zurfi

From HausaDictionary.com | Hausa English Translation, Dictionary, Translator
Jump to: navigation, search

m

 1. depth, deepness <> tsawo musamman na rami daga doron ƙasa zuwa ciki.

Derived Terms

See also zurufi

Glosbe's example sentences of zurfi

 1. zurfi. <> asleep, deep intensity, deep spiritual, deep, deeper into, deeper, deepest, depth, intense.
  1. Farisawan sun yi imani da cewa matalauta, wadanda ba su yi zurfi a Doka ba, “la’anannu ne.” <> The Pharisees held that lowly people, who were not versed in the Law, were “accursed.”
  2. Bada jimawa ba bayan sun tashi, Yesu ya kwanta a bayan jirgin kuma barci mai zurfi ya ɗauke shi. <> Shortly after they shoved off, Jesus lay down in the back of the boat and fell fast asleep.
  3. Waɗannan aukuwa biyun, inda iyaye suka yi hasarar yara fa, ya misalta misalin zurfi da kuma daɗewar baƙincikin idan wani yaro ya mutu. <> These two experiences, where parents lost children, illustrate how deep and lasting the wound is when a child dies.
  4. A kwanan bayan nan ya ce: “Cikin shekaru tara da suka shige tun nazarina na farko cikin Littafi Mai Tsarki, dangantakata da Jehovah ta yi zurfi. <> He recently said: “In the nine years that have passed since my first Bible study, my relationship with Jehovah has grown.
  5. Matar ta ce: ‘Malam ba ka ma da abin ɗiba ruwa kuma ga shi rijiya tana da zurfi. <> ‘Sir,’ the woman says, ‘the well is deep, and you don’t even have a bucket.
  6. Akwai itatuwa a ƙasar amma suna a ware, kuma akwai kwari masu zurfi. <> The region consisted mostly of high, sparsely wooded tablelands cut through by deep ravines.
  7. Ta bakin annabi Zephaniah, Jehobah ya ce: “Wannan rana ranar hasala ce, ranar wahala da ƙunci, ranar kaɗaici da risɓewa, ranar duhu da gama gira, ranar hadura masu-zurfi da duhu baƙi ƙirin.” <> Through the prophet Zephaniah, Jehovah answers: “That day is a day of fury, a day of distress and of anguish, a day of storm and of desolation, a day of darkness and of gloominess, a day of clouds and of thick gloom.”
  8. Sau da yawa sai mun biɗi abubuwan da muke sha’awa ne za mu yi bincike mai zurfi sosai. <> It is often when we pursue matters that intrigue us that we delve the deepest.
  9. Domin sun guji “abinci mai ƙarfi” ko kuma koyarwa mai zurfi. <> Because they avoided “solid food.”
  10. Wannan labarin na cike da motsin zuciya mai zurfi. <> The gripping drama is packed with human emotions expressed with deep intensity.
  11. Gama na kawar da shakka, ba mutuwa, ba rai, ba mala’iku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amura na zuwa, ba ikoki, ba tsawo, ba zurfi, ba kuwa wani halittaccen abu, da za ya iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” <> For I am convinced that neither death nor life nor angels nor governments nor things now here nor things to come nor powers nor height nor depth nor any other creation will be able to separate us from God’s love that is in Christ Jesus our Lord.”
  12. Mai yiwuwa ne cewa wannan matar da ta tuba kuma mai godiya tana cikinsu, ta soma rayuwa da ke faranta wa Allah rai da lamiri mai tsabta, sabon fahimi game da ƙuduri, da ƙauna mai zurfi ga Allah.—Luka 8:1-3. <> The possibility cannot be ruled out that this repentant and appreciative woman was now among them, embarking upon a godly way of life with a clean conscience, a renewed sense of purpose, and a much deeper love for God.—Luke 8:1-3.
  13. Amma ƙauna mai zurfi ga gaskiya ta motsa wasu miliyoyi, a dukan ƙasashe su biɗi Allah na gaskiya. <> But intense love for truth has impelled millions of others, in all lands, to search for the true God.
  14. 4. Me ya sa Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi? <> Why did God make Adam fall into a deep sleep?
  15. Ya kamata mu kawo tunani mai zurfi daga zukatanmu don mu yi bimbini a kansu. <> We should muse over deep spiritual thoughts, become absorbed in them, and meditate on them.
  16. 17 Babban kifin nan dolpin yana iya tsalle daga sama zuwa daben ruwa da zurfinsa ya kai ƙafa 150, amma tsalle mafi zurfi da ya taba yi da aka rubuta shi ne na ƙafa 1,795! <> 17 The bottle-nosed dolphin normally dives to depths of 150 feet [45 m], but the deepest recorded dive for a dolphin is 1,795 feet [547 m]!
  17. (Luka 3:21, 22) Saboda haka lokacin da Yesu ya fara hidimarsa, ya yi hakan da sani, fahimi, da kuma juyayi mai zurfi da babu wani mutum da ya taɓa kasance da shi. <> (Luke 3:21, 22) So when Jesus embarked on his ministry, it was with knowledge, insight, and depth of feeling that no other man could have had.
  18. Kowannenmu yana iya ƙoƙarinsa a kai a kai don ya samu sani mai zurfi kuwa?—Mis. <> Are we individually putting forth constant effort to gain a deeper knowledge?—Prov.
  19. Ku tuna, “shawara a cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai-zurfi: amma mutum mai-fahimi za ya jawo ta.” <> Remember, “counsel in the heart of a man is as deep waters, but the man of discernment is one that will draw it up.”
  20. Yoh. 16:14) Ta wajen yin amfani da fasahar magana, manzo Mikah ya rubuta: “Duwatsu kuma za su narke . . . kwaruruka kuma za su tsagu, kamar kakin zuma a gaban wuta, kamar ruwa da an zubar da shi a magangari mai-zurfi.” <> 16:14) In vivid figures of speech, the prophet Micah wrote: “The mountains must melt . . . , and the low plains themselves will split apart, like wax because of the fire, like waters being poured down a steep place.”
  21. (Mai-Wa’azi 9:5, 10; Yohanna 11:11-14) Da haka, ba ma bukatar mu damu game da abin da zai faru da mu bayan mun mutu, yadda ba ma damuwa yayin da mun ga mutum yana barci mai zurfi. <> (Ecclesiastes 9:5, 10; John 11:11-14) Thus, we need not worry about what happens to us after death, any more than we worry when we see someone sleeping soundly.
  22. Sa’ad da kake barci mai zurfi, ka san abin da yake faruwa ne?— Kuma sa’ad da ka farka, ba za ka san ko barcin awa nawa ka yi ba sai ka duba agogo. <> When you are in a very deep sleep, you do not know what is going on around you, do you?— And when you wake up, you do not know how long you have been sleeping until you look at a clock.
  23. 4 Kalmar Ibrananci da aka fassara ta “ƙauna ta alheri” tana da ma’ana mai zurfi fiye da kalmar nan “aminci.” <> 4 The Hebrew word rendered “loving-kindness” is also more encompassing than the word “loyalty.”
  24. 4 Nazari yana gamsarwa sa’ad da muka yi amfani da abubuwan taimako dabam dabam na Littafi Mai Tsarki domin mu tona da zurfi cikin wani batu, musamman sa’ad da muka yi haka domin mu amsa tambayar wani. <> 4 Personal study is satisfying when we use various Bible aids in order to dig deeper into a subject, especially when we do so to answer someone’s sincere questions.
  25. A nan ne ya yi barci mai zurfi. <> There, he went fast asleep.

[17-08-11 15:16:05:198 EDT]