da ya fi zama shiru a duk duniya. [38]

#: To put that in context, [39] <> Ta yadda za ka kara fahimtar yanayin wurin karara, shi ne, [40]

#: a human whisper is about 30 decibels [41] <> idan mutum ya yi rada tana linkawa kusan sau talatin a kara, [42]

#: while the sound of someone breathing normally comes in at just 10 decibels. [43] <> yayin da karar numfashin mutum kuma ke linkawa sau goma. [44]

#: It is a very unique experience inside with the door closed,” says Munroe. [45] <> Munroe ya ce, Idan aka rufe kofar dakin yanayin wani ne na daban wanda ba ka taba ji ba, [46]

#: When you stop breathing, [47] <> idan ka tsayar da numfashinka [48]

#: you can hear your heart beating and the blood flowing in your veins. [49] <> za ka iya jin zuciyarka tana bugawa da tafiyar jininka a jiki. [50]

#: I dont stay inside with the door closed very often.” [51] <> Ni kaina ba kasafai nake zama a ciki ba da kofar a rufe. [52]

#: It took almost two years to design and build the chamber [53] <> Sai da aka dauki kusan shekara biyu ana zayyanawa da gina dakin, [54]

#: where Munroes team now spend their days putting Microsofts technology through its paces. [55] <> inda a yanzu Munroe da abokan aikinsa ke aiki a kullum na kirkiro da kayayyakin fasaha na kamfanin Microsoft. [56]

#: Even finding a suitable building [57] <> Hatta samo ginin da ya dace inda za a yi wannan daki [58]

#: took nearly eight months of testing to find one quiet enough to house it. [59] <> sai da aka dauki kusan wata takwas ana gwaje-gwaje domin samun wurin da yake shiru ba hayaniya ko wata kara da za a iya yinsa. [60]

#: This nest of rooms within rooms[61] <> Dakin dai an yi shi ne can a cikin tsakiyar wasu dakuna [62]

#: each with walls up to 12 inches thick[63] <> wadanda kowanne bangonsa ya kai kaurin inci 12, [64]

#: helps to cut the noise reaching the chamber by around 110 decibels. [65] <> wanda hakan ya sa ba wata kara daga waje da za ta shigo cikinsa. [66]

#: If a jet was taking off just outside the building, [67] <> Idan jirgin sama na yaki zai tashi a kusa da ginin gidan da dakin yake [68]

#: you would hear little more than a whisper inside the final concrete bunker where the chamber is. [69] <> abin da za ka ji a daki na karshe da wannan ofis yake ciki bai wuce kamar rada ba. [70]

#: This insulation makes a huge difference,” [71] <> “An tsara ginin ofishin ta wata hanya ta musamman ta yadda ba inda gininsa kai tsaye ya taba ainahin ginin gidan da yake ciki.” [72]

#: explains Hundraj Gopal, principal human factors engineer at Microsoft who led the team that built the anechoic chamber. [73] <> In ji Hundraj Gopal, babban injiniyan al'amuran da suka shafi mutane na kamfanin na Microsoft. [74]

#: The anechoic chamber is a cube measuring 21ft (6.36m) in each direction. [75] <> Wannan daki ko ofis yana da fadin kafa 21 ta kowane bangare. [76]

#: Each of its six surfaces is lined with clusters of 4ft-long (1.2m) wedges of sound absorbing foam, [77] <> Kuma a dukkanin bangarorinsa shida an shinfida masa abin da ke hana sauti wucewa mai tsawon kafa hudu, [78]

#: helping to prevent any echoes bouncing off the walls from any sound produced inside. [79] <> wanda ke hana amsa amo na duk wani sauti da aka yi a cikin dakin. [80]

#: Seals around the doors of the chamber and the rooms surrounding it also [81] <> Ita kanta kofar da sauran duk wasu tsare-tsare na dakin an yi su ne na musamman [82]

#: help to keep noise from leaking in. [83] <> ta yadda ba wani sauti ko kara daga ciki da zai fita ko kuma ya shigo ciki daga waje. [84]

#: The chamber itself is one that is commercially available so anyone can buy it,” says Gopal. [85] <> Gopal ya ce; Ga duk wanda yake bukatar irin wannan daki zai iya saye akwai shi. [86]

#: The secret is in the extra time and energy we put into isolating the sprinkler system, putting in door seals, a specialised air supply, staggering the openings and the way cables go in. There is a lot that went around this chamber that makes it unique.” [87] <> Sirrin abin kawai shi ne yadda muka yi dabara da bata lokaci wurin sarrafa hanyar da iska za ta kai ga dakin. [88]

#: Before officials from the Guinness Book of Records arrived to [89] <> Kafin jami'an littafin bajinta na duniya na Guiness Book of Records su je wurin [90]

#: take measurements in Gopals anechoic chamber [91] <> su yi nazarinsa har ya zama na daya a duniya (-20.6), [92]

#: the world record for the quietest spot on Earth was held by Orfield Laboratories in Minneapolis, which had an anechoic chamber that had noise levels of -9.4 decibels. [93] <> dakin bincike na kimiyya na Orfield Laboratories da ke Minneapolis shi ne ke da wannan bajinta ta dakin da yake mafi shiru a duniya (-9.4 decibels). [94]

#: We didnt set out to build the quietest chamber on the planet,” says Gopal. [95] <> Gopal ya ce; Ba wai mun yi niyyar gina wurin da shi ne ya fi shiru ba a duniya. [96]

#: My intention was to have something that was at least zero decibels, which is the lowest the average human can hear.” [97] <> Niyyata mu yi wurin da babu hayaniya ko iya karar da kunnen mutum zai iya ji (0 decibels). [98]

#: You would think that a place so quiet would also be peaceful. [99] <> Za ka dauka cewa wurin da yake shiru kamar wannan, zai kasance wuri ne da yake lami lafiya. [100]

#: But for those who spend any time in there, it is far from the case. [101] <> To amma ga wadanda suka taba shiga dakin lamarin ba haka yake ba ko alama. [102]

#: Gopal often gives visitors to Microsoft a tour of the audio laboratories, [103] <> Gopal yakan ba wa bakin da suka ziyarci hedikwatar ta Microsoft damar ziyarar dakunan bincike da gwaji na kamfanin, [104]

#: which includes a trip inside the anechoic chamberand most find the experience very uncomfortable. [105] <> har ma da wannan daki na musamman. [106]

#: Some people want out within a few seconds,” he confides. [107] <> Kuma yawancin mutanen ba sa jin dadi idan suka shiga dakin, ta yadda wasu nan da nan da shigarsu dakin sai su nemi hanyar fita, in ji Gopal. [108]

#: They say they just cant be in there. [109] <> 'Sukan ce ba za su iya zama a dakin ba. [110]

#: It unsettles almost everybody. [111] <> Kusan kowa za ka ga ba ya jin dadi. [112]

#: They can hear people breathing on the other side of the room and hear stomachs gurgling. [113] <> Suna iya jin numfashin wadanda suke can gefe a dakin, da kuma kugin cikin mutane. [114]

#: A small number of people feel dizzy.” [115] <> Wasu mutanen ma 'yan kadan sukan ji juwa ko jiri. [116]

#: This might seem like a strange reaction [117] <> Wannan zai zama kamar wani abin mamaki [118]

#: when most of us spend our lives seeking a bit of respite from the noise we are bombarded with every day. [119] <> kasancewar yawancinmu muna kokarin samun kanmu a wurin da za mu kaurace wa hayaniyar yau da kullum da ke damunmu. [120]

#: But Peter Suedfeld, a psychologist at the University of British Columbia who has studied sensory deprivation, [121] <> Amma Peter Suedfeld, masanin tunanin dan adam a jami'ar British Columbia, [122]

#: compares stepping into one of these chambers to being like entering a dark room. [123] <> ya kwatanta lamarin da rashin sabo, inda ya ce kamar shiga dakin da yake da duhu ne dudum. [124]

#: We are used to every sound producing a small echo from the world around us,” he points out. [125] <> 'Da farko za ka ga ba ka ganin komai, amma da ka dan jima a ciki sai idonka ya saba da duhun ka fara gani. [126]

#: Cut off from the daily noises that usually drown out our body functions, [127] <> Idan ka kaurace daga wurin da ake jin kara ko sauti na yau da kullum, [128]

#: it becomes possible to hear the grind of bones as your joints move, [129] <> to za ka iya jin hatta motsin kasusuwa ko gabban jikinka a lokacin da kake motsi, [130]

#: the ringing of tinnitus can become deafening. [131] <> har ma ka ji karar ta dame ka matuka. [132]

#: But Gopal says there are some people who enjoy the experience of being inside his chamber. [133] <> Amma Gopal ya ce; Duk da haka akwai wadanda suke jin dadin kasancewa a dakin, suna ma daukar kamar yanayi ne na daidai da zaman natsuwa na ibada. [134]

#: But the longest Ive seen someone stay inside for is an hour, [135] <> Sai dai ya ce mafi dadewa da ya gani wani ya yi a dakin daga cikin masu ziyara shi ne sa'a daya, [136]

#: and that was to raise money for charity. [137] <> shi ma din domin tara kudin bayar da agaji ne. [138]

#: I think if you spent too much time in there it would drive you crazy. [139] <> Ya ce, ina jin idan ka dade a dakin ka za ka ji ya dame ka. [140]

#: Every swallow you make is really loud.” [141] <> Duk yawun da ka hadiya za ka ji karar hadiyar ta dame ka. [142]

#: For Munroe, this silence has a far more constructive use than simply eavesdropping on the grumblings and gurglings of the human body. [143] <> A wurin Munroe wannan shirun na dakin yana da wani amfanin wanda shi ne mafi muhimmanci, fiye da jin karar jikin mutum. [144]

#: They are looking for tiny vibrations that are produced by capacitors on electronic circuit boards as current passes through them. [145] <> Akwai karar da kayan da aka harhada aka tashi na'ura suke yi lokacin da lantarki ya shige su, [146]

#: These can make the components on the board produce annoying hums that can be off-putting for consumers. [147] <> wanda kila karar zai iya damun mai amfani da na'urar. [148]

#: We try to find out where on the board a noise is coming from [149] <> Ya ce: Ta wannan hanya muke iya gano inda karar ke fitowa [150]

#: and what strategies we can use to mitigate it,” explains Munroe. [151] <> sai mu duba yadda za mu yi mu dakatar ko rage karar. [152]

#: They also look at other components on computers that can make noisesfrom the power supply to the cooling fan and the sound from your display as you increase the backlighting. [153] <> Haka kuma akan yi amfani da hanyar wajen saitawa ko dadada karar da misali danna wayar salula ke haifarwa ta yadda za ta yi dai ga kunnen mutum maimakon ta sa ya ji ba dadi, idan karar ta kasance wata iri. [154]

#: Gopal is reluctant to branch into medical and behavioural studies. [155] <> Sai dai Gopal yana taka-tsantsan wajen barin a yi amfani da dakin a fannin likitanci da ya shafi kwakwalwa ko masu larurar tabin hankali, [156]

#: Putting patients into such an unusual environment would likely require volumes of special legal clearance. [157] <> domin abu ne da ke bukatar matakai na izini daga hukuma, [158]

#: The laboratorys busy testing schedule also makes it difficult to find time for such studies. [159] <> saboda hadarin dake tattare da sanya mutumin da ke da larurar kwakwalwa a irin wannan daki. [160]

#: On a personal level, however, the real power of the chamber for Munroe and Gopal comes when they leave after a spell inside. [161] <> Ainahin tasirin dakin akan Munroe da Gopal na bayyana ne idan sun fita daga dakin bayan sun dan jima a ciki. [162]

#: When you open the door it is almost like a waterfall of sound hitting your ears,” says Munroe. [163] <> Munroe ya ce; Da ka bude kofa za ka ji kamar wata kara mai karfin gaske tana ta bugun kunnuwanka. [164]

#: It is like stepping out into a different world. [165] <> Kamar ka shiga wata sabuwar duniya ne, [166]

#: You hear things that you wouldnt normally notice. It gives you a new perspective.” [167] <> za ka ji karar da idan da haka kawai ne ba za ka ji ba, kuma zai sa ka fahimci wani abu. [168]