Open main menu

HausaDictionary.com | Search > β

ɓata

Verb

 1. to go missing, loss/being lost, to lose something <> rashin ganin mutum ko abu; kasa gane hanya zuwa wani waje; rashin samin wani abu
  You'd be surprised as to how many kids have gone missing every year. <> Ka yi mamakin adadiin yaran da suka ɓata a kowace shekara.
 2. (religious) misguided, to go astray <> kauce wa madaidaiciyar hanyar addini.
 3. mistake, to err, error <> ɓaci, ɓatanci.
  and already they have misled many. and, [ my lord ], do not increase the wrongdoers except in error." <> "kuma lalle ne sun ɓatar da (mutane) masu yawa, kuma kada ka ƙara wa azzalumai (kome) sai ɓata." = [ 71:24 ] "kuma suka batar da (mutane) masu yawa. saboda haka, bari azzalumai su qara zurfi cikin bata." --Qur'an 71:24
  You made three mistakes while reciting <> Ka ɓata sau uku a karatunka.
 4. to ruin, spoil, soil, mess up/mess with.

Glosbe's example sentences of ɓata

 1. ɓata. <> corrupts, damage, destroying, displease, displeasing, erode, missing, offend, offended, polluting, slanderous, spoil, waste, wasted.
  1. Idan da gaske muke, ba da haƙuri zai haɗa da yarda da laifinmu, neman gafara, da kuma ƙoƙarin mu gyara abin da muka ɓata yadda zai yiwu. <> If we are sincere, our apology will include an admission of any wrong, a seeking of forgiveness, and an effort to undo damage to the extent possible.
  2. Littafin nan Biomimicry—Innovation Inspired by Nature ya ce: “Abubuwa masu rai sun yi kome da muke son mu yi, ba tare da shan mai da ake samu daga ƙasa ba, halaka duniya, ko kuma ɓata rayuwarsu ta nan gaba.” <> Notes the book Biomimicry—Innovation Inspired by Nature: “Living things have done everything we want to do, without guzzling fossil fuel, polluting the planet, or mortgaging their future.”
  3. Sa’ad da ɗaya cikin tumakin ya ɓata, sai mutumin ya bar tumaki casa’in da tara a cikin jeji kuma ya je neman tunkiyar da ta ɓata har ‘ya same’ ta. <> When one of the sheep was missing, the man left the 99 behind in the wilderness and went after the lost sheep ‘until he found it.’
  4. Saboda “duniya duka kuwa tana hannun Mugun” abubuwan da za su iya nauyaya mu suna iya gajiyar da mu kuma su ɓata daidaitawarmu na Kirista. <> Because “the whole world is lying in the power of the wicked one,” we are surrounded by negative forces that can wear us down and erode our Christian balance.
  5. Bai ɓata masa rai ba. <> Of course not!
  6. Yana ganin na ‘ɓata’ ilimin da nike da shi ta wajen yin aikin goge-goge don na taimaka wa kaina a hidima. <> He felt that I had ‘wasted’ my education by taking a job as a cleaner to support me in my ministry.
  7. ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YIN ADDU’A ƁATA LOKACI NE? <> COVER SUBJECT | DOES IT DO ANY GOOD TO PRAY?
  8. (Nehemiah 2:10, 19) Abokan gaban Nehemiya sun ƙudurta ɓata shirin Nehemiya na ginin, har ya kai ga yin ƙulle-ƙulle na mugunta. <> (Nehemiah 2:10, 19) Nehemiah’s enemies were bent on stopping Nehemiah’s building plans, even resorting to evil schemes.
  9. 11 Tun da yake mu Kiristoci ne, ya kamata mu guji yin abin da zai sa mu ɓata wa Allah rai. <> 11 As Christians, we need to resist pressure to do things that would displease God.
  10. Alal misali, wani yana iya ɓata mana rai, ko da bai da niyyar yin hakan. <> For example, someone may offend us, even with well-intentioned words.
  11. Wannan ba ɓata lokaci ba kawai, domin an yi wa mutane 265,469 baftisma, ta wannan aikin, suka zama Shaidun Jehovah suna nuna a fili cewa sun ƙi da nuna ƙarfi. <> This was not time wasted, for as a result of this activity, 265,469 persons were baptized as Witnesses of Jehovah, thus showing publicly their categorical rejection of violence.
  12. Babu wuri a ikilisiya domin ɓata suna da yake ta da ayyukan jiki irin su “hasala” da kuma “tsatsaguwa.” <> There is no room in the congregation for slanderous speech that stirs up such works of the flesh as “dissensions” and “divisions.”
  13. Sa’ad da ni da Eva muka sauke karatu, sai muka soma hidimar majagaba ba tare da ɓata lokaci ba. <> As soon as Eva and I completed our schooling, we entered the pioneer service.
  14. 17 Tarayyar banza takan ɓata halin kirki, amma cuɗanya mai kyau takan kawo sakamako mai kyau. <> 17 Although bad associations spoil useful habits, good associations produce fine results.
  15. Ya kamata lokacin ya zama na farin ciki da bege mai kyau, amma wasu da suke zawarci sun ɓata shi ta yin wasa da lalata. <> That period should be a joyful time, full of hope and anticipation, but some young couples mar it by toying with immorality.
  16. Waɗanda suke zama a irin waɗannan ƙasashe sun son su sa hannu a takardar don ba sa son su kashe kuɗi ko kuma ɓata lokaci, amma hakan ba dalilin da ya sa aka shirya wannan takardar ba. <> Not understanding the Declaration Pledging Faithfulness, some who live where divorce is possible have asked about signing such a document rather than face any complications or inconveniences.
  17. Kafin mutane su gama halaka kansu, Allah zai halaka waɗanda suke ɓata duniya. <> Before all life on this earth is eradicated, God will step in to destroy those destroying the earth.
  18. Mutumin ya fahimci cewa idan yana wa’azi kuma yana sayar da wannan abu, hakan zai ɓata sunan ikilisiya kuma ya ɓata dangantakarsa da Allah. <> The man discerned that if he preached publicly but still sold such a product, this would put the congregation in a bad light and could damage his relationship with God.
  19. (2 Korinthiyawa 11:3) Shaiɗan yana ɓata azantan mutane kuma ya dagula tunaninsu. <> (2 Corinthians 11:3) Satan corrupts people’s minds and warps their thinking.
  20. Abin da ya faru tsakanin ta da kishiyarta mai suna Peninnah ya ɓata mata rai sosai. <> Recall that she was sorely vexed over a family situation involving her rival wife, Peninnah.
  21. Mis 19:11—Ka kwantar da hankalinka idan an ɓata maka rai (w14-E 12/1 12-13) <> Pr 19:11—Remain calm if you are offended (w14 12/1 12-13)
  22. An yi wa Yahudawa da kuma shigaggu dubu uku da suka saurari jawabin Bitrus baftisma babu ɓata lokaci. <> The three thousand Jews and proselytes who listened to Peter’s speech at Pentecost likewise got baptized without delay.
  23. Kirista yana iya ɓata lokacinsa a kan abubuwan da ba a haramta ba, kamar yin abubuwan da muke so ko karatu ko kallon talabijin ko yawon shakatawa ko sayayya da biɗan fasaha ko alatu na zamani. <> A Christian can easily waste an excessive amount of time on things that are not wrong in themselves, such as hobbies, recreational reading, TV watching, sightseeing, window shopping, and seeking out the latest electronic gadgets or luxuries.
  24. Yoh. 18:9, 10, 16, 19) Da yake Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furcin nan “sa’a ɗaya,” hakan ya nuna cewa wannan aukuwa zai faru babu ɓata lokaci. <> 18:9, 10, 16, 19) The Bible’s use of the words “one hour” shows that this event will take place relatively swiftly.
  25. Wannan tsoron ɓata masa rai tana sa su ƙi halin son kai na duniyar Shaiɗan. <> This wholesome fear of displeasing him helps them to resist the spirit of Satan’s world.

[17-08-16 07:23:42:497 EDT]

Examples