meeting

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Noun

Singular
meeting

Plural
meetings

 1. A meeting is when a group of people come together to talk about something important. <> taro, haɗuwa, mitin (cognate)
  The meeting will be in the green room after lunch. I hope you'll be there. <> Za a yi mitin ɗin a koren ɗaki bayan an ci abincin rana. Da fatan za ku halarci wajen.
  1. So whoever would hope for the meeting with his Lord - let him do righteous work <> Sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai - Quran 18:110
  2. VOA ta shirya taron bita akan shirin yaki da cutar murar Tsuntsaye <> VOA organizes meeting to discuss Avian Flu prevention program [1]

Verb

Plain form
meet

Third person singular
meets

Simple past
met

Past participle
met

Present participle
meeting

 1. The present participle of meet.

Google translation of meeting

Taro, gamuwa.

 1. (noun) gamuwa <> meeting, encounter, connection, session; ganawa <> meeting, appointment; saduwa <> meeting, appointment;

[17-08-14 18:12:56:497 EDT]

Glosbe's example sentences of meeting

 1. meeting. <> Hidima, a, biya, gamu, sadu, su, taro, taron, taronmu, taronsu, ƙalubalen.
  1. Obviously, no law or standard proposed by any human, no matter how intelligent or sincere, can meet that need. <> Hakika, babu doka ko mizani da mutum ya kafa, ko yaya hikima da gaskiyar wannan mutumin da zai biya wannan bukata.
  2. What can be done to make meetings for field service practical and beneficial? <> Menene za a yi don a amfana daga taron fita wa’azi?
  3. He and his wife, Maureen, say that one of the blessings they are enjoying at Warwick is “meeting and working with the many wonderful brothers and sisters who have spent their life serving Jehovah at Bethel.” <> Shi da matarsa Maureen sun ce aiki a Warwick albarka ce domin “suna haɗuwa da kuma aiki tare da ’yan’uwa maza da mata masu kirki da suka daɗe sosai suna hidima a Bethel.”
  4. So I agreed to do as they said for three months, but I promised Jehovah that I would attend the meetings again when that time was up. <> Saboda haka, na gaya wa iyayena cewa zan daina halartar taro na tsawon wata uku. Amma na yi wa Jehobah alkawari cewa zan soma halartar taro da zarar na gama jarabawar.
  5. At those meetings and at assemblies and conventions, we consider Bible-based material that builds faith in God and his promises.—Heb. <> A wuraren taron nan da manyan taro, muna nazarin littattafai da ke sa mu kasance da bangaskiya ga Allah da kuma alkawuransa.—Ibran.
  6. We should take into consideration the background of our listeners when we engage in the Christian ministry or give talks at congregation meetings. <> Ya kamata mu yi la’akari da asalin masu sauraronmu sa’ad da muke yin hidima ta Kirista ko kuwa sa’ad da muke ba da jawabi a taron ikilisiya.
  7. Moses did not tell the Israelites in Egypt: ‘I will meet you at the Red Sea. <> Musa bai gaya wa Isra’ilawa da suke ƙasar Masar cewa: ‘Zan sadu da ku a Jar Teku.
  8. * What did you think of the meeting? <> * Kin ji daɗin taron kuwa?
  9. □ Service Meeting: <> □ Taron Hidima:
  10. Similarly today, we can find wise counselors and enjoy wholesome spiritual food at congregation meetings. <> Hakazalika a yau, za mu samu mashawarta masu hikima kuma mu more abinci na ruhaniya mai kyau a taron ikilisiya.
  11. Amos tells them: “Get ready to meet your God.” <> Amos ya ce masu: ‘Ku yi shiri ku gamu da Allahnku.’
  12. 15 Individuals wanting to become part of the Christian congregation must meet certain requirements. <> 15 Mutanen da suke so su shiga cikin ikilisiya ta Kiristoci dole ne su cika wasu farillai.
  13. 8 We will conclude our meeting today with the new song entitled “The Kingdom Is in Place—Let It Come!” <> 8 Za mu rufe taronmu na yau da sabuwar waƙar nan “An Kafa Mulkin a Sama—Bari Ya Zo!”
  14. (Proverbs 18:1) Imagine the disappointment of any who might have missed the meeting in the upper room in Jerusalem at Pentecost 33 C.E.! <> (Misalai 18:1) Ka yi tunanin yadda wanda ba ya taro a bene a Urushalima a shekara ta 33 K.Z., zai ji!
  15. Would you like to meet them when they come back?— <> Za ka so ka gan su sa’ad da aka ta da su?—
  16. Physical relief efforts help to meet short-term needs. <> Ba da gudummawar abubuwan jiki na kawo gamsuwa ta ɗan lokaci ne kawai.
  17. But I do read the Bible every day, attend meetings when my health permits, and enjoy participating in the ministry as much as I can. <> Amma har ila, ina karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Ƙari ga haka, ina zuwa taro da kuma wa’azi a duk lokacin da zan iya yin hakan.
  18. 15 At weekly meetings, Jehovah’s people receive the needed training and encouragement to be faithful Witnesses of Jehovah. <> 15 A taronsu na mako-mako, mutanen Jehobah suna samun koyarwa da kuma ƙarfafa da suke bukata don su kasance Shaidun Jehobah masu aminci.
  19. Note how the apostle Paul emphasizes that specific goal of Christian meetings in his first letter to the Corinthians. <> Ka lura da yadda manzo Bulus ya nanata wannan makasudi na taron Kirista a wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korintiyawa.
  20. To help us meet that challenge, “the faithful and discreet slave” prepared a book that is especially designed for our use in our Christian ministry. <> Don mu fuskanci wannan ƙalubalen, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya shirya wani littafin da za mu yi amfani da shi a hidimarmu ta Kirista.
  21. Where several congregations share the Kingdom Hall and a meeting cannot be rescheduled, the meeting may be canceled. <> A wurin da ikilisiyoyi da yawa suke amfani da Majami’ar Mulki guda kuma ba za su iya canja ranar taron a makon ba, suna iya soke taron.
  22. In addition, elders may arrange for talks to be recorded for infirm members of the congregation who are unable to attend the meetings. <> Ƙari ga hakan, dattawa za su iya sa a ɗauki jawabai domin ’yan’uwa marar lafiya da ke ikilisiyar da ba su samu halartar taron ba.
  23. (Ecclesiastes 9:5; Luke 23:43; John 5:28, 29; Revelation 21:3, 4) You may have started to attend meetings of Jehovah’s Witnesses and believe that they practice true worship. <> (Mai-Wa’azi 9:5; Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Wataƙila ka soma zuwa taron Shaidun Jehobah kuma ka fahimci cewa su ne suke bin Allah da gaske.

[17-08-14 23:14:38:112 EDT]