zai

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search
 1. will / would / shall...
  zai zama <> will become
 2. he can/could <> zai iya.

Glosbe's example sentences of zai

 1. zai. <> Can, He will, affect, be, can, coming, could, he will, he would, might, possible, result, the, to, will, would.
  1. Idan da gaske muke, ba da haƙuri zai haɗa da yarda da laifinmu, neman gafara, da kuma ƙoƙarin mu gyara abin da muka ɓata yadda zai yiwu. <> If we are sincere, our apology will include an admission of any wrong, a seeking of forgiveness, and an effort to undo damage to the extent possible. | possible
  2. Saboda haka, ya dace a cikin wasiƙarsa zuwa ga Timotawus, manzo Bulus ainihi ya ambata ƙauna a cikin halayen da Timotawus zai kafa misali mai kyau a kai. <> It was fitting, then, that in his letter to Timothy, the apostle Paul specifically mentioned love as one of the qualities in which Timothy was to be exemplary.
  3. Hakika, babu doka ko mizani da mutum ya kafa, ko yaya hikima da gaskiyar wannan mutumin da zai biya wannan bukata. <> Obviously, no law or standard proposed by any human, no matter how intelligent or sincere, can meet that need. | can
  4. Kuma sa’ad da muka kafa makasudai da za mu iya cim ma, ayyukanmu na ruhaniya zai kawo mana ƙarin gamsuwa da farin ciki. <> And when we have balanced expectations and set reachable goals, our spiritual activities will bring us more satisfaction and joy. | will
  5. 9 Idan muna da tawali’u kuma muna a shirye mu dogara ga Jehobah, zai ba mu ruhunsa mai tsarki don ya yi mana ja-gora. <> 9 If we are humble and willing to depend on Jehovah, he will impart to us his holy spirit as a sure guide for our steps. | he will
  6. (Yusha’u 1:4; 4:9) Wannan gargaɗin yana da ma’ana a gare mu domin Jehobah zai hukunta waɗanda suke yin lalata kuma suke saka hannu a bauta marar tsarki a yau. <> (Hosea 1:4; 4:9) This warning has significance for us because Jehovah will hold an accounting against those practicing immorality and engaging in unclean worship today. | will
  7. Da haka ikonsa zai burge mu kuma mu motsa mu amince cewa shi Allah Mahalicci ne. <> We may thus be impressed by his power and be moved to acknowledge him as God the Creator. | be
  8. (Ishaya 55:7) Jehobah zai kula da bukatunsu, na zahiri da na ruhaniya.—Matta 6:33. <> (Isaiah 55:7) Jehovah would take care of their needs, both physical and spiritual.—Matthew 6:33. | would
  9. Idan muka tuna albarkar da Naomi ta samu hakan zai taimaka mana mu dogara ga Jehobah <> Remembering how matters turned out for Naomi will help us to trust in Jehovah | will
  10. 3 Duk da haka, Yesu ya tabbatar wa mabiyansa cewa ruhu mai tsarki zai kasance tare da su wajen yin aikin da ya ba su. <> 3 Nevertheless, Jesus assured his followers that holy spirit would be with them in carrying out the work that he had given to them. | would
  11. 7 Dukan wanda bai dogara ba ƙwarai ga Jehobah zai yi tunani dabam. <> 7 Anyone who does not trust firmly in Jehovah might think differently. | might
  12. A shekara ta 1959, ofishin reshe ya gayyaci kowa da zai iya ya ƙaura zuwa lardin Quebec, inda ake bukatar masu hidima sosai. <> In 1959 the branch office invited any who could do so to move to Quebec, where there was a great need for evangelizers. | could
  13. 7 Kasancewa masu neman salama zai zama da wuya musamman idan muna jin wani ɗan’uwa mai bi ya ɓata mana rai. <> 7 Being peaceable can be a challenge when we feel that we have been unjustly treated by a fellow believer. | can
  14. Don mu ƙara nuna godiya ga Jehobah kuma mu ƙarfafa begenmu na tashin matattu, bari mu bincika abin da ya sa za a yi tashin matattu da kuma yadda wannan zai shafe mu ɗaiɗai. <> To deepen our appreciation for Jehovah and to strengthen our hope in the resurrection, let us consider why the resurrection will occur and how this should affect us personally. | affect
  15. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Saboda haka, dukan abin da muka lura da su game da wannan Mulkin da abin da yake yi, zai jawo mu kusa kusa da Jehovah kansa. <> (Revelation 11:15) So everything that we observe about this Kingdom and what it accomplishes can draw us closer to Jehovah himself. | can
  16. Ba zai taɓa manta da mu ba idan muna da aminci a gare shi. <> He will never forget us if we are faithful to him. | He will
  17. Ta yaya za mu tabbata cewa muna shirye don abin da zai faru a nan gaba? <> How can we make sure that we are ready for what is coming in the near future? | coming
  18. Akwai Wanda Zai Iya Sanin Gobe? <> Can Anyone See the Future? | Can
  19. 3 Idan muka yi tunani a kan yadda aikinmu na wa’azi zai ceci rayukan mutane hakan zai sa mu ga cewa muna bukatar mu yi wa wa’azi da gaggawa. <> 3 When you consider what stands to be gained or lost as a result of our preaching, you probably feel an urgent need to speak to others about the good news. | result
  20. Ka tuna da Musa, wanda surukinsa ya ba shi shawarar yadda zai bi da aikinsa mai girma. <> Consider Moses, whose father-in-law gave him counsel on how to handle his heavy work load. | to
  21. Ka tambayi ɗanka shawarar da zai ba ka a ce kai ne ɗansa. <> Ask your teen what advice he would give you if you were his child. | he would
  22. 7:25) Da akwai darassi da za mu koya a nan: Idan muna son ruhun Allah ya yi mana ja-gora, muna bukatar mu guji saka kanmu cikin yanayi da zai sa mu cikin jarraba. <> 7:25) There is a lesson for us: If we want God’s spirit to lead us, we need to avoid placing ourselves in the path of temptation.
  23. Ta yaya yin wa’azin bishara zai amfane ka da kuma wasu? <> How has sharing in preaching the good news benefited both you and others? | the
  24. Ruhu mai tsarki na Allah hatimi ne a lokacin da kuma a yanzu don “abin da zai yi nan gaba” ga shafaffu masu aminci. <> God’s holy spirit was and still is a seal, or an advance “token of what is to come” for anointed integrity keepers. | to
  25. Me ya sa da irin wannan bambancin, kuma ta yaya hakan zai shafi shawararmu? <> Why are there such differences, and how should they affect our decisions? | affect