bbchausa verticals/018 paranoia success

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Revision as of 00:04, 22 June 2017 by Admin (talk | contribs)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)
Jump to: navigation, search


Contents

#: Paranoid? It could be the key to your success [1] <> Dalilin da ya sa shugabannin ke bukatar ririta fargabarsu. [2]

#: There are lots of reasons Catherine Ulrich ought to feel confident [3] <> Akwai dalilai da yawa da za su sa Catherine Ulrich ta samu kwarin gwiwa [4]

#: in her achievements at work. [5] <> game da nasarorin da ta samu a bakin aiki. [6]

#: In fact, she has every reason to feel downright certain things are going well. [7] <> A gaskiya ma ta na da cikakkiyar hujjar da za ta sakankance cewa komai na tafiya daidai wa daida. [8]

#: Ulrich is chief product officer at Shutterstock [9] <> Ulrich ita ce jami'ar samar da sababbin haja a kamfanin Shutterstock [10]

#: and her firm has become one of the largest stock image companies in the world. [11] <> wanda ya na daya daga cikin manyan kamfanin samar da hotunan amfanin yau da kullum a fadin duniya. [12]

#: But Ulrich says shes always looking over her shoulder. [13] <> Sai dai kuma Ulrich ta ce a kullum ta na cikin dar-dar. [14]

#: Ill always be a little paranoid,” Ulrich admits. [15] <> "Ba zan iya rayuwa ba fargaba ba," in ji Ulrich. [16]

#: Im often thinking about whether the customer is going to find a better product out there. [17] <> "Koda yaushe na kan yi tunanin abokan huldarmu za su sami hajar da tafi ta mu a wurin wani kamfanin. [18]

#: Maybe it makes me sound weird, [19] <> Ba mamaki hakan ya sa na zama wata iri, [20]

#: but paranoia is one word that makes me stay on top.” [21] <> amma dai tsoro na daga cikin abinda ya sa mu ke ci gaba da yin zarra." [22]

#: Weird? [23] <> Wata iri? [24]

#: Perhaps not. [25] <> Ba lallai ba. [26]

#: Honing your fear is exactly what you need to do when youve mastered an industry. [27] <> Kasancewa cikin fargaba, shi ne babban makamin da ya kamata ka rike idan ka zamo na daya a wani fagen sana'a ko kasuwanci. [28]

#: If youre overseeing a company [29] <> Idan ka na shugabantar kamfani, [30]

#: or division thats currently beating the competition, [31] <> ko wani sashe a cikin kamfanin wanda ya yi abokan kasayya zarra, [32]

#: worrying about whats coming up behind you may be the only way to remain on top. [33] <> fargabar mai zai biyo baya na iya zaman hanya daya tak da za ta sa ka ci gaba da rike kambunka. [34]

#: Paranoia is good [35] <> Fargaba na da kyau [36]

#: Concern about whats next [37] <> Damuwa kan abinda zai biyo baya, [38]

#: is exactly what Bruce Aust thinks about [39] <> shi ne abinda ke ran Brust Aust [40]

#: every time he walks into a meeting with senior management. [41] <> don lokacin da zai tattauna da manyan shugabannin kamfaninsu. [42]

#: Aust has a big job: [43] <> Aust ya na da babban aiki: [44]

#: hes vice chairman of the NASDAQ, [45] <> shi ne mataimakin shugaban NASDAQ, [46]

#: the worlds second-largest stock market, [47] <> kasuwar hada-hadar hannayen jari mai daraja ta biyu a duniya, [48]

#: after the New York Stock Exchange. [49] <> bayan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York. [50]

#: He prefers to start those meetings celebrating his team's successes. [51] <> Ya kan fara tattaunawar ne ta hanyar yabawa nasarorin da kamfaninsu ya samu. [52]

#: Then its time to discuss what competitors are doing. [53] <> Daga nan kuma sai su fara tattauna abinda abokan kasayyarsu ke yi. [54]

#: Paranoia is good,” Aust says. [55] <> "Fargaba ta na da kyau," in ji Aust. [56]

#: Paranoia makes you think about your competitors, [57] <> "Fargaba na sa ka yi tunanin abokan kasayyarka, [58]

#: and thats going to make you better.” [59] <> wannan zai sa ka kara zage damtse." [60]

#: The key is harnessing that paranoia to create new ideas, according to Aust. [61] <> Babbar hanyar amfana da fargabar ita ce samar da sababbin dabaru, a cewar Aust. [62]

#: At NASDAQ, one way that happens is through the GIFT program, [63] <> A NASDAQ, su na da wani tsari mai taken GIFT, [64]

#: which encourages all 4,000 of the companys employees to present new ideas. [65] <> inda daukacin ma'aikatan kamfanin 4,000 ke kawo sababbin dabarun aiki. [66]

#: Proposals must include a P&L and detailed business plan, and then a senior team review these suggestions. [67] <> Duk shawarar da za a kawo sai ta hada da hasashen riba da faduwa, da cikakken tsarin gudanarwa, sai a mika ta ga manyan ma'aikata da za su yi nazari a kai. [68]

#: Approved ideas receive preliminary funding and a trial period. [69] <> Shawarwarin da aka amince da su za a zuba jari tare da ware musu lokacin gwaji. [70]

#: Not all of them work, and thats OK, Aust says. [71] <> Ba duka ne ke nasara ba, amma hakan ba matsala ba ce, in ji Aust. [72]

#: Showing that its alright to sometimes fail means more ideas come to the surface. [73] <> Yarda da cewa ba laifi ba ne don an fadi a wasu lokuta, shi ke sa sababbin shawarwari su ci gaba da fitowa. [74]

#: Among the bigger concepts that worked [75] <> Daga cikin sababbin dabarun da su ka yi aiki [76]

#: is the NASDAQs private market fund. [77] <> har da asusun hada-hadar hannun jarin kamfanonin da ke hannun daidaikun al'umma. [78]

#: It allows private companies to trade shares and [79] <> Aust ya ce NASDAQ na matukar samun kudi da wannan. [80]

#: this turned out to be a money maker, Aust says. [81] <> Aust ya kara da cewa ba NASDAQ ce ta kirkiro da wannan dabarar ba. Sauran abokan kasayya na yenta. [82]

#: That idea wasnt novel, [83] <> Amma wannan na daga cikin sirrin daukaka; [84]

#: other competitors were already doing it, Aust adds. [85] <> sa ido a kan abinda abokan kasayya ke yi. [86]

#: When Im in a meeting with upper management, [87] <> "Duk lokacin da nake ganawa da manyan shugabannin kamfani, [88]

#: I like to ask, [89] <> na kan tambayesu, [90]

#: What would competitors be saying in their meetings right now?’” Aust says. [91] <> me ku ke ji abokan kasayyarmu na cewa yanzu haka a tasu ganawar?'" [92]

#: Worrying about them is what will make you stay competitive.” [93] <> A cewar Aust, "Damuwa da su shi ne zai sa su kasa wuce ka." [94]

#: Staying at the top of your game [95] <> Rike kambunka [96]

#: Once youve harnessed your paranoia, [97] <> Daga zarar ka sanya fargaba a cikin lamarinka, [98]

#: its time to make sure your office culture is up to the challenge of staying at the top, says Chris Edmonds, [99] <> sai kuma ka tabbatar dabi'ar kamfaninka ta dace da ta masu rike kambinsu, in ji Chris Edmonds, [100]

#: management consultant and author of seven books, [101] <> mashawarci kan tafiyar da kamfanunnuka kuma marubucin littattafai bakwai, [102]

#: including The Culture Engine. [103] <> ciki har da 'The Culture Engine'. [104]

#: Often, [105] <> A mafi yawan lokuta, [106]

#: small companies [107] <> kananan kamfanoni [108]

#: stand a better chance of nurturing innovation to bring a product to market, [109] <> ne su ka fi damar samar da sababbin hajar da za su kai kasuwa, [110]

#: so big companies must figure out a way to stay nimble. [111] <> don haka wajibi ne ga manyan kamfanoni da su samo hanyoyin da su ma ba za a bar su a baya ba. [112]

#: If youre in a senior role, that means empowering your team, Edmonds says. [113] <> Idan kai babban ma'aikaci ne, hanyar ita ce ka karfafi na kasa da kai. [114]

#: If youre lower down in a red-tape-strangled company, its time to take risks. [115] <> Idan kuma kai karamin ma'aikaci ne to lokaci ya yi da za ka gwada karambani. [116]

#: Give the people who are talented and creative the power to make decisions. [117] <> Ka bai wa mutanen da ke da basirar kirkira damar daukar hukunci da kansu. [118]

#: This also requires courageous managers [119] <> Wannan na bukatar manajoji masu karfin halin [120]

#: to break bad policies in order to do whats needed. [121] <> halin da za su karya dokoki mara sa ma'ana domin cimma abinda aka sa gaba. [122]

#: Agility [123] <> Yi da wuri [124]

#: Shutterstock launched an idea earlier this year [125] <> Shutterstock ya kaddamar da wata sabuwar dabara a bana, [126]

#: spun out frompods’, little teams of five to 10 people it created purely to focus on customer needs, Ulrich says. [127] <> wacca aka samar ta hanyar kafa gungun mutane biyar zuwa 10 wadanda su ke zuzzurfan tunani kan bukatun abokan hulda. [128]

#: They came up with a new feature for the companys search function. [129] <> Sabuwar dabarar, in ji Ulrich, ita ce samar da sabuwar hanyar binciken hotuna a shafin kamfanin na intanet. [130]

#: It allows users to upload a photo and ask Shutterstock to show you similar pictures. [131] <> Sabuwar dabarar na bai wa abokan huldar Shutterstock damar saka hotunansu a shafin sannan su bukaci kamfanin da ya nemo musu hotunan da su ka yi kama da shi. [132]

#: It took a year from discussion in a pod to its launch. [133] <> Shekara guda aka dauka daga tattaunawa shawarar zuwa aiwatar da ita. [134]

#: a turn-around Ulrich says is lightning fast for new technology. [135] <> abinda Ulrich ta ce ya yi gaggawa matuka a tsarin kamfanonin fasahar zamani. [136]

#: Encouraging that kind of quick turnaround comes at a cost, Ulrich says. [137] <> Amma fa akwai hanzari ba gudu ba, in ji Ulrich. [138]

#: For her, it means always being worried, [139] <> Samar da irin wannan yanayi ya na tattare da kasancewa cikin fargaba a koda yaushe [140]

#: always thinking about whats coming from someone elsealways being a bit paranoid. [141] <> game da abinda sauran kamfanoni ke shiryawa. [142]

#: My whole life is more stressful because Im wired that way,” Ulrich says. [143] <> "Gaba daya rayuwata babu hutu saboda kullum ina cikin damuwa," in ji Ulrich. [144]

#: But theres also a big upside to that mind set. [145] <> Sai dai kuma akwai dimbin alfanu tattare da wannan dabi'a. [146]