giwa

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Noun

Tilo
giwa

Jam'i
giwaye or giye

Singular
elephant

Plural
elephants

m

 1. dabbar dawa da ta fi kowace dabba girma mai haure biyu dogaye da hanci mai kama da hannu da manya-manyan kunnuwa. <> An elephant is a very large animal with two long teeth called tusks and a long nose called trunk. Elephants live in Africa and Asia.
 2. kirarin da ake yi wa sarki ko wani mai ƙasaita.
 3. abincin da aka yi tsakanin la asar da magariba.
 4. tsirkiyar molo mai tsawo.
 5. gungun mayaƙa.
 6. turo wa abokan gaba ƙaton dutse daga saman tsauni.
 7. dinƙe tabarmi biyu don zuba kudi na wuri ko kaya.
 8. giwar basa = watau wata irin tufa mai ratsin fari da baki.
 9. giwar fito, watau wani irin kwami da ake yi da ƙirgi
 10. giwar gari watau mace mai mugun hali.
 11. giwar ruwa, watau wani irin kifi.
 12. giwar kamba, watau wata irin dawa mai tsawo da saurin yi da wuri.
 13. giwar kara; watau tarin karan hatsi
 14. giwar kudi, watau kudin wuri da aka zuba a cikin kilago.
 15. hannun giwa = watau (a) hancin giwa (b) taimakon da ake yi da hannun da ba ya riƙe da komai.
 16. wata irin dawa.
 17. kan giwa = ƙofar fada.
See also Giwa

Google translation of giwa

Elephant.

 1. (noun) elephant <> giwa;