Difference between revisions of "Quran/18/tanzil"

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search
Line 32: Line 32:
 
# [[18]]|[[27]]|[[Ka]] [[karanta]] [[abin]] [[da]] [[aka]] [[yi]] [[wahayi]] [[zuwa]] [[gare]] [[ka]], [[na]] [[littafin]] [[ubangiji|Ubangijinka]]. [[babu|Babu]] [[mai]] [[musanyawa]] [[ga]] [[kalmomi|kalmominSa]] [[kuma]] [[ba]] [[za]] [[ka]] [[sami]] [[wata]] [[madogara]] [[ba]] [[daga]] [[wani|waninsa]].
 
# [[18]]|[[27]]|[[Ka]] [[karanta]] [[abin]] [[da]] [[aka]] [[yi]] [[wahayi]] [[zuwa]] [[gare]] [[ka]], [[na]] [[littafin]] [[ubangiji|Ubangijinka]]. [[babu|Babu]] [[mai]] [[musanyawa]] [[ga]] [[kalmomi|kalmominSa]] [[kuma]] [[ba]] [[za]] [[ka]] [[sami]] [[wata]] [[madogara]] [[ba]] [[daga]] [[wani|waninsa]].
 
# [[18]]|[[28]]|[[Ka]] [[haƙurtar da|hakurtar da]] [[ranka]] [[tare]] [[da]] [[wadanda]] [[ke]] [[kiran]] [[ubangiji|Ubangijinsu]], [[safe]] [[da]] [[maraice]], [[suna]] [[nufin]] [[yarda|yardarSa]]. [[kuma|Kuma]] [[kada]] [[idanu|idanunka]] [[su]] [[juya]] [[daga]] [[bari|barinsu]], [[kana]] [[nufin]] [[ƙawa|kawar]] [[rayuwar]] [[duniya]]. [[kuma|Kuma]] [[kada]] [[ka]] [[bi]] [[wanda]] [[muka|Muka]] [[shagaltar da]] [[zuciya|zuciyarsa]] [[daga]] [[hukunci|hukuncinMu]], [[kuma]] [[ya]] [[bi]] [[son]] [[zuciyar|zuciyarsa]], [[alhali]] [[kuwa]] [[al'amarin|al'amarinsa]] [[ya]] [[kasance]] [[yin]] [[barna]].
 
# [[18]]|[[28]]|[[Ka]] [[haƙurtar da|hakurtar da]] [[ranka]] [[tare]] [[da]] [[wadanda]] [[ke]] [[kiran]] [[ubangiji|Ubangijinsu]], [[safe]] [[da]] [[maraice]], [[suna]] [[nufin]] [[yarda|yardarSa]]. [[kuma|Kuma]] [[kada]] [[idanu|idanunka]] [[su]] [[juya]] [[daga]] [[bari|barinsu]], [[kana]] [[nufin]] [[ƙawa|kawar]] [[rayuwar]] [[duniya]]. [[kuma|Kuma]] [[kada]] [[ka]] [[bi]] [[wanda]] [[muka|Muka]] [[shagaltar da]] [[zuciya|zuciyarsa]] [[daga]] [[hukunci|hukuncinMu]], [[kuma]] [[ya]] [[bi]] [[son]] [[zuciyar|zuciyarsa]], [[alhali]] [[kuwa]] [[al'amarin|al'amarinsa]] [[ya]] [[kasance]] [[yin]] [[barna]].
# [[18]]|[[29]]|[[kuma|Kuma]] [[ka]] [[ce]]: "[[gaskiya|Gaskiya]] [[daga]] [[ubangiji|Ubangijinku]] [[take]]." [[saboda|Saboda]] [[haka]] [[wanda]] [[ya]] [[so]], [[to]], [[ya]] [[yi]] [[imani]], [[kuma]] [[wanda]] [[ya]] [[so]], [[to]], [[ya]] [[kafirta]]. [[lalle|Lalle]] [[ne]] [[Mu]], [[mun|Mun]] [[yi]] [[tattali]] [[domin]] [[azzalumai]] [[wata]] [[wuta]] [[wadda]] [[shamakunta]], [[sun]] [[kewaye]] [[da]] [[su]]. [[kuma|Kuma]] [[idan]] [[sun]] [[nemi]] [[taimako]] [[sai]] [[a]] [[taimake]] [[su]] [[da]] [[wani]] [[ruwa]] [[kamar]] [[dabzar]] [[mai]], [[yana]] [[soye]] [[fuskoki]]. [[tir|Tir]] [[da]] [[abin shan|abin shansu]], [[kuma]] [[wutar]] [[ta]] [[yi]] [[munin]] [[zama]] [[mahutarsu]].
+
# [[18]]|[[29]]|[[kuma|Kuma]] [[ka]] [[ce]]: "[[gaskiya|Gaskiya]] [[daga]] [[ubangiji|Ubangijinku]] [[take]]." [[saboda|Saboda]] [[haka]] [[wanda]] [[ya]] [[so]], [[to]], [[ya]] [[yi]] [[imani]], [[kuma]] [[wanda]] [[ya]] [[so]], [[to]], [[ya]] [[kafirta]]. [[lalle|Lalle]] [[ne]] [[Mu]], [[mun|Mun]] [[yi]] [[tattali]] [[domin]] [[azzalumai]] [[wata]] [[wuta]] [[wadda]] [[shamakunta]], [[sun]] [[kewaye]] [[da]] [[su]]. [[kuma|Kuma]] [[idan]] [[sun]] [[nemi]] [[taimako]] [[sai]] [[a]] [[taimake]] [[su]] [[da]] [[wani]] [[ruwa]] [[kamar]] [[dabzar]] [[mai]], [[yana]] [[soye]] [[fuskoki]]. [[tir|Tir]] [[da]] [[abin shan|abin shansu]], [[kuma]] [[wutar]] [[ta]] [[yi]] [[munin]] [[zama]] [[mahuta|mahutarsu]].
# [[18]]|[[30]]|[[lalle|Lalle]] [[ne]] [[wadanda]] [[suka]] [[yi]] [[imani]] [[kuma]] [[suka]] [[aikata]] [[ayyukan]] [[kwarai]] [[lalle]] [[ne]] [[Mu]] [[ba]] [[Mu]] [[tozartar]] [[da]] [[ladar]] [[wanda]] [[ya]] [[kyautata]] [[aiki]].
+
# [[18]]|[[30]]|[[lalle|Lalle]] [[ne]] [[wadanda]] [[suka]] [[yi]] [[imani]] [[kuma]] [[suka]] [[aikata]] [[ayyukan]] [[kwarai]] [[lalle]] [[ne]] [[Mu]] [[ba]] [[Mu]] [[tozarta|tozartar]] [[da]] [[ladar]] [[wanda]] [[ya]] [[kyautata]] [[aiki]].
 
# [[18]]|[[31]]|[[Wadannan]] [[suna]] [[da]] [[gidajen]] [[Aljannar]] [[zama]], [[koramu]] [[na]] [[gudana]] [[daga]] [[karkashinsu]], [[ana]] [[sanya]] [[musu]] [[kawa]], [[a]] [[cikinsu]], [[daga]] [[mundaye]] [[na]] [[zinariya]], [[kuma]] [[suna]] [[tufantar]] [[wadansu]] [[tufafi]] [[kore]], [[na]] [[alharini]] [[rakiki]] [[da]] [[alharini]] [[mai]] [[kauri]] [[suna]] [[kishingide]] [[a]] [[cikinsu]], [[a]] [[kan]], [[karagu]]. [[Madalla]] [[da]] [[sakamakonsu]]. [[kuma|Kuma]] [[Aljanna]] [[ta]] [[kyautatu]] [[da]] [[zama]] [[wurin]] [[hutawa]].
 
# [[18]]|[[31]]|[[Wadannan]] [[suna]] [[da]] [[gidajen]] [[Aljannar]] [[zama]], [[koramu]] [[na]] [[gudana]] [[daga]] [[karkashinsu]], [[ana]] [[sanya]] [[musu]] [[kawa]], [[a]] [[cikinsu]], [[daga]] [[mundaye]] [[na]] [[zinariya]], [[kuma]] [[suna]] [[tufantar]] [[wadansu]] [[tufafi]] [[kore]], [[na]] [[alharini]] [[rakiki]] [[da]] [[alharini]] [[mai]] [[kauri]] [[suna]] [[kishingide]] [[a]] [[cikinsu]], [[a]] [[kan]], [[karagu]]. [[Madalla]] [[da]] [[sakamakonsu]]. [[kuma|Kuma]] [[Aljanna]] [[ta]] [[kyautatu]] [[da]] [[zama]] [[wurin]] [[hutawa]].
 
# [[18]]|[[32]]|[[kuma|Kuma]] [[ka]] [[buga]] [[musu]] [[misali]] [[da]] [[wadansu]] [[maza]] [[biyu]]. [[Mun]] [[sanya]] [[wa]] [[dayansu]] [[gonaki]] [[biyu]] [[na]] [[inabobi]], [[kuma]] [[muka|Muka]] [[kewayesu]] [[da]] [[itacen]] [[dabinai]], [[kuma]] [[muka|Muka]] [[sanya]] [[shuka]] [[a]] [[tsakaninsu]] ([[su]] [[gonakin]]).
 
# [[18]]|[[32]]|[[kuma|Kuma]] [[ka]] [[buga]] [[musu]] [[misali]] [[da]] [[wadansu]] [[maza]] [[biyu]]. [[Mun]] [[sanya]] [[wa]] [[dayansu]] [[gonaki]] [[biyu]] [[na]] [[inabobi]], [[kuma]] [[muka|Muka]] [[kewayesu]] [[da]] [[itacen]] [[dabinai]], [[kuma]] [[muka|Muka]] [[sanya]] [[shuka]] [[a]] [[tsakaninsu]] ([[su]] [[gonakin]]).

Revision as of 14:30, 10 November 2019

Done with https://pteo.paranoiaworks.mobi/diacriticsremover/ and https://regexr.com/3geqs, original text from http://tanzil.net/trans/ha.gumi

 1. 18|1|Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bawansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.
 2. 18|2|Madaidaici, domin Ya yi gargadi da azaba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushara ga muminai, wadanda suke aikata ayyuka na kwarai da (cewa) suna da wata lada mai kyau.
 3. 18|3|Suna masu zama a cikinta har abada.
 4. 18|4|Kuma Ya yi gargadi ga wadanda suka ce: "Allah yana da da."
 5. 18|5|Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyayensu ba su da shi, abin da ke fita daga bakunansu ya girma ga ya zama kalmar fada! Ba su fadan kome face karya.
 6. 18|6|To, ka yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai domin ba su yi imani da wannan labari ba saboda bakin ciki.
 7. 18|7|Lalle ne Mu, Mun sanya abin da ke kan kasa wata kawa ce gare ta, domin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
 8. 18|8|Kuma lalle Mu, Masu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turbaya kekasasshiya ne.
 9. 18|9|Ko kuwa ka yi zaton cewa ma'abuta kogo da allo sun kasance abin mamaki daga ayoyin Allah?
 10. 18|10|A lokacin da samarin suka tattara zuwa ga kogon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka ba mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka saukake mana (samun) shiriya daga al'amarinmu."
 11. 18|11|Sai Muka yi duka a kan kunnunwansu, a cikin kogon, shekaru masu yawa.
 12. 18|12|Sa'an nan Muka tayar da su, domin Mu san wane dayan kungiyoyin biyu suka fi lissafi ga abin da suka zauna na lokacin.
 13. 18|13|Mu ne ke jeranta maka labarinsu da gaskiya. Lalle ne su, wadansu samari ne. Sun yi imani da Ubangijinsu, kuma Muka kara musu wata shiriya.
 14. 18|14|Kuma Muka daure a kan zukatansu, a lokacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da kasa. Ba za mu kirayi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, hakika, mun fadi abin da ya ketare haddi a sa'an nan."
 15. 18|15|"Ga wadannan mutanenmu sun riki waninSa abin bautawa! Don me ba su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (wadanda ake bautawar)? To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya kaga karya ga Allah?"
 16. 18|16|"Kuma idan kun nisance su su da abin da suke bautawa, face Allah, to, ku tattara zuwa ga kogon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya saukake muku madogara daga al'amarinku."
 17. 18|17|Kuma kana ganin rana idan ta fito tana karkata daga kogonsu wajen dama kuma idan ta fadi tana gurgura su wajen hagu, kuma su, suna a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shi ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya batar to ba za ka samar masa wani majibinci mai shiryarwa ba.
 18. 18|18|Kuma kana zaton su farkakku ne, alhali kuwa su masu barci ne. Muna juya su wajen dama da wajen hagu, kuma karensu yana shimfide da zira'o'in kafafuwansa ga farfajiya (ta kogon). Da ka leka (a kan) su (da) lalle ne, ka juya daga gare su a guje kuma (da) lalle ne ka cika da tsoro daga gare su.
 19. 18|19|Kuma kamar wannan ne Muka tayar da su, domin su tambayi juna a tsakaninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mene ne lokacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini daya ko sashen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da dayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya duba wanne ne mafi tsarki ga abin dafawa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."
 20. 18|20|"Lalle ne su idan sun kama ku, za su jefe ku, ko kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma ba za ku sami babban rabo, ba, a sa'an nan har abada."
 21. 18|21|Kuma kamar wancan ne, Muka nuna su (gare su) domin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a babu shakka a cikinta. A lokacin da suke jayayyar al'amarinsu a tsakaninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Wadanda suka rinjaya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riki masallaci a kansu."
 22. 18|22|Za su ce: "Uku ne da na hudunsu karensu."Kuma suna cewa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jifa a cikin duhu. Kuma suna cewa, "Bakwai ne da na takwas dinsu karensu."Ka ce: "Ubangijina ne Mafi sani ga kidayarsu, babu wanda ya san su face kadan."Kada ka yi jayayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kowa daga gare su a cikin al'amarinsu.
 23. 18|23|Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatawa ne ga wancan a gobe."
 24. 18|24|Face idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "tsammani na ga Ubangijina, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya."
 25. 18|25|Kuma suka zauna a cikin kogonsu shekaru dari uku kuma suka dada tara.
 26. 18|26|Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shi ne da (sanin) gaibin sammai da kasa. Mune ne ya yi ganinSa da jinSa! Ba su da wani majibinci baicinSa kuma ba Ya tarayya da kowa a cikin hukuncinsa."
 27. 18|27|Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littafin Ubangijinka. Babu mai musanyawa ga kalmominSa kuma ba za ka sami wata madogara ba daga waninsa.
 28. 18|28|Ka hakurtar da ranka tare da wadanda ke kiran Ubangijinsu, safe da maraice, suna nufin yardarSa. Kuma kada idanunka su juya daga barinsu, kana nufin kawar rayuwar duniya. Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhali kuwa al'amarinsa ya kasance yin barna.
 29. 18|29|Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Saboda haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Lalle ne Mu, Mun yi tattali domin azzalumai wata wuta wadda shamakunta, sun kewaye da su. Kuma idan sun nemi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yana soye fuskoki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi munin zama mahutarsu.
 30. 18|30|Lalle ne wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai lalle ne Mu ba Mu tozartar da ladar wanda ya kyautata aiki.
 31. 18|31|Wadannan suna da gidajen Aljannar zama, koramu na gudana daga karkashinsu, ana sanya musu kawa, a cikinsu, daga mundaye na zinariya, kuma suna tufantar wadansu tufafi kore, na alharini rakiki da alharini mai kauri suna kishingide a cikinsu, a kan, karagu. Madalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa.
 32. 18|32|Kuma ka buga musu misali da wadansu maza biyu. Mun sanya wa dayansu gonaki biyu na inabobi, kuma Muka kewayesu da itacen dabinai, kuma Muka sanya shuka a tsakaninsu (su gonakin).
 33. 18|33|Kowace gona daga biyun, ta bayar da amfaninta, kuma ba ta yi zaluncin kome ba daga gare shi. Kuma Muka bubbugar da koramu a tsakaninsu.
 34. 18|34|Kuma dan itace ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abokinsa, alhali kuwa yana muhawara da shi, "Ni ne mafifici daga gare ka a wajen dukiya, kuma mafi izza a wajen jama'a."
 35. 18|35|Kuma ya shiga gonarsa, alhali yana mai zalunci ga kansa, ya ce: "Ba ni zaton wannan za ta halaka har abada."
 36. 18|36|"Kuma ba ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiina, to, lalle ne, zan sami abin da yake mafi alheri daga gare ta ya zama makoma."
 37. 18|37|Abokinsa ya ce masa, alhali kuwa yana muhawara da shi, "Ashe ka kafirta da wanda Ya halitta ka daga turbaya, sa'an nan daga digon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"
 38. 18|38|"Amma ni, shi ne Allah Ubangijina, kuma ba zan tara kowa da Ubangijina ba"
 39. 18|39|"Kuma don me, a lokacin da ka shiga gonarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) babu wani karfi face game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi karanci daga gare ka a wajen dukiya da diya."
 40. 18|40|"To, akwai fatan Ubangijina Ya ba ni abin da yake mafi alheri daga gonarka, kuma ya aika azaba a kanta (ita gonarka) daga sama, sai ta wayi gari turbaya mai santsi."
 41. 18|41|"Ko kuma ruwanta ya wayi gari fakakke, saboda haka, ba za ka iya nemo shi ba dominta."
 42. 18|42|Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itacensa, sai ya wayi gari yana juyar da tafunansa biyu, saboda abin da ya kashe a cikinta, alhali kuwa ita tana kwance a kan rassanta, kuma yana cewa, "Kaitona, da dai ban tara wani da Ubangijina ba!"
 43. 18|43|Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, wadanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba.
 44. 18|44|A can taimako da jibinta ga Allah yake. Shi ne kawai Gaskiya, shi ne Mafifici ga lada kumaMafi fici ga akiba.
 45. 18|45|Ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin kasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wayi gari dudduga, iska tana shikar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ikon yi ne a kan dukan kome.
 46. 18|46|Dukiya da diya, su ne kawar rayuwar duniya, kuma ayyuka masu wanzuwa na kwarai sun fi zama alheri a wurin Ubangijinka ga lada kuma sun fi alheri ga buri.
 47. 18|47|Kuma a ranar da Muke tafiyar da duwatsu, kuma ka ga kasa bayyane, kuma Mu tara su har ba Mu bar kowa ba daga gare su.
 48. 18|48|Kuma a gitta su ga Ubangijinka suna sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne hakika kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lokaci. A'a, kun riya cewa ba za Mu sanya mukuwani lokacin haduwa ba."
 49. 18|49|Kuma aka aza littafin ayyuka, sai ka ga masu laifi suna masu jin tsoro daga abin da ke cikinsa, kuma suna cewa "Kaitonmu! Mene ne ga wannan littafi, ba ya barin karama, kuma ba ya barin babba, face ya kididdige ta?" Kuma suka sami abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa.
 50. 18|50|Kuma a lokacin da Muka ce wa malaiku, "Ku yi sujada ga Adamu." Sai suka yi sujada face Iblisa, ya kasance daga aljannu sai ya yi fasikanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kuna rikon sa, shi da zuriyarsa, su zama majibinta baicin Ni, alhali kuwa su makiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzalumai.
 51. 18|51|Ban shaida musu halittar sammai da kasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rayukansu ba kuma ban kasance mai rikon masu batarwa (da wani) su zama mataimaka ba.
 52. 18|52|Kuma da ranar da Allah Yake cewa, "Ku kirayi abokan tarayyaTa, wadanda kuka riya." Sai su kiraye su, sai ba za su karba musu ba, kuma Mu sanya Maubika (Mahalaka) a tsakaninsu,
 53. 18|53|Kuma masu laifi suka ga wuta suka tabbata lalle ne, su masu, auka mata ne, kuma ba su sami majuya ba daga gare ta.
 54. 18|54|Kuma lalle ne, hakika, Mun jujjuya, a cikin wannan Alkur'ani, daga kowane irin misali ga mutane (domin su gane, su bi shari'a), kuma mutum ya kasance mafi yawan abu ga jidali.
 55. 18|55|Kuma babu abin da ya hana mutane su yi imani a lokacinda shiriya ta zo musu, kuma su nemi gafara daga Ubangijinsu, face hanyar farko ta je musu ko kuma azaba ta je musu nau'i-nau'i.
 56. 18|56|Kuma ba Mu aika Manzanni ba face suna masu bayar da bushara kuma masu gargadi, kuma wadanda suka kafirta suna jidali da karya domin su bata gaskiya da ita, kuma suka riki ayoyiNa da abin da aka yi musu gargadi da shi abin izgili.
 57. 18|57|Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda aka tunatar game da ayoyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannayensa suka gabatar? Lalle ne Mu, Mun sanya abubuwan rufi a kan zukatansu domin kada su fahimce shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan ka kiraye su zuwa ga shiriya, to, ba za su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
 58. 18|58|Kuma Ubangijinka Mai gafara ne, Ma'abucin rahama. Da Yana kama su saboda abin da suka sana'anta, lalle ne, da Ya gaggauta azaba a gare su. A'a, suna da lokacin alkawari, (wanda) ba za su sami wata makoma ba, baicinSa.
 59. 18|59|Kuma wadancan alkaryu Mun halaka su, a lokacin da suka yi zalunci, kuma Muka sanya lokacin alkawarin, ga halaka su.
 60. 18|60|Kuma a lokacin da Musa ya ce wa yaronsa, "Ba zan gushe ba sai na isa mahadar teku biyu, ko in shude da tafiya shekara da shekaru."
 61. 18|61|To, a lokacin da suka isa mahadar tsakaninsu sai suka manta kifinsu, sai ya kama tafarkinsa a cikin teku kamar biga.
 62. 18|62|To, a lokacin da suka wuce ya ce wa yaronsa, "Ka kawo mana kalacinmu. Lalle ne hakika mun hadu da wahala daga tafiyarmu wannan."
 63. 18|63|(Yaron) ya ce: "Ka gani! A lokacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle ni, na manta kifin, kuma babu abin da yamantar da ni shi, face Shaidan, domin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin teku, da mamaki!"
 64. 18|64|Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance muna bida." Sai suka koma a kan gurabunsu, suna bibiya.
 65. 18|65|Sai suka sami wani bawa daga bayinMu, Mun ba shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu.
 66. 18|66|Musa ya ce masa, "Ko in bi ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?"
 67. 18|67|Ya ce: "Lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni, ba."
 68. 18|68|"Kuma yaya za ka yi hakuri a kan abin da ba ka kewayeda shi ba ga jarrabawa?"
 69. 18|69|Ya ce: "Za ka same ni, in Allah Ya so mai hakuri kuma ba zan saba maka ba ga wani umurni."
 70. 18|70|Ya ce: "To idan ka bi ni to kada ka tambaye ni daga kome sai na labarta maka ambato daga gare shi."
 71. 18|71|Sai suka tafi har a lokacin da suka hau a cikin jirgi, ya huje shi, ya ce, "Ka huje shi domin ya nutsar da mutanensa? Lalle ne, hakika, ka zo da wani babban abu!"
 72. 18|72|Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba?"
 73. 18|73|Ya ce: "Kada ka kama ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarina."
 74. 18|74|Sai suka tafi, har suka hadu da wani yaro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe ka kashe rai tsarkakakke, ba da wani rai ba? Lalle ne hakika ka zo da wani abu na kyama."
 75. 18|75|Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba?"
 76. 18|76|Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bayanta, to, kada ka abuce ni. Lalle ne, ka isa ga iyakar uzuri daga gare ni."
 77. 18|77|Sai suka tafi, har a lokacin da suka je wa mutanen wata alkarya, suka nemi mutanenta da su ba su abinci, sai suka ki su yi musu liyafa. Sai suka sami wani bango a cikinta yana nufin ya karye, sai (Halliru) ya tayar da shi mike. (Musa) ya ce: "Da ka so, lalle ne da ka karbi ijara a kansa."
 78. 18|78|Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Za ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin hakuri ba a kansa."
 79. 18|79|"Amma Jirgin, to, ya zama na wadansu matalauta ne suna aiki a cikin teku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhali kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yana karbewar kowane jirgi (lafiyayye) da kwace.
 80. 18|80|"Kuma amma yaron, to, uwayensa sun kasance muminai, to, sai muka ji tsoron ya kallafa musu kangara da kafirci."
 81. 18|81|"Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alheri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi."
 82. 18|82|"Kuma amma bangon, to, ya kasance na wadansu yara biyu ne, marayu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tasu a karkashinsa, kuma ubansu ya kasance sahihin mutum ne, domin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyakar karfinsu, kuma su, su fitar da taskarsu, saboda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnina. Wancan shi ne fassarar abin da ba ka iya yin hakuri ba a kansa."
 83. 18|83|Kuma suna tambayar ka daga zulkarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."
 84. 18|84|Lalle ne Mu Mun ba shi mulki a cikin kasa kuma Muka ba shi daga kowane abu, hanya (zuwa ga muradinsa).
 85. 18|85|Sai ya bi hanya.
 86. 18|86|Har a lokacin da ya isa ga mafadar rana, kuma ya same ta tana bacewa a cikin wani ruwa mai bakar laka, kuma ya sami wadansu mutane a wurinta. Muka ce: "Ya Zulkarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riki kyautatawa a cikinsu."
 87. 18|87|Ya ce: "Amma wanda ya yi zalunci, to za mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azaba, azaba abar kyama."
 88. 18|88|"Kuma amma wanda ya yi imani kuma ya aikata aikin kwarai to, za mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma za mu gaya masa sauki daga umurninmu."
 89. 18|89|Sa'an nan kuma ya bi hanya.
 90. 18|90|Har a lokacin da ya isa ga mafitar rana, ya same ta tana fita a kan wadansu mutane (wadanda) ba Mu sanya musu wata kariya ba daga barinta.
 91. 18|91|Kamar wancan alhali kuwa hakika, Mun kewaye da jarrabawa ga abin da ke gunsa.
 92. 18|92|Sa'an nan kuma ya bi hanya.
 93. 18|93|Har a lokacin da ya isa a tsakanin duwatsu biyu, ya sami wadansu mutane daga gabaninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba.
 94. 18|94|Suka ce: "Ya Zulkarnaini! Lalle ne Yajuja da Majuja masu barna ne a cikin kasa. To, ko za mu Sanya haraji saboda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakaninmu da tsakaninsu?"
 95. 18|95|Ya ce: "Abin da Ubangijina Ya mallaka mini, a cikinsa ya fi zama alheri. Sai ku taimakeni da karfi, in sanya babbar katanga a tsakaninku da tsakaninsu."
 96. 18|96|"Ku kawo mini guntayen bakin karfe". (Suka kai masa) har a lokacin da ya daidaita a tsakanin duwatsun biyu (ya sanya wuta a cikin karfen) ya ce: "Ku hura (da zugazugai)." Har a lokacin da ya mayar da shi wuta, ya ce: "Ku kawo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa."
 97. 18|97|Domin haka ba za su iya hawansa ba, kuma ba za su iya hujewa gare shi ba.
 98. 18|98|Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijina. Sai idan wa'adin Ubangijina ya zo, ya mayar da shi nikakke. Kuma wa'adin Ubangijina ya kasance tabbatacce."
 99. 18|99|Kuma Muka bar sashensu a ranar nan, yana garwaya a cikin sashe, kuma aka busa a cikin kaho sai muka tara su, tarawa.
 100. 18|100|Kuma Muka gitta Jahannama, a ranar nan ga kafirai gittawa.
 101. 18|101|Wadanda idanunsu suka kasance a cikin rufi daga tuna Ni, kuma sun kasance ba su iya saurarawa.
 102. 18|102|Shin fa, wadanda suka kafirta sun yi zaton (daidai ne) su riki wadansu bayiNa, majibinta baiciNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyafa ga kafirai.
 103. 18|103|Ka ce: "Ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka?"
 104. 18|104|"Wadanda aikinsu ya bace a cikin rayuwar duniya, alhali kuwa suna zaton lalle ne su, suna kyautata, (abin da suke gani) aikin kwarai?"
 105. 18|105|Wadancan ne wadanda suka kafirta da ayoyin Ubangijinsu, da kuma haduwa da Shi, sai ayyukansu suka baci. Saboda haka ba za Mu tsayar musu da awo ba a Ranar _iyama.
 106. 18|106|Wancan ne sakamakonsu shi ne Jahannama, saboda kafircinsu, kuma suka riki ayoyiNa da ManzanniNa abin izgili.
 107. 18|107|Lalle ne, wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyafa a gare su.
 108. 18|108|Suna madawwama a cikinta, ba su neman makarkata daga barinta.
 109. 18|109|Ka ce: "Da teku ta kasance tawada ga (rubutun) kalmomin Ubangijina, lalle ne da tekun ta kare a gabanin kalmomin Ubangijina su kare, kuma koda mun je da misalinsa domin kari."
 110. 18|110|Ka ce: "Ni, mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, saboda haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na kwarai. Kuma kada ya hada kowa ga bauta wa Ubangijinsa."