Talk:izini

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Glosbe's example sentences of izini [1]

 1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar izini:
  1. A tashinsu kuma ta wurin Yesu Kristi, suna zama marasa mutuwa kuma marasa ɓatanci yadda Jehovah ya ba da izini, wanda shi “Sarki na zamanu, mara mutuwa, mara ganuwa, Allah makaɗaici.”
   In their resurrection and by means of Jesus Christ, they partake of immortality and incorruption granted by Jehovah, “the King of eternity, incorruptible, invisible, the only God.” [2]

  2. (b) Ta yaya ’yan’uwa waɗanda suke da izini suka bi da wani cikin ƙauna da ya yi tuhuma ta ƙarya a kan Shaidun Jehovah?
   (b) How did responsible brothers deal in a loving way with an individual who made false accusations against Jehovah’s Witnesses? [3]

  3. María Isabel ta karɓi izini don ta bi aji-aji tana rarraba takardun.
   Then, María Isabel asked to visit all the classrooms. [4]

  4. Filimon yana da izini ya hukunta Unisimus, amma Bulus ya gaya wa Filimon cewa ya “karɓe shi” hannu bibbiyu bisa ga ƙauna da kuma mutunci da ke tsakaninsu.—Filimon 10, 11, 15-18.
   Even though Philemon had the legal right to punish Onesimus severely, Paul asked Philemon to “receive him kindly,” on the basis of love and personal friendship. —Philemon 10, 11, 15-18. [5]

  5. Da ya ƙi, sai shugaban sansanin ya je wajen Heinrich Himmler shugaban SS (Schutzstaffel, rukuni mai girma na masu tsaron Hitler), ya nemi izini ya kashe Dickmann a gaban dukan sauran fursunoni na sansanin.
   When he refused, the camp commander contacted Heinrich Himmler, head of the SS (Schutzstaffel, Hitler’s elite guard), and asked permission to execute Dickmann in the presence of all other camp inmates. [6]

  6. Ba mu da takardar izini na masu koyarwa daga makarantar tauhidi.
   We have no appointment as teachers from a theological seminary. [7]

  7. (Matta 28:18-20) Da waɗannan kalmomi, Yesu ya ba “bayinsa” izini su yi ciniki “kowa ya ba shi gwargwadon iyawatasa,” har sai ya dawo.
   (Matthew 28:18-20) With these words, Jesus authorized his “slaves” to do business until his return, “each one according to his own ability.” [8]

  8. Ta nemi izini daga maigidanta kuma ta yi tafiyar kilomita 30 zuwa Dutsen Karmel wurin Elisha.
   With her husband’s permission, she traveled about 19 miles (30 km) to Elisha at Mount Carmel. [9]

  9. ’Yan’uwa waɗanda suke da izini suka tunkaro shi da ƙarin bayani.
   So responsible brothers approached him again with more information. [10]

  10. 4 Bayan Ruwan Tufana, Allah ya ba wa mutane izini su ci nama na dabbobi amma ba jininsu ba.
   4 After the Noachian Flood, God gave humans permission to eat the flesh of animals but not the blood. [11]

  11. Za a iya kashe mutum idan ya je gaban sarki ba tare da izini ba.
   Appearing before the king unsummoned could have meant death. [12]

  12. Don ta ta da marmarin malamanta da ’yan ajin, ta karɓi izini ta saka littattafai na Littafi Mai Tsarki dabam dabam a laburaren.
   To arouse the interest of her teacher and classmates, she obtained permission to place several Bible publications in the library. [13]

  13. Darius ya ɗaga hanin ya kuma ba da izini cewa a cire kuɗi daga ma’aji na sarauta a ba wa Yahudawa domin biyan bukatar aikin gina haikalin.
   So Darius rescinded the ban and authorized that money from the royal treasury be given to the Jews to help pay the expenses of the work. [14]

  14. Ko da yake Luca ya ji tsoro, ya nemi izini daga malaminsa don ya gyara wasu kurakurai da ke littafin, kuma malamin ya yarda.
   Although he felt hesitant, he asked permission to correct these false claims, and the teacher agreed. [15]

  15. Sa’ad da ta nemi izini daga wurin shugaban aikinta don ta halarci taron gunduma, ya faɗa da fushi cewa idan ta je, zai kore ta daga aiki.
   When she asked her employer for permission to take some days off to attend one of our conventions, he angrily retorted that if she went, he would fire her. [16]

  16. TAƘAITACCEN BAYANI Mutanen wani ƙauye da ke garin Stratton a jihar Ohio, sun kafa wata doka da ta bukaci duk waɗanda suke wa’azi gida-gida su karɓi izini kafin su yi hakan.
   FACTS The village of Stratton in the state of Ohio issues an ordinance that requires anyone engaging in door-to-door activity to obtain a permit. [17]

  17. Amma ya nemi izini ya rubuta labari game da yadda ya ɗauki Yesu Kristi.
   He offered instead to write an essay that would explain how he viewed Jesus Christ. [18]

  18. Ko da yake tana da ’yancin ta yi kala, Rut ta nemi izini.
   Despite having the right to glean, Ruth asked for permission before doing so. [19]

  19. Doka ta ce wanda ba shi da izini kada ya taɓa shi, ta ba da gargaɗi cewa za a kashe wanda ya taka dokar.
   The Law specified that it was not to be touched by unauthorized individuals, explicitly warning that violators would be punished by death. [20]

  20. Darektan ya ba ta izini ta ziyarci gidaje dabam dabam da suke wajen.
   The director gave her permission to visit the rooms of different residents. [21]

  21. Amma za a kashe duk wanda ya je gaban sarki ba tare da izini ba.—Esther 4:4-11.
   But anyone going in to the king when not summoned was put to death. —Esther 4:4-11. [22]

  22. Basu sayan kayan sata da ganga ba ko kuwa ɗauki wani abu babu izini. —Fitowa 20:15; Afisawa 4:28.
   They do not knowingly buy stolen property or take things without permission.—Exodus 20:15; Ephesians 4:28. [23]

  23. Wataƙila hakan zai ƙunshi karɓar takardar izini daga wajen ma’aikacin gwamnati da aka ba ikon yin haka, kuma a yi wa auren rajista.
   This may involve obtaining a license, using a State-authorized marrying agent, and perhaps registering the completed marriage. [24]

  24. Ɗaya cikinsu mahayin jan doki ne, kuma aka ba shi izini “ya ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma bashi babban takobi.”
   One of them rides a fiery-colored horse, and to him it was granted “to take peace away from the earth so that they should slaughter one another; and a great sword was given him.” [25]

  25. “Ya nemi izini ya yi addu’a ga Jehovah tare da mu.
   “He asked permission to pray to Jehovah with us. [26]


Retrieved December 5, 2019, 2:00 am via glosbe (pid: 22954)