Difference between revisions of "Talk:dabbobi"

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search
(Created page with " ==Category:GlosbeGlosbe's example sentences of dabbobi [https://glosbe.com/ha/en/dabbobi?page=1&tmmode=MUST&stem=false#translationExamples]== #...")
 
(No difference)

Latest revision as of 17:08, 13 June 2019


Glosbe's example sentences of dabbobi [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar dabbobi:
  1. Jehobah ya ƙi karɓan hadayar waɗanda suka ƙi yin biyayya da umurninsa ta wajen miƙa dabbobi naƙasassu, marasa lafiya, ko kuma makafi.—Mal.
   Jehovah strongly censured those who flouted his direction by offering lame, sick, or blind animals for sacrifice. —Mal. [2]

  2. Kirista zai so ya bi daidai da nufin Allah lokacin da yake bi da dabbobi.
   A Christian would want to act in harmony with God’s will when dealing with animals. [3]

  3. Ba su sami masauki ba sa’ad da suka kai Bai’talami. Saboda haka, suka je suka zauna a ɗakin dabbobi.
   When they arrived at Bethlehem, the only place they could find to stay was a stable. [4]

  4. Waɗannan ɗakuna na Nuhu da iyalinsa ne, da kuma dabbobi da kuma abincinsu duka.
   The rooms were for Noah and his family, the animals, and the food all of them would need. [5]

  5. Saboda haka, ko da yake mutum yana da iko bisa dabbobi, ba zai ɓata ikon da aka ba shi ba amma zai yi amfani da shi daidai da ƙa’idodin Kalmar Allah.
   Thus, while man has dominion over animals, he should not abuse that authority but use it in harmony with the principles of God’s Word. [6]

  6. Duniya za ta cika da ’ya’yansa kuma za su ji daɗin kula da duniya da kuma dabbobi.
   The earth will abound with his offspring, who will delight to oversee it and enjoy its many life forms. [7]

  7. 22 Zabura 148:10 ta ce: “Dabbobi da dukan bisashe; masu-rarrafe da dukan tsuntsaye masu-fukafukai.”
   22 “You wild animals and all you domestic animals, you creeping things and winged birds,” says Psalm 148:10. [8]

  8. Wanda ma ya fi riba shi ne sayar da dabbobi.
   The business of selling animals was also very profitable. [9]

  9. Alal misali, hadayar dabbobi tana wakiltar mutuwar hadayar da Yesu zai yi, wadda za ta cim ma ainihin gafarta zunubai.
   For example, the sacrificing of animals foreshadowed Jesus’ sacrificial death, which would accomplish true forgiveness of sins. [10]

  10. (Ayuba 38:31-33) Jehovah ya yi magana da Ayuba game da wasu dabbobi—zaki da hankaka, awakan dutse da jakin dawa, ɓauna da jimina sai kuma doki da gaggafa.
   (Job 38:31-33) Jehovah directed Job’s attention to some of the animals —the lion and the raven, the mountain goat and the zebra, the wild bull and the ostrich, the mighty horse and the eagle. [11]

  11. Ishaya ya sake nanata cewa dabbobi ko mutane ba za su yi wa Isra’ilawa da za su dawo barazana ba.
   Isaiah further emphasized that the returnees would not be threatened by animals or humans. [12]

  12. Babu furanni ko itatuwa ko kuwa dabbobi.
   There were no flowers or trees or animals. [13]

  13. Suna iya sauka bisa ’yan adam da dabbobi.
   They can possess humans and animals. [14]

  14. Akwai wuri mai suna Swiss National Park, inda furanni da dabbobi dabam dabam masu kyau suke yaba wa Mahaliccinmu Mai Girma, Jehobah.
   It is also home to the Swiss National Park, where the area’s natural beauty and rich variety of flora and fauna praise our Grand Creator, Jehovah. [15]

  15. Da sannu sannu, Mulkin Allah zai sake mai da dangantaka ta salama da ta kasance cikin lambun Adnin tsakanin dabbobi, da kuma tsakanin dabbobi da mutane.
   In time, God’s Kingdom will even restore the peaceful relations that existed in the garden of Eden between animals, and between animals and humans. [16]

  16. Allah yana da babban aiki kafin ya mai da duniya ta zama wuri mai kyau domin dabbobi da kuma mutane su zauna cikinta.
   God had a lot more work to do to make the earth really nice for animals and people to live on. [17]

  17. Lalle sa zuciya ne mai girma—ciwo da tsufa ba za su ƙara kasancewa ba, za ka rayu ka more riban aikinka, salama za ta kasance tare da dabbobi!
   What a marvelous hope —sickness and old age will be no more, you can live on to enjoy the fruits of your labor, and there will be peace with the animals! [18]

  18. Shin wannan annabcin yana magana ne game da lokacin da dabbobi za su kasance cikin salama da ’yan Adam?
   Is this prophecy merely foretelling a time when animals will live in harmony with humans? [19]

  19. Ɗan Allah ya haɗa hannu da Ubansa Jehobah sa’ad da ya tsara ya kuma halicci dabbobi da shuke-shuke iri-iri a nan duniya da kuma sa’ad da ya kafa Aljanna da za ta zama gidan ’yan adam da aka halicce su cikin surar Jehobah.
   The Son of God also cooperated with his Father when Jehovah designed and created the huge variety of animal and plant life here on earth and when He prepared the Paradise that would be home to creatures made in Jehovah’s image and likeness. [20]

  20. 18 Sa’ad da yake matashi, a yawancin lokaci Dauda yana waje yana kiwon dabbobi.
   18 As a youth, David was often outside, shepherding the flocks. [21]

  21. Ta rufe shi da zani kuma ta kwantar da shi a inda ake sa wa dabbobi abinci.
   She wrapped him in soft cloths and laid him gently in a manger. [22]

  22. 10 Mutane ba za su ƙara jin tsoron yaƙi, aikata laifi, yunwa, ko kuma dabbobi masu kai hari ba.
   10 No more will people be threatened by war, crime, hunger, or even predatory animals. [23]

  23. 4 Bayan Ruwan Tufana, Allah ya ba wa mutane izini su ci nama na dabbobi amma ba jininsu ba.
   4 After the Noachian Flood, God gave humans permission to eat the flesh of animals but not the blood. [24]

  24. A wajen, dabbobi suna jan ƙatuwar guduma mai dutse mai ƙaifi ko kuma mai haƙorin ƙarfe bisa hatsin don su murtsuke ƙwayoyin daga ƙaiƙayin.
   There sledges with sharp stone or iron teeth on their underside were pulled over the grain by animals to break the stalks into pieces and loosen the kernels from the chaff. [25]

  25. Yaya hikimar Jehovah take a bayyane a halittun dabbobi?
   How is Jehovah’s wisdom evident in the animal creation [26]


Retrieved June 13, 2019, 1:00 pm via glosbe (pid: 24938)