ɓacin rai
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
- upset, greif, sadness, displeasure, frustration
- mai bacin rai <> one who's displeased
Glosbe's example sentences of ɓacin rai
- ɓacin rai. <> bitter, bitterness, despair, disappointment, disappointments, emotional feelings, heartache, hurt, disappointments.
- Muna fuskantar wahaloli da kuma ɓacin rai saboda dalilai uku. <> Difficulties and distress come our way for three main reasons.
- ƁACIN RAI. <> DISILLUSIONMENT.
- Damuwa da aka furta cikin tawali’u yana rage ɓacin rai. <> Concerns and worries expressed with mildness defuse tensions.
- (1 Korinthiyawa 1:11, 12) Barnes ya ce: “Kalmar nan da aka yi amfani da ita a nan [domin tsawon jimrewa] gaba take da garaje: cika da fushi da tunani, da kuma ɓacin rai. <> (1 Corinthians 1:11, 12) Barnes points out: “The word here used [for long-suffering] is opposed to haste: to passionate expressions and thoughts, and to irritability.
- Mephibosheth da gaske ya kafa misali mafi kyau na jimre wa naƙasa, tsegumi, da ɓacin rai.—2 Samu’ila 19:24-30. <> Mephibosheth truly set a sterling example by enduring disability, slander, and disappointment.—2 Samuel 19:24-30.
- Jimiri yana sa mu kahu a lokacin da mun fuskanci ɓacin rai ko wahala. <> Endurance enables us to stand firm in the face of disappointments or hardships.
- Hadayunsu ma abin ɓacin rai ne ga Jehobah Allah. <> Their sacrifices were offensive to Jehovah God.
- Mutumin da yake yin rashin hankali yana abubuwa a hanyar da ba ta dace ba ko kuma mai kawo ɓacin rai. <> A person who behaves indecently acts in an unseemly or offensive manner.
- Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Hannatu ta yi “ɓacin rai” domin ba ta haihu ba. <> The Bible tells us that Hannah was “bitter of soul” because of her childless state.
- Domin Allah ya dubi Habila da idon rahama da kuma hadayarsa, wannan ta jawo ɓacin rai ga Kayinu. <> God’s benevolent view of faithful Abel and his sacrifice prompted an adverse reaction on the part of Cain.
- A’a, hawayen da Allah zai share, hawaye ne da wahala, baƙin ciki, cin mutunci, ɓacin rai, da kuma azaba suke kawowa. <> No, the tears that God will wipe out are tears caused by suffering, grief, disappointment, hurt, and agony.
- Wahala da ya sha ba ta sa ya yi ɓacin rai ba; ko kuma ta hana shi gyara hanyar rayuwarsa ta jitu da sabon mazauninsa ba. <> The adversities that he had suffered did not leave him bitter; nor did they prevent him from learning to adjust his life-style to his new surroundings.
- Amma, wasu abubuwa kamar ɓacin rai ko rashin lafiya ko rashin kuɗi ko kuma rashin sakamako masu kyau a wa’azi, za su iya sa mu ɗauka cewa Jehobah ba ya ƙaunarmu kuma. <> It is easy to become discouraged if this need is not satisfied because of unexpected events or disappointments, loss of health, financial setbacks, or a lack of success in the ministry.
- 19 Munanan abubuwa da suka shaida na iya sa wasu su ji cewa nuna ƙauna zai kai ga ɓacin rai kawai. <> 19 Unpleasant experiences may have left some with the feeling that showing tender affection would lead only to further disappointment.
- Kamar Margarita da kuma Jane, wataƙila ke ma kina fama da ɓacin rai, matsalar kuɗi, da kuma fama a ruhaniya don maigidanki ya ci amanar ki. <> Like Margarita and Jane, you may be suffering emotional, financial, and spiritual distress because your husband has betrayed you.
- Abin ɓacin rai ne idan aka nuna rashin godiya ga wani abin kirki da aka yi, mafi muni ma, idan aka mance. <> It can hurt deeply when a generous act is taken for granted or, worse yet, completely forgotten.
- Ta hakan za mu fuskanci ɓacin rai da takaici. <> In that case, we are sure to meet with disappointment and frustration.
- A dukan matuƙa fa zaya nuna kulawarsa mai-girma garemu ta wurin zuba albarkatai nasa fiye da wani ɓacin rai da muka taɓa sha a cikin rayuwa a dā. <> Throughout eternity he will show his great care for us by showering down blessings that will far more than make up for any hurt that we received in our past.
- Hanyar watsa labarai na nuna cewa lalata tana kawo farin ciki maimakon ɓacin rai. <> The media constantly portray illicit sex as a source of happiness rather than heartache.
- Idan sun tsufa, dabbobi suna iya ciwo ko kuma naƙasa da zai sa ubangidansu ɓacin rai idan ya tuna lokacin da dabbar take ƙarama. <> In old age, pets may suffer sicknesses and disabilities that can be distressing to their owners, who remember the younger and more active years of these animals.
- 1:2-7) A wata ziyarar da ta kai wuri mai tsarki na Jehobah, Hannatu ta yi “ɓacin rai, ta yi addu’a ga Ubangiji, ta yi kuka kuma da zafi.” <> 1:2-7) During one of her visits to Jehovah’s sanctuary, Hannah became “bitter of soul, and she began to pray to Jehovah and to weep greatly.”
- Abin baƙin ciki, irin waɗannan matsalolin suna iya jawo ɓacin rai, da kuma hasarar ruhaniya. <> Sadly, such problems can result in heartache, bitterness, and even loss of spirituality.
- Tunani da ayuka masu ginawa da zasu zama halayen mutane duka fa da sannu sannu zasu kawas da tuni masu ɓacin rai nan. <> The upbuilding thoughts and activities that will be the everyday life of people will gradually erase the painful memories.
- A waɗanne hanyoyi ne Bulus ya nuna cewa shi ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne duk da cewa ya nuna ɓacin rai a wasu lokatai? <> In what ways did Paul show that he was flexible in spite of his strong feelings at times?
- Hakan zai iya sa mutane a zamaninmu mamaki, amma Yahudawa suna yin hakan ne domin su nuna cewa suna baƙin ciki ko makoki ko kuma ɓacin rai. <> Such an action may seem strange to modern-day readers, yet among the Jews it was an expression of strong emotion caused by despair, grief, humiliation, indignation, or mourning.
[17-08-16 07:23:41:076 EDT]