makoki

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Noun

Tilo
makoki

Jam'i
makoka

m

 1. to grieve, mourning <> mai kuka ko mai baƙin cikin an rasa mutum.
  Ibrahim ya yi makoki sosai sa’ad da matarsa Saratu ta rasu <> Abraham mourned the loss of his beloved Sarah
 2. wurin da ake zama ana karɓar gaisuwa bayan an yi rasuwa.
 3. The plural form of maki; more than one maki.

Glosbe's example sentences of makoki

 1. makoki. <> Lamentations, Mourn, bereaved person, bereavement, dirge, grief, grieve, grieving, mourn, mourned, mourning ones, mourning, of grief, stricken.
  1. (Zabura 72:16) Ba za a yi jana’iza, makoki, makabarta, ɗakin gawawwaki da kuma baƙin ciki da ke biyo bayansu ba. <> (Psalm 72:16) No more funerals, wakes, cemeteries, morgues, or the misery that accompanies them.
  2. Yadda Za a Ta’azantar da Masu Makoki 6 <> Comforting Those Who Mourn 6
  3. 2 Muna yin rashin lafiya, makoki, kuma muna fuskantar gwaji iri-iri. <> 2 We also experience illness, bereavement, and other trials.
  4. “Ubangiji ya shafe ni . . . in yi ma dukan masu-makoki ta’aziyya.”—ISHAYA 61:1, 2. <> “Jehovah has anointed me . . . to comfort all the mourning ones.”—ISAIAH 61:1, 2.
  5. Me ya sa ake makoki a Shiloh? <> Why was Shiloh full of grief and mourning?
  6. Baƙin ciki, da makoki, da ganin ba abin da za mu iya yi sai su cika mutum. <> The pain, the grief, and the feelings of helplessness can seem unbearable.
  7. (Makoki 5:21) Jehobah ya amsa addu’ar da suka yi kuma mutanensa sun dawo suka ci gaba da bauta masa da farin ciki. <> (Lamentations 5:21) Jehovah answered that prayer, and his people returned to serve him with renewed joy.
  8. 7 Wasu sun ba da ƙarfafa ta ruhaniya ga masu makoki da suka sarƙu da Littafi Mai Tsarki ta karanta 2 Korinthiyawa 1:3-7. <> 7 Some have conveyed a spiritual blessing to grieving ones who are acquainted with the Bible by reading 2 Corinthians 1:3-7.
  9. (Zabura 132:7) Saboda haka, “matashin” Makoki 2:1 na nuni ga gidan bauta na Jehobah, ko kuma haikalinsa. <> (Psalm 132:7) Hence, the “footstool” of Lamentations 2:1 refers to Jehovah’s house of worship, or his temple.
  10. 4:17) Ta wurin aikin wa’azi na zamani, muna yi wa mutane da yawa masu makoki ta’aziyya. <> 4:17) As a result of our present-day preaching work, great comfort is being given to mourning ones.
  11. Babu shakka, sun ƙarfafa juna duk da yake suna makoki. <> Surely, though, each found in the company of the other some measure of comfort in the face of grief.
  12. Ka Yi Wa Masu Makoki Ta’aziyya <> Give Comfort to Those Who Grieve
  13. Ɗakin yana cike da dangi da suke makoki ne? <> Is the house filled with grieving relatives?
  14. Abubuwan da Jehobah ya ce game da yanayin Urushalima kamar yadda aka rubuta a littafin Makoki ya koya mana darussa biyu masu muhimmanci. <> Jehovah’s evaluation of Jerusalem’s situation as expressed in the book of Lamentations teaches us two vital lessons.
  15. Ibrahim ya yi makoki sosai sa’ad da matarsa Saratu ta rasu <> Abraham mourned the loss of his beloved Sarah
  16. Addu’ar Habakkuk, ko kuma waƙar makoki, tana ba mu dalili mai ƙarfi na yin murna cikin Jehovah, Allah mai cetonmu. <> Habakkuk’s prayer, or dirge, gives us strong reason to be joyful in Jehovah, the God of our salvation.
  17. (Makoki 3:22, 23) Duk cikin tarihi, bayin Allah a cikin yanayi mafi muni sun biɗi su kasance da hali mai kyau, har na farin ciki.—2 Korantiyawa 7:4; 1 Tasalonikawa 1:6; Yakubu 1:2. <> (Lamentations 3:22, 23) Throughout history, servants of God in the most difficult circumstances have sought to maintain a positive, even joyful, attitude.—2 Corinthians 7:4; 1 Thessalonians 1:6; James 1:2.
  18. 21, 22. (a) Ta yaya Yesu ya nuna baƙin cikinsa a gaban waɗanda suke makoki? <> 21, 22. (a) How did Jesus reveal his feelings for those who mourn?
  19. Za ka iya gayyatar mai makoki don ku ci abinci tare ko kuma ku ɗan zagaya gari. <> You could invite a bereaved person to a simple meal or to go for a walk.
  20. ’Yan’uwanmu sun fahimci cewa wannan ba lokacin gaya wa masu makoki game da tashin matattu ba. <> Our brothers discerned that immediately following the tsunami was not necessarily the best time to tell the grief-stricken victims about the resurrection hope.
  21. Irmiya ya ci gaba: “Gwamma waɗanda takobi ya kashe su da waɗanda aka kashe su da yunwa; Gama su suna shacewa, sokakku ne domin rashin anfanin ƙasa.”—Makoki 4:6, 9. <> Jeremiah continues: “Better have those slain with the sword proved to be than those slain by famine, because these pine away, pierced through for lack of the produce of the open field.”—Lamentations 4:6, 9.
  22. An rubuta littafin a shekara ta 607 K.Z., jim kaɗan da yi wa Urushalima kwanton ɓauna na watanni 18 kuma daga baya aka halaka ta, saboda haka littafin Makoki ya nuna baƙin cikin Irmiya sarai. <> Composed in 607 B.C.E. while the memory of the 18-month-long siege followed by the burning of Jerusalem is still fresh in the prophet’s mind, the book of Lamentations vividly expresses Jeremiah’s heartfelt anguish.
  23. Littafin Makoki ya ƙunshi tarin littattafan waƙoƙi biyar. <> The book of Lamentations is a collection of five lyrical poems.
  24. Ɗaya daga cikin ayyukan da Allah ya ɗanka masa shi ne ya “warkar da masu-karyayyen zuciya” kuma ya “yi wa dukan masu-makoki ta’aziyya.” <> Among other tasks that God assigned him, Jesus was “to bind up the brokenhearted” and “comfort all who mourn.”
  25. Muna makoki sa’ad da ɗan’uwanmu ya mutu, amma muna da bege. <> If a loved one dies, we grieve, but we do not lose hope.

[17-08-13 17:25:35:669 EDT]