race

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

Noun

Singular
race

Plural
races

A relay race <> Gudun ba da sanda.
 1. A race is when people compete to see who is the fastest at either driving or running. <> tsere, gasa, gudu.
  The children were running a race. <> Yaran na tsere.
  There was a race to see who could finish first. <> An gudanar da gasar tsere don a gano wa zai gama da farko.
  The arms race. <> Gasar ƙera makamai = gasar sarrafa makamai.
  A relay race <> Gudun ba da sanda.
 2. horse race <> sukuwa, kurus.
  Race course. <> Filin sukuwa.
  Among the events, there was even a horse race at the race course. <> A cikin shagulgulan bikin har da tseren dawakai a filin sukuwa na Kano. [1]
 3. the human race <> jinsin ɗan Adam = bil Adama.
 4. (group descent) jini, ƙabila
  they are of the same race <> jininsu ɗaya.
  the black race <> baƙar fata.
  He is of mixed race. <> Shi ruwa biyu ne.

Verb

Plain form (yanzu)
race

3rd-person singular (ana cikin yi)
races

Past tense (ya wuce)
raced

Past participle (ya wuce)
raced

Present participle (ana cikin yi)
racing

 1. When a person races, he competes with other people to see who can go the fastest. <> garzaya, ruga da gudu, yi gudu da sauri.
  I jumped into the car and raced to the hospital <> Sai na fad'a mota na garzaya zuwa asibiti.
  He raced to get the to the bus <> Ya ruga da gudu don ya samu bas ɗin.
 2. bugawa
  When the chicks were puffed, the hens' hearts began to race and they called more frequently to the chicks. [2] <> Duk lokacin da 'yan tsaki suke numfashi da kyar, sai zuciyar kaji ta fara bugawa, inda za su yi ta kiran 'yan tsakin akai, akai. [3]
  My mind began to race. <> Sai na soma mugun tunani.


Google translation of race

Tseren.

 1. (noun) kabila <> tribe, clan, nationality, race; sukuwa <> horse race, race, ride;
 2. (verb) yi sukuwa <> race, ride;